← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 114

Sashe 11

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin k’ada kai nayi alamun Eh. Na bi bayan sa da sauri, Yana ta fadan abu da wani yare, Da alamun dai zagi na yake yi. Oho masa dai. Canmakadus-dus! Karatu ne dai sai an yi hi ba fashi. Ajin mu ya kai ni. Yara suka hau tafi. Na sake buda hanci ina daddaga musu hannu. Can gefen taga ya nunamin benchi yace na zauna. Ina zama ya tayar dani Wai nafi cikakken sunana dana baba na.

“Da farko dai: Baba na na kira na da Ummi na, Saboda kasancewar sunan mahaifiyar sa da naci. Matar baba na na kira na da Dije itada wasu tsirarrun mutane a karkarar mu. Mafi yawancin yan karkarar mu na kira na da Dijengala ko Ta mai gari. Kawaye na da matasan karkarar mu na min laqabi da Dije Oganniya. S..”

“Ya isa Malama dakata. Sai zuba kike uwa’yayan kanya. Bush girl. Sunan ki fa kawai na tambaya dana baban ki zansa a register.”

“Yo ai da kayi hak’uri su dinma zaka ji ai ko? Duk sunaye na ne wanda na fada..”

“Ke wai bakisan me kike bane? Toh Malama sunan ki na yanka d’aya zaki gayamin dana baban ki.”

“Toh ai Baffa nama sunan sa biyu dan kaji ehe.”

Wani uban tsaki Malam auwal yaja, Ya furzar da iskar bakin sa kafin ya sake duba na kamar yaga kahi.

“Wallahi zan kore ki daga makarantar nan.”

“A hayye sama lubaye! Sede in mutuwa nayi hine zandena zuwa Malam. Amma yadda kowanne yaro da yarinya yake ajin nan du matsayin mu d’aya. Mai gari ne yakarb’o tallafi awajen hakimi, Shima hakimi daga wajen sarki na birni ya samo. Shima sarkin daga wajen hyugaban kasa. Dan kaji inada matsayi kamar kowa ehe.”

Malam Auwal ya girgiza kai kawai kafin ya sake cewa,

“Illiteracy is a disease! Menene sunan ki na ainihi dana baban ki?”

“Sunan da Baffa na ya radamin Nana Khadija ne. Baffa na sunan sa biyu. Alquranin Ubangiji bazan fadi na gaskiyar sa ba ai rahin kunya ne.”

“Zauna kawai..”

Malam auwal ya fada yana dafe goshin sa, Sunan ta ya rubuta a register da ‘Nana Khadija Baffah.’ ya rufe register ransa a matukar b’ace yake koya musu darussan har aka kada kararrawar fita break. Ana futa na kwasa a guje nayi wajen Malama Mardiyya ina haki.

“Malama ga ni.”

“Sannun ki Khadija.. Hakin me kike? Ko gudu ki kai? Ki dena ba’asan yawan haki. Babu ma dacewa ‘ya mace ta rika zunduma gudu kinji?”

Kada kai nayi kawai na tsugunna a kasa.

“Khadija ina maman ki?”

Tana fadar haka, Kwakwalwata ta shiga tariyo min sanda Ummah na ta rasu, Da wayo na lokacin. Domin har yanzu ina iya tariyo sanda ta rasu. K’asan d’ankwali na nasa na goge hawaye na dake yar tsere kafin nace,

“Malama mahaifiya ta Allah ya mata rasuwa shekarun baya.”

“Allahu Akbar! Allah ya jikan ta da Rahama, Kiyi hak’uri Khadija bansani ba, Da bazan taso miki da radadin ciwon rashin ta ba.”

Saurin girgiza kai na nayi kafin na sake cewa,

“Malama a har kullum ina fad’awa zucia ta me so na shine zai tambayi wane irin hali na ke ciki. Wadda tambaya ta farko kuma mahaifiya ta Za’a tambaya. Shin tana raye ko akasin haka?.”

