Sashe 44
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.
______________________
_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, AMANA CE A HANNUN DUK WANDA YA SIYA, NEMI NAMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFIN DOMIN MALLAKAR NAKI, KI GUJI KARANTA NA BATI.. DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU RUBUTAWAR..._
_*KIBIYAR AJALI......*_
_(SULKE BAYA TARE TA SAI TA WUCE)🏹🥰_
*2___3*
*KHADIJAA*
*Kukan* rabuwa da Mas'oud da nake yi ashe ba komai bane sai da naji ance Sarki Salman shine miji na, A take na yanke jiki na sume ban sake sanin inda kai na yake ba. Haka yake a bangaran Mami, tana jin wanda aka aura min itama ta yanke jiki ta fadi, ganin mu biyu abun ya faru, sai ba ayi tunanin bakin cikin darajar wanda na aura shine yasa Mami suma ba, aka dinga cewa ai mayya ce ta kama mu, wasu suce jefa aka yi mana ni da ita. Aka dinga bamu taimako har Allah yasa Mami ta dawo cikin hayyacin ta, ta tambaya waye mijin nawa suka tabbatar mata cewar sarkin Basannabas.
Amman Alhaji ya Munafince ta da gaske, shi yanzu saboda tsabar rashin tunani ya bar ya'yan cikin sa ya dauki yar kauye wacce iyayenta basu bar mata gadon komai ba ya bawa sarki guda. Anya akwai miji irin nata kuwa marar lissafi idan ba na dukiya ba? Ban da haka ya zai yi wannan shirmin sai kace wanda aka cewa jeka ka gani. Shikenan aikin gama ya riga ya gama tunda har an riga an daura babu yadda za ta yi, Dije tayi sa'a sauran su Shukrah wanda take hango musu matsayin matan shugabanin kasashen waje ko na cikin gida Nijeriya.
*SAS*
Sarki Salman kuwa ana gama daurawa ya tattara suka tafi, Bai yadda ma sun koma masarauta ba yace a kai shi airport zai jira lokacin tafiyar shi ya yi. Kamar ya sani dan da ya koma da yaga abin da ya ragowa kansa, saboda su Galadima sun sanarwa su Gimbiya Shaheedah zancen auran tana can tana haukan kuke koke da zage-zage tare da cewa sai yasan yaci amanar ta, ya Munafince ta ya yo mata kishiya kuma yar matsiya ta. Labari ya kuma zuwar musu cewar ai ba zai dawo ba ya wuce Cyprus. Koda su ga kai shi guri na musamman aka bashi ya zauna dan jiran lokacin tafiyar, mulkin kuma ya barshi a hannun waziri duk kuwa da yaso su tafi tare amman Salman d'in ya ce aka ya yarda dashi shi yasa yace ya koma ya rike masarautar kafin ya dawo.
Yana zaune ya rasa yadda zai yi saboda Alhaji Isma'il ya tambaye shi a wane muhalli zai ajiye Khadija saboda suna son aje a shirya gurin, yace masa zai kira shi a waya idan ya gama shawara. Da wa zai yi shawarar ma oho masa. Wani tunani yazo masa sai ya kirawo bafadansa da ke yi masa wasu abubuwan masu muhimmanci wanda be son kowa yaji, yana can bakin kofar da yake saboda tare zasu. Ya shiga tare da dukawa har kara ya yi gaisuwa tare da yin shiru yana jiran umarni.
“Ka kira mahaifin yarinyar nan kace idan sunje a nuna musu bangaran Abdullah, idan an nuna musu nan zasu kai ta har na dawo.”
“Takawarka lafiya sarkin mu mai share hawayen mu. Aiki ya gamu da ikon Allah, gaba salamun baya salamun d'an toron giwa.”
Al-hassan bafade ya fada yana mai ficewa daga cikin dakin.
Yana fita ya kira lambar Alhaji Isma'il tana ta ringing amman be daga ba, ya yi tunanin kila yana cikin mutane dan shi kansa Al-hassan yaga yadda yan kasuwa suka cika gurin daurin auran, sai da aka dan jima ya sake kira sannan yaji ya dauka, suka gaisa ya sanar dashi sakon sarki Salman. Da farin ciki Alhaji Isma'il ya amsa sannan yaje ya gayawa su Mami cewar azo aje a gyara bangaran da za'a kai Dije. Aikuwa sai ta je itama kodan taga me zai faru, daman kuma ba shiga masarautar ta taba yi ba yau gashi ta sanadin Dije zata shiga son ranta.
*KHADIJAA*
Ni kuwa sai da ta kai ta kawo an saka min drip, kawu daddy sai addu'a yake Allah yasa na samu sauki a kai ni gida na kamar yadda ya yi alkawari, ba ya san a samu matsala shi yasa da ya fita zai dawo yace ya jikin nawa. Allah sarki Mas'oud abin kauna ta, an raba ni dashi a lokacin da zuciyata ta makance akan shi. Tabbas nasan zan rayu ne cikin kunci da zama da makiyi, ba wai nafi karfin auran sarki Salman ba. A a kawai zuciya ta bashi take so ba, na kuma san akwai wata manufa da ya sanya shi auran ta, ban da haka me yasa lokacin da ta karaci kwanciya a asibiti be taba zuwa ya duba ta ba sai da ta warke sannan ya turo dan munafunci wai a duba ta.
