Sashe 81
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“To naji.. Amma ka koma wajen ka ka zauna.. I..I..Idan aka tsaya akai na jiri nake.”
“Tsayawa nai akan ki...? Na dauka na dan rissina ko? Zo mu sake gwadawa.”
“Nooo.. dan Allah ka bari.”
“Toh naji zo ki zauna..”
Zama nayi, Meyakwan ya zauna awajen sa, Sai ya janyo kujerar ya sake matsowa gab dani, Kafafun mu na gogar na juna.
“Ina jinki...”
Bayani na shiga yi masa muryata sai rawa take, Shi kuma ya zuba tagumi yana kallo na kawai, Har wani lumshe idanu yake ya bude su akai na,
“Na gama...”
“Bravo alaiki Zawjatiii...”
Mik’ewa nai zan tafi ya riko hannu na,
“K’amshi kike yi...Me tafiyar da tunani na.”
Kwace hannu na na shiga yi ahankali ya mike shima ya janyo ni jikin sa, Na shiga janye jiki na ina tirjewa..
“Dan Allah ka bari...”
“Zawjatuk aleaziza .. rayihatuk jamila.. Kinsan me nace..uhm?”
Yana magana yana neman cire dankwalin kai na, Na zame hannun sa dak’yar ina hade rai,
“Nace.. Dear wife! You smell nice.”
Shiru nai kawai nide ina sauraron sa, Ya hanani tafiya gashi duk na karar da k’arfi na.
“Khadijaaa... Dan Allah kiyi hak’uri.. Ki dena fushi dani. Kinji? Love.. pls.”
Yau da ace wanda nakeso ne kalaman nan suke fita daga bakin sa da nafu kowacce mace jin dadi. Amma kash, Sam bana jin sa a rai na.
“Zan tafi.. Bacci nake ji.”
“Shikenan.. Sai da safe.”
Har na kai bakin kofa na juya tunawa da maganar Ammi..
“Kaci abinci kuwa..?”
Da sauri ya girgiza kansa alamar a’ah.
“Meyasa baka cin abinci ne? kamar wani k’aramin yaro.”
Murmushi kawai yayi yana kallo na,
“Yanzu me kakeson ci?A dama maka oat? Ko porridge? Ko akwai abunda kakeso?”
Gyada kai yayi, Na zauna akan hannun kujera ina binsa da kallo,
“Me kakeso to...?”
“Ke... Ke nakeso Khadija.. You are all I want.”
Kikkifta idanu na shiga yi, Gashi a haka sam ba zaka ce daga bakinsa maganganun nan suke fita ba. Hade rai na d’anyi Ina matsa yatsun hannu na,
“Abinci nake magana.”
“Nima shi nake fada ai... Ko baki gane magana na ba.”
Mik’ewa nai kawai na shiga kitchen, Babu abunda babu, Don haka na hada masa shayi me kauri na kawo masa, Na koma na jima ina aiki kafin na fito da dankalin turawa da kwai sai yar sauce ta kaza.
“Gashi nan bismillah fara ci. Ammi ta damu sosai, Dan Allah ka dinga cin abinci. Kaji?”
“Ni ban iya zama na ci abinci da kai na bane...”
Na gwalalo idanu tunawa da shi din sarki ne sai kuma na mayar da idanun ina tabe baki,
“Saka suke agaba kaci...? Fadawan naka?”
Murmushi yai kawai yana langabar da kai kamar wani karamin yaro...
“Ki bani da kan ki... Saboda Idan kika tashi ma ba iya ci zanyi ba kasa Zan sauka abuna kawai.”
“Kai da cikin naka..?”
Ya gyad’a Kai yana ko’karin tashi, Nai saurin komawa gaban sa ina masa Kallon sama da kasa,
“Toh Ai kuwa dole ka koya cin abinci, Katoto da kai kamar wani baby..”
“To ai babyn ki ne... “
Nide shiru nayi, Naje wajen sink na wanke hannaye na tas, Sannan na dawo na tsugunna agaban sa,
“Toh sakko..”
