← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 114

Sashe 21

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gajiyalle ta dire tsallen albarka ta shiga zundumawa mai gari ashariya tana karkada masa hannu. Mai gari ya murtuke fuska ya fice mabiyan sa na bin sa a baya. Ba jimawa dangin Ummana suka Zo, Domin sai jiya aka sanar musu. Sunyi mamakin ganin girma na, Ni kuwa na shiga raba idanu ina binsu da kallo, Yan gayu ne sosai wanda suka shaki ilimin boko dana addini. Sun jima sosai kafin su tafi bayan sun dire mana kayan abinci fal, Suka ce zasu dawo nan ba da jimawa ba.

<><><>. <><><>. <><><>.

Bayan rasuwar Baffa da wata biyu abubuwa da dama sun faru, Kamar raba gadon Baffan mu da akayi. Gajiyalle ta samu gidan da muke ciki a matsayin tumunin takabarta ni kuma gado na shine ragowar gonar Baffa guda d’aya dake bayan gari. Tunda ta samu gidan nan yazo a gadonta na shiga 3, shiga dari fita dari sai tamin gori, Kamar ba ubana ne ya rasu ta gada ba, Ta rata kawai nake. Kullum cikin addua nake. Allah ya nema min mafita kawai. Gaba zatai dana sani. Haka rayuwar ta cigaba da garawa. Kullum ta Allah sai na zubarda hawayen rashin iyaye na. Abincin da yan uwan Umma na suka kawo ma ta siyar da rabi ta b’oye wasu.

<><> ••. <><>••. <><>••.

Ina cikin da’ki ina kwance wajen shabiyu da rabi na dare. Na jiyo an bude asaberin dake jikin kyauren dakin da na ke. Na nemi cocilan na rasa dakyar na ganta a gefen hijabi na,

“Waye.?”

“Sssh! Ni ne nan. Kwantar da hankalin ko. Had’in kai kawai zaki bani. Na miki alk’awarin komai.”

Ta muryar sa na gane ko wanene?! Torchlight na kunna na haske shi,

“Mudi.. Me kakeyi a daki na a daren nan?”

Kasa magana yai sai kiciniyar cire riga da yai ya jefar ya yo kai na na mike da sauri ina zura hijabi na,

“Mudi meye hakan.”

“Kiyi shiru dan Allah! Wallahi zan miki duk abunda kikeso. “

Murya na rawa na shjga bashi hak’uri ina damke hijabi na. Yayo kai na ya fincike zanin jiki na,

“Wayyo Allah na gajiyalle..”

Ban karasa ba yai taku biyu ya rufemin baki,

“Ki saurare ni yammata.. Ga ki da kayan aiki a tare dake, Karki zama mai duhun kai man-“

“Yayana ne fa kai Mudi.”

“Uwa muka raba, Uba kuma Kowa da nasa. Kingane? Ma’ana bamu hada jini dake ba.”

“Dan Allah karka lalatamun rayuwa Mudi.”

Inata k’ok’arin kwace kai na, Shi kuma yana ko’karin ciremin hijabi. Kafata nasa na tattake na dirka masa ita a gaban sa. Ya tsugunna ya rike wajen da hannu biyu yana matse idanu, Ficewa mai da sauri ina kiran Gajiyalle da mamaki na hangeta a kofar dakin tana lab’e, Tana gani na ta dubibi ce tana haske hasken fitila, Ha’din baki ne? Ko kuwa so take ya lalata ni tamin sharri da hakan? Ficewa nai da sauri banbi takan riko ni da take ba. Da tsakar daren nan na tafi gidan mai gari, Dakin Ummita matar sa na shiga bayan anmin iso, Na sheda mata komai, Wajen Kwana ta bani tace na kwanta da safe zata sanarwa mai gari.

*WASHE-GARI*

Kiran sallar farko na asubah sai ga Gajiyalle tazo gidan mai gari. Ta faffada masa karya da gaskiya, Mai gari ya kirawo ni da Mudi, akace kowa ya maimaita abunda ya faru. Lalle Mudi yaban mamaki ya murtuke fuska yace shi wallahi bai shigo gari bama sai safiyar yau. Naci kuka sosai, Bayan tafiyar su Mai gari yaban hak’uri yace yasan ni ce mai gaskiya. Kwanana goma a gidan Mai gari. Kafin na koma gidan Gajiyalle a ‘darare.

++ A kuma satin ne jarabawar mu ta fito. Sai ga Malama Mardiyya har gida ta kawomin nawa. Hakika nagodewa Allah domin bantaba kawo result dina zaiyi kyau haka ba. Ban boyewa Malama Mardiyya komai ba na sheda mata. Taji rasuwar Baffan mu kwarai matuk’a. A ramar ta sa na shirya mukaje birni na zana jarabawar jamb ta shiga Jami’a. Sannan ta sani a mota na dawo gida. Tunda na dawo Gajiyalle ke hantara ta tana yadamin magana kan naje yawon ta zubar. Ni kuwa murna nake na zana jarabawar shiga jamia. Na cike gurbin masscom/journalism. A jamiar dake birni. Allah yasa inada rabo amin.

