← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 114

Sashe 54

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan kuwa aka yi, Da yake Allah ya rubuta da alkalamin qudura, Sai sarki Aliyu salmanu ya karbi kambun mulki, Tare da daurin auren sa ga Sa’adatu wato yar sarkin kofar kudu. Babu yadda kowa ya iya haka aka sanya amarya a lalle aka kaita dakin ta na sunnah. Bayan auren sarki Aliyu Salmanu da amaryar sa Sa’adatu ‘karamar ya ta karshe ga d’aya daga cikin babban bawan sarki mai rasuwa, Wato (Sarki Salmanu). Mahaifin sabon sarki Aliyu. Sarkin kofar kudu. Wanda ke kula da zaurukan kofar kudu da farfajiyar bangaren kudu me suna Abdullahi. Wanda ake mai lakabi da sarkin kofa. Babban ruguntsumi ne ya tashi a lokacin da sarki Aliyu ya hau karagar mulki. Bangarori da dama suka rika sukar sarautar sa suna aibatar sa. Haka dai Allah ya kare shi da matar sa Sa’adatu. Bayan wata tara cif babu doriya Gimbiya Sa’adatu ta haife kyakkyawan danta kato TubarkAllah, Tamkar sarki Aliyu ne yayi kaki ya tofar. Dake itama bafulatana ce gaba da baya hakan yasa jaririn nasu zubin kyau tamkar dan larabawa. Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin sarki Aliyu. Inda aka sanya masa Salman Aliyu Salmanu(Sunana kakan sa). Babu wani sunan da ake Kiran sa bayan hakan, Saboda sarki yace ba Za’a boye masa suna ba. Sosai an kakkawo wa jariri Salman farmakin halaka shi, Amma dake Allah yasa da kwanan sa agaba babu abunda yasame shi sai kara girma ma da yake yana wayo.

Ganin sun kasa cin galaba ta nan, Sai suka sake dawo da maganar ai dole sarki Aliyu ya kara aure. Ba zai zauna da yar bayi ba. Babu yadda Sarki Aliyu ya iya tunda tsarin al’adar su haka ya tana da a dole ya bada kai aka sake aura masa mata har uku, Duk daga cikin ahalin dangin su.

Mata uku rigis aka sanya a lalle aka d’aura aure. Kowacce tana ji da kanta ita yar sarauta ce. Gashi duk ahalin tsatson su d’aya ne. Sai dai asamu nisan alaka. Amma dukkanin su y’ay’an manyan hakimai ne. Gimbiya Jaleelah yar waziri ce. Waziri dake bawa sarki Aliyu shawara, Sai Gimbiya Najawa yar Galadima, Sai Gimbiya Huwaila babbar ‘ya ga ciroma. Dukkan su a rana d’aya aka kai su d’akunan su bayan an daddaura auren. Ran sarki Aliyu sam bai so hakan ba. Shi gaba d’aya tun tasowar kuruciyar sa Sa’adatun sa yake so ita kadai.

