← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 114

Sashe 103

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kit ya katse kiran, Nabi wayar da kallo, Goma na dare saura kwata. Yana iya? Mikewa nai na shiga band’aki nayo wanka, Badan inason kamshin turaren jikin sa ba Allah ba wani zance da zan bari yazo, Wasu riga da wando nasa na English wears nayi packing gashin kai na. Ba dadewa sai ga kiran sa ya shigo,

“Ki sakko ina k’asa...”

Sai dana mula na huta tukun sannan na mike na sauka kasan, Ina hango shi akan kujera ya bada baya yana danna waya, Tun kafin na karasa ya taro ni yana riko hannu na,

“TubarkAllah! My queen.. Kinyi kyau sosai. Komai nake me mekyau ne, Sahibar zucia ta.”

Janyo ni yayi zuwa jikin sa yana shafa gadon baya na, Duk kuwa da fushin da nake dashi, Hakan be hanani lafewa a jikin saba, Na cusa fuska ta a k’irjin sa ina shakar daddadan kamshin dake fita daga jikin sa,

“Ina fatan za’ayimun afuwa akan kowane lefi ne da nayi? Duk kuwa da bansan laifin da nayi ba.”

Hannu nasa ina duddukan kirjin sa,

“Shine.. Shine.. Shine.. Ka fad’awa Kawu daddy zancen cikin nan.. Meyasa?”

Dariya yayi yana shafa gashin kai na,

“Ayimin afuwa my love, Na kira shine na gayda shi yake tambayar ki? Nace bakida lapia... To kinsan manya da gano duk wata kwana da kayi, Har yake sanarmun za’a kawo kudi da kayan sisters dinki...”

“Ya gayamun wai basai naje ba, Ni gaskia inason zuwa.”

“Kiyi hak’uri! Zakije bikin da yardar Allah, Amma ganin kayan ne dai ki hakura kya gani daga baya, Kinsan hayaniyar mutane, Dr. ta hanaki, Kinji? Sai me kuma nayi na kara bada wani hakurin?”

“Shikenan ya wuce...”

Sumbatar gefen kunne na yayi, Ya koma kan fuskata daga nan ya dawo tafin hannu, Nai saurin riko bakin ina murmushi, Shima murmushin yayi ya cigaba da cewa,

“Wata dayan dana deba mana akan game dinmu ta cika, Kuma naga nasarori sosai ta bangaren ki sai dai abu d’aya kacal ne da har yau banji daga bakin ki ba”

“Me?”

“Yadda nake nuna miki kulawa.”

Ya fada yana tabarbare fuska kamar zaiyi kuka.dariya na shiga yi, Mikewa yai ya dakko wata leda acan kasan kujera,

“Na manta nazo da toshiyar baki....”

Karba nai da sauri jiki na bari na zazzage ledar, 1 liter bucket ne na mint Ice cream da kuma sausage shawarma guda 5 da zafin su, Sai tarin chocolates. Habawa bararrajewa nai zan fara ci ya ri’ko hannu na,

“Bara mu kira Ammi dai muji ko? Ko zaki iya cin komai.”

“Na hakura da fushin da nake yi fa, Dan Allah ka kyaleni naci... Wallahi bakaji yadda babyn ka yakeso yaci ba.”

“Toh i sauri ci.”

Ya fada yana cire takardar jikin shawarman, Nayi murmushi kawai, Ya samun a baki, Na k’arba gaba d’aya na faraci ina gyada kai saboda dadi. Sai da nacinye har guda 3 nasha ice cream din sosai sannan naji na koshi, Banyi aune ba naji harshen Salman kan lebe na yana lashe gefen bakina, Daganan lamarin nasa ya zarce zuwa ga kiss din mai gaba d’aya, Ture shi nai dakyar ,

“Abu ne awajen shine na cire.”

“Daga cire abu kuma sai ka...”

“Sai me??? Dan kadan nayi fa love. Tuba nake to. Sai albishir na biyu amma gaskia bazan fada ba sai kin bani tukwici.”

“Me kakeso?”

“Kalamai daga zuciar ki... Wanka tare, Sai dan kisses and hugs haka masu zafi kafin miyi bacci.”