Sakkowa yai kamar wani yaro yana tankwashe kafafu yadda nayi,
“Bude bakin.... Haaaaa”
Budewa yai ahankali, Na debo dankalin na hada da sauce na cusa masa a bakin, Yana ci yana yanga a haka na gama bashi, Ina hada masa da tea. Lomar karshe ma haka na sa masa abaki ya rike hannun, Yatsuna dana debo dankalin suna cikin bakin sa,
“Sakarmun yatsuna mana...”
Meyakwan ya sakar mun seya shiga lashe su ahankali, Sekace hannu na ne dankalin. Kamar hannun sa haka ya sude su tas yana murmushi. Zanyi magana ya rigani,
“Sunnah ne lashe yatsu idan an gama cinye abinci.”
Ji wani renin hankali wanda ba’atabamun shi ba ko a durbun.
“To ai ba hannun ka bane na wane..”
“Kai da kaya ai mallakar wuya ne. Abincin nan yayi dadi. Gobe ma shi zaki mun.”
Wani kallo nayi masa na debe kwanukan na kai kitchen. Tashi yai shima ya nufi sink yana kuskure bakin sa da mouthwash. Salman ba dai tsafta ba. Komai nashi tsatsaf.
“To ni zan tafi s.....”
Ban karasa ba, Sakamakon bugun kofar sashen sa da aka shiga yi, Hayaniyar su Mama Huwaila ne, Tamkar zasu fasa kofar, Ina jiyo dogarai na basu hak’uri amma sunki denawa. Wani madanni ya danna naga kofar kasan ta bude, Ta window na hango su da yawa sun shigo ciki suna hayaniya. Nasan dai akan dazu ne, Don haka ko ajiki na, Na samu kujera na zauna ina karkada kafafu,
“Wannan hayaniyar tawa ce... Babu ruwanka, Ni da su Munaya ne, Naga zasu tabo ka da Ammi shine fa nima na nuna musu ba tsoro ne dani ba, Na shake wuyan sabeera take ko sabeena...”
Zare idanu yayi, Na sheke da dariya kawai ina jujjuya agogon hannu na,
“Sun kai ni karshe ne.. Oganniya nake ta Gajiyalle mai yar hakiya... Sanyi nayi wallahi.”
Zai yi magana kenan suka banko kofar, Tuni ya sauya fuskar sa izuwa dolo yana jujjuya idanu,
“Mama barkan ku da dare.”
“Dallah gafaracan... Sullutu kawai, k’aramar Yarinya ta tsare ka agaba tana maka dabaru. Dazu dazun nan ta shake wa yaran nan wuya, Ta musu dukan kawo wuka, Kalli jini a dantsen Munaya, Saboda tsabar mugunta taga saura sati d’aya bikinta.”
Kasa jure jin Sharrin su nayi, Na mike ina tafa hannaye,
“Kai Mama H.. Yo badan kin kusa jika dani ba ai da nace Allah ya sakamun.”
“Kai Kai Kai Kai... Ke Kinsan wa kike gayawa haka kuwa?”
Cewar Munaya.
“Dakata ke kuma can daya ... Mama Huwaila ce, Kina wani tashin jijiyoyin wuya ai nasan ba ita ta haife ki ba, ki bari sabeera ‘yarta tayi magana.”
“Ke ni kike gayawa magana..?”
“Ah haba Mama H.. Ni na isa.. Ko sunan ki bakiga na kasa karasa fada ba? Gani nayi duk garin nan waye baisan mai girma chiroma ba, tsatson sarki ismaila rabo, wato jika na farko ga masekiri tajiri.. Allah dai ya Kara miki lapia.”
Ina kallon sanda tayi murmushi tana jin dadi, Kunsan yan sarauta da son girma da kasaita. Ta kasa cewa komai. Gimbiya jaleela taja tsaki tana karasowa kusa dani,
“Akan me... Zaki daga hannun ki ki dora akan fatar yaran nan.. Shin wacece ke? Me kike ji dashi?”
“Haba Mama Jaleelah! Banji dadi ba da kika d’auki wasan mu dasu gaske. Ya za’ai na sa hannu na dake su? Kinji Allah wallahi bandaki kowacce ba. Idan Karya nake dan Allah su rantse da qur’ani gashi nan. Allah ya kara miki lapia, Ai ko dan darajar waziri ba na soma haka ba.”
