Sashe 83
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Idan har zancen da ya kawo ku kenan.. To ina ganin tashin ku awajen nan ku fita shi yafi alkhairi.”
Cewar waziri yana nuna musu kofar fita.
Galadima yayi daria yana bubbuga k’afar sa ta dama,
“Waziri kenan... Karka kuskura ka kaimu karshe, Domin idan ka kaimu karshe.. Yar wazintakar da kake ji da ita zamu tuge ka.. A juri zuwa rafi dai.”
SAS ya dagawa Waziri hannu alamun yayi shiru, Waziri yai shiru kamar wani mutumin kwarai. Su wambai suka shiga magana da fada, Ta inda suke shiga ba tanan suke fita ba, Shi dai Salman idanu ne nasa kawai, Addua yake cikin zuciar sa kan Allah ya bashi ikon ganin bayan su, Allah ya dora shi akan su.
“Saboda haka lokaci zamu baka...Nan da yan watanni biyu zuwa uku.. Ko dai ka fadi wa’enda kakeso a tsatson sarautar mu.. Ko kuma mu hadaka da duk wa’enda mukaga dama. Sannan abu na biyu, Idan dik zance biyun kayi biris dasu... Toh abdulqadeer shine zai hau karagar mulki, Kai da sarautar basannabas kuma sai dai labari, Domin bakada magaji da zakai tunanin zai gajeka nan gaba, Balantana su...”
“Ba sai ka karasa bama wambai. Mutumin da bai san wayesu ba, Kai ko kasan Khaleel da Abdullah? Ya kuke dasu..?”
Salman yai shiru yana jujjuya kai tamkar wani sauna,
“Bangane su waye ba Baba..”
“Ahap...! Ai na sani. To ko su din da baka tuna su Waye ba, Suma ba zasu gaji mulkin kaba atoh..”
“Yauwa galadima... Sai magana ta gaba. Zancen bikin yaran nan.. Kudin daka bayar basu isaba Salman, Ka karo biyun su, Domin biki za’ai na kece raini, Kaga bikin masarautar kalwa da akai yafi namu, Idan bamuyi wanda yafi nasu ba zamu sha daria ne a idanun masarautun kasanmu, Ina fatan ka fahimta?!”
Salman ya daga kansa alamun Eh. Can ahankali yace,
“Waziri... Kayi musu transfer din kudin account din nan na wajen ka baki d’aya.”
Waziri jiki na rawa ya tsugunna yana rawar baki,
“Ranka ya dade.. Du? Du? Du fa kace? Wannan uban makudan kudin Za’a bayar suyi hidimar miki biki dashi? Haba ranka ya dade.. Tuba nake.. Amma dan Allah ka sake shawara.”
“No... issokay waziri. Baba zasu isa ko?”
“Zasu isa tunda naji yaron ka (waziri) yana kambama yawan su.”
Tashi sukai suka tafi.. Suna sake jadda da masa kudirin su da suka yanke. Parlorn ya rage daga shi sai waziri bayan futar su, Waziri ya rarrafa ya rissina,
“Allah ya kara maka lapia... Bazeyiwu ka janye maganar makudan kudin nan ba..?”
“Bakomai waziri... Ka basu. Allah zai kawo wasu.”
Ajiyar zuciya waziri ya sauke yana kada kansa,
“Samun adalin sarki mai tausayi da hak’uri irin ka sai an tona.. Ran sarki ya dade..Ina fatan mafarkin nan da kakeyi yayi sauki ko..?”
“No waziri... Abu sai dada gaba yake yi. Dak’yar na fito fada ma... Naga wani garin magani daka ban kwanaki na hayak’i dinnan..? Nayi naji mafarkin matar duk na dena..”
Waziri ya dashe baki yana shafa rawanin sa,
“Haka mukeso.. Mugayen mutane ne suke bibiyar ka ta mafarki.. Kuma da yardar Allah karshen su tazo, Zan sake karb’o maka wasu, Zaka dena mafarkan baki d’aya. Yanzu ga wani ma ka sashi a karkashin pillown ka, Ka kwanta kai da mafarkan nan sai dai ka bani labari kawai..”
