← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 114

Sashe 36

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gimbiya Shaheeda ta riko gaban sleeping dress d'in ta da botiran suke a bude, ta sake matsowa kusa da shi a tsorace dan gaba daya ya canza sai faman cije baki yake yi da hakoransa. Leka idanunsa tayi taga yana zubar da hawaye, abin da ta dade bata gani ba a tare da shi. Sai ta marairaice tana share masa kwallar saman kirjinsa, murya a sanyaye ta fara masa magana.

“Na tsorata da ganin ka cikin wannan yanayin, nasan mafarki kayi, kuma da alama bashi da dadi duba da yadda kake zubar da hawaye. Shin me ka gani a cikin mafarkin naka?”

Ya yi shiru ba tare da ya kalleta ba, ga wani irin azababban sanyi da yaji yana huda duk wata kofar gashi dake jikin shi. Zare hannunsa ya yi daga rikon da ta yi masa, ya janyo jarkar ruwa tare da budewa ya kafa kai yana sha. Tun da ya fara sha bai sauke ba sai da ya kusa shanyewa taji ya ja wani dogon numfashi tare da saukewa yana lumshe ido.

“Ko mafarkin Ammie ka yi?”

Sai tambayar ta ta tayi matukar daure masa kai, ya dago tare da kallon ta da jajayen idanunsa. Take yaji wani faduwar gaba, sai ya sunkuyar da fuska yana girgiza mata kai.

“Idan mafarkin ta kake yi ya kamata ka dena, domin Ammie sam bata kaunarka. Ka manta sanda za'a nada ka matsayin sarkin Basannabas ita tazo ta dinga gayawa mutane cewar kai juya ne baka haihuwa kar a baka? Ka manta?”

Salman ya yi shiru kafin daga bisani ya daga kai alamar haka aka yi. Shaheeda ta yi murmushi sannan ta sake matsawa jikin shi ta shige tana faman shafa shi, cikin tsantsar makirci tace masa.

“To ka dena damuwa da duk wanda be damu da san ganin abinda Allah ne ya mallaka maka shi. Ni zan kasan ce da kai a duk yanayin da kake ciki, zafi rana da damuna ba zan taba rabuwa da kai ba.”

Cikin matukar farin ciki Salman ya jinjina kai, sai kuma ya matsa ya kwanta akan pillow still tana jikin shi sai lailaya shi take kamar ta samu jariri sabuwar haihuwa. Daga haka ya manta da wannan mafarkin da ya yi da mahaifiyar shi, bacci ya kuma daukar shi. Gimbiya Shaheeda ta mike zaune lokacin da ta tabbatar da cewa ya yi bacci da gaske. Sakkowa ta yi daga kan gadon ta ciro wani farin zare daga cikin gashin kanta tana kare masa gani kafin ta yi murmushi wanda ita kadai ce tasan matsayin shi.

Boyewa tayi sannan ta shiga toilet ta tsarkake jikinta ta fito ta shirya ta kwanta tana jin farin ciki. Basu farka ba sai wajan karfe shida, ya bude ido da kyar sai yaga Shaheeda a kusa da shi, ya fara duba jikin shi. Gabaki d'aya bai san sunyi wani abu ba sai yanzu da yaga yanayin shi, ya duba agogo yaga lokacin sallah har ya wuce. Da sauri ya tashi ya tashe ta sai tace masa ai tayi wanka tun dare. Yaji haushi kuwa sai dai ko a fuska kasa nunawa ya yi, kawai ya wuce bathroom shima ranshi a bace.

*KHADIJA (Dije).....*

Tun da na idar da sallah nake jiran kiran kawu daddy da yace zai ganni da anjima amma naji shiru, sai na fito daga daki naje parlor na koma kitchen amman shiru yana daki be fito ba. Hakura na yi na koma daki na zauna ina duba wani littafi. Kamar jira ake na zauna sai ga kiran shi ya shigo waya ta, na daga yace na sakko na same shi a parlorn kasa. Jiki na rawa na dauki hijab nasa na fito dan na kagu naji abin da zai sanar da ni, wanda sam na kasa kawo ko meye a cikin zuciyata. Yana zaune rike da waya yana dannawa nayi masa sallama ya dago ya kalle ni, kafin na zauna ya ce yace na rufe kofar naje na rufe sannan na dawo na samu gefen kujera nesa dashi na zauna. Ya yi gyara murya tare da aje wayar a gefen sa ya dan matso daga gefen kujerar yace.

“Alhamdulillahi Khadija a kullum na kalli yadda rayuwar ki ta dawo na kanji dadi da farin ciki. Gashi cikin ikon Allah ya sake daga daraja da mutuncinki ta hanyar da bamu tunani ba, yanzu bani da wani buri irin naga na mika ki zuwa dakin mijin ki, wannan shine buri na na biyu akan ki Khadija. Ina fatan zaki ci gaba da kulawa da kanki kamar yadda kike yi a koda yaushe. Na ga yanzu Allah ya baki miji wanda nake saka ran insha Allahu shine fitila na gaba da zai ci gaba da haskakawa a cikin duniyar ki. Ni dai ya yi min, tarbiyarsa, dabi'unsa da kuma kalamarsa duk ba bu wanda ban duba ba. Kema nasan zai yi miki, naga yaro ne matashi mai jini a jika, Allah ya daukaka shi a cikin tarin ni'imomin da yake da su.”

