← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 114

Sashe 3

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kai! Aradun Allah bani ba yin karatu, kullum kana zaune cikin wani ɗaki, na taɓa ganin yadda ake zama a wani fim da muka kalla gidan kansila, wallahi Baffa bani ba zama guri gudu kamar akuya a daure.”

Sai na tashi nayi tafiya ta na barshi a gurin, nasan yana tausaya min kawai babu yadda zai yi min ne, na tafi nayo faɗa ko na siya sai na samu abin da zan sawa ciki na.

<<<<>>>>> <<<<<<>>>>

Ranar wata laraba da safe misalin karfe takwas Kauyan mu ya samu halartar wasu mutane daga can birni, su kusan goma sha huɗu suka zo a mota, yan garin mu suka cika kofar gidan mai gari kasan cewar anan bakin suka sauka. Mune yan sahun farko a wajan kallo, mun kasa mun kuma tsare kamar wadanda aka tilastawa zama. Suka zauna akan tabarma suka korawa mai gari jawabin da yake tafe dasu akan cewa za'a zo a buɗe makarantar boko a kauyan saboda yara su samu ilimi. Tunda jama'ar kauyen mu suka ji wannan al'amarin suka fara bijirewa suna tsinewa wanda ya bada shawara da umarnin cewa azo a gina makarantar bokon.

”Gaskiya bama so, mu ba arnaye bane.” Na faɗa da karfi yadda kowa sai da ya juyo yana kallo na.

”Ke! You're very very stupid, kinga sa'anninki a cikin maganar da ake yi?”

Cewar wani mutumi da yake sanye cikin kotu (suit) sanye da gilashi fari a idanunsa. Yadda naga yana hararata ya tabbatar min da cewar ransa a ɓace yake da furuci na, dan haka na yi fari da ido na tare da turo baki na gaba ina kun-kuni. Kalmar sa ta very stupid ta tsaya min a zuciya tana sani jin wani nishad'i, duk a zato na kalmomin farin ciki ne. Mai gari ya gyara zama ya kalli manyan dake zaune dashi wato mai unguwa, liman da dai sauransu yace.

”Ku duba wannan zancen nasu, ya kuke ganin za'a yi. Shin mu yadda da umarnin gwamnati ko kuwa dai a barshi ba sai an yi ba tunda ba wai sabawa mukai da irin karatun ba?”

”Beri sutufid....!”

Na faɗa bayan mai gari ya kai maganar sa karshe.

Duk suka buɗe baki suna kallo na da tsantsar mamaki a fuskokin su. Ni kuwa ban gane ba na ci gaba da ƙirgar duwatsu ina sawa a cikin ramin da na yi ina kirgawa. Wani saurayi da yafi kowa kankanta a cikin bakin ya taso yazo gurina tare da kafe ni da ido yana yatsina fuska tamkar yaga kashi yace.

”Ashe baki da mutunci?”

”Aramma da na yi maka me?”

”Ohhh! Bama kisan abin da kikai cewa mai gari ba ko? Saboda baki da mutunci kinga saanininki a can gurin?”

Ya faɗa yana nuna da'irar da suke zaune, na gyada kai alamun a'a ban ga sa'ana ba.

”Toh ki sake magana a gurin nan ki gani, sai na turmushe wannan dogon hancin naki mai kama da yatsun kaza.”

Yana gama faɗa ya koma gurinsa, ya yin da yaran gurin suka saka dariya saboda tanka min hanci da ya yi, ni kuma na dinga shafa hancin nawa dan gano ko da gaske yake yi irin yatsun kaza ne. Haushi ya kamani da na gano cewa rashin mutunci kawai ya yi min. Daga cewa very stupid kawai zai tanka min halittar da Allah ya yi min. Na sake dubansa tsab daga sama har ƙasa naga shi sam bama shi da hancin har yake tanka nawa, haushi ta ishe ni na yi kwafa dan bani da abin cewa kuma. Can kuma ana ta kai ruwa rana tsakanin jami'an birni da namu na gargajiya sun kafe kan cewa ba za'a kawo musu wata makaranta ba indai ba ta addini ba, a ganin su zuwan boko zai sanya al'adun mu da tarbiyar mu zasu lalace. Da kyar da sidin goshi Allah yasa suka yarda suka amince.

Bayan bakin sun tafi mai gari yasa aka kirawo mutanan gari ya shaida musu duk abinda suka tattauna tare da sharaɗin cewa indai aka kammala gina makarantar, dole kowa zai kai ɗan sa ko ƴar sa dan a koyar da su karatu. Hmmm Ina daya daga cikin yaran da basu son makaranta, Baffa na ya kira ni ya yi ta lallashi amman fur na ce ba zan yi boko ba dan bazan je nasha wahala ba.

Ci kawai nake ina shaƙewa saboda rashin ruwan da zan kora dashi, gashi sai loma nake dan kara Gajiyalle ta shigo ta kwace. Sai da naci kusan rabi na ajiye ragowar ba dan na koshi ba, a'a tausayin Baffa naji dan nasan shi zai zo yaci shima ya kwanta. Na sake lallaɓawa na leko tsakar gidan naga babu kowa sannan ta yi wuf na shige inda nake kwana tare da jigawa jikina kayan wankin Gajiyalle ta yadda ba zata gane ina ciki ba. Kamar dama ɗan lokaci Allah ya aramin sai kuwa naji muryar ta a tsakar gida tana masifa ita kadai.

