Sashe 10
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Na* dubi garejin makarantar mu dake d’auke da wasu watsalallun rubutu da bansan me suke nufi ba. Gaba na ya yanke ya fadi. Banason bokon nan amma ya zanyi? Cikar buri na da farin cikin Baffa na shine ya sanya na yanke zuciar zuwa makarantar. Shaf na mance ban dakko takardar shedar kai dan makarantar bane. Na manto ta a gida. Bakwa mantawa ba gani nake ba amfanin da za tai. Domin dazu na gutsiri ‘kasan ta ma na kwakwulo dattin kunne na. Fankan fankan na shiga cikin makarantar ina bin dandazon dalibai da kallo, Suma yawancin su ni suke kalla, Menene suke kallo na haka tamkar basu san Dijen Baffan ta ba? Murgud’a baki nayi na dankara musu harara, Cikin haka sai ga Siyama k’awata taci ado cikin kaya irin na sauran daliban. Ja na tayi gefe tana raba idanuwa,
“Dijengala mai kike anan? Ko waje na kiki zo? Ki bari a..”
“Dalla yi min shiru. Wajen ki? Saboda me zan zo wajen ki? Nan ashe Nana ta hada partyn sunan gidan su an gayyaci kowa kunje kunci dadi shine ba wanda ya gaya min, Taron munafukai.”
Siyama zata rike min hannu na wafce ina tsirtar da yawu a gefe,
“Banzariya kawai. Ai in gaya miki kawaye zan sake, Kuma sai nabi kowannen ku nayi ‘kuli-kulin kubra da ku.”
“Kai su waye anan... Wacece wannan siyama ce?”
Oh nagane shi shegen malamin nan ne mai gashin hab’a irin na bunsurun Gajiyalle. Tahowa yake wajen mu yana cilla bulalar sa sama. Bazan taba mantawa da karfen d’aya saukarwa kai na ciwon sati ba. Na masa tofin Allah tsine yafi dubu. Na wulkita idanu na sama na zabga masa harara. K’arasowa yai wajen mu yana kallon Siyama kafin ya mai da duban sa kai na,
“Na kore ku yafi a kirga, Nace banda talla, Banda talla. Yan talla su dena zuwa da safe sai lokacin break yayi. Kina jina? Ko kuwa kunnen k’ashi ne da ke?”
Daga hannu nai zai zabga min bulala naja baya ina binsa da kallon ya haka?
“Ha’ah magana kake ko zubar gudawa? Uhm.”
“Ke da wa kike? Siyama ke kika kawo mana wannan marar kunyar?”
Siyama tai saurin girgiza kai tana ja baya. Sauran yan makarantar suka yo kanmu suna kallon mu. Naja dankwalin kai na nai damara dashi na dira agaban sa,
“Dan kaji nima nan daliba ce kamar kowa, Banyi niyyar fara zuwa makarantar bane sai yau. Kuma ni ba marar kunya bace ehe..”
Ya-yo kai na zai make ni wata malama ta dakatar dashi,
“Haba Malam Auwal meye haka?”
“Malama Mardiyya ki bari na zazzabga mata mari, Irin marasa kunyar yarannanne, Kangararru wanda basajin maganar iyayen su. Bakya jin me take cewa. Wannan k’aramar yarinyar ni zata gayawa magana.?”
Ya karasa fada yana kwafa. Malama Mardiyya ta riko hannu na tana janyo ni kusa da ita. Hannun ta laushi ba irin nawa ba duk yayi kanta ya daddauje. Bata kyamata ta ta janyo ni jikin ta? Kallo na tayi kafin tace,
“Kanwata makarantar nan kikazo koyan karatu ko kuwa wani abun ne daban ya kawo ki?”
Saurin girgiza kai nayi,
“Karatu nazo koya, Nima d’aliba ce kamar kowa, Kawai dai ban fara zuwa da wuri bane sai yau.”
Malama Mardiyya ta ka’da kai kafin tace,
“Toh ina uniform dinki?”
