← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 114

Sashe 31

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance tayi akan doguwar kujera tana waya, kan cikin ta kuma plate ne mai dauke da fruits tana dauka tasa a bakin ta cike da nishad'i. Mas'oud ne yake ta kashe mata jiki da sassanyar soyayyar shi, wacce take sanya ta rasa a wace duniya take tsabar sauki. Shukrah ta shigo tana faman nishi da alamar gajiya tayi, ta bude fridge ta dakko ruwan sanyi tare da budewa tana kwankwada. Sam ba tayi zaton waya Dije kiyi ba saboda ganin idanunta a rufe, tayi tunanin ma bacci ne ya dauke ta da plate d'in a jikinta, sai ji kawai tayi tana cewa.

“We are two bodies, but our heart beat as once. Be mine, forever, do not leave me ever Abu Waleed.”

Cikin wani irin juyi Shukrah ta waigo tare da zuba idanuwanta akan Dije. Cikin tsantsar mamaki na ganin ashe yarinyar nan idanunta biyu tana jin shigowar ta amman tayi mata banza babu wani alamun taji ta. Da waye take wannan wayar ita kuwa? Allah yasa ba Mas'oud bane data fara ganin sa sandiyyar kwanciyar Dijen a asibiti. domin harga Allah gayen ya yi mata dari bisa dari, zuciyar ta babu abinda take muradi irin su kasance tare, hakan yasa bata fatan ace suna soyayya da Dije dan kar ta zo ta bayyana mutane su ga rashin adalcin ta ko su yi mata fassara da maciya amana. Sai kawai ta samu kanta da zama a parlorn tana sauraran wayar duk da cewar bata jiyo muryar d'aya bangaran.

“You're my dawn, You are my twilight.”

Shukrah taji Dijen ta kuma fada, duk da cewar bata san ko waye ba, samun kanta tayi da cewa Dijen.

“Wai baki ji ana ta sallama bane Dije? Na dauka ma bacci kike yi ashe kina nan kina yaudara bayan ga Tk can yana jiran ki a parking lot.”

Yadda tayi maganar da karfi ne ya sanya Mas'oud jiyo abin da take fada, daman kuma tayi ne dan koma waye Dije ke wayar dashi ya jiyo. Musamman idan Mas'oud din ne da tayi domin shi. Ai kuwa yaji d'in, nan da nan hankalinshi ya yi mugun tashi yana ta tambayar ta.

“Ummu Waleedah waye Tk? Meye hadin ki dashi? Wace a kusa da ke?”

Dai dai lokacin Dije ta bude ido ta kalli Shukrah da ta kura mata nata idanuwan. Bata ce mata komai ba, haka ma bata dauke ido akan ta ba tace da Mas'oud.

“Duk wadannan tambayoyin ni kadai zan amsa su?”

“Eh mana, ai nasan duk kina da amsoshin su, kuma zafi ganewa idan kika min bayani da kanki.” Ya yi maganar yana tsuke fuska tamkar suna ganin juna.

“Amman fa karka manta da bahaushe yace, idan ka ga kare yana shinshina takalmi, toh dauka zai yi. Ni babu abinda ya hadani da duk wadannan tambayoyin da kayi min.”

“Toh wace ce ta yi miki wannan maganar?”

“Ya Shukrah ce.”

Shiru ya yi na dan wani lokaci yana nazarin abin da tace maza na kare. Murmushi ya yi har ya na dan fito da saurin sa, wanda ya sanya Dije gano cewar ya fahimci abinda take cewa.

“Gaskiya ne yar jarida, wato kema kinsan kiyi irin wannan language d'in ko? Wallahi kin bani wahala wajan yin tunanin abinda kike nufi, oya ki lallashe ni kar na yi fushi.”

Saboda ta sake batawa Shukrah rai dan ta gane cewa abin da ta fada ba damunta ya yi ba, sai cewa ta yi dashi.

“Uhm-uhmm-uhmmm..., ka yi hakuri dear, for you, my heart beat aches, and only you can ease the pain. Kar kai fushi kasan zazzabi yake sani idan kayi.”

