← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 114

Sashe 114

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

“Kai Yareemah meye hakan! Bashi hak’uri”

Mama Huwaila ta umarce shi tana zare idanu, Chiroma ma yashiga tsakani yana bada hak’uri.

“Kiyi hak’uri amma bazan bayar ba, Mena masa? Mtsss”

Yaja tsaki kawai ya fuce waje yana bugo musu kofar, Nan kowa ya kidime aka shiga baiwa Waziri hak’uri, Murmushin yake kawai yake yana amsa ‘bakomi ya wuce..’ Ransa a bace yaita danne zuciar sa har shaheedah ta aiko sadiya da wata brief case baka mai dauke da sakamakon komai, Karba kawai waziri yayi ya fice su wambai na biye dashi a baya suna faman ban hakuri..

*SAS*

Yana zaune shi da falaki suna kallon komai, Wani suyi daria wani suyi Allah wadai. Salman ya sauke ajiyar zuciya kafin yace,

“Mutanen nan sunfi shedan rashin imani, Allah ya kyauta... shin ka gama tura masa komai tuntuni ko?”

“Ai sun kai kusan sati ma a wajen sa, Har videos da komai na cctv duk na tattara komai na kai masa, Har cikin babban parlorn sa aka kaini. Gaskiya gwamna na da kirki wallahi.”

Salman ya numfasa yana murmushi,

“Ai adalin shugaba ne, Yanzu abinda ya rage kawai tattara komai a watsa shi agaban manyan yan majalisa. Jiran su nake su tunkaro mu kawai sai mu saki babban bomb din. Ka dai samu masu tsibbun nasu ko?”

“Allah ya Kara maka lapia da nisan kwana, Duk munyi magana dasu, Sun amince, Nace Za’a dakkosu a duk sanda muka nemi ganin su, Ai bokan Waziri shi yafi ban dariya, Yana ganin kudaden nan, Da mukullin sabon gidan nan daka bayar wallahi ya kunce komai ya shiga magana caaa. Wani lokacin wai har kulla toka yake ya bashi yace ya barbad’a a abinci.”

Salman yai murmushi kawai yana bubbuga mouse pad din hannun sa,

“Ai kamar doctors dinnan ne, Ina ce musu zan kai karar asibitocin su kotu, Suka shiga ban hakuri, Acikin awa d’aya gaba d’aya asibitocin da muka jajje duk kusan a tare kowanne ya turomin original results din, Harda karin signatures na board of directors. Gobe alhassan zai karb’o a airport, Kowanne a rana d’aya zai zo.”

“Kai Alhamdulillah..! Allah yakara maka lapia da nisan kwana.. Lalle akwai kallo agaba. Ranka ya dade kayi matukar kokari wallahi, kayi bincike sosai a matsayin ka na lawyer.”

“Ai mun dogara da Allah, Hmm! Kaga na’urar kimiyya tagama mana komai na bankado sirrikan su, So Inde ka san yadda zaka tafiyar da technology a yanzu to sannu ahankali zaka gano komai.”

“Allah yaja zamanin sarki, Ya cigaba da dora ka akan makiyan ka Aamin.”

“Aamin Yaa Rabbi... IN SHAA ALLAH! Cikin satin gaba zaka raka zawjati garin su.”

Salman ba kunya ko kadan agaban kowa baya iya boye soyayyar Khadija, Shiysa duk wani mai kusanci dashi yasan sunan Zawjatii na dije ne.

“Toh ranka ya dade. Allah ya yarda.”

“Aamin, Anjima idan gari yayi duhu sosai sai ka dakko Khaleel, Sashen Ammi zai je kansa tsaye. Ku raba hanya tun a zauren bayi. “

Mikewa falaki yai yana rissina masa, Cikin girmamawa ya shiga yi masa sallama,

“Toh ranka ya dade.. Insha Allah kuwa hakan zaayi, Ka huta lapia.”

Ficewa yai yana sake rissina masa, Shi kuma Salman ya maida duban sa ga Waziri, dake dakin sa ya ciro takarddun da shaheedah ta kawo na sakamakon karyar ciwon Salman da akai yana duddubawa. Girgiza kai kawai Salman yayi ya mike ya haye sama abinsa, Bayan ya danna recording akan bidiyon bangaren waziri..

