← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 114

Sashe 38

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai bai karasa magana ba na fashe da kuka, Me yasa su Ya shukra da Hameeda su ba za’ai musu auren ba sai ni? Okay! saboda ni ba yar gidan bace ba ko kuwa? Ko dan banda gata ne? Tsana ce wannan kome? Wayyo Allah na ni Khadija..Ashe daman ba Mas'oud aka zaba min ba? Kuka Sosai nake yi ina rike kai na. Duk duniya babu d'a namijin da nake so, gangar jiki na keson mallaka irin Mas'oud ba. Ina son Mas’oud saboda shine first love dina. Ina son Mas’oud saboda shi ya koya min so har nasan menene so? Ina son Mas’oud saboda shi ya rai ni zucia ta ya koya mata abinda take so. Ina son Mas’oud saboda yana so na so mai wuyar fassarawa.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un...”

Shi naketa nanatawa a fili ina bubbuga kai na ajikin kujera, Kawu daddy ya sauke zuciya ina jiyo sautin ta,

“Kiyi hak’uri Khadija. Na rantse da Allah ban amince da aura miki shi ba don na cuce ki. Wallahil azim ba zan kai ki inda zaki wahala ba don na lalata miki rayuwa ba Khadija. Wallahi Khadija wannan auren ni inaji ajiki na alkhairi ne a gareki damu gabaki d'aya. Saboda Ina ji ajiki na nan gaba zaki ya ba min wannan rana..”

Kuka nake sosai shabe shabe ina fyace majina da kasan dankwali na.

“Kawu Mas'oud fa.. Mas’oud Kawu! Ina son Mas’oud.”

“Wanene haka kuma Khadija.?”

“Kawu shine wanda ya ke sona. Tun service dina muke tare Kawu daddy. Munyi alk’awarin aure dashi wallahi Kawu daddy..”

“Khadija me yasa be zo ya same ni da zancen ba? Akalla kafin ya fara neman ki sai ya nemi yarjewa ta kamar yadda wannan ya yi. Amman Me yasa bai turo Manya sunzo ba idan har da gaske yake yi Eh?”

Shiru nayi ina ajiyar zuciya.

“Yace ne.. Ko wansa bai yi aure ba kuma shine karami. Sannan bai gama ginin sa ba..”

“Sai Yaushe kenan zai fadawa manyan ki Uhm!? Ko kuwa zama za kiyi tayi kina jiran sa kina faman tsufa agida? Shi kuma yana bata miki lokaci? Daga karshe ma yazo yace miki an hada shi aure da yar uwar sa! Uhm? Shikenan tunda baki dauke ni amatsayin uba ba Khadija. Na ky’ale ki sa..”

Riko kafafun sa nayi ina Kuka, Ni din banza zan ki amincewa da maganar Kawu daddy? Mutumin da ya mayemin gurbin uwa da uba? Halacci d’aya zanyi shine na amince. Ba Wai don ina son wanda za’a daura min aure dashi ba. Kawai dai saboda Kawu daddy ne. A duniya banida mafiyin sa idan ka tsame sauran yayyun Umma ta.

“Bar Kuka Khadija.. Na kyaleki wallahi. Zan ku..”

“Na amince Kawu daddy.. Na amince wayyo Allah karkai fushi dani.”

“Allah ubangiji ya miki albarka. Ya biya miki bukatun ki na alkhairi, Allah yasa wannan auren ya zamo wanzuwar farin cikin ki, Yasa ki zama wata aba a rayuwa, Allah yasa ayi a sa’a. Nan da sati d’aya wato mai kamawa za’ayi in Shaa Allah!..”