Shiru Gim. Jaleelah tayi tana kallon su Munaya, Su kuma na tabbatar saboda nace su rantse da qur’ani ne shysa sukai shiru. Kafin Gimbiya Najwa tayi magana na rigata,
“Ranki ya dade barka da dare...Tabbas sai yau na ga ainihin kamar ku da mai girma galadima, Kada na cika ku da surutu, Nadiya yarki naga batada hayaniya ko ita Zata fa’di yadda komai ya kasance. Kuma da zasu fadi gaskia ma.. Su suka takalo komai, Suna cewa ai shaheeda kaza kaza. Gasu idan nayi karya. Amma nasan basu fada muku dai dai bane da da girman ku ba zaku taho nan da daren nan ba, Domin bantaba ganin hakan tafaru ba. Ni zuwa nayi naga jikin sa, Domin kusan kwana nawa ance bayacin abinci, Kuma yana surutai da daddare, Shine nazo yaketa kira na da shaheeda, Tashin da zanyi na tafi kenan kuka shigo.”
Sai kuma suka shiga kallon kallo, A kunyace kowacce ta kwashi jikin ta suka fara fita,
“Munaya... Karki manta a aikomin da kati da dan yawa pls inada gayya.”
Harara ta dankaramin ta fice, Na zube akan kujera ina kwasar dariya.
“Nice moves....Zawjati!”
“Moves ai sai kai... Lalle ka iya acting. “
“Mugayen mutane ne.. Sai kana takatsantsan, Ka samu ka gama komai naka ahankali. Bara na gaya miki komai nasu a takaice.”
Ahankali kuma a nutse ya shiga gayamun irin wahalhalun da yasha a hannun su, Da yadda ya maida kansa soko saboda samawa kansa da mahaifiyar sa lapia. Ajiyar zuciya na sauke bayan ya gama gayamun nace,
“Gaskia na yadda ba Allah a aran su. Domin kaga wahalar danasha kuwa nima? Suka sakarmun da jini na dauka na al’adah ne, Suka sani firgici da daddare na kasa bacci, Ga tsoron masarautar dana dinga yi, Har wani wari Suka sa nake ji ni kadai.. Wasu abubuwan ma na manta, Amma kam nasha wahala.”
“Kiyi hak’uri please.. Insha Allah da komai ya wuce zamu ji dad’in rayuwar mu.”
“Kayi hak’uri... Amman gaskia banda ra’ayin zama acikin masarautar nan...”
Zeyi magana na sake katse shi,
“Banda ra’ayin zama da kai... Da masarautar. Dan Allah ka sawwakemun na tafi. Dan Allah”
“Khadijaaa... Kin dauka na aure ki ne kawai saboda ki kawo karshen matsalolin mu? Wait duk abunnan haka kika dauka ko? Shin me kikeso nayi na ki tabbatar kaunar ki ce tasa na aure ki..? Should I beg on my knees? Wait dole nema.”
Banyi aune ba naga ya zuba gwiwoyin sa ak’asa yana kallo na, Hannun sa yasa ya riko nawa hannayen yana mun wani kallo dana kasa fassara shi,
“Zawjati aleazizat , 'uhibukkthyraan. wana tazawajtuk lanani ahbabtuk kathira. wala 'astatie takhayul hayaati bidunik fiha... Yes dear wife, Ina kaunar ki.. Sannan na aure ki saboda ina sonki, Rayuwa ta zata zama wata iri idan babu ke cikin ta... Khadijaaa ki bani dama na nuna miki kaunar da nake miki.”
Gaba d’aya kalaman sa sai suka shiga rudamun ciki ma, Da alamun sun wa kwakwalwata yawa, Ga kwadan salad danaci da alama ya fara aiki shima, Wata gudawa ta matso ni, Ciki na ya shiga kokarin bada iska, Mik’ewa nai zan gudu ya riko hannu na, Lalle gayen nan besan mayuwacin halin da nake ciki bane.
“Kin yadda...? Kin yadda zaki zauna da ni?”
Kai na shiga juyawa alamun a’ah, Don ko awani hali nake ciki banajin Zan yadda.
“Tohm shikenan bazan takura ki ba... Amma ki shirya zuwa na gobe, Zan zo mu fara magana ta hankali dake. Zanzo as Salman ba sarki Salman ba. Ina neman yarjewar ki... Kin yadda?”