Falaki na dakko Khaleel dayai badda kama ba zaka taba kawowa shidin bane saboda shigar dogarai yayi, Tun a zauren bayi suka rabu. Ya shige sashen Ammi kansa tsaye, Dama tasan da zuwan sa, Tai masa iso suka haye parlorn sama, Acan ya rungume Ammi yana kuka mai tsuma zuciya, Na shekara da shekarun da bai sanyata ba cikin idanun sa.........

*SAS****

Jikin sa sai rawa yake yana wanka a sashen sa, So yake ya gama kawai ya ji shi ajikin khadijan sa, Kwana biyu yanata aiki ba dare ba rana a dakin sirrin sa, Sai da ya tabbatar komai na shedar sa ya kammala tukun sannan ya danji sassauci a ran sa. Fitowar sa daga bandaki keda wuya yana shafa madaran turare a kayan baccin sa, Wayar sa tafara kara, Dauka yai cikin hanzari ganin Ammi ce, A ransa yana adduar Allah yasa lapia, Domin bata taba kiran sa. Gaishe ta yai cikin biyayya,

“Barka da dare Ammi....”

“Barka mai babban suna. Kaga na kira ka yanzu ko?”

“Ahh haba bakomai Ammi, Ni kinganni ma inata kokarin harhada abubuwan shedun nan.”

“Masha Allah! Allah ya temaka ya bada nasara.”

“Aamin Ammi.”

“Dama zancen Khadija ne.”

Zama yai akan gado yana taje sumar kansa, Yana kallon kansa ta mudubi.

“Ina sauraron ki Ammi..”

“Eh.. Wani tunani naketa yi, Har na kira gwaggon ma itama tace hakan zai fi”

“Koma menene Ammi na baki wuk’a da nama.”

“Ah’ah sai da amincewar ka, Dama maganar komar Khadija gidan Gwaggo ne. Idan komai ya dan lafa saita dawo d’akinta, Amma Kaga yanzu dai dubi yadda kowa idanun sa akan ta, Duk wata mugunta so ake a jefa mata.”

Nannauyar ajiyar zucia ya sauke yana kallon karamin frame din hotan Khadija dake gefen gadon sa, Ahankali ya janyo shi yana shafa dai dai wajen fuskar ta,

“Hakane, Na amince Ammi. Ni kaina sai nafi samun nutsuwa.”

“Yauwa.... Idan ka saka rana sai ka sa akaita.”

“Ko gobe ma Ammi.. Gwara ayi awuce wajen.”

“Babu takura ko?”

“Babu Ammi.. Nagode Allah ya saka da alkhairi ya dora ku akan makiyan ku. Aamin.”

Sallama sukai, Ya mike jikin sa a sanyaye, Sam dai dai da second d’aga bayason dije tai nesa dashi. Ajiyar zucia ya sauke ya nufi d’akinta jikin sa duk ba kwari.

*G. KHADIJA*

Ina kwance ina aikin shan mangoro Salman ya shigo, Sanye nake cikin shigar half vest da zani, Kai na ba dankwali na bararraje ina shan mangoro, zama yai a gefe na yana janyo ni jikin sa,

“Zawjatii na...”

“Uhm.. Honey bunny naaa. Ya aiki?”

“Alhamdulillah ya ciye ciye? Ya baby na?”

“Gashinan munata fama. Mangoro na hudu kenan.”

“Ai kuwa ya isa haka nan, Zo mu wanke hannun da bakin.”

Daga kai nayi, Yana tayani mikewa, Ya zare hular kansa marar nauyi ya dora mun muka shiga bandaki, Ya temakamun nai brush, Na watsa ruwa muka fito. Har kan gado ya temaka ya kwantar dani sannan ya koma gefe na yana gyaramun kwanciya,

“Sannu zawjati..”

“Yawwa my love.. Amma meya faru naganka ba walwala?”

Murmushi yayi ya kamo hannuna yana sumbatar cikin sa,

“Bakomai fa Zawjatii.. Gajia ce kawai.”

