← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 114

Sashe 24

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Toh sai akai yaya? Ina ruwana dan ta kasa sa yar ta. Ni Khadija ba ‘yata bace? Kafin na samu nawa ‘yayan wana fara samu a duniya? Mahaifiyar ta Jamila daga ni sai ita, Kuma duk duniya babu wanda nakeso sama da ita duk cikin yan uwana, Kuma gudan jininta wadda itama ‘ya ce agare nin zan ki kyautatawa? Shekara nawa ina rokon abani ita na rike hakan bai samu ba sai yanzu. Karki batamin rai hajia. Yauwa Khadija monday zaki fara attending classes dinsu, Na tsawon watanni uku ne kacal. Hameeda ga MasterCard dina da safe ki kaita shopping ki sauya mata da irin shigar mu tanan, Ku bawa tailor dinku dinkunan ta, Ki kaita saloon a gyaro mata kan ta amata manicure..”

Ni dai shiru nayi ina sauraron Kawu tamkar a mafarki, Mami tayi kwafa tana kada kafa,

“Alhaji wannan yawon ai ba na Hameeda bane sai dai ko driver ya kakkaita. Amma ya za’ai ta katse schedules dinta ta kaita koina?”

“Toh Hajia ai gidan ki ne, Ya’ya kuma naki ne ko? Shikenan yayi kyau! Khadija ki shirya da sassafe ni zan kaiki ko’ina. Jeki debi abinci kici ki kwanta.”

Kada kai nayi na silale na gudu da’ki, Ina jiyo sanda ya koma parlorn sa, Mami nata tsaki tana mita, Hameeda ma na taya ta. Jiki na gaba d’aya ya saki yayi sanyi, A darare Na fita na shiga kitchen na zuba abinci naci acan, Na koma daki na kwanta. Saboda Banda nauyin Bacci ina jiyo sanda Ya Shukra ta dawo suka hau bata labari . A haka bacci yai awun gaba dani, Bansan sanda suka dena magana ta ba.

*WASHE-GARI*

Da wuri na tashi na shirya, Na wanke bandaki, saboda na fara gane kanshi da amfanin wasu abubuwan dake cikin sa. Sunata kumbure fuska a haka na bisu na gaggayshe su, Ranar Kawu ko abincin safe bai ciba yace muje, Gurare sosai ya kai ni ya narkomin kayan yan gayu da atamfofi da laces da materials, Abayoyi suma fal da takalma da jakankuna Harda kayan kwalliya dana man shafawa. Ya biya ya bawa tailor ya gwada ni, Daga nan muka je salon aka wankemin kai na, Aka gyaramin kafata da farata na. Wallahi tamkar ba ni ba. Daga nan ya biya dani kasuwar waya, Ya siyamin dalleliyar waya ta zamani. Wallahi tsabar farin ciki Bansan sanda nasa hawayen dadi ba, Na shjga kwararawa Kawu addua. Ranar dai gaba d’aya cinyeta mukai a bukatu na, Sannan ya dire ni a gida ya wuce kasuwa.

______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_*SIRADIN RAYUWAR BILKISU, KIBIYAR AJALI, MIN QALB, ABINDA KE CIKIN ZUCIYA, SARAN BOYE... DUKA NA KUDI NE. AKAN NERA DARI BAKWAI KACAL. NEMI NAKI YAR UWA. KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA WADANDA KE RUBUTAWAR..DOMIN MALLAKAR NAKI ZAFAFA BIYAR DIN TUNTUBE MU A NAMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFIN_*

____________________________
_*ANNUR PERFUMES_*
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_INA MASOYA TURAREN WUTAN MAIDUGURI? YERWA FATO😉😍TO KU MATSO KUSA... GA DAMA TA SAMU, KINA SAN TURAREN WUTAN DA ZAI KAMA GIDA YAYI SATI YANA KAMSHI? KINASON TURAREN KAYA DA KO KIN WANKE BA ZAI DENA KAMSHI BA? KINASON KHUMRAHS HADADDU DA SUKA AMSA SUNAN SU? SHIN KIN TABA AMFANI DA KULACCAM DIN YAN MAIDUGURI? WANDA KAMSHIN SA KESA KISHIYA KWAFA?😉 KADA NA CIKAKU DA SURUTU.._

_*ANNUR PERFUMES* MASARAUTAR KAMSHI KENAN, MUNA BADA TURAREN MU AKAN FARASHIN SARI DA KUMA SAYI ‘DAI-DAI, SHIN NA LISSAFO MUKU ABUBUWAN DA MUKE SIYARWA KUWA?_

_TURAREN WUTA (NA KAYA/ GIDA/ JIKI/ DA TSUGUNNO. KHUMRAH, KULACCAM,_
_MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)_
_DECORATIONS (NA GIDA/OFIS/ KAMFANI DA SAURAN SU/ MUNADA INGANTATTUN KAYAN INFECTION (HERBAL WANDA BA ZAI SAKI WANI SIDE EFFECT BA, MUNADA DANA MATSI (STEAMING)_

_ANNUR PERFUMES NA GARIN *KANO* ADIRESHIN MU: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!. LAMBOBIN TARHON MU: 07086341096//07069037534. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NIJERIYA. SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA SAI ANNUR PERFUMES_

_WANNA SCENT EXOTIC??HEY.. WHICHEVER WAY YOU WANT IT WE’VE GOT YOU COVERED AT *ANNUR PERFUMES(CASTLE OF SCENTS)* FOR YOUR MIND/ YOUR SOUL.. AND YOUR HOME.. BE THE CENTER OF ATTRACTION WITH ANNUR PERFUMES.. WE ARE YOUR SCENT PLUG..TANTALIZE YOUR SENSE OF SMELL AS YOU SINK INTO BLISS. SAY NO!! TO DAMP SMELL LOVELIES. OUR DUKKANS LAST’S LONGER AND LINGER. VERY AFFORDABLE... DELIVERY IS NATIONWIDE 😉😘😍_