Zare idanu nayi jin abunda ta fada da bansan ko menene ba, Matsawa nai ina raba idanuwa,
“Inifan? Meye shi Malama?”
Sauran yara suka sa daria, Na juya na zabga musu harara, Domin sun san hali na sarai yanzun sai na hada gagarumin fa’dan da sai mai gari jamilu yayi shari’a.
Malama Mardiyya tayi murmushin da kyakkyawan hakorin makkan ta ya bayyana, Inaga irin dan nera goman nanne da Yusha’u ke sawowa a birni ya sassaidawa mutan garin mu.
“U-ni-form ake cewa kinji kanwata? Yana nufin kayan makaranta iri d’aya da sauran yara suka sa kinji? Ya sunan ki ne?”
“Yu-nun-fan!”
Na fada a hankali ina dashe baki kafin na sake cewa,
“Sunana da yawa, Baba na na kira na da Ummi na, Saboda kasancewar sunan mahaifiyar sa da naci. Matar baba na na kira na da Dije itada wasu tsirarrun mutane a karkarar nan, Mafi yawancin yan karkarar nan na kira na da Dijengala ko Ta mai gari. Kawaye na da matasan karkarar nan na min laqabi da Dije Oganniya...”
Na karasa fada ina dashe baki. Malama Mardiyya da sauran mutane suka kada kai, Gaba d’aya sun zubamin ido. To ni Meye nawa tunda Sunana ta tambaya kuma du sunaye na ne. Malama Mardiyya tace,
“Dakyau! Kenan sunan ki Khadija?”
Na daga kai alamun Eh!
“Wow nice name! Toh Ina takardar shedar ke yar makarantar nan ce?”
‘Anzo wajen’ Na fada a hankali ina nannada d’ankwalin kai na.
“Iya gida yasin, au wai so ake yi?”
Gyada kai tayi! Na kwasa aguje ban ce komai ba na tafi gida na dakko. Ina tafiya ina waiwayen su, Na hango Malam auwal din ya matsa kusa da Malama Mardiyya suna magana.
“Dan bakin ciki hede ya mutu, Ba fasawa karatu ne dai he anyi, Me kayin giginya kawai.”
Da gudu na shige gida ina haki, Gajiyalle na tsakar gidan mu tana dama kunu.
“Yan bokoko! Mu dai babu ruwan mu idan aka dakko abun kunya.”
Sam bangane me take nufi na da dakko abun kunya ba. Nidai nai shigewa ta dakin Baffa. Akan taga na gano takardar inda na dora ta dazu. Dauka nayi da gudu zan fice sai kuma na dawo na tsugunna a kusa da Gajiyalle Ina lashe lebe,
“Dan sanmun kunun.”
Harara ta dankaramin tana janye bokitin kunun daga kusa dani,
“Matsa kafin na hanbare ki. Dan uban ki ubanki ne ya sayo da Za’a baki? Ba dai kin dena tallen ba.? Bazan baki ba ko zaki mutu.”
K’wafa nayi na mike ina jujjuya idanu na,
“A hayye! Dijengala ta mai gari, Ba auren talaka ba, Talaka mai sara da sassake. Gajiyalle ki bani kar na auri chiyamin din birni ginin bulo. Ki ciji yatsa.”
“A mafarki? Nace a mafarki? Wane shashashan ne zai aure ki? Zaki matsa daga kai na ko sai na lakada miki na jaki?”
Tabe baki nayi, Na fice aguje na koma makaranta. Ina zuwa na tarar an tara yan makarantar ana koya musu wani abu kamar waka an jera su a layi. Malama Mardiyya ta yafito ni tace na tsaya a bayan Adaman liman.
“Assembly ake yi..”
“Assambuli? Me kenan da hausa Malama?”
“Kowa da kika gani a jere, Kowa ajujuwan su daban. Kema a bayan yan ajin ku kike, Wasun su sun iya Abun da ake fada mai taken ‘National anthem’ Taken najeriya kenan. Yana da matuk’ar muhimmanci.”