“Godia nake waziri.. Tabbas ka rike ni tamkar kai ka haife ni.. Ka tsaya tsayin daka akan makiyana, Waziri na gode sosai, Ka zamo min katanga mahallar makiya, Banda bakin godia s....”
Bai karasa ba waziri ya rissina hannu bi biyu,
“Ranka ya dade Ka dena godia dan Allah..Bazan taba cin amanar sarki Aliyu ba, Domin shi ya bani amanar Ka, Hannu da hannu ya riko ni a asibiti yana kan gadon rasuwar sa, Sunan kane abakin sa yana dankamin amana..”
SAS yai murmushi kawai yana jin k’arairakin waziri,
“Ni zan koma ciki... Bana jin da’din jiki na.”
Mik’ewa waziri yai, Bayan ya rissina masa , Ya kira dogaran sarki suka kare shi ya mike, Suka rakashi har sashen sa suna masa kirari. Yana shiga ya shige daki, Ya sakarwa kansa ruwa a shower. Yai flushing maganin waziri a masai, Yana fitowa ya canza kaya zuwa wata arniyar shadda ya dora alkyabba akai, Ya taje kanannadadden gashin sa kwantacce sannan ya dora hula akai, Ya shafa turaruka masu sanyin kamshi, Sannan ya zauna akan kujera yana nazari..
Tashi ya yi kai tsaye ya nufi sashen Khadija, lokacin da ya shigo ni kuma dawowata daga gurin Ammi kike nan ina cire alyabbar jikina ya shigo.
“Daga gurin Ammi ko?”
Ya tambaye ni yana kasa da idanuwasa. Kai kurum na iya dagawa naje na mayar da rigar inda sauran suke, ji kawai nai yace.
“Kina san Ammi na da yawa ko?”
Har cikin zuciya ta naso bashi amsa saboda banga amfanin yin karya ko neman gurin zama ba, ina ci gaba da gyaran wardrobe d'in saboda idan ba hakan nayi ba ban san me zan yi a dakin ba nace.
“Ammi uwace a gare ni, ban taso tare da mahaifiyata ba, shi yasa nake jinta tamkar itace ta haifeni. Bani da wata da zan kalla na nuna ta matsayin uwa sai yanzu da na samu Ammi. Amman uba kam har yanzu Ina dashi, duk da cewar bana manta wanda ya haifeni koda da second daya.”
Salman ya jijiga kai tare da karasowa ciki dan da a kofar ya tsaya be shigo ba. Ganin yana nufowa inda nake ne yasa nai saurin birkito da alkyabban cikin wardrobe d'in, na durkusa da sauri dan na kwashe. Shima sai ya karaso tare da dukawa yana taya ni, daman kuma rike ni ne bana son ya yi dan ya saba duk sanda muka hadu ya wani rungume ni. Murya a sanyaye yana daukar riga daya ya gyara ninkinta yace.
“Ni ne kawai ban miki ba ko?”
Nayi shiru dan bana son furta komai a gurin saboda rashin kyan furucin. Amman ni ba yimin ne beba no, zuciya tace har yanzu ta kasa karbarsa a matsayin abokin rayuwa ta. Na kasa mantawa da Mas'oud da irin soyayyar mu har ma da yadda muka shirya rayuwar mu. Da ace zuciya ta zata amince da Salman da zan zauna dashi na so shi kamar yadda yake gaya min irin wanda yake min. Toh taki yarda da duk wani furucinsa, ta kasa goge tarayyarta da abinda ba muharraminta bane a yanzu, tana son Mas'oud har yanzu kamar tai hauka.
“Toh ko tsufa nai miki ne?”
Na girgiza kai, taya zance ya yi min tsufa bayan shima din har yanzu matashi ne?
“Okay saboda na aure ki ba tare da na fara tuntub'arki ba?”