Wannan Salman din A ne wajen wayo ne,

“Na yadda..”

“Na samu gwamna da kai na ba’ai keba, Munyi magana sosai ta fahimta dashi akan yayi hak’uri da batin tashin yan yankin gaba d’aya, Illa dai gonakin dake gefen yankin, Za’a biya manoman ayi babbar makaranta awajen ta kwana. Hakan yayi miki ko?.”

Bansan sanda na wawuro shiba na rungume abuna tsam ina hawayen farin ciki,

“Nagode, Nagode, Nagode... Allah ya biya ka da alkhairi, Ya baka abinda kake nema dunia da lahira. Ina fatan gwamna yaji da’din shawarar taka?”

Handkerchief ya janyo a aljihun sa ya shiga gogemin hawayen cikin wani salo,

“Bar kuka My love.. Ai nima garin mu ne, Hakki na ne nayi abunda ya dace kinji? Kuma ya gamsu da shawarata dari bisa dari. Nasa a musu titi kyauta daga gare ki. So muje a wanke ni tas.”

Zanyi magana ya dauke ni a kafadar sa muka hau saman tare, Bai direniba sai akan gado,

“Baby kin kara nauyi tubarkAllah.. Oya ciremin kayan ki wanke ni ki sabe ni.”

Sai na samu kai na da ce masa,

“Wani lokacin sai nayita mamakin haka kakeda magana? Mutane bazasu taba yadda ba.”

“Ke ka’dai nake iya sakewa nayita magana sosai, Ni kaina Ina mamaki, Kuma sai bayan na auroki bakina ya bud’e haka, So kaunar kice sila my love.”

“Lalle na ciri tuta, Godia nake takawa... Takawarka lapia sarkin sarakunan nigeria baki d’aya, Nagode kwarai da duk kanin alkhairin ka gare ni, Hakika mutanen durbun zasu ji da'din wannan titi, Allah ya biya ka da mafificin alkhairin sa. Da sauran sarakuna zasuyi koyi da kai, Hakika da ansamu ci gaba sosai a kasar nan. Lalle Ka musu zarra nawan. Muje band’akin kafin na canza ra’ayi.”

Da sauro ya mike, Hannu cikin hannu muka shjga band’akin, Anan ma sai da muka bata lokacin yin wata soyayyar kafin mu fito mu shirya cikin kayan bacci.

“Saura kalaman da sauran aiyukan ladan.”

Daria nayi jin wani wayo na daban. Kwanciya mukai akan pillow d’aya muna kallon juna, Hannun Salman na cikin jiki na yana yawo dashi. Cikin lumshe idanu nasa hannu ina shafa kwantacciyar girar sa,

“Miji na sinadarin rayuwata, Tauraro mai qawata rayuwata, Zuma naaa, A Ido da kyawun kallo a baki dadi mai dad’ad’awa, Salman ibn Aliy bin Salmanu dina nawa ni kadai, Zaki kake ga isa ga kasaita....”

Na karasa fada ina rufe bakunan mu waje d’aya, Nayi saurin jan zanin gado na rufe mu gaba d’aya, A ranar duk wani abu da Salman keso biye masa nayi, Na kuma yi amfani da karatun hazikar nan *BillynAbdul* marubuciyar da nake bin books dinta wajen ganin na faranta masa nima daren ranar Salman kuwa..Harda hawayen farin ciki, Ya shi mun albarka fiye da tunanin mai tunani, Tare da zayyano abubuwan alkhairi kan sune kyautata,Ni dai biye masa nayi kawai muka gurji lobayya tamkar cin kwan makauniya...

*MAI BABBAN DAKI...*

Fitowa tai daga kitchen, Hannun ta dauke da food flasks da flask na shayi, Sai wani tray daya sha kayan alatu akai, Umma Hansatu (Amintacciyar hadimar ta) Na gefen ta tana shirya kayan abincin acikin wani tsaftaccen kwando.

“Ranki ya dade dole gimbiya da mai martaba suji dadin abincin nan, Tun daga k’ofar bayi ake jin kamshin sa fa, Dad’in ‘dadawa kuma da hannun ki kika sarrafa komai.”

