Sashe 51
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jakadiya ta bar sashen tana ta bata hakuri. Aikuwa Shaheedah ta kira mahaifiyar ta cikin tashin hankali ta sanar da ita cewa ta kasa haduwa da Salman yace baya bukatar ganin kowa. Ta shiga kwantar mata da hankali tare da shaida mata cewa ta bari za ta yi wani aiki a kan lamarin. Ai kuwa kafin wani lokaci sai gashi sarki Salman ya kirawo Shaheedah a waya yana shaida mata ya dawo amman zai huta ne zuwa wani dan lokaci, yanayin da taji muryar shi ne yasa taji zata hakura da zuwa inda yake har sai ya huta zata ji zai ma fi gane abin da zata sanar dashi. Ta koma wani daki inda ta ajiye kayayyakin da ta zo dasu, ta dauki wani abu a cikin wata yar tukunya, ta zuba a borner, aikuwa dakin ya dauki hayaki mai kauri, ita kam ko a jikinta. Alamun warin baya damunta sam-sam.
Misalin karfe uku na rana ina kwance a kan gado ina bacci cike da jin dadi, kawai naji kamar ana tashi na, na yi juyi kafin na bude ido a hankali. Babu kowa hakan yasa na kuma gyara kwanciya ta naci gaba da yin bacci na harda murmushi saboda tsabar dadi da ya yi min. Sake tashi na naji anyi wannan karan amsawa nayi.
“Uhmmm....”
Abin mamaki ba a dena tashi na ba sai da na tashi da sauri ina buge hannun da naji yana tashi na akan kafada, a fusace nace.
“Wai meye ne?”
Na bude ido fuskata da alamun bacin rai, abin da na gani shine ya sani sakin wata gigitacciyar kara tare da sakkowa daga kan gadon na fito da gudu sakamakon wata irin halitta da na gani a kusa da fuskata. Bakikkirin ne gashi d'an guntu, ma'ana wada ne, hakoransa zako-zako, idanuwa jajur kamar wanda aka zubawa barkono. Hadimai na sai taro ni suke yi ina turo su ina faman ihu kamar wata zararriya, koda yake zarewar nayi tunda naga halittar da ban taba gani ba a rayuwa ta. Ganin ina shirin fita daga cikin sashe na yasa duka suka rike ni da karfi suna tambaya ta abin da yake faruwa.
“Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun, yana daki na wallahi aljani ne. Na ganshi da ido na.”
“Subahanallahi ranki ya dade Kodai sharrin mafarki ne? Amman duk muna parlor bamu ga wani abu da ya shigo ba.”
“Daman nasan haka zaku ce, na tambaye ku kuna jin wari kunce a'a, a karshe a gabana kuka sake gyara jeran aka goge ko'ina. Still ban dena jin warin nan ba kamar na mutuwa. Yau gashi ina bacci an je an tashe ni naga abin da na gani kunce min babu komai mai koke tunani toh? Zan yi karya ne ko zan yiwa wani sharri?”
Duk sai suka yi shiru kansu a kasa, sai da daya daga cikin su tace.
“Ranki ya dade kiyi hakuri ki koma ciki kafin mutane su ji a fara surutu. Zamu dudduba mu gani ko meye zamu fito dashi.”
Naja gwauron numfashi tare da saukewa a hankali, ta ya zasu gane yadda nake ji a cikin gidan nan? Koda yake kila dan na kasa kwantar da hankali na ne shi yasa bana jin dadi har nake ganin wadannan abubuwan. Da kyar na iya daga kafa na koma ciki amman sai na zauna a parlor, suka shiga suna ta dube-dube ko zasu ga wannan abun da na gani amman babu komai. Na dinga girgiza kai cike da takaici, kamar na ce su nemo min lambar Salman dan ji nake tamkar na zazzage shi, amman sai naji nauyin haka, ace kamar ni bani da lambar shi sai na fito na samu? Kuma idan ya dauka me zance dashi bayan ko muryarshi bana son ji....?!
