← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 114

Sashe 50

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali tasa hannun ta toshe kunnenta d’aya saboda yadda sautin bushe bushen algaitu ke tashi ta ko’ina a masarautar. Da alamun wani babban taro ko nad’i za’a yi. Amman batada masaniya ko kadan. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Bayan ta bawa hadimarta izinin shigowa,

Hadimarta ce ta shigo kanta a kasa. Gurfane tayi awajen bayan ta kwashi gaisuwa,

“Uwar daki na.. Allah yakara miki lapia da nisan kwana..”

“Aamin Khairat!”

“Uwar daki na.... Yarima ne yace na masa iso wajen ki.”

“Ahh! Na baki dama. Hanzarta ki shigo da shi.”

Shigowa yayi sanye cikin manyan kaya na sarauta, Kansa yasha rawani me kunnuwa biyu. Kana kallon sa kasan tsatson gimbiya Huwaila ne. Domin kamar su d’aya tamkar dai tayi kaki ta tofar. Sede shi dogo ne sosai ya dakko zubin tsayin marigayi Aliyu Salmanu, Mahaifin su.

Yana shigowa gaban ta ya yanke ya fadi. Domin batai zaton Abdulqadeer bane, Ta dauka wani ne daga cikin yaran dai. Gaba d’aya sai jikin ta ya nemi d’aukar rawa, Ta shiga kalle kalle tana duban ta ina zata hango shi..

Murmushi yai irin na gefen bakin nan kafin ya shafi kasan rawanin sa inda gemun sa yake.

“Ammi... Ni baki farin cikin gani na bane?”

Muryarta na rawa ta girgiza kai da saurin gaske tana mai neman saisai ta zuciar ta dake barazanar fad’owa saboda tashin hankali tace,

“Abdulqadeer! Barka da dawowa!”

“Hmm! Kamar gaske! Barka kadai Ammi, Fatan na same ku lapia?”

“Alh... Alhamdulillahi!”

“Khal ko?... Nasan Khal kike begen gani. Well long story shot, Yace bazai zo ba. Wannan karon ma yace bai da ra’ayi. Ko fa sunan ku na kamo masa ca...”

“Ya isa Abdulqadeer! Ya isa dan Allah.” Tai saurin katse shi tana dartse hakoranta.

Wata shegiyar hamma ya saki kafin ya mike yana duba hadadden agogon hannun sa,

“Sarauta za’amin fa.. Tunda wancen juyan baya haihuwa. Kuma idan akace za’a raba shi da kujerar zai iya rasa ransa saboda mayatar so. Anyways yau dai za’amin nadin hakimci. Na manyan yan majalisar sarki, Nasan ba wani sani kikai ba, Tunda ba gada ki kai ba, Well.... Uhmm! Kowacce fada akwai manyan yan majalisar sarki da duk harkar data shafi fada sai an dama dasu, Duk wata sarauta ko wani nadi bayan ta manyan yan majalisar sarki, To suna ne kawai domin sarautar sunan ta ta taka haye bata gado bace.. Kamar irin su shirmen mukaman sarkin kofa haka ko... Kingane?”

Murmushi kawai tayi, Saboda tasan zuwa yayi kawai ya tada mata da hankali kuma ya ci mata mutinci. Tunda ya tabo mahaifin ta yanzu( Marigayi Malam Abdullahi( Dogari/Sarkin kofar kudu).

“Nagane.. Kuma nagode.”

“Yauwa...So za’a bani hakimcin waje.. Babban hakimi/Makaman Basannabas.”

“Allah yabada sa’a Abdulqadeer!”

Ya sheke da dariya yana kureta da idanu,

“Anya.. Anya har zuci wannan adduar take? Saboda zaki so ace Khal ne keda wannan mukamin ko? Wait ai da yazo kila shima abashi dallatu haka.. Koya kikace Ammin mu ta mutunci?”

Shiru tayi tana maida kanta ga shiegegiyar talabijin din dake nuna wani wasan kwaikwayo na india,

“Toh bara na kyale ki haka. Sai gani na biyu.”