Haka rayuwa taita garawa, Safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare. Naci jarabawar shiga jamia karo ta farko, Na samu gurbin jami’ar, Nanma Malama Mardiyya ta sake d’auka na ta kaini na zana ta biyu wato post-utme. Alhamdulillah Allah abun godia. Kamar da wasa itama ta fito na haye. Cikin haka yan uwan Ummana suka turo da maganar zasu turo a tafi dani na koma wajen su. Gajiyalle ranar wuni tayi tana bakin rai. Na fita kitso na dawo na tarar ta yiwa kayana fata-fata. Na kira Malama Mardiyya da y’ar wayata mai torchlight na sheda mata komai tace nayi hak’uri.

Domin bafa masifa na dena ba ko kad’an, Kawai dai na girma na kara sanin yadda rayuwa take. Duk irin mugun bakin da take yimin nasan bazai taba kama ni ba domin mahakurci mawadacine. A satin na wanke kayana tatas na goge na zuba su a ghana must go. Gajiyalle ta wuni tana harara ta, Na shiga band’aki na fito naga igiyar dana shanya underwear’s dina an yankota kayan sun zube. Tamkar an barbada musu toka ma. Dauke su nayi na sake wanke wa saboda banason neman magana.

Ana sauran kwanaki biyu na tafi, Na zazzaga ya ko’ina a karkarar mu duk gidan dana sani na shiga nayi musu sallama. Mai gari ya siyar mun da gonata ya aikomin da kudin yace na sai kayan aure a birni. Na nannade kud’in a cikin kaya na. Ranar da zan tafi ina duba kayan na nemi kudin na rasa, na fito tsakar gida na hangi Gajiyalle da Mudi sun tasa jarida cikinta fal tsire ne suna ci.

“Gaji! Waya daukar min ku’di na acikin ku?”

Tamkar na zuba mata ruwan zafi haka ta mike tana surfamin masifa, Kuma wallahi sune suka dauka, Na girgiza kai kawai na koma ciki na dakko jakata dai dai lokacin da direban da aka aiko dauka ta ya shigo yana cewa na fito,

“Gani nan! Ina zuwa..”

Na fada masa, ya gyad’a yai ya fuce bayan ya kinkimi jakar kayana. Duba na na mayar kan Gajiyalle da Mudi.

“Shekara da shekaru tun ina kankanuwa har na mallaki hankalin kai na, Baki dena kuntatamin ba, Kin uzzurawa rayuwata. Kin sani cikin uqubar rayuwa. Sam bakyasan ganin cigaba na sai dai lalacewa ta. Keda dan ki kuka hada baki don ya raba ni da martaba ta, Allah ya tseratar da ni, Alhamdulillah na rabu da iyayen da suka kawo ni duniya lapia, Tun Baffa na yana raye har yau rayuwata bata lalace ba duk da kwadaituwar son lalacewar da kikeso kiga nayi. Duk sharrin da kike nema na dashi baya samu na, Hmm sharri dan aike ne, Duk inda zai zaga sai ya dawo wajen ka,

“Shin wannan bai isheki ishara ba? Kisani kwakwalwar yaro bata manta duk abubuwan da aka yi mata na dadi ko akasinta. Ni Nana Khadija na zamar miki kainuwa dashen Allah, Duk da yadda ba taso na rashin uwa ba kyakkyawar tarbiyya hakan bai sa na lalace ba, Ni Nana Khadija na zamar miki murucin kan dutse ban fito ba sai dana shirya, Nan gani nan bari wallahi Gajiyalle, Na zama dakalin majina dole a hau ni a zame, Ni Nana Khadija na zamar miki *KIBIYAR AJALI* wadda (sulke baya tare ta sai da ta wuce) Daukaka yanzu na fara ta. Duk abubuwan da ki kai min na bar ki da mahaliccin mu, Zai mana sakayya ranar sakamako, Kudi kuma da kuka sata kun dauki kudin cizo, Kina ganin keda dan ki kunci bulus? Allah ya kara miki tsahon rai ki, Ki dade kiyi ‘karko kamar bishiyar dabino, Ki saurari dawowata Durbun, Zaki madaukakin mamaki mai wuyar fassarawa. “

Ina gama magana nai ficewa ta na bar su a daskare kamar shekararriyar kankara. Direba ya budemin mota na shiga muka dau hanyar birni. Wannan ce rana ta karshe dana saka Durbun a idanu na. Munata wuce dajin Allah bishiyo gasunan a jere da manyan duwarwatsu. Allah gwanin hikima!

“Ya Allah kasa na shiga birni a sa’a, Allah kasa su karb’e ni hannu dubu. Allah ka bani ikon cigaba da karatu na. Allah ka shiga lamura na. Kai ka iya, Kai zaka yi Ya Allah! Ka temaki mareniyar baiwar ka Nana Khadija..”

Ina kammala addu’ar na shafa a fuska ta, Kafin na janyo carbina na shiga azkhar na yamma, Na fada kogin tunanin yadda zan yi rayuwata ta biyu, Sabuwar rayuwa a dangin Umma ta..

*KANO STATE*
*DR ISMA’EL MUHAMMAD SINGA RESIDENCE*

...

Ainihin labarin yanzu zamu tsoma ‘kafa cikin sa🥰😍❤️... Oya put ya belts.. 😉The start of something new🏌️‍♀️🥂

ASHA HUTUN SUNDAY LAPIA❤️🥰..ZAFAFA FAM😘👋
______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*
Chapter 21 · 0% Book details