Nifa gaba d’aya ba gane abunda take cewa nake ba, Gashi bana shiru na cuci kai na akan abunda ban gane ba. Na dube ta ahankali nace,
“Malama yasin bangane duk abunda kike fada ba”
“Babu damuwa Khadija.. Idan an tashi break kizo na miki bayani. Yanzu dai ina takardar?”
Mika mata nayi, a cukurkude tayi dik’in-di’kin da dau’dar kunne na dana sassakato, Malama Mardiyya ta zare idanu tana bin takardar da kallo,
“Khadija ya haka? Me kika goge da ita tayi datti haka?”
Kunya ta mamaye ni, Na sunkuyar da kai na kasa. A hankali nace,
“Yasin kunne na na gogo. Da da gashin kaza nake yi. Toh mugun kansilar garin nan yasa an yahe hyarar kududdufin baki d’aya wai tuk’a tuk’a (borehole) Za’ai awajen.”
Malama Mardiyya ta kada kai, Kafin ta karba ta mikar da ita. Komawa tayi gaban makarantar tana bin mu dalibai da kallo,
“Yan makaranta nace muku a dinga tsafta. Satin sama zamu fara duban tsafta, a turance ana cewa ‘censorship day’ . Dole ne ku kara kai mi wajen tsaftace jikin ku da kayan ku dama kayan karatun ku. Mata a dinga wanka ana wanke kai, A kuma yanke farata na hannu dana kafa, Kuma dole ayi kitso, Dik bayan sati biyu za’ai sabon kitso. Kuna jina?”
Da k’arfi kowa yace,
“Eh..”
Na dubi kai na tun daga sama har kasa, Sanye nake cikin wata yarkacacciyar koriyar hyadda (shadda) da na manta sanda Baffa ya dinka mun, Doguwa ce har kasa amma Saboda tsabar tamin kadan yanzu, Ta dangale ta dawo gaba da gwiwata kadan, Zif (zipper) din ya cire, Kafata babu takauni (takalmi) farata na na hannu dana kafa duk sun yi zako-zako abun tsoro ga uban datti aciki. Gahin kai na kuwa na mance yauhe rabon dana wanke hi balle kitse hi. Ni kadai tashin wari nake yi, Rabon da nai wankan sabulu tun wanda Dara’ifa tace na siya shima ya kare sauran sa Gajiyalle ta kwace hi. Ashe na zurfafa tunani bansan an kammala assambulin ba. Kowa ya watse. Malama Mardiyya ta kira Sunana da karfi tana bubbuga yatsun hannunta biyu a kofar kunne na,
“Khadija..”
“Na’am Malama..”
“Tunanin me kike yi ne? Kinga dai barshi kije aji yanzu. An jima da break kizo ki same ni.”
“Burek? Malama meye shi.”
“Lokacin cin abinci da wasa da ake baku Idan an kada kararrawa ta uku..”
“Kan balastin can. Harda hi? Harda lokacin wasa? Wayyo ni Dije ba karamin hirme nayi ba da banzo tun sanda aka fara karatun nan ba.”
Malama Mardiyya tayi daria kafin ta nunomin dan banzan Malam auwal dinnan,
“Je ki ga malamin class din. Au ajin ku can. Ki bishi zai kai ki ajin ku. Allah ya bada sa’a Khadija. Banda tsokana da fada kinji? Da anyi break kice staffroom Za’a nuna miki. Kinma ganshi can? Shine dakin malamai.”
Har ga Allah banso ajin Malam auwal Za’a kai ni ba. Domin tun had’uwar farko ni da hi jinin mu bai hadu ba. Ya tsane ni nima na tsane hi. Tsana mai tsanani ma kuwa.
“Malama nafuson ajin ki dan Allah!”
“Ni ajina yan kanana ne Khadija. Ki dai bishi kinji? Malam auwal nada kirki sosai, Ya nasan daliban sa suyi karatu. Amma bayasan wasa ba kuma ya shiri da masu wasa ko fada a aji kina jina?”