_13//KASBTSTW_

*BRITISH ENG LEARNING CENTRE*

Idanuwa na shiga zarewa a lokacin da driver yai parking mota a harabar wajen. Fitowa nayi dakyar ina harhade tafiya ta, Koda wasa bantaba hasashen kasancewa ta acikin jajayen kunnuwa ba. Gyara zaman rigar abayar jiki na nayi na shiga ciki. Tamkar a k’asar waje haka wajen yake, Sai hada hada akeyi, classes ne sosai tamkar makaranta. Kowa kagani awajen nan kasan dan wani ne. Wai yau ni Dije ni ce acikin manyan mutane? Alhamdulillah Yaa Rabbi. Zuwa nayi na karb’o ID card dina da sauran abubuwan da Za’a buk’ata na handouts da books.

Ajinmu aka kai ni, Kowa da computer a gaban sa da earpiece saqale a jikin kunnen sa, Wurin zama na aka nuna min na zauna nima nayi duk abunda naga sauran daliban nayi, Sosai ake koyar damu ilimin turanci da yadda zamu dinga magana irin na British English. Both oral and written. Sosai nake enjoying lectures din da Mr Charles yake koya mana, Gashi yan ajin kowa kansa a waye, Gaskia birni tayi ba irin karkarar mu ba masu duhun kai, Lalle Ilimi na kai ka inda baka tab’a Zata ba.

Haka dai malaman sukai ta koyar damu duk sati banda ranakun hutu (weekend days). Kafin kace me? Mun kammala koyan turanci kasar ingila, Hakika Idan nayi maka magana na juye baki da turanci ba lalle kace ni ce Dije Oganniya ba. Saboda gaba d’aya yadda nake magana a hankali cikin turanci da iyawa Kai ka dauka wallahi baturiya ce. Cikin haka aka fara lectures na university. Sai na mayar da zuwa koyan turanci Ranar asabar da lahadi kawai..

Yau ni Dije ce a jamia? Sosai muka fara lectures babu wasa, Kullum driver ne ke kai ni ya dakko ni, Kawu Ismail ya tsayamin tamkar uba na. Matsala d’aya nake fuskanta a gidan nan bangaren Mami da yaranta.

Bantaba sanin ana tsantsar Kishi da hassada tsakanin matar kawun ka da ya’yan ta akan ka ba, Meyasa? Oho! Na bawa kai na amsa. Wallahi dik iya tsawon shekaru na da duhun kai na alokacin da ina k’auye, Na dauka Gajiyalle abinda yasa takemin haka saboda nazo a yar kishiya ne. Na dauka lokacin da na dawo dangin mahaifiya ta zanji sassauci. Yanzu a gidan nan gaba d’aya Mami da su Ya Shukra da Ya Hameeda basa shiga shirgi na, Tsakani na dasu sai hantara da kyara. Kawu ne kawai baya min komai, Yana ko’karin ganin ya yaye min kuncin rayuwa, Kai ko siyan kati shike turomin bana siya, Ga bani kudi da yake akai akai. Jin sa nake tamkar mahaifiya ta wallahi, Kuma suna kama sosai da mahaifiya ta, Ya nunamin hotunan su sanda suna k’anana..

Na fara zuwa lectures a jami’a, Sannan ina zuwa tahfiz a islamiyar dake bayan gidan mu. Ga British Eng learning centre da nake zuwa ranar weekends da yamma. Na kara wayewa, Kala ta tafito, Na murmure, Kai idan kasan Dijen Durbun a baya ba zaka tab’a cewa ni ce Nana Khadija a yanzu ba. Saboda yawan fad’an da su Ya Hameeda ke takala na dashi yasa Kawu ya raba mana dakin Kwana. Akwai wani k’aramin da’ki da ake zuba shirgi, Rannan yasa aka debe komai aka saka madedecin gado mai cin mutum d’aya, Yace na kwashi kaya na na koma can. Hakan kuwa akayi, Na tattara na koma can.

<<<<<>>>>>> <<<<<<<>>>>>> <<<<<>>>>>>

Haj Abeeda ce ta shiga zagaye a dakin ta, Tunda Alhaji Ismael yake wa Dije hidima tafara jin haushin hakan, Ta kuma dora yaranta akan network din tsanar Dijen. Wayar ta ta janyo dake chaji akan dressing mirror ta kira Haj Lubna bugu biyu ta dauka ta kara a kunnen ta,

“Hello Hajjaju..!”

“Na’am Haj Abeeda! Ya gida? Ina yarana?”

“Sunanan qalau Haj.. Kina gida ne?”

“Ina gida dawowa ta a office kenan..”

“Toh gani nan zuwa.”

“Lapia dai ko Hajia?”

“Hmm’ Kede bari labari ba zeyi a waya ba.”

Shiryawa Haj Abeeda tayi ta fuce, Dama already ta gayawa Alhaji Ismael Zata fita yau. Driver na sauke ta ta shige ciki ranta a bace, Bayan sun gaysa ne, Haj Abeeda ta sake jan tsaki a karo na ba adadi,

“Hajia.. Subhan’Allah! Meya faru?”

“Ki bari kawai.. Ashe yarinyar nan munafuka ce? Shigo shigo ba zurfi tai mana? Ai Alhaji ya rufe ni Haj, Ke kinga hidindimu. Hmm!”

“Kin sani a dubu! Wacece haka?”

“Yarinyar nan mana Dije. Wadda kika dauka yar aiki ce? Kinga uban barin kudin da Alhajin yake mata?.”
Chapter 24 · 0% Book details