Mikewa yayi ya fuce yana murmushin mugunta. Yana fita ta bada damar a kulle mata kofar sashen ta. D’akin ta ta koma ta bude shafukan kuka tana jijjiga kanta,

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yaa Allah! Ka shiga lamuran mu. Astagfirullah! Allah na tuba..”

Kuka kawai take na tsantsar tashin hankali, Ace babban d’anta ne sarki, Amma batasan komai na harkar mulkin sa ba? Shi kansa ba tada ikon ganin sa. Sauran yan uwan sa da zata kalla tadanji dadi suma ana neman mata katangar K’arfe tsakanin ta dasu. ? Shin wa zata gayawa damuwarta a duniya taji sassauci. Kirjinta cike yake da damuwa kala-kala. Gashi batada wani dan uwa da zata tunkara da maganar...

Ranar gabaki d’aya a daki ta wuni tana kuka, Sannan tayi nafilfili tana mai rok’on Allah daya sassauta mata kangin rayuwar da take ciki da iyalin ta.....

<><><><><><>

*KOFAR KUDU...*
(SASHEN GIMBIYA KHADIJAA)

Yan kwanakin nan gaba d’aya a hargitse nake, Cikin bacci zan farka na shek’a da gudu nayi wajen kofar parlor, Gaba d’aya ko’ina na sashe na tsoran sa nake. Ji nake tamkar ana kiran sunana.

“Wayyo Allah na! Wayyo Umma na, Wayyo Bappah na... “

Na rufe kai na da hannaye na ina hawaye. Gaba d’aya yanayin da nake ciki yana da wuyar fassarawa. So nake na bude kofar na fita, Kashedin Kawu daddy daya min ranar da Za’a kawoni kan cewar Kar naje ko’ina sai da izinin mijina, shine yake hanani tafiya. Tunda nazo bana fita, Sai rakiyar baki zuwa bakin kofa, Gashi yanzu kwata kwata ba’kin ma sundena lekomin tamkar anyi ruwa an dauke.

Razana nake yi, Jiki na sai kakkarwa yake. Da dare yayi shikenan bani da sukuni, Sai fargaba. Wallahi na tsani masarautar nan da abunda yake cikin ta. Ni dai gwanda zaman kauyen mu na durbun sau dubu, Da kuma zaman gidan Mami wallahi. Akan masarautar nan. Kwanciyar hankali ? Bacci mai dadi? Ina tuntuni nayi sallama dasu, Na nemi farin ciki na rasa, Saboda tsabar tashin hankali wallahi ko wayata bana dauka, Gashi jinin nan sai zuba yake. Ni na rasa wane irin period nake? Tabbas don ina cikin tashin hankali ne shi yasa bai tsaya ba.

Ina tsaye har akai assalatu. Na koma kan kujera na rakube ina jiran gari yayi haske. Ina tsakure a kujera har gari yai haske. Bandaki na shige nayo wanka. A tsorace na zura kaya na fito da gudu daga dakin na koma dayan parlorn,

Naja tsaki lokacin da na jiyo kirarin dogarai suna yiwa SAS, Ta sashe na suka wuce lambun sa, Nayi Allah ya isa tafi dubu. Na tsane shi, Na tsani mai kiran sunan sa, Na tsani abunda ya dangance shi. Ni wallahi zaman gidan nan tamkar akan kaya nake. Shima bai damu dani ba, Tunda yai tafiyar sa har ya dawo baitaba nemana ba ko da awaya. Babu ruwan sa dani, Duk yadda akai ya aure ni ne ya tarwatsa farin ciki na ya raba ni da Mas’oud.. Allah ka bimin hakk’i na..

Ina zaune na jiyo duriyar dawowar su, Hasken kyalli kyallin lemar sa da ake dagawa har ta window na. Zuciya ta amsa dai dai lokacin da shi da fadawan sa suka wuce..