“Hakane. Toh Allah ya baku hakurin rashin ta. Yanayin ki yasa na kasa samun nutsuwa a zucia ta Khadija. Shin meke faruwa dake? Menene labarin ki Khadija...?”

K’atuwar bahaguwar zuciya na sauke, Kafin na gyara tsugunnen da nayi na fara cewa,

*TUNA BAYA....*

..
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_ZAFAFA 5 (2021) NA KUDI NE, DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHIN NERA 700 KACAL! KA/KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SIYA DA KUDIN KI KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI, KA/KI/KU GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU SIYARWAR!!! DOMIN SIYAN NAKI TUNTUBI: +234 903 318 1070 KO +234 903 234 5899, AKWAI ‘KARUWA SOSAI ACIKIN WADAN NAN LITTATTAFAN😍MUNA FARIN CIKIN KASANCEWAR KU A TATTARE DAMU😘 MASOYAN MU ABUN ALFAHARIN MU🙌🏻_

_*KIBIYAR AJALI..!!!*_
_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_
🥰❤️👑🏹

_(PAID STORIES/ZAFAFA 5 BOOKS DIN KUDI NE..)_

_*MALLAKAR: NANA HAFSAT_*
_(MISS XOXO)🧕🏼_

_*BABI NA: 6_*

_*TUNA BAYA...!_*

****Malam Basheer (Bashari) Inuwa na Alkali, Shine cikakken sunan mahafi na, Kuma karkarar Durbun itace tushen su, Anan aka haifi kaka na marigayi Malam Inuwa na Alkali, ance aminin marigayi alkali ne, Mutumi na farko a karkarar mu daya je birni yayo karatu ya zama alkali. Mahaifi na Malam Bashari shi kadai ne ‘da awajen iyayen sa, Baffan mu yace sauran yan uwan sa da anhaife su suke rasuwa, Shi kadai ne awajen iyayen sa. Mahaifiyar sa fulanin karkarar Gandar ce. Gaba da baya mahaifi na bashi da yan uwa, Domin mahaifiyar shi dama kafin rasuwar ta irin fulanin tashin nan ne. Toh bayan ta auri kakana ma’ana mahaifin Baba na sai yan uwanta suka tashi daga karkarar Durbun suka koma wani k’auyen.

Mahaifin sa kuwa dama ya manyan ta, Bai da wasu sauran yan uwa, Sai kanwar baban sa, Ita kadai ce tayi ragowa tana can cikin kauyen nan wajajen rijiyar badamasi, Kuma ta manyanta ko gani bata yi sosai.

Baffan mu yace ya hadu da Umma ta ne a birnin, Acan gefen gari suke. Yace hakika Umma ta tafuto daga tsatson babban gida, Domin gida ne na malaman addinin musulunci, Domin har makarantar islamiyya suke da ita a kofar gidan. Ba dai masu arziki bane, Amma suna da wadatar zuci. Yayan mamana yana da makarantar allo ta almajirai. Shi dai Baffa na abunda ya kai shi birni alokacin neman kudi yaje, Ya fara sana’ar wankau, Daga nan ya dena ya koma sana’ar gini. Inda yake leburanci yana debewa ma’aikatan dake gini ‘kasa da kuma ruwa. A rijiyar gidan su Umman mu yake debo ruwa, Kasancewar akwai samari a layin, Sai ya zamto Baffan mu ya fara wanke takalma (shoe shiner) Yakan wanke musu takalman su ya kuma goge musu har da dinke wa. Har Allah ya hada jinin su da Yayan Ummah ta, Suka fara abota. Ta sanadiyyar yayan umma ta, Baffa yasan Umma. Inda suka fara zumunci na yaya da kanwa, Domin abotar su da yayan umma ta ta kara kulluwa sun zama aminai.