”Wato wannan shegiyar yarinyar ba zata dawo gidan nan ba ko? Daman ta saba zama a titi dan haka yau idan ta kwana a can ba wani abin tashin hankali bane, ja'ira kawai da fuskarta kamar kwallon kwakwa.”

Ni dai tun daga nan ban sake jin muryarta ba kasan cewar bacci mai nauyi da ya ɗauke ni. Kiran sallar farko naji an kwaro min ruwa mai wari da doyi a jikina, gashi sanyi karara dashi, na tashi a firgice ina neman hanyar fita.

”Ina zaki munafuka? Yau mai rabani dake a gidan nan sai Allah dan kuwa sai na yi miki jina-jina da fatar jikin ki.”

”Dan girman Allah Gajiyalle kiyi min rai, dan Allah karki doke ni wallahi na dena bazan sake yi miki gardama ba, kiyi hakuri.”

Wata irin bulalace da ko kaɗan bata karyewa da ita Gajiyalle take doka na duk sanda taso. Da yake ba mutunci da tausayi gare ta ba, haka ta zage ta dinga labtar min jiki kamar ta samu jaka. Baffa ya fito daga cikin ɗakin sa yana son ya kwace ni amman Gajiyalle ta haɗa dashi wajan dukan tamkar wasu ya'yanta. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta rabu da mu. Baffa ya rungume ni a jikinsa yana shafar baya na, duk da bai yi magana ba a zahiri, baɗininsa a bace yake, gashi ba zai iya yi mata hukunci ba, shi kanshi wani lokacin shakkarta yake yi.

”Gobe ma na kuma saki aiki kiyi min rashin kunya, wallahi sai na dinga lallasaki a gidan nan marar kunya kawai. Kuma ki tashi kije ki debo ruwa dan ko na wanke fuska ba zaki samu ba a cikin gidan nan. Tashi nace ko nazo na sake zaneki a nan gurin.”

Baffa ya sake ni da sauri, ganin haka da nayi ne yasa ni kuma fashewa da kuka ina tuna mahaifiya ta. Nasan da tana raye ba zata bari ayi min wannan wulakancin ba, duk yadda za tayi sai ta sanya ni farin ciki, ba zata zuba min ruwan dauda mai wari ba bare har ta sanya bulala a jikina, uwa akwai daɗi duk lalacewar ta tasan muhimmancin abin da ta haifa. Na sosa cikin idona zuciya ta na sake tsagargarewa na kalli Baffa sannan na dakko mayafi na wani baki da kullum shine a jiki na tamkar na gado, na yi damara tare da nufar kofar gida. Sai da nayi kamar zan ɗauki abin dibar ruwa sai kawai na ruga da gudu na bar musu gidan.

”Bazan debo ruwan ba wallahi sai dai ayi kuli-kulin tara sisi dani, an mai dani jakar gidan ko? Toh sai dai a yanka ni aradu dan na dena wahala a gidan uba na, kiji ni da kyau Gajiyalle.”

Ina gama faɗa na tsaya a kofar gida, Baffa sai kira na yake amman nayi shiru dan idan na amsa mai dani zai yi ta doke ni ba iya cewa komai zai yi ba. Duk da cewa duhu ne garin masallacin kofar gidan liman ana ta assalatu da yake akwai farin wata sai ban wani ji tsoro ba, haka na fara tafiya ga sanyi saboda a jike nake iska na sake hurani naje na zauna a kofar gidan Aramma Auwalu, da yake akwai buhun-hunan taki a wajan. Zuciya ta ce take ta hasashen yadda zan yi na samu kuɗi yadda zan wulakanta Gajiyalle domin rashin su ne yasa ta mai dani tamkar wata bola abar zuba datti. Ina nan zaune har Aramma Auwalu ya fito ya wuce masallaci ba tare da na bari ya ganni ba, a gurin bacci ya kuma ɗauke ni duk da irin iskar da take shiga jiki na.


ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

*MISS XOXO*
*ZAFAFA BIYAR (2021) NA KUDI NE !(PAID STORIES) KAMAR YADDA KUKA SANI, LITTATTAFAN NA ZUWA MUKU NE GUDA BIYAR CHAS. DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHI MAI RAHUSA NERA DARI BAKWAI (700 NAIRA ONLY). *

*KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR. DAN ALLAH KI SIYA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI YAR’UWA, AKWAI KARUWA SOSAI ACIKIN BOOKS DINNAN. MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.. DOMIN MALLAKAR NAKI BIYAR DIN, KI TUNTUBE MU A PAYMENT DETAILS DINMU DAKE ‘KASAN WANNAN SHAFIN..*

*KIBIYAR AJALI.....!!!*
(Sulke baya tare ta sai ta wuce..)
👑🥰❤️

*MISS XOXO🧕🏼*

*WHO DOESN'T LOVE A ROMANCE NOVEL? 😉*
*ITS EASY TO LOVE EACH OTHER WHEN DIFFICULTIES NEVER CROSS YOUR PATH. 🤔HOWEVER, IN REAL LIFE, ALL RELATIONSHIPS ARE TESTED AT ONE POINT OR ANOTHER. 😓❤️🥂*

*BABI NA UKU*
(FREE PAGE)🏌️‍♀️
Chapter 3 · 0% Book details