*SAS*

Tun wucewar sa ta farko yake son ya shiga sashen nata, Amma gangar jikin sa ta hane shi, Gaba d’aya tun ana’i washegarin ranar da zai dawo daga cyprus ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali, Haka kawai yaji tamkar an zare masa ita aransa, So yake yayi tunanin ta ya kasance da ita amma tamkar an musu katanga da juna, Tana zaune a masarauta inda yake amma kamar ba matar sa ta sunnah ba? Hawaye ne suka shiga reto ta cikin gilashin sa,

‘He badly wants her by his side... Amman yarasa meyasa duk lokacin da zai so ganin ko da fuskar tane sai yaji tamkar an hanashi ya kasa. Gashi ginin da yasa ana mata sai nisa yake yi. An kusa kammala shi abunka da masu nera, Kwana akeyi ana aikin gina shi... Wayar sa yar karama ya janyo a drawer k’irar torchlight, Haka kawai ya tsinci kansa da kiran kanwar kakan sa, Gwaggo Ta fada (Haj Hajara Ibrahim).. Kiran ta yayi.. Sun jima suna magana kafin ya katse kiran yana mai dafe da kansa. Ita ba acikin masarautar take ba, Tana cikin gari gidan ta daban.

°°°°°°° °°°°°°°°

Cikin kwanaki kalilan mahaifiyar Shaheedah ta kammala tanadar mata da duk abinda zata tafi dashi, daman tun tuni suka fara aiwatar da wasu abubuwan. Ganin ta gama samun komai yasa ta fara shirin dawowa Basannabas, taji gaba daya ba zata iya yin sati daya da tace ba. Gashi daman taji labarin dawowar Salman. Haka ta biyo jirgi ta dawo, bata bi ta kan sarautar da aka yiwa Abdulqadeer ba burin ta kawai ya zata raba wannan auran na Dije da Salman dan shine kawai tashin hankalinta.

Jakadiya tasa aka kirawo mata wato Zainabu Abu, ita kadai ce Jakadiya a cikin Basannabas, sauran guda biyun duk ba'a neman su an jinginar da su basu da wani amfani sakamakon duk tafi su iya kai gulma da hada gwarama tsakanin duk wanda tasan yana neman bayan d'aya. Tsaye ta tarar da ita sai zagaye take a tsakiyar parlorn ta, cikin sauri ta kai guiwarta kasa tana gaisheta cike da kaskantar da kai.

“Sannu da dawowa farin cikin sarki Salman, takawarki lafiya Gimbiyar Gimbiyoyi, kowa ya yi kewarki a cikin masarautar nan, sannu da dawowa uwar daki na.”

Shaheedah ta lumshe ido tare da dauke kai daga kallon Jakadiyar tana cewa.

“So nake kije kiyi min iso wajan mai martaba yanzu.”

Jakadiya ta yi jimmm! Saboda a yanzu babu ta yadda zata iya zuwa gurin Salman, kafin ya shiga cikin daki ya shaida mata baya son ganin kowa yau ya gaji yana son ya huta, yace komai ake da bukata a sanarwa Waziri tunda yana cikin fadar shi kam a barshi.

“Baki ji abin da nace bane Jakadiya?”

Sai ta daburce ta rasa yadda zata yi mata bayani saboda tasan Shaheedah idan ta kwallafa rai akan son ganin Salman, to da kamar wuya taki ganinsa, dan ko da bala'i ne sai sun hadu. Baki na rawa tace mata.

“Ranki ya dade mai martaba yace dani karna shiga inda yake, yace koma menene a je a sanarwa Waziri.”

“Mtwwww zan cen banza zancen wofi, to ni ba waziri nake son gani ba, shi Salman din shi zan gani bayan ya gama fito da abin da yake boyewa? Meye na cewa babu wanda zai gani saboda rainin hankali.”

Ita dai Jakadiya ta kasa magana, ran Shaheedah ya kuma baci tace.

“Ki tashi ki bani guri, tunda ke baki san yadda zaki yi naje gurin sa ba.”
Chapter 50 · 0% Book details