Kasa magana nayi, Ni wallahi ji nake tamkar bacci nake yi. Gaba d’aya bana gane me kawun yake fada. Na sandai nace na amince amma gaba d’aya wani dishi dishi ma nake gani. Zucia ya da idanu na Mas’oud kawai suke nuna min, Sanye cikin kananun kaya yana rataye da ID card dinsa na wajen aiki. Cikin haka Mami ta banko kofa ta shigo,

“Meye haka ne? Koke-koken me aketayi ne uhm? Tun daga karamin parlor nake juyowa, Me akai ne?”

Tana magana tana sakace hakorin ta da toothpick.

“Babu komai ya akai..?”

Kawu daddy ya tambayeta yana duban ta da kyau .

“Koke koken da muketa jiyowa ne shysa na shigo ganin Lapia? Kar ma’kota su fara lek’owa suna tambaya.”

“Lapia Alhamdulillah Hajia. Ba kukan wani abun bane na farin ciki ne.”

“Toh faa! Tooo”

Mami tace hakan tana mai zama a gefen sa.

“Tashi kije Khadija. Allah ya miki albarka Khadija!”

“Aamin Kawu daddy..”

Mikewa nai dakyar ina tafiya. Ina jiyo mami nata tambayar sa menene?

“Wai meke faruwa ne alhaji. Alkhairin menene?”

“Hajia.. aure ne! Wani bawan Allah ne ke neman auren ta ya biyo ta kai na.”

“Aure..”

Mami tafada tana dafe da kirjin ta, Ni kuwa sauri nayi Na fita na jawo musu kofar. Ina fita na haye sama ina mai bude sabon shafin wani kukan. Mami ta muskuta kusa da Kawu daddy,

“Alhaji bangane me kunnuwa na suke jiye min ba, aure? Aure fa kace? Waye zai auri wa?”

“Hajjaju da hausa fa nake miki magana. Nace neman auren ta akazo waje na.”

“Au ashe da saninta ma shine take kukan munafurci kuma?”

“A’a Hajia wanda takeso daban. Wanda kuma yai tambaya daban.”

“Toh fa! Alhaji Kai wa ka bata kenan..?”

“Wanda ya fara magana mana.”

“Shi din wanene shi! Wai ka na nufin bada masaniyar ta ka bayar da auren nata ba? “

“Eh ban isa bane? Ni ba mahaifin ta bane.?”

Yatsina fuska Hajia Abeeda tayi tana sosa idon ta,

“Toh shi wannan Waye manemin kenan? Dan wanene?”

“Wallahi wani bawan Allah ne kawai nutsatstse ya kwanta min arai kuma.”

“Ya'yan abokan ka Wai..?”

“Ko d’aya wallahi.. wani ne daban. Marainiya ce gwara na aurar da ita hankali na yafi kwanciya.”

“Dankari Makari.. Ai shikenan! Toh su Shukra Alhaji ka nemo musu mana acikin yaran abokanan ka. Ko Yayan commissioners dinnan da kukayi makarnta.”

“Ai nagaya miki inde sai dan wane da wane zaki bari su aura ni babu ruwana na tsame hannu na, Muyi ta zama ana k’irga mana shekaru tare.”

“Wai dan anbiyo takan ka ance anason Dije? Tab Alhaji ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, Dai dai ruwa dai dai tsaki. Su ana ganin kai ne mahaifin su babu kasakantaccen da zai biyo takan ka yace yana neman auren su.. “

Dr. Ismael yayi daria yana kurbar ruwan hannun sa, Yasan halin matar sa sarai, Shi yasa bazai taba gaya mata gidan da dije Zata shiga ba sai an daura aure ko kuma an kawo kayan aure abu ya kusan tabbata. Yasan kuma Zata titsiye Dijen da tambaya shiysa bai sanarwa Dijen bama, Duk ya tattara ya rufe su a fai-fai. Mami ta jima tana neman bugar cikin Dr. ismael don jin waye? amma tsabar zurfin ciki irin nasa duk nacinta haka ta hakura bataji Waye manemin na dije ba. Data dame shi ma sai ya rufe fuskar sa da jarida wai kansa ciwo yake. Tashi Tai ta fice ta kyale shi.