Na yunkura dakyar na zauna ina tallabo fuskar sa,

“Noo! Meya faru please?”

Hannun sa yasa akan cikina yana shafawa, A hankali murya a raunane yake gayamun,

“Bakomi wallahi, Kawai Ammi ce ta kira ni ba da’dewa, Itada Gwaggo sun tsara... Zaki koma gidan Gwaggo da zama na dan wani lokaci. Nace na amince gobe zaki tafi ma.”

Ni kaina sai naji wani rass, To amma ya zanyi? Kila hakanne mafi alkhairi, Kuma tinda yace Ammi da Gwaggo ta fada ai zance ya kare. Hannuna nasa nima cikin nasa ina murzawa a hankali,

“Na amince nima zawj.. Allah yasa hakane yafi alkhairi.”

“Insha Allah kuwa, Ammi tace kodan saboda yadda ake farautar ku keda babyn mu.”

Na numfasa ina kallon ciki na daya girma ba lefi. Nasa dayan hannun na dora shi akan na Salman muka shiga shafa cikin atare. Zafafan hawaye ne na hango suna reto a kyakkyawar fuskar Salman,

“Zawjati zanyi kewar ku sosai, Gaskia ba zaki dade ba zan dakko abata...”

“Ka rufamana asiri zawj, Kaga fa su Ammi ne suka yanke shawarar. Ni kam na amince da hannu dubu.”

“Ai dama haka kikeso..”

Ya fada yana turo baki gaba. Lakuce bakin nayi ina daria,

“Ba haka bane, Kasan manya da hangen nesa... Mu dai fatan mu Kayi nasara a wannan yakin dake tunkaro ka.”

“Hmm Aamin dai baby...”

Kamo hannun sa nayi na shjga zagaye su a duk wasu sassa danaga yanaso a jiki na, Hakan da nayi ba a karamun dadi Salman yaji ba, Domin nagani a yanayin sa, Kwantar dani yai akan pillow yana shafa gashin kai na,

“Banda raki dai... Yau zamu gurji kauna a daren nan, Duba kiga har anfara ruwan sama mai dadad’a daren masoya, Zan baki tukwici, Tukwicin kuwa shine zakije... Durbun idan kin koma gidan Gwaggo Addah maryama seta raka ki....”

Bansan sanda na finciko shi ya fado kan hannunaba saboda murnar jin zanje durbun,

“Godia nake zawj dina... Zumana mai dadad’a rayuwata, zaki kake, Ga isa ga ‘kasaita..”

Wata iriyar rantsattsiyar sumba mai tafiyar da duk wani damuwa sas ya shiga yiwa dije, Don dadi sai da takusa shidewa tana kara kankame shi. A haka ya dinga nuna mata kauna wadda takasa tantance gardinta da first night d’insu. Sumbatu masu daraja da kima ya shiga yi mata tana kara makalkale shi, Kowannen su hawayen dadi da farin ciki yakeyi, Wanda Salman ya shiga lashe na idanun dije cikin salon kauna, Yana kuma gaya mata kalamai masu dadi,

“Kece burin rai na, Rayuwata, Qalbi na da gangar jiki na baki d’aya, Zawjatii! A koda yaushe ina fatan ki kasance cikin farin ciki a rayuwar ki, Kasancwar farin cikin ki shine abu mafi tsada da daraja a wuri na.. Your kiss mends my heart, your touch lights up my soul, and your presence makes a difference to my world. Deejah na.. Although I may not have the right words to express you how I feel about you and how blessed I am that you came into my life. I just want to let you know that I love you with everything I’ve got and can’t imagine a life without you...”

Daga nan bansake sauraron duk wasu kalamai nasa ba saboda wata duniyar dadi daya jefa ni, Ranar na kara tabbatarwa zucia ta, Tabbas wata iriyar K’auna Salman kemun marar gauraye. Hawayen farin ciki ne suka shiga reto a fuska ta.... Duk kanin kofofin jikina sai suka shiga maraba lale da zafafan sakonnin dayake aika musu, Harta Kai na zama ni ke shugabanta shi ke daukan darasin daren ranar.......

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
Chapter 114 · 0% Book details