Umma ta tafara boko har aji biyar, Bata gama ba suka fara soyayya da Baffa na. Baffa ya nemi auren ta aka bashi. Ya kasance Baffa yace da yazowa da yan uwa da yan karkarar nan maganar auren sa sai suka soki zancen, Kan ya za’ai ya auro yar boko? Bayan ba bokon yai ba? Kuma yar birni masu abun kunya. Baffa ya toshe kunnuwan sa da surutan mutane yai biris da zancen su. Ya auro Umma na suka dawo nan Durbun da zama. Baffa yace sam bata kyamace shi ba ba kuma ta kyamaci yan kauyen nan ba. Suka zauna cikin lumana da kaunar juna, Kafin ta haife ni ta haifi har jarirai uku duk suka rasu, D’aya kuma bai zo da rai ba. Sai daga baya Allah ya azurta ta da samun ciki na, Baffa yace tasha wahalar ciki na, Domin Sai da suka yita zuwa birni a asibiti ana kara mata jini. Allah yasa ta haife ni lapia. Kuma tunda ta haife ni, Shikenan tayi sallama da lapiar ta, Yau tana Lapia gobe tana gadon asibiti. Ina shekara shida Allah ya mata rasuwa..

Malama Mardiyya ta zare tagumin da tayi tana matsar hawaye, Nima hawayen nake. Na Kasa cigaba Sai da Malama Mardiyya ta sake tambayata cewar,

“Kiyi hak’uri Khadija, Allah ya jikan Umman ki da rahama, Allah ya dubi maraicin ki ya baki miji nagari. Yanzu yan uwan mahaifiyar ki suna ina? Shin ba sunan halin da kike ciki bane? Ko dama can mahaifin ki nada wata matar?”

Saurin girgiza kai nayi, Na fyato kakkaurar majina na katse da wani kara a gefen kafar Malama Mardiyya kafin na cigaba da cewa,

“Yan uwan Umma ta na can birni, Kuma duk maza ne Ita kadai ce mace a dakin su, Bayan tayi aure Baffa yace iyayen ta sun rasu daga baya kafin a haife ni. Amma su hudu ne a wajen iyayen su, Maza uku, Mace d’aya, Ita kenan. Akwai Kawu Hashim, Kawu Kabiru, Da Kawu Isma’el, Sai ita Umma ta mai suna Jamila. Sun taba zuwa su duka ukun da wata sallah, Suka bani kudi da yawa da kaya, Lokacin Baffa na ya auro Gajiyalle walle ta kwace komai. Kinsan fa Baffa na tsoron ta yake wallahi, “Yan uwan mahaifiya ta gaba ki dayan su ba wuri d’aya suke zaune ba, kowanne yana wani gari shi da iyalin sa, Shi Kawu Isma’el shi kadai ne a birni inda kuka zo, Sai Kawu Hashim shi yana garin legas, Sai Kawu Kabiru Shi kuma yana garin Jos. Duk kanin su kowanne a tare yake da iyalin sa, Kowanne da irin aikin sa, Domin Kawu Hashim shi malamin makaranta ne bangaren arabi a jami’ar Legas. Sai Kawu Kabiru shi ma babban malamin sunnah ne yana kuma da makarantar kansa a garin na Jos,

“Sai Kawu Isma’el shi yana Birni. Kuma Baffa yace min babban dan kasuwa ne shi da ake ji da shi a birnin. Wallahi da suna kula da ni fushi sukai daga baya. Sunce Baffa ya bar musu ni yaki. Kuma yazo ya auro Gajiyalle da wayo na sunzo ta musu rashin mutinci har ta juyewa kawu Isma’el ruwan randa a kayan sa. Shine tun daga lokacin ba su sake zuwa ba. Amman nace idan na zama babba walle sai naje birni wajen kawunni na..”

Malama Mardiyya ta kada kai kafin ta sake cewa,

“Yaushe aka auro Gajiyallen?..”
Chapter 11 · 0% Book details