Ai kuwa tun kayan da nasa da safe ban cire ba, Babu yadda ba’a yi dani ba akan na canza amman naki dan banga dalilin yin kwalliyar ba. Aisha ma tun tana jin haushin naki canza kaya har ta dawo tana lallashi na akan auran dan ita kanta ta yarda da cewa Mas'oud shine buri na, amman babu yadda zanyi kaddara ta riga fata. Ta kuma yi min murna cewa matarsa daya ni ce ta biyu, amman nasan ai zai karo biyu tunda sarakuna baka raba su da aure-aure. Amman da Mas'oud ne nasan sai mutuwa nida shi babu kishiya.
••<>••. ••<>••.
Yan tafiya gidan jere suka tafi kusan mota uku saboda kowa yana son zuwa ya ganewa idanunsa. Na kuma fashewa da kuka tabbas zanje gidan can tunda gashi har an tafi shirya min kaya na a can, wayyo Allah, sai naji har gwara zama wajan Gajiyalle da auran nan da za ayi amfani da ni wajan cin mutunci.
*MASARAUTAR BASANNABAS..*
Lokacin da su Mami suka shiga masarauta daman waziri yasan da zuwan nasu hakan yasa basu sha wahala ba gurin shiga cikin gidan. Nan suka tambayi sashen da za a sanya amarya, waziri yasa aka nuna musu wani waje can kusa da sashen Gimbiya Sa'adatu wato mahaifiyar sarki Salman, wacce ba ta san wainar da ake toyawa ba a masarautar, kasan cewar tana zaune ta tashi da wata irin ciwon kafa (muscle spasm) ta yadda ko tashi ba ta iya yi. Matar kawu Hashim ce ta fara bude kofar tayi bismillah tare da kallon kowa da suka zo tace suma suyi sannan su shiga. Haka suka dinga yi har suka shige cikin sashen masu guda nayi masu hotuna suna yi masu fara shirya-shiryan gurin suma duk sun fara.
Gurin ba laifi babba ne, sai dai be kai gurin sauran matayen ba kasan cewar daman an yi shi ne dan yarima Abdul kuma ba a nan yake zaune ba shi yasa aka bawa Dije shi. Suna cikin aiki sai ga gimbiya Jaleela tare da bayin ta masu take mata baya. Babu ko sallama haka ta shigo tana kallon su one by one daga bisani kuma ta tabe baki sai faman hura hanci take yi, su kuma duk sun dauka cewa uwar gidan sarki Salman ce.
“Wacece gwaggon amarya?”
Aka fara kallon kallo ko wacce jira take ace itace, sai kuma matar kawu Kabiru tace.
“Ko wacce a nan akwai matsayin ta, amman ga marikiyarta wacce ta rai ne ta har zuwa yau.”
Suka nuna Mami wacce itama saboda mulki wai ita matar babban d'an kasuwa. Gimbiya Jaleela ta kare mata kallo tas, ganin babu abin da zata yi mata gori dashi sai ta rausayar da kai.
“Ya yi kyau uwar amarya, muna fatan dai kun shirya mana ita sosai.?”
Itama Mami sai da ta sha kamshi tamkar ba zata ce komai ba sai suka ji tace.
“Sai ma ta shigo zaku tabbatar da hakan. Shin maman sa ce ke?”
Gimbiya Jaleela ta cije lebe ganin da ta yi ba ta da tsoro kenan.
“Eh tamkar uwa nake a gareshi, amman dai zaku sani nan gaba.”
“Shikenan ranki ya dade, Allah ya nuna mana lokacin.”
Juyawa gimbiya Jaleela tayi ta nufi sashen gimbiya Najwa, a can duk ta same su zazzauna sun zabga tagumi da alama ita suke jira daman. Guri ta samu ta zauna itama tare da jan numfashi ta sauke da karfi tana cewa.
“Ashe ma yar riko ce, shi kuwa yaron nan a gidan waye ya ganta?”
“Yanzu dai kin makala man a jikin wani abun na ta ko kuwa?” Gimbiya Huwaila ta tambaya cike da zakuwa.
“Na makale shi a jikin one seater d'in parlorn.”
“Good job Jaleela, yanzu sauran na kofar dakin, shi kuma sai da yamma idan Allah ya kai mu. Zanje nasa shi kamar yadda Abba Galadima yace.” Cewar Najwa tana tsuke baki.
“Bamu san abin da zai faru ba kenan wallahi, da duk ba zama mu bari ta shigo cikin gidan nan lafiya ba ma. Salman ya ci ka marar mutunci wallahi, ace har kana ta shirye-shiryen aure amman baka sanar da kowa ba sai a ranar dan tsabar wulakanci? Amman babu komai zai gane duk wannan abun nashi babu inda zai kai shi. Shaheeda ki dena kukan nan haka, kinji dai abin da Baba ciroma yace, sai ya gwammace beyi wannan auran munafincin ba.” Najwa ta yi maganar cike da tsantsar takaici.