Tun ada kinsan masarauta acikin ta babu abunda babu, Gaba d’aya rayuwar su aciki suke yin ta, Duk abunda zaku bukata na rayuwar duniya akwai aciki, Balle masarautar Basannabas tana da mashahuriyar girma, Gari guda ce. komai akwai acikin ta, Toh idan sarki Aliyu yaje makaranta ya dawo ya kan tsaya a bakin kofar kudu yana kallon Sa'adatu dake taya mahaifinta jiran kofa, A lokacin tana kankanuwa, bata san wanne irin Kallo sarki Aliyu yake mata ba, Tun yana buya a bayan zaure yana kallon su, Har ta kai yakan tsaya daga nesa yana kallon Sa’adatu tana y'an wasanninta. Har ta kai Sarkin kofa Abdullahi ya ganshi, Ya gaishe shi ya fara tambayar sa matsalar sa. Tun sarkin kofa na kokarin hana Sarki Aliyu har ya hak’ura ya dena, ganin sha’kuwar da ta shiga tsakanin Aliyun da Sa’adatun sa. Tun Kan Sa’adatu ta mallaki hankalin ta hartazo ta mallaka Sarki Aliyu ya koya mata sonsa, Sarkin k’ofa da ya riga yasan al’adun masarautar basa auren bare sai jinin su, Hakan yasa ya dinga tausar Aliyun yana kokarin janye shi daga zuwa wajen Sa’adatun. Amma fafur Aliyu ya’ki. Haka sarkin kofa ya ha’kura ya zura musu ido kawai. Har Aliyu ya kare secondary alokacin ya nemawa Sa’adatu itama ta fara karatun. Shi kuma ya tafi waje karo karatu bayan ya bawa Sarkin kofa amanar Sa’adatun sa. Kuma duk wuya duk rintsi zai aureta Idan ya dawo babu fashi. Hakan kuwa aka yi bayan shekarun daya d’auka awaje yana karatu ya dawo ya tarar da Sa’adatun sa itama ta kare sakandire. Yaso auren ta alokacin sai kuma mahaifin sa sarkin lokacin Wato marigayi sarki Salmanu Ibrahim yayana kenan da muke uba d’aya da shi, Sai ya sake tura shi nahiyar ketare yin wani kasuwanci. Bai dawo ba sai da aka kira shi aka sanar masa rashin lapiar sarki Salmanu. Bayan dawowar sa gida ba jimawa sarki ya cika. Daga nan aka fara shrye shiryen nadashi sarauta, A nanne rabuwar kawuna ta sake barkewa ganin zai auro musu yar bayi. Gashi kowanne bangare daga bangare biyun jiran gadon sarautar suke yi. Wato yankin tsatson Marigayi Durbin Jirgau dana Marigayi Masekiri Jirgau. Kowanne bangare ya cancanta ya karbi kambun mulki. Sai dai bangaren tsatson marigayi Ilyasu Jirgau sune suka fi cancanta domin sune suka kara farfad’o da masarautar Basannabas, ance a bangaren tsarin izzar sarauta Marigayi Sarki Ilyasu Jirgau tafi karko,

Ya kasance kasaitaccen Sarki mayaki, kuma masanin gudanar da mulki wato a turance ‘intellectual administrative leader‘. Yayi yake-yake daban-daban wajen ganin ya tabbatar da girman kasa da sarautar Basannabas da ikon ta. Don haka ne ma girman Basannabas ya kasaita. Daga Yamma tun daga iyaka da garin bullo inda masarautar bullo take, zuwa kauyen durbi a gabas. Sannan daga iyaka Kazaure a arewa zuwa yankunan duwatsun jigawa a iyaka da garuruwan Birom a Kudu duk sun kasance fadin ikon Masarautar Basannabas.

A bangaren tsarin izzar sarauta da kuma nadin hakimci, Marigayi Sarki Ilyasu ya bada gudun mawa. Don a lokacin sa ne ya sake fito da mukamai guda biyu a kasa wanda a turance ake kira da ‘district heads’ da kuma marasa kasa wato a turance ‘title holders’. Don haka ne, tun daga wannan kirkirar gundumomin hakimai Masarautar Basannabas ta kasance ta kunshi gundumomin hakimai masu yawa. Kuma alokacin sa ne yaso talakawa sosai, Ya ‘yanta bayi, Ya kuma fito da tsare tsare na zaman fada. A tsarin Sarautar Basannabas, Majalisar Fadar Masarautar Barnabas ta kasance karkashin Sarkin Basannabas, wanda yake shugabantar zamanta.

