← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 114

Sashe 26

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalaman ta na karshe ce tasa kirjina bugawa, nayi saurin dafewa ina fito da idanuwa. Ban taba tunanin duk irin wulakancin da zasu yi min zai kai ga yi min sharri irin wannan ba, tabbas wannan mugun sharri ne dan ko a school bani da abokai maza bare yanzu da nake da wanda zuciya ta ke so.

“Ya Shukrah ni nake bin maza?”

“Oh! Zan miki sharri ne? Har driver daddy ya baki amman kika hana shi zuwa daukar ki sai wani Kato ne ya dawo dake.”

Jiki na ya yi mugun sanyi hankali na ya tashi, yanzu kallon da zasu yi min kenan? Sufa duk suna da motocinsu, kuma babu kalar mutanan da basa dauka a ciki, sai ni daga yi sau daya shine zasu ce ina bin maza saboda kawai basa ganin mutunci da daraja ta. Hawaye suka fara kokarin zubo min nayi saurin mayar dasu ina kakalo murmushi wanda aka ce yafi kukan cewo nace mata.

“Wallahi ban taba bin wani namiji ba, idan kika dauke driver na gidan nan. Sannan bana muku fatan irin wannan abun bare ni kai na Ya Shukrah, dan Allah ku dinga yi min kyakkyawar fahimta da kuma hangen alkairi a tattare dani. Wannan da kika ga ya kawo ni gida, shine wanda muka kulla alkawarin aure a tsakanin mu, kuma insha Allahu zamu mallaki junan mu kamar yadda muke mafarki kullum.”

Sai kawai ta waigo tare da sakin wata banzar dariya, irin wadda kana ji kansan ta mugunta ce kawai.

“Kice ku a yan iskan ma lamba d'aya ne? Wato har mafarki kuke yi gaku akan jun.....”

Ban bari ta karasa ba saboda jin kalar sharrin da zata kuma yi mana, rai na yana zafi zuciya ta tana kuna nace da ita.

“Nagode nasan me zaki fada Ya Shukrah, bari naje na gyara mata dakin.”

Nasa hijabi naje zan wuce ta gefenta, tasa hannu ta janyo ni nayi baya har na kusa faduwa Allah ya taimakeni na dafe madubi.

“Ni zaki nunawa ba ki damu da abinda nake fada ba? Kin yi kadan yarinya, wallahi sai nayi miki shegen duka a cikin gidan nan, sakarai kawai.”

Duk da ina jin zuciya ta na zugi tana tunzura ni akan cewa na yi mata abinda zai sa ba zata kara koda gigin yi min magana ba, sai dai na daure taci albarkacin mahaifinta da wallahi sai na nuna mata wacece Dije Oganniya yar Baffan ta. Na kuma tashi na yi ficewa ta sai ta biyo ni tana ta min masifa har na shiga cikin bedroom din Mami. Ita kuma ta juya ta wuce dakin su, na kalli madubi ina hawaye, wai yau ni Khadija ake yiwa sharrin bin maza. Koda ina karama ina cikin duhun kai da jahilci ban bi maza ba bare yanzu da nasan mutuncin kai na. Cigaba nayi da gyara gadon na share nayi mopping tare da kunna turaran wuta duk lokacin Mami ba ta shigo ba har na kammala na koma daki na a lokacin ne Mas'oud ya kira wayata, soyayyar da nake yi masa bata hanani duk yanayin da nake ciki sai na dauka.

“Oum Waleed wa waleeda, masoyiyata abar kaunata ya kike?”

Naja numfashi da kyar sannan na janyo dauriya dan kar ga gane yanayin da nake ciki na ce.

“Na'am abu Waleed da waleeda, uhmm wai kai kallo ma kake yi na jiyo karar tv?”

Yayi murmushi wanda idan naji ya yi sa yana kara min shaukin soyayyar shi.

“Uhmmm toh, tv d'in dai a kunne take, amman zuciya ta gabaki d'aya tana gareki mai sona kuma zabi na.”

“Nima haka wallahi, to wai yaushe zaka fara zuwa tadi ne gidan nan? Nifa na gaji da hirarar waya bana ganin fuskar ka.”

“Zan zo Oum Waleed, jira nake yi sai na fara yiwa mahaifina magana ya bani fili idan yaso sai nazo da ƙwari na gidan naku. Fata na kawai idan nazo Allah yasa Daddyn ku ya bani auranki, ina tsoran kar nazo ace ni ba tsarinki bane my love.”

Tamkar a gabansa nake haka na zaro idanuwa hannuwana dafe a saman kirjina, kafin nayi magana naji muryar Mami tana kira na. Cikin sauri na kallo bakin kofar tare da cewa Mas'oud ya kashe zanje na dawo. Doguwar riga na dauka na zura tare da fitowa ina yafa mayanfin rigar na tsaya a kusa da Mamin ina cewa.

“Gani Mami.”

“Ina system d'in da Alhaji ya siyo miki?”

“Tana gurin Mas'oud Mami zai saita min ita.”

“Ohhh! Har kinje kin bayar da ita ko? Ni zaki rainawa hankali Dije? Wato kinje kin siyar da ita baki san cewa za'a iya tuntubar ki inda take ba ko?”

Baki na yana ta rawa nake magana cike da tashin hankali.

“Wallahi Allah Mami ban siyar da ita ba, bari na dakko wayana kiji daga bakin Mas'oud d'in.”

“Rufe min baki, ni zaki yiwa Wayo? Kin dauka ban san irin dabarun nan naku na yan kauye ba? Duk irin abubuwan da kuke yi na san shi wallahi. Wato kin waye ko? Zaki ci duniyarki da tsinke a gidan arziki. Kizo kije ki dora abincin dare, su Jummai basa nan na basu hutu na kwanaki uku, duk aikin da suke yi kece zaki yi shi a gidan nan kinji na gaya miki ko?”

Zafafan hawaye suka zubo min, nasa bayan hannuna tare da gogewa. Ina ta daga kai alamun naji sannan ta juya ta koma parlor ta dauki remote ta kunna tv tare da zama ta dora kafa daya akan daya tana karkadawa. Ni kuma na juya na shiga kitchen ina kuka wanda na rasa ko na menene....
...
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_SAS...🥰😍🥂_

_14_

_NH_

Jollof d'in taliya na dafa, kasan cewar na yi ta bana cikin nutsuwa yasa ta d'an fara cabewa kadan. Na zuba cikin kula sannan na yi apple and pineapple juice nasa cikin freezer saboda sai an zauna akan table sannan ake fito dashi asha dan kar a ajiye ya huce. Dakina na koma na dauki wayata ina dubawa naga 6missed calls na Mas'oud sai 2missed calls na Aisha kawata da muka hadu a British English learning centre. Sai da na fara yin alwala nayi sallah sannan na kira Aisha muka gaisa tare da yin yar hira sannan na kira Mas'oud, yaki dagawa sai da ta katse sannan ya kira ni da kudin sa.

“Ni na isa na fara cin kudin Oum Waleeda tun kafin ta zo hannu na, salon tace abu Waleed ba shi da kirki son banza gareshi?” Ya yi maganar ta sigar tsokana.

“Ka cancanci ka fara cin kudin ne ai tun a yanzu, dan ka gane cewa lallai Oum Waleed mallakin ka ce da komai na ta.”

Ina jiyo sanda ya sauke katuwar numfashi yace.

“Gaskiya Allah yana sona gashi ya hadani da abar kauna mai tausayi na tun kafin ta zama a karkashin iko na. Madam ina kika shiga tun dazu daga cewa ina zuwa shikenan naji shiru?”

Nayi murmushi ina lumshe idanuwa.

“Mami ce ta sani aiki shi yasa kaji ni shiru.”

“Yayi kyau Oum Waleedah. Nasan ki akwai biyayya, Allah ya nuna min ke a cikin gida na ganki kina yi min tausa.”

Wata irin kunya ta mamaye ji tamkar ina gabansa haka na rintsa ido. Shi kuma ya dinga dariya saboda yasan dole kalamansa zasu sani cikin kunya. Jin na kasa yin magana ne ya sashi tsaida dariyar tashi yana cewa.

“Kunya kike ji wai?”

“Uhmm toh kai ma meye nayi min wannan maganar bayan kasan dole inji nauyinta.?”

“Tabdijan! Wai wannan yar maganar itace ta saki jin nauyi? Kice ma sam ba zaki iya dauka ta ba dan gaskiya ina da nauyi ki dena ganin bani da jiki wallahi. Gwarama ki zage damtse wajan shirya yadda zaki dauki nauyi na idan munyi aure.”

Tsabar tsagwaran kunyar da ya kuma sanya ni a ciki ne yasa ni katse wayar da muke yi na kifa kai na cikin pillow ina dariya mai cike da shaukin kaunarsa. Ji nayi kamar naje na ganshi da ido na, dan na hango yadda yake zaro min wadannan bayanan nashi da suke bani kunya. Ya sake kirana na dauka ina murmushi har hakorana suna fitowa a bayyane.

“Ya zaki kashe min kira bayan ni na kira madam? Gaskiya ki bari idan ba haka ba zanyo shirin bacci nazo gidan ku na kwana sai naga yadda zaki da wannan kunyar.”

“Kai! Lallai ma, kai yanzu sai kazo gidan nan da kayan bacci?”

“Tsab ma kuwa, ko na gwada miki dan ki tabbatar?”

“Lallai ma kai din nan.”

“Bafa ki bani amsa ba Oum Waleed kinsan ai dama ni Waleedah ita ce tawa idan mun haife so.”

“Haka dai kake cewa, amman ni ina ji a jiki na cewar Waleed zai fi Waleedah kyau, kar ka dawo daga baya kace na bar maka shi.” Ya sake sakin wata shu'umar dariyar tare da cewa.

“Toh mu jira mu gani ko madam? Yanzu dai ki gaya min na taho d'in na taya ki kwana? dan nasan ki da tsoro.”

Nayi saurin cewa.

“A'a gaskiya ni bani da wani tsoro ka ganni nan, dan babu inda bazan iya zuwa ba cikin dare.”

“Bafa irin wannan tsoran nake nufi ba, ina nufin na...”

Ban bari ya karasa ba nayi saurin cewa.

“Kawu sannu da zuwa.”
Chapter 26 · 0% Book details