Sake girgiza masa kai nayi tare da cewa.
“Ko kadan daga cikin abubuwan da ka lissafa, kawai dai zuciya ta har yanzu tana gurin wanda ya koyar da ita menene SO.”
Zuciyar Salman ta harba da karfi. Da ace Khadija tasan yadda yaji da ba zata sake gaya masa cewar zuciyarta tana son waninsa ba harma ta kasa mantawa da wancen d'in bare ta karbe shi. Cikin dauriya irin tashi ya mike yaje ya saka mata rigar cikin wardrobe
dai-dai lokacin da nima na tashi zan saka wacce na ninke muka bugi goshi, nasa hannu da sauri ina shafa gurin nawa, ya yi saurin riko ni cike da kulawa yana mulmula min gurin.
“Sorry my dear.”
Ya fada yana shirin kwantar da kai na saman kirjinsa, amman na hana hakan faruwa saboda ni bana son kusancin mu dashi yana yawa. Baya san bata mata rai saboda nemarwa kansa masauki a zuciyarta, hakan yasa sakar mata jikin ta ya koma yana ci gaba da ninke kayan.
“Naga anata shirin biki ke banji kinzo kin karbi komai daga guri na ba. Shaheedah ta karbi kudi tace zatai kayan fitar biki da kuma gudin mawar da zata bayar, kefa.?”
Cikin tab'e baki ina yatsina fuska, nifa wallahi da zama tare dashi gwara min zama a durbun wajan Gajiyalle tayi ta bani wahala saboda rashin son da nake yi masa. Na mike tsaye Ina cewa.
“Ai ita matarka ce shi yasa ta nemi abu a gurinka.”
“Toh ke d'in meye a gurina?”
Bance komai ba har muka kammala gyara wardrobe din na tsaya na rasa me zanyi ya dauke min hankali daga kanshi.
“Kin abinci kuwa?”
“Eh a gurin Ammi.”
“Alhamdulillah naji dadi, yanzu me kike bukata nayi miki?”
“Ka bani shaidar rabuwar mu da kai shine nake bukata a gurin ka.”
Rintsa ido ya yi ya rasa ya zai yi da ni na dena furta masa wannan kalmar dan baya son jin ta. Ya mike tsaye tare da gyara alkyabbarsa yana murmushi wanda na rasa ko na menene yace.
“Zan baki hakkinki kema kamar yadda na bawa Shaheedah. Amman dan Allah ki dena min maganar saki domin Allah ma baya son kalmar. Ina sonki my yar jarida.”
Daga haka ya shafa fuskata ya juya ya koma sashen shi ya barni Ina karewa bayansa kallo. A raina Ina tunanin anya yana da zuciya kuwa? Taya nace bazan zauna dashi ba amman sai ya zauna dani dan dole, ni wallahi bazan yadda dashi ba Sai ya barni na koma inda nake so dan banga dalilin zama dani ba. Na ciro dankwali na tare da karkade turaran jikinsa da ya barmin a dakin kai kace zai koru saboda haushin Salman din da nake ji. Ganin bani da mafita yasa na haye kan gado ina hawayen bakin ciki.
GIM. SHAHEEDAH!
Gaba d’aya ta susuce da yin abubuwan da boka ya bata na tsibbance tsibbance, Cikin kwanakin har rama tayi. Ta kira hadimarta batula tana ta zagaye cikin dakin a birki ce,
“Ranki ya dade gani...”
“Duba kiga kafa ta dauke a sashen? Kizo ki sanarmun yanzu, Ki tafi da fatanya ki b’oye awani wajen kinji?”
“Toh ranki ya dade...”
Hadimarta na fita ta janyo wata qullin leda da kwado aciki marar rai an daure bakin sa da laya an nannade ta, Ta shiga tuntsura dariya tana babbakata,
“Khadija... Kinyi gangancin shigowa gonata.. Wacece ke da har zaki tunanin jerawa da ni?.”