Sashe 64
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar an tsunkule ni haka na zabura na tashi, toilet na shiga nai wanka tare da dauro alwala na fito. Sai da na fara yin sallar isha nayi shafa'i dama wuturi sai cikin dare nake yi, kawai na bude wardrobe ina bin kayan ciki da kallo, zuciya ta na gaya min cewa ya kamata na saka kayan da zasu ruda shi. Wata kuma na gaya min idan ma sun ruda shi ai zai dauka Shaheedah ce, zai yi miki abin da ya taba yi kwanaki, kawai kisa hijabi ma yadda ba zai taba ganin wani abun ba bare ya yi sha'awa tunda daman ba san shi kike yi ba. Kar ki sa kuma wanda zai rai naki, kije garin nuna rashin so ya kuma ci miki mutunci tunda dai baki san manufar da tasa shi ya auro ki ba. Naji wata zuciyar itama ta ayyana min hakan.
“Oh God...!”
Na fada ina dafe saman gushi na. Toh ni yanzu ya zan yi? Mene ne mafita a gare ni yanzu? Duk na rasa ya zanyi ina ta tunani kawai sai idanuna suka sauka kan wani lace pink da ratsin milk color a jiki, na zaro shi naga dinkin riga da skirt ne, na sanya shi a jikina ya kuwa zauna yai das dashi. Alkyabba na dakko na sanya sannan na nufi gurin madubi na gyara fuska ta, duk da ba kwalliya nai ba, nayi kyau ba laifi, nasa janbaki shima pink daga nan na fara tunanin ta ya zan je sashen nashi?.
Adda Maryama na kira dan gabaki d'aya na rasa mafita, tace nasa a kirawo Jakadiya tai min iso a gurin shi. Ta kuma cewa.
“Kin san menene Gimbiyar mu?”
“A'a sai kin fada Adda.”
“Yauwa idan tafiya tai tafiya ki samu duk yadda za ai ki dawo da sauran jakadun guda biyu. Dama uku ne toh sai suka sauke biyun, yanzu kisan yadda zaki wajan ganin sauran sun dawo dan basu kai wannan hada makirci ba, kinga idan suka dawo zaki samu saukin yin wani abu koda waccen bata kusa.”
Kamar tana gabana haka na dinga gyada kai, kafin daga bisani nace.
“Toh shikenan Adda zan kokarta, na gode.”
Daga nan muka ajiye wayar, na mike na fito parlor na samu hadimai na suna ta goge-goge, na aiki guda d'aya cewar taje ta nemo min Jakadiya. Ashe tana can gurin su Gimbiya Jaleela ana ta kulle-kulle kamar an ce dasu duniyar ba zata tashi ba, ko kuma sun dauka cewar za'a barsu har su gama cin duniyar su da tsinka. Bayan tazo ne na sanar da ita bukata ta, cikin tsantsar ladabi ta amsa min tare da tashi ta tafi dan yi min iso. Kin bin ta da man nai saboda koda yake a'a bazan ganshi ba, bazan ji kunya ba, akan na bi bayan ta na dawo da borin kunya.
Kamar an jeho ta daga sama haka ta shigo cikin parlorn, ta ce Waziri yace zan iya zuwa. Na tashi bayi ba suka rufa min baya, ina tafiya suna biye daji duk sai naji wani iri, kamar wata marar gaskiya da za'a raka prison. Na tsaya na kallesu cike da kulawa nace su tsaya a nan naje na dawo, dan har ga Allah bana son wannan bibiyar da suke yi mun. Babu yadda suka iya dole suka bi umarni na, ni kuma da Jakadiya muka nufi sashen sarki Salam.
Muna zuwa muka tarar da su Waziri da su Shamaki su Galadima sun fito, na duka na gaishe su cike da ladabi, wasu sun amsa ya yin da wasu banji sun bude koda baki ba duk da ban san su ba kuma ban kalle su ba ballantana na gane fuskokin su saboda kai na yana kasa. Sai da suka wuce sannan na mike tsaye tare da juyawa na bisu da kallo har suka fice. Kasan cewar nasan inda yake a kwance yasa na kalli Jakadiya tare da yi mata godiya, na dai nuna mata tsananina da ita iya nan ne bana son ta bini ciki dan naga take-taken ta na son bi na ciki.
Na tsaya a bakin kofar bedroom d'in na zaro jarkar dana boye mai dauke da ruwan magarya, nai addu'a sosai kafin na sanya kafata baki na dauke da sallama. Babu kowa sai shi kadai a kishingiɗe kan gado, be kallo bakin kofar ba bare na saka ran zai amsa min sallamar da nayi. Haushi ya kamani, sai kace wani kurma, a zaune yake ido biyu amman saboda mulki yana ji ana sallama ba zai amsawa mutane ba, naja tsaki a cikin rai na ina karasawa gurin shi cikin taku na isa da kasa ita. Lumshe ido naga ta yi yana dan daga fuskar sa, da alama kamshin turaran wutar da ke jikin kayana yake shaka, duk da cewar be nuna ba.