A tsarin Fadar Basannabas, akan gudanar da ayyuka kamar fadanci; akan yi fadanci don karbar gaisuwa da kuma saduwa da baki, abokai, da yan uwa da makamantan su. Sosai talakawa da jama’ar gari a lokacin sunyi maraba da wannan Sabon tsari na marigayi sarki Ilyasu. A zaman fadar da akeyi sarki Ilyasu ko wazirin sa lokacin sun kasance masu sauraron koke koke na al’umma, Da sulhunta husuma Idan ta taso. Kai wani lokacin ma har wasa da dariya ake yi. Sam marigayi sarki Ilyasu ba shida girman Kai ko dagawa irin na wasu sarakunan. Shi yasa yanayin sarautar da yayi ya dora Yayan sa suma suka dora Yayan su akan akidar sa. Har gobe mutanen Basannabas sunfi son jinin marigayi Ilyasu suyi ta karbar ragamar sarautar Basannabas. Hakan kuwa ba karamin sake janyo ruguntsumi yake ba tsakanin ahalin marigayi Ilyasu da ahalin marigayi Masekiri Jirgau da kuma marigayi durbin jirgau.

Alokacin da marigayi sarki Ilyasu ya k’ara bud’a hakimci da nadin sarautun gargajiya a masarautar Basannabas, Sai ya raba gaba d’aya rabin mukaman daya sake nad’awa har ‘ya'yan ’yen uwan sa ya dauka ya babbawa sarauta, Sai ya zamto alokacin dan sa kwaya d’aya ya bawa sarauta. Gaba d’aya muk’aman guda shida ya raba su kaso biyu. Kashi d’aya na farko ya bawa tsatson marigayi durbin jirgau mukamai guda uku: Madakin Basannabas, Makaman Basannabas da Sarkin dawaki mai tuta wato hakimin waje. Sai bangaren marigayi Masekiri Jirgau wanda nasu suka kunshi: Wamban Basannabas, Da shamakin Basannabas sai Dan rimin Basannabas. Hakimci d’aya da ya rage kuma alokacin sai ya bawa jikan sa wato marigayi Ibrahim, Mahaifin marigayi salmanu baban sarki Aliyu mahaifin Salman. lokacin da marigayi Ilyasu Jirgau yai wadannan nade-nade Sosai ya fuskanci matsaloli ta fuska da dama. Domin har asiri sai da aka jefe shi da shi ya zamto baya zuwa fada sai dai waziri ne kadai ke gudanar da komai, Amma da yake shi din namijin duniya ne da baya wasa da karfin addu'a, Sai ya tashi tsaye yayi yaki da makiya har yaci galaba akan su, Sihirin jikin nasa ya karye ya cigaba da gudanar da abubuwan sarauta. Hakan ba karamin sake girgiza masharranta da mahassada yayi ba ganin ya dawo garau dashi bai lalace ba kamar yadda sukai zato. Sosai marigayi sarki Ilyasu ya zage k’aimi wajen kara karfafa sarautar Basannabas. Ya zamto a kullum sai anyi saukar qur’ani safe, rana, yamma da dare. Ya Kara yawaitar ranakun sadaqa. Ya sake ‘yanta bayi baki d’aya. Har wa’adin sa ya kare Allah ya d’auki ransa makiya basu sake cin galaba akan sa ba.

Toh bayan Sarki Aliyu ya hau karagar mulki da temakon sarkin bullo sarki Ibrahim hashimu da shekaru uku. Alokacin Salman na karami. Sai sarkin bullo (Ibrahim Hashimu) ya ziyarci masarautar Basannabas da tulin kayayyaki, Tun da ga kan kayan abinci, Dokuna kosassu da makaman yaki. Turaman sawa dana jariri. Kaya himili guda yazo dasu Basannabas, Bai kuma bar Basannabas ba sai da su kai zaman sirri shi da sarki Aliyu babu wanda yasan abunda suka tattauna. Amman dai mutane da dama sun fassara zuwan sarki Ibrahim Hashimu ba zuwan alkhairi bane, Domin kafin sarki Aliyu ya zauna zaman sirri da sarki Ibrahim Hashimu ance fuskar sa a sake take yana walwala, Amman bayan ya fito daga ciki sai akaga fuskar sa ta sauya zuwa bacin rai, Shi kuma sarki Ibrahim Hashimu ya koma masarautar sa fuskar sa cike da annushuwa.

••++. ••++. ••++. ••++..
Chapter 54 · 0% Book details