Ammi tayi murmushi kawai tana gyaggyara gyalen da aka rufe kwandon dashi.

“Hansatu kenan, Allah yasa yadda yayi dadi a hanci a baka ma yafi haka dad’adawa..”

“Aamin ranki ya dade. Ai dole nema yayi dadi. Ina dawowa daga aiken nan zan kwashi nawa ganimar dad’in. Allah dai ya kara karya asirin da akai na shiga tsakanin ki da yaran ki, Ya waiwayo da hankalin Yareemah Khaleelullahi gare ki...”

Ammi ta fad’ad’a murmushin ta, Kafin ta dan sake matsawa daf da Umma Hansatun. Murya kasa kasa ta shiga ce mata,

“Ai Hansatu wata muhimmiyar magana nake son sanar dake, Amman bansan koda wasa wani yasan da ita, Kin san dai yadda masarautar nan take ko?”

“Insha Allahu ranki ya dade babu matsala, Allah dai ya kara miki lapia da nisan kwana mai amfani.”

“Aamin Yaa Rabbi! Tare da ke..”

“Ina sauraron ki ranki ya dade, Allah yasa alkhairi ne kunnuwana zasu jiye mani, Kuma Allah ya bani ikon rufawa wannan amana asiri.”

“Aamin! Zancen shine, Kinga dai kusan ko yaushe a dan tsukukun nan, Ina tura ki sashen gimbiya Khadija ki bawa falaki abincin ya karba ko? Bakida masaniyar abincin wanene acikin su ko?”

“Allah yaja zamanin ki, Wannan haka shike.”

“Toh abincin gimbiya Khadija ne, Harda shi mai martaban, Amma dai da abunda yasa akeyin sa hususan saboda Khadija ne... Ki tayasu da addua, Uwar dakin naki Allah ya albarkance su da...”

Zubewa Mama Hansatu tayi tai sujjada tana godewa Allah,

“Allah mungode maka, Allah abun godia, Allah Alhamdulillah! Masha Allah! Ubangiji Allah ya bata lapiar sauke shi lapia, Ya yiwa abunda za’a haife albarka. Allah ya kauda idanun makiya akai ya inganta.. Kai Alhamdulillah!”

Mikewa tai tashiga taka rawa, Ammi na dariya ahankali Itama farin ciki fadade akan fuskarta.

“Aamin Hansatu! Aamin. Yanzu sai ki hanzarta ki kai musu, Kuma idan da hali ma so nake kije ki zauna da ita, Kinga shi shi kullum yana fada, Gashi sauran hadiman nata ba wasu manya bane.”

“Zuwa kai ran ki ya dade, Me zai hana? Da yardar Allah zan koma da gari yai duhu.”

“Masha Allah! Toh Allah ya yi albarka.”

Gyaggyara mata komai tayi, Umma Hansatu ta dauka ta nufi sashen Dije, Tana zuwa yau har ciki akai mata iso tashiga. Dije tayi murnar ganin kuloli shake da abinci, Zaman dabaro tayi tashiga ci hannu baka hannu kwarya. Ta kora da kunun tana shiwa Ammi hamdalah.

“Nagode Umma Hansatu, Allah ya saka da alkhairi.”

Umma Hansatu taita mun addua kafin ta mike ta sauka ta wanko komai, Ta dawo tana mammatsa kafata dakemun ciwo sosai,

“Ai uwar gijiya tace na dawo na zauna dake idan babu damuwa, Nace babu zan dawo idan gari yayi duhu. Hakan ya miki??”

“Kwarai ma kuwa sosai Umma Hansatu, Allah sarki Ammi ina godia sosai. Allah ya saka da alkhairi.. Yanzu ma kiyi zaman ki ba sai anjima ba dan Allah.”

“Tuba nake ranki ya dade, Wai da so nake na dan d’akko abubuwan da zan bukata.”

“Eh da haka! Toh Allah ya kaimu.”

Mun dan jima muna hira sama sama, Kafin Umma Hansatu tayimun sallama tatafi. Ni kuma na bararraje awajen raina cike da dadi, Inata sakawa Ammi da alhairi bisa ga dawainiyar da take yi da ni.

*GIM. SHAHEEDAH!*
Chapter 103 · 0% Book details