Kallansa nai na sakar masa harara a zuciya ta nace 'kaji dashi ni ba bata min rai zakai ba' kawai ma sai na shiga neman burner bayan na ciro garin maganin da zan yi masa hayaki amman ban samu ba. Shi kuma har lokacin be bude idanunsa ba, nai ta dube-dube har Allah ya taimaka na ganta a can wani guri aka ajiye ta na musamman da ba zaka taba zaton ita bace. Na zuba su garin habbatussauda din nan dakin ya fara canzawa daga kamshin da yake yi ya koma kauri, dalilin da yasa Salman saurin bude ido yana toshe hanci. Na kalle shi naga sai faman yatsina fuska yake da alamar kamshin be yi masa ba.
“Ke! Mene haka?”
Yayi maganar a dan rude. Na sake zuba garin hayaki ya kuma turnukewa ina cewa.
“Magani ne.”
“Bana so please fitar min dashi.”
Ai kamar ya sake zuga ni sai na kara karawa, ya kuwa shiga yin tari da atishawa ba kakkauwa, still kuma hancin sa yana toshe da tafin hannunsa, na ce.
“Shi magani ai ba dan so ake yin sa ba.”
“Please bana son wannan warin, ki fita da shi nace.”
Nai masa banza, na karasa bedside d'in sa na dauki glass cup na zuba masa ruwan addu'ar nan, na dan matsa kusa dashi tare da mika masa ina cewa.
“Karbi kasha.”
Kai tsaye yace dani.
“Bana sha.”
“Karka ce haka idan ba haka ba zan je na sanarwa da Ammi.”
Kalmar Ammi da na fada ne yasa shi saurin dagowa ya kalle ni karan farko tun shigowa ta dakin. Bakin sa na rawa yake son yin magana amman ya kasa, cikin ransa kuwa tunani yake a ina ma yasan wannan sunan? Babu shakka ya taba jin wannan sunan har ma yana tunanin ya taba alaka da mai irin sunan amman kuma ya kasa tuna a ina ne, yaushe ne kuma wacece hakan. Gabaki d'aya ya saka hannunsa ya dafe kansa yana wani irin cije baki kamar irin wanda ya ke kukan shiga uku nan.
“Karbi kasha dan Allah.” Na fada ina mika masa kofin.
Sai kawai ya kalli kofin amman be karba ba ya tsaya kamar wani me tunanin wani abun. Ganin haka yasa na daure na zauna kusa dashi tare da jan munfashi na sauke, hannunsa da ya dora a kansa na janyo tare da kokarin sanya idanuna cikin nasa amman yaki bari hakan ta faru, na ce.
“Ashe haka kake? A waje idan kana yawo tamkar wani sarki mai cikakken iko. Amman a cikin masarautar ka sai ka zama tamkar wani lagwani wanda sai yadda aka sarrafa shi why? Naji tarihin yadda mahaifinka ya gudanar da mulkinsa, cikin isa da iko, amman kai sai yadda akai da kai me yasa?”
“Nima ban sani ba.” Ya fada cikin sauri.
“Naji toh karbi kasha wannan zaka ji dadin jiki da zuciyar ka.”
Na fada tare da kai kofin sai tin bakinsa, amman ya kawar da kai alamar ba zai sha ba. 'yau na ga taurin kai' na fada a rai na. Wai duk dan saboda ya sha, sai na sake matsawa kusa dashi har jiki na yana gogar nashi, na kwanto da kansa saman kirji na ina shafa lallausan gashin kansa, murya kasa-kasa na fara masa magana cikin taushin harshe.
“Kayi hakuri komai lokaci ne kuma jarabawa ce daga Ubangiji, daure kasha wannan magani ne da aka yi shi da ayoyin ubangiji na waraka. Kayi bismillahi tare da kyakkyawar niya ka daure kasha kaji sarkin sarakuna...”
Sai ya bude bakin bayan ya rintsa ido na saka mishi ya sha har ya shanye, ya fara kakarin amai na dinga shafa masa bayan shi har Allah ya taimaka be yi aman ba. Ganin yasha yasa na zame jikina na daga nasa, na yalle ni na kawar da kai dan kar ya yi zaton zama nazo yi a gurin shi. Ya yi shiru yana ta tunanin yadda zai tambaye ni wacece Ammin amman bakin sa ya gaza budewa, ya kasa min zan cen har na tashi tsaye na cire alkyabba ta na shiga bathroom ya bini da kallo.
Tsab yake ga wani kamshi da yake tashi mai daɗin gaske, na dakko wani d'an bokiti na fito, yadda na barshi haka na dawo na tarar da shi, sai dai idanunsa yana kan kofin da na gama bashi ruwan maganin nan. Ko me yasa ya kura masa ido oho, ni dai nasan ban yi abin da zai cutar dashi ba, idan na cutar da shi me zai tsinana min? Buri na kawai ya samu lafiya ya gaya min dalilin da yasa shi aure na har ya wofin tar dani tsawon lokaci. Ruwan jarka na dakko tare da nufa inda yake na ce ya taso ya yi alwala ya dena zama babu ita ko a wane irin yanayi yake ciki.
Sam ban yi zaton yana iya mikewa tsaye ba, na dauka yana yin komai a kwance ne ko a zaune. Babu musu kuwa ya dago ina zuba masa yana yi har ya kammala, na dauki ruwan naje na zubar. Bayan na dawo na zo zan dauki alkyabba ta tace daukar ni inda kika ajiye. Na gama kalle-kalle na a dakin ban ganta ba, daga karshe dai na mayar da kai na gare shi sai na ga kamar be san ina ne man abu ba dan ko kula ni be yi ba.
“Ammhh dan Allah riga ta fa, ka ganta ne?”