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
*ZAFAFA BIYAR (2021) NA KUDI NE !(PAID STORIES) KAMAR YADDA KUKA SANI, LITTATTAFAN NA ZUWA MUKU NE GUDA BIYAR CHAS. DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHI MAI RAHUSA NERA DARI BAKWAI (700 NAIRA ONLY). *
*KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR. DAN ALLAH KI SIYA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI YAR’UWA, AKWAI KARUWA SOSAI ACIKIN BOOKS DINNAN. MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.. DOMIN MALLAKAR NAKI BIYAR DIN, KI TUNTUBE MU A PAYMENT DETAILS DINMU DAKE ‘KASA*
*28....*
_*KIBIYAR AJALI.....!_*
_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_
🏹🥰😍
*MASARAUTAR BASANNABAS*
Shi kuwa sarki Salman yana daki ya rasa abin da yake yi mishi dadi, jikinsa ya yi zafi rau kamar wanda ake gasawa cikin oven haka yake ji. Manyan rigunan da yasa basu ishe shi ba ya kara da barguna a jikinsa nan ma beji sassauci ba, sai karin zafin da yake ji. Wani irin kuka ya saki mai cike da rauni saboda Allah kadai yasan yadda yake ji a jikin nasa. Kukan da tsuntsaye keyi a saman dakin kuwa, ji yake kamar yana tsakiyar mai Dj, karar ta yi masa yawa sai rike kai yake yana juyi akan gadon. Bakin sa yana rawa ga kuka mai sauti da yake yi yana cewa.
“Wayyo Allah na.... Wayyo Allah ka tausaya min wuta jiki na zata kona ni... Wayyo ni.”
Magana yake yi tamkar yana yi da wani a kusa dashi, sai faman nishi yake yi yana juye-juye. Har dare ya yi bai fito ba, hakan ne ya d'an bawa dakarunsa na kofa mamaki, anyi magariba bai fito ba, ga isha'i anyi still basu ji koda motsin shi ba, sai suka fara tuhumar kansu Anya kuwa lafiya sarki be fito ba? Tunda suke dashi basu taba ganin ya yi haka ba, ko ciwo yake yi yana kokarin yin sallah amman yau shiru.
Kasa shiga suka yi saboda tsoran kar wani abu ya same shi, sai daya daga cikin masu tsaron kofar ya tafi ya sanarwa waziri. Kusan a tare suka isa sashen nashi, waziri da shamaki suka shiga suna mika gaisuwa gareshi. Babu kowa a ciki amman kan gadon an jibga bargona, waziri yasa hannu ya d'an daga bargunan kawai suka ganshi sai rawar sanyi yake yi.
“Subahanallahi, Allah ya kara maka lafiya ba ka da lafiya?”
Sarki Salman ya kasa komai bare ya yi musu alama, Waziri ya kalli Shamaki cike da tashin hankali yace ayi maza a kirawo likita yazo ya duba shi. Kai arziki kashi kafin kace kwabo sai ga likita da kayan aikin shi, ya shiga duba shi ta hanyar yi masa gwaje-gwaje. Amman babu abin da ya gani, sai dai ya yi masa allura wacce zata dauke masa zazzabin.
A lokacin ne daya daga cikin fadawan sarki Salman ya yi sallama daga nesa yace dasu Gwaggo Hajara wato gwaggo ta fada tazo tana so a yi mata iso ciki. Ba karamin mamaki sukai ba da jin zuwan ta, suka fara tambayar kansu me ta zo yi a daren nan? Sai dai babu mai basu amsa dole sai ta shigo sunji daga bakin ta. Sanye idanunta da gilashin kara gani (medicated glasses) irin brown d'in nan na tsofaffi. Su waziri suka gaishe ta cike da girmamawa ta kalli kan gadon taga Salman kwance kamar matacce, ta karasa gurin tare da dafa goshin shi taji zafi.
“Subahanallahi! Me yake damun sa haka?”
“Wallahi gwaggo ta fada muma zuwa akai aka ce mana ba'a ji motsin shi ba, shine muka zo sai muka tarar dashi cikin wannan yanayin.”
“Ikon Allah, munyi waya dashi yace yana son gani na dan Allah na taimaka nazo, shine ina idar da isha'i nasa driver ya kawo ni. Ashe zan zo akan gaba, na tarar bashi lafiya.”
Sai suka ga yayi wata irin zabura tare da wancakalar da bargunan jikin shi yana ta wani irin kuka marar dadin ji. Gwaggo ta kalleshi sosai taji a jikinta cewar tabbas Salman baya cikin haiyacinsa, koma menene aikata mishi ake yi har yanzu. Su kuma su waziri suna ta faman ririk'e shi, Dr Naufal yana kokarin zuko allurar bacci dan ya yi masa ko za a samu sassaucin kukan nasa da kuma yunkurin tashi da yake yi.
“Ina matarsa? Da kuma amaryar da aka ce ya yi?”
Waziri ya gaya mata cewar kila suna sashen su, amