Sashe 100
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ido na ne yakai kan jallabiyar da ya cire yanzu, Sai kawai na kwace jikina na ruga da gudu na dauki rigar tare da karawa. Shi kuma tsorata ya yi da gudun da nayi shi yasa be yi wani motsi ba sai da yaga ta zauna a bakin gado ya karasa wajan tare da durkusawa a gaban ta ya dora kai saman cinyarta yana magana cikin rauni da karyar da zuciya.
“Please baby dan Allah ki dena irin wannan gudun, ki lallaba min kanki da kuma babyn cikin ki. Ina son ku bana son na rasa ku a rayuwata kiyi min wannan alkawarin na kula da kanki please.”
Ba karamin tausayi ya bani ba, hakika nasan Salman yana matukar so na, kuma nima ba zan ce bana son sa ba saboda Iya kulawa da tarairaya yana bani Iya yinsa. Ban san lokacin da na dora hannu a saman sumarsa ba na shiga wargaza ta ina mikar da ita tsaye tana komawa saboda santsi da sumar ke dashi.
“Karka damu kaci gaba da yi min addu'a, ina tea dina?”
Saman bedside ya nuna min na hango cup d'in ba laifi yafi na dazu girma, saboda ya daga min cinya nasa riga yasa na shagwabe fuska ina cewa.
“Toh ka dakko min na sha.”
Ya dago kai ya kalle ni da idanunsa masu kama da ruwa a ciki.
“Yadda kika ce haka zanyi Gimbiya sarauniyar zuciyar Salman bin Aliy.”
Yana matsawa kuwa nayi saurin mikewa Ina zuwara yana waigowa. Dariya ya yi ganin yadda nake saurin saka rigar dan kar ya gani, ya matso yana cewa.
“Madam wane dare ne jemage be gani ba?”
Ina yatsina fuska nace.
“Ai kuwa be ga na mutuwarsa ba.”
“Wayyo dena ambato min mutuwa yanzu, ina son naga gudan jini na, ina son na nunawa duniya cewa komai lokaci ne dashi, mutum baya fidda rai da rabo.”
Tea dina na karba duk da ya fara hucewa a haka na shanye shi tas, na kalle shi yana ta shirinsa na fita fada nace.
“Naje sashe na saboda babu wanda yasan na dawo.”
“KI bari ki shirya ni mana my love.”
“Amfanin me zanyi ma wajan shiryawar tunda ba Iya nad'a rawani nayi ba?” Yana saka kayan sa na ciki yace.
“Idan Ina kallon ki zan fi samun nutsuwa har na shirya tsab.”
Babu yadda zan yi dole na koma bakin gado na zauna, Tunawa nayi da shifa beci komai ba, na mike na shiga hada masa coffee dan yafi son shi akan tea. Yana gani na ya shafa fuskata tare da cewa.
“Allah ya yi miki albarka dear.”
“Amin na gode.”
Cake din da ya kawo min ban ci ba shi na hada na bawa yaci sannan nayi masa sallama bayan ya sumbaci goshi na ya fita ni kuma na nufi sashe na da sauri dan karma wani ya zo ya ganni da rigar shi.
Ina zuwa sashe na kaya na nema na saka, hijabi na sanyi saboda gani nake kamar Ina fita za'a hango cewa ina dauke da juna biyu. Hankali na duk yana gurin Ammi, na fito, hadimaina suka ganni duk suka zube suna kwasar gaisuwa, zuciyoyon su cike da tambayoyi dan basu san ta kofar da na bi ba lokacin da na dawo, gashi duk babu mai Iya tambaya ta a cikin su.
Zaune na tarar da ita da wasu baki, tana gani na ta sallame su cike da fara'a ta nuna min gurin zama inda dama can ne kamar parmanent seat dina idan naje. Gaishe da ita nayi cike da girmamawa ta nuna min warmer tace na zuba abinci, daman Ina da bukata dan haka na bude karamar naga wainar shinkafa ce tayi kyau sai kamshi take yi. Plate na janyo na diba tare da zuba miya wacce tasha man shanu da tsokokin nama.
Ina ci Muna hira ta tambaye ni yan uwa na, na ce lafiya suna gaishe da ita. Kallo na kawai take da alama tana son ta gano wani abun a tattare da ni, amman zuciyarta taki amincewa saboda tasan babu ta yadda za ai hakan ta kasan ce. Kiran wayar ta shine yasa ta janye idanunta daga kai na, dubawa tayi taga Salman ne, ta dauka ya tambaye ta ita da waye a gurin tace Dije ya sauke numfashi tare da sosa keya kamar yana gabanta yace.
“Ta...dai gaya miki cewa ba ta da lafiya ko?”
“A'a sai dai ni naga kamar hakan, me yake damunta.?”
“Ammie bata wayar.”
Miko min tayi na karba tare da karawa a kunne Ina masa sallama cike da girmamawa har sunkuyar da kai.
“My love ya jikin ki?”
“Alhamdullah.”
Na fada a takaice ina jujuya wainar da na gutsiro.
“Ya baki sanar da Ammi wannan kyakkyawan albishir d'in ba?” Cikin tsantsar mamaki nace.
“Kai! Tabdi wallahi bazan Iya ba da nauyi.”
“KI gaya mata nima kunyarta nake ji.”
“Nima wallahi haka bazan Iya ba.”
“OMG, My Dijah sarkin kunya, ki fada zata baki tukwici.”
“Na yafe wallahi.”
“Shikenan kin samu abinci kici ko? Bana son kina zama da yunwa gashi ba ke daya bace yanzu.” Nasa wainar a baki Ina cewa.
“Gashi Ina ci kaima a kawo Maka?”
“Nooo bawa Ammi wayar.”
Hannu biyu na mika mata sannan na juya naci gaba da cin abincin. Shi kuma yana ta kokawa da zuciyarsa yadda zai yi ya sanar mata zuwan jikanta. Sai da ya rufe ido sannan ya sanar mata Sai jiyowa nayi Ammi na cewa.
“Kai alhamdullah masha Allah, Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana. Ina rokan Allah ya nuna min zuwan sa/ta lafiya, Allah ya tsare mana shi ya sauke ta lafiya.”
Kasa amsawa ya yi a fili Sai a zuciyarsa ya amsa tare da katsewa. Ammie cike da zumudi ta nemo lambar Gwaggo tana fadin.
“Abokin kuka shi ake gayawa mutuwa.” ji kawai nai tana cewa.
“Allah ya yi Zaki ga jika... Eh wallahi yanzu yake gaya min.. Wallahi kuwa Gwaggo.. Amin ya rabbil amin a ci gaba da Taya mu addu'a... Toh shikenan..”
Ai ban bari ta gama wayar nan ba na tashi na gudu saboda kunya da tabi ta dabaibaye ni. Ammie kuwa dariya tayi a gurin kuma ta kafa goshinta a kasa tana yiwa Allah godiya....
*YAREEMAH IBRAHIM-(KHAL)*
*INCHEON INT. AIRPORT*
A tsaye Khal yake, Da akwatunan sa guda biyu, Ya saqale wata jaka a jikin hannun akwatin. Waya ce a hannun sa da alama magana yake da wani mai matuk’ar muhimmanci saboda yadda yake sakin tattausan murmushi. Sanye yake cikin kananun kaya riga da wando ya d’aura overcoat akai, Samun waje yayi ya zauna akan kujera, Ya kira lambar da yai saving da (Yeobo-Bintu naah)🌷’
“Bintuunaahhh....! Lapia lou ina airport! Uhm...? Ki tayani da addua my love! Fushi kuma?”
Mikewa yai da sauri tamkar tana wajen, Domin kana iya jiyo zazzakar muryar budurwar dake magana ta cikin wayar. Shafa kwantaccen gashin kansa yai yana jan kasan leben sa, Kallo d’aya zakai masa kasan sun hada jini da SAS. Ha’kuri ya shiga bata yana sake rage sautin muryar sa.
“I’m sooo sorry yeobo (honey) Bansan fushin me ake dani ba, But kiyi hak’uri zan karb’i kowane punishment banda na rashin ki... Ina kaunar ki Dr. matar Dr. IN SHA ALLAH! Saranghaeyo ( I love you in Korean) .. An hak’ura? Masha Allah! Godia nake, Take kia love.”
Katse kiran yai yana murmushi ahankali yace,
“Kai.. mata.. sai a slow. Dole naje na bada hak’uri.”
Wani kiran ne ya sake shigowa, Jikin sa na rawa ya dauka sahibar ce sai kuma yaga SAS ne. Dauka yayi da sauri ya gayda shi cikin girmamawa, Salman din ma na bashi amsa cikin kulawa,
“Yasu Ammi da Abdullah...?”
“Kowa lapia lou! Ka taho kuwa?”
“Eh saura mintina kadan ina airport..”
“Ai na kira naji busy.. Kanata waya.”
Shafa sajen sa yayi yana daria,
“Da wani ne...”
“Ko dai da Dr. dinnan danaga itace wallpaper dinka ba.”
Daria Khal yayi. Ya shiga shafa keya kunya duk ta kama shi,
“Ayi hak’uri yallabai, Tuba nake.”
“Ahh bakomai.. Allah yasanya alkhairi, Idan ka dawo komai ya daidaita sai ayi bikin a huta ko.”
Da’di ya kama Khal da har sai da ya kasa boye murnar sa yayiwa SAS godia.
“Yanzu aina zaka sauka kenan?”
“Zan sauka Abuja yallabai...”
“Wajen Dr....?”
Nanma Khal yayi shiru yana daria ahankali, kafin yace.
“No zanyi submitting wasu takaddu ma. “
“Toh Allah ya dawo da kai lapia Khal.. Allah ya bamu nasara, Ya dora mu akan makiyan mu.”
Sallama sukai, Khal yayi hanyar departure.....! Zuciar sa dauke da adduar Allah yasa ya koma a sa’a...
_Afuwan zafafa fans.. Ba zaku samu kibiyar ajali ba na yan wasu kwanaki. Saboda wani uzuri daya taso🤲🏻Dana kammala zan cigaba da posting IN SHAA ALLAH!_
_Yar uwa kinason karanta zafafa amma documents? To zafafa na harhada kayan su. Da an kammala Za’a yi documents dinsu duka akan Naira dubu d’aya da........_
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more
Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_
_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_
_Wattpad: missxoxo00_
_PG:27_
_BOOK:2_
*GIM. KHADEEJAH*