Kai na a kasa farin ciki ya mamaye ni, ashe kawu daddy kallon takun mu kawai yake yi nida Mas'oud bamu sani ba? Lallai babba-babba ne inji bahaushe da yace yaro ko ya hau rimi ba zai iya hango komai ba. Wayyo Allah dadi sai na hango gashi har an daura mana aure an kai ni gidan Mas'oud birnin zuciya ta muna ta shan soyayyar mu.

“Nan da dan wani lokaci za'a daura auran ku insha Allahu. Duk da cewa bani ne wanda zai bada auran ki ba, amman na dauki alkawarin zuwa can dangin mahaifinki da kai na nayi musu bayani yadda zasu fahimta. Allah ya yi miki albarka Khadija tashi kije daki ki kwanta nasan gobe akwai aiki.”

Ciki da jin kunya na tashi na ruga da gudu, farin ciki da nishad'i na suka dadu ba. Kan gado na fada ina tsalle tamkar wata yar shekara uku, na kagu Mas'oud ya kirani dan na kyankyasa masa wannan zazzafan labarin wanda nasan idan yaji ko bacci ba zai iya yi ba saboda murna. Wani ikon Allah sai be kira ba sai sako da ya turo min na text message cewar suna tare da Abban su ba zai samu damar kira ba mu hadu gobe a gurin aiki. Banji komai ba saboda ina cike da murna na je kitchen na zuba abinci naci sannan na dawo na kwanta cike da zakuwar ganin gobe.

*WASHE GARI*

Yau kam na fi koda yaushe saurin shiryawa dan zuwa gurin aiki saboda zumudi, na shirya tsab na dauki jakata Tukur driver ya dauke ni sai gurin aiki. Babu kowa sai wadanda suka yi aikin kwana, na shiga muka gaisa sannan na wuce office na zauna dan jiran lokacin da zan yi program dina. Bamu hadu da Mas'oud ba sai wajan karfe goma sha d'aya dalilin rashin zuwan sa da wuri. Sai da na jira har karfe d'aya lokacin da ya gama nashi sannan mukai sallah nace ina son yin magana dashi. Yana ta zolaya ta ganin yadda na cika da nishad'i ba kamar kullum ba, ya samar mana gurin zaman muka zauna.

“Ko ranar da aka daura mana igiyoyin aure sai haka madam, irin wannan murna da farin ciki haka, meye sirrin a ban nasha nima.”

Na yi dariya tare da rufe ido da hannayena, na bude ina wasa da zoben yatsa na nace.

“Albishirin ka?”

“Goro Oum Waleedah.”

“Fari ko baki?”

“Ahhh! Sai ma an jani tukunna? Toh na zabi uhmmmm... Uhmmmm... Zabar min dai da kanki.”

Ya yi maganar cike da shagwaba, ban san lokacin da na saki dariya ba ina cewa.

“Gaskiya kai zaka zaba, ai ni zan gaya ma albishir d'in.”

“Toh shi kenan na zabi fari tartar.”

“Yauwa jarumi na kasan me?”

“Sai kin gaya min da bakin ki sweetheart.”

“Kawu daddy ya gano cewa muna soyayya, jiya da kanshi ya kira ni yace ya yaba da hankalin ka ya amince za'a yi auran mu nan ba da jimawa ba.”

Mas'oud ya bude baki tare da zaro ido cike da tsantsar mamaki, ya kasa ma magana saboda yadda abin ya zo masa daga sama.

“Wai kina nufin kice min min daddy da kanshi ya gano cewa soyayya muke yi?”

Na gyada kai ba tare da na yi masa magana ba sai dariya nake yi. Kasan cewar a cikin office din su muke, kuma babu kowa a ciki sai kawai ya taso tare da yin juyi yana rawa ina dariya. Kusa dani na ji ya matso tamkar zai hade jikina da nashi nayi saurin rintsa ido saboda na riga na saddakar da faruwar hakan, sai naji yace.

“Ina ma ace ina da wannan damar, dana nuna miki irin tsantsar farin cikin da na shiga ta hanyar baki lafiyayyan runguma. But ya zama bashi, Allah ya kai mu lokacin da zamu zama abu d'aya zan biya ki harda na yau.”

Sai ya d'an matsa daga kusa da ni ya zauna akan kujerar da ya taso, sannan ne na samu damar bude idanu na.

“Kin fiye jin tsoro Oum Waleed, ya kamata kuma na rage miki yawan shi.”

“Ai ni wani lokacin wallahi tsoranka nake ji, dubi yanzu fa kana kokarin taba ni.”

“Ban taba ba ai Oum waleedah, but soon zan yi miki abin da yafi tabawa ma.”

Na share shi dan idan na biye masa tsab zai sanya ni cikin wani yanayin da ban shirya zuwan sa ba. Muka ci gaba da hira saboda zakewa harda yadda bikin zai kasance muke ta tattaunawa hankali kwance. Tun daga wannan lokacin muka sake d'in kewa ni da Mas'oud saboda ganin zamu mallaki juna. Daga ni har shi bamu taba kawowa cewar kawu daddy ba junan mu ya mallakawa ba, saboda bai fito fili ya bayyana mana cewa ga yadda yake nufi ba. Haka muka ci gaba da rayuwa lokaci yana ta tahowa, Mas'oud yana ta hada kudin da zai turo gidan mu dan nema masa aure na kamar yadda ake yi.

*FADAR BASANNABAS*
Chapter 36 · 0% Book details