“Mami ya akai kuma..?”

“Kukan me take Mami.?”

Shukra da Hameeda suka tasata a gaba da tambaya ganinta fito daga wajen Dr. Ismael

“Hmm! Makira algunguma aure Zata yi fa..”

“Aure! Wa Zata aura Mami..?”
Hameeda ta tambaya tana raba idanuwa.

“Ba dai Mas’oud ba?”Shukrah ma ta tambayi Mami tana dafe kirji.

“Waye Mas’oud kuma? Du basu bane. Wani ne daban yazo neman auren ta. Shine take wannan kukan batasan wanene ba..”

“Kuma Daddy ya yadda?”

“Kwarai kuwa.. Yace ma afara shiri sabon sati me kamawa zaayi bikin.”

Hameeda ta tabe baki,

“Allah ya raka taki gona..”

Shukra ma jin ba Mas’oud bane sai ta samu kanta cikin jin dadi,

“Masha Allah! Allah ya kai mu.”

Harara Mami ta dankara mata. Tanemi waje ta zauna,

“Gwara kuma ku fito da mazajen aure...”

“Soon In Shaa Allah!” Cewar Shukra tana murmushi.

Hameeda khma ta shiga raba idanuwa. Haka dai suka tasa zancen auren agaba sunata ta kwashewa dije albarka. Musanman Mami dake bakin cikin auren dw zatai. Amma Idan ta tuno kila ba auren jin dadi bane sai ta shiga murmushi kuma tana k’ada k’afa.

Ni kuwa inacan d’aki ina kuka. Ba kalar wanda ban ba. Kai har karamin hauka sai da nayi. Naita buga kai na ajikin bango duk ya daddauje. Naita bori. Ina tunanin ko hada kayana zanyi na gudu ne yadda ake a film. Wata zuciar tace bakisan halacci ba.

Dole nayi hak’uri zuciya mai halacci bata manta alkhairi komai girman sharri . Kawu daddy ya zamar min uba ya zamarmin uwa. Shine gatana. Yana gatantani fiye da tunani. Me yasa zan bijirewa abinda yake so ya kuma nuna isa akan sa? Wacece Ni? Dole na hakura. Illa dai koma wanene ya yankemin buri na na auren Mas’oud saiga rayuwa. Wallahi sai ya bambancewa aya zakinta na shiga hurumin soyayya da yayi. Ina ruwan sa? Lallai ni na hadu da sharrin late comer mai datse farin cikin zukatan masoya biyu . Bansan ka ba, Dan jaraba da kalata kace ni kakeson aura? Wannan wacce irin bahaguwar kaddara ce? Wata zuciar tace taki kaddarar kenan Khadija. Zaki shiga wata ukubar rayuwar kenan ta uku. Na bigi wajen kirjin nawa inda zuciar take tamkar dai zaucacciya. Ni kadai nace ah k’arya kike wallahi sai dai shi ya shiga uqubar rayuwa. Ba shine ya ce yaji ya gani yana so ba? Ai kuwa zai San ya tafka babban kuskure.

Mas’oud sai kira na yake na kasa dauka. To me zance masa? Koma menene shi ya janyo mana wallahi. Ni dai ranar gaba d’aya haka na yita rabi kuka rabi zancen zuci, rabi magana ni kadai. Wani lokacin kuma na bubbuga kai na a jikin gado. Wayata kuwa daga karshe kashe ta ma nayi gaba d’aya. Oh ni dije. Wai ni za’aiwa auren dole da wanda bansani ba? Kuma cikin wata d’aya jal aka gama komi. Nashiga uku sau dubu uku. Haka nayita sallolin nafila ina wa Allah kuka a sujjada kan ya tarwatsa wannan auren da za'a yi min koda kuwa anzo daurawa ne......

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥.
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac.

_*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_*
Chapter 38 · 0% Book details