Kamar Dije tasan amsa zai bata kuma mai dadi ta nuna soyayya, hakan yasa tasa hands-free dan Shukrah taji da kyau ko zata rabu da su. Sai da ya ja numfashi kamar irin wanda ya dawo daga shiga tashin hankalin nan, sannan yace mata.

“Har naji dadi, rai na ya sanyaya. Forever walk by my side Oum Waleedah, promise me that you will meet me in my cham.....”

Kafin ya karasa ta yi saurin cirewa daga handsfree d'in dan karya fadi abin da zai sanya Shukrah kuma yi mata kazafi, taje tace maganganun batsa suke yi. Cikin jin haushi kuwa ta suri jakarta tayi daki tana masifa kamar wacce a ka yiwa wani abu. Cikin ranta banda bakin ciki babu abin da yake cikin sa, koda ace gaske ne Mas'oud da Dije soyayya suke yi sai ta rugurguza duk da cewar tare ta gansu, kuma ta silar Dijen tasan Mas'oud din. Toh amman ya za ta yi da zuciyar ta wacce a cikin rashin adalci ta sanya soyayyar shi a zuciyar ta. Tayi wurgi da jakar ta tare da fadawa kan gado tana wani irin nishi, ƙirjinta ya shiga bugawa ga zafi da taji yana yi mata (yo bakin ciki ne da hassada).

“Abu Waleed yaushe zaka zo ne?”

“Uhmmm....zan zo sai ranar da bamu da aiki, kinga yau juma’a, San da kika dawo aiki. Idan kin zo sai muyi shawara ko?”

“Toh shikenan Allah ya kai mu.”

“Amin my dear wife to be. Bari naje Abba yana kira na.”

“Toh shikenan a mika min gaisuwa ta musamman.”

“Lalalah! Toh in ji waye zan ce masa.”

“Kana nufin kace be sanni ba?”

“Mama ta sanki wallahi, kinsan sunan mahaifiyarta gare ki shi yasa take girmamaki.”

Wani sanyi ya ziyarci birnin zuciya ta jin wacce zata zama sirika a gare ni tana ganin mutunci na, Lallai idan nayj sa'a, Zan yi dace da uwar miji mai so na. Jin ana ta kiran sa daga nesa ne, Yasa na sauke wayar na katse dan nasan idan ba hakan nayi ba tabbas ba zai tashi yaje kiran da gaggawa ba, saboda baya son rabuwa da ni yana jin dad'in kasancewar mu masoya. Tashi nayi nima na shiga bedroom d'i na, sauki ya samu ba lefi, kuma ya zuwa yanzu nasan yadda zan zauna da kowa na cikin gidan.

*MASARAUTAR BASANNABAS*

Gurfane yayi a gaban sa tamkar shi ne sarkin, Shi kuma yana hakimce akan kujerar zaman fada ta sarki. Su uku ne kadai aciki. Daga manyan dattawan biyu sai shi sarki Salman, Shi wanda ke kan kujerar zaman sarki ya harde kafa yana dudduba ipad din hannun sa. Sarki salmaan na tsakure a gaban wanda ke zaune akan kujerar. Dayan kuma yana zaune a d’aya daga cikin royal chairs din fadar. Dukkanin su kowanne yasha rawani. Daka gansu kasan sudin jinin sarauta ne kuma masu ji da kambun mulki.

“Ya akai hakan ta faru......?!”

Shiru sarki Salmaan yai kawai kansa a kasa, Na kan kujerar sarkin ya sake buga hannun kujerar da yake Kai yana taune lebe,

“Salmanu ba magana nake maka ba..?”

“Kawu I’ve no idea... Kawai nasan mutane na bukatan abinci shysa nace a kwashe a raba musu.”

Ya karasa fada yana mai gyara zaman gilashin dake saqale a idanun sa.

Dogon tsaki dayan yaja yana karkada kafa,

“Kar mu sake jin kwatankwacin haka, Shin ya zancen zuwa gidan gwamnati nemo wannan tallafin?”

“Munyi magana na tura waziri yace za’a samu.”

“Ka dai kara pushing wannan karan banda wasa.”

Sarki salman bai amsa ba ya kalli gefe kawai yana taune leben sa,

“Sai ana maka magana ka tsiri wani cin fuska, Wai Kai sarki ko? Sannu sarki... Kar ka kai mu ma’kura wallahi. Kuma ba zeyi wu har mu muna maka magana kana saqale da wannan shegen gilashin naka ba. Na kinubibi..”

Cewar na kan kujerar sarki. Mikewa yayi, Ya cilla ipad din akan cinyar sarki Salman.

“Gatanan nayi mailing united nation din suyi haku’ri ba zaka samu zuwa ba. Saboda mun gama magana da madaki watan gobe zaka tafi cyprus taron nan. Kana jina?”

Kansa ya daga musu kawai, Suka fuce. Yana jiyo sanda bafadensa na kofa yake musu kirari,

“Takarwar ku lapia.. A sauka lapia Galadiman Basannabas da Wamban Basannabas.. Sarkin kofa na gaisuwa da fatan alkhairi.”

Silalewa sarki Salman yai yai zaman dab’aro awajen yana dafe kansa dake masa barazanar fadowa,

“Ya Allah!....”

Komawa yai kan kujerar sa ya zauna, Cikin haka jakadiyar sa mai suna Abu (Zainab) ta shigo tana rissina masa,

“Allah ya karawa sarki lapia.. Za’a yiwa wani iso ne? Naga masu jiran nada yawa a zaure na biyu.”

Hannu ya d’aga mata kawai.. Da baya da baya ta juya har takai k’ofa ya danyi gyaran murya ta juyo,

“Ina..... Alhassan? (Amintaccen bafaden sa)”

“Allah yaja da zamanin Sarkin Basannabas, Shima yana cikin masu jiran.”

“To a masa iso..”

“Allah ya Kara maka lapia da kwanciyar hankali. Yanzu kuwa.”

Ficewa tayi da sauri. Cikin mintina k’alilan bafaden ya shigo bayan Sarkin kofa yayi shelar zuwan sa,

Yana shigowa ya zube yana kwasar gaisuwa, Maganganu su kai ba masu tsawo ba, Naga bafaden ya fice da Sauri, Shi kuma sarki salmaan ya lumshe idanu kawai, Kafin jakadiya ta sake dawowa tayiwa wasu mutanen iso...

*DR ISMA’EL MUHAMMAD SINGA RES*

Zaune Dr/Alh. Ismael yake, Gaban sa kuma wani babban Yaron sa ne (Abdul) dake rike da ma’adanar kudaden sa dake bankuna (banks) kasancewar bashi da ‘da namiji.

“Alhaji ba lefi gaskia cinikin wannan karon yafi kowanne, Sai dai b’angaren taliya ne aka samu akasi, Sun rage ingancinta, Shiyasa mutane suka dena siya Kwana biyu.”

“Masha Allah! Haka akeso. Eh itama munyi magana da Alhaji Sabitu zamu tura wakili can kamfanin domin susan yadda ake ciki ko kuwa..?”

“Hakan yayi Alhaji..”

Magana sosai suke yi, Mai gadi ya shiga doko sallama parlorn yana zura kansa ta kofa,

“Oga! Ana sallama da kai..”

“Waye?”

“Wani ne wai daga gidan sarki.”

“Toh! Shigo da su.”

“Ai mutum d’aya ne..”

“Eh ba lefi.”

Abdul ya mike da littafan gaban sa yana rissinawa alhajin.

“Alhaji ni zan wuce.. Sai gobe idan Allah ya kai mu!”

“Allah ya kai mu Abdul.. “

Fita abdul yayi, Bafaden sarki kuma ya shiga. Gaisawa su kayi cikin amintawa, Kafin Alhassan ya gyara zama domin shedawa Alhaji abinda ke tafe dashi,

“Ni suna na Alhassan, Babban bafaden sarki ne ni, Domin zuwa na na uku kenan, Bana samun ka sai yau, Na farko naje asibiti ban samu ganin ka ba, Na danyi bincike na gano inda kake a kasuwa, Nan ma ban same ka ba, Da tambaya na gano nan gidan ka..”

“Allah sarki an samu sabani kenan. Afuwan to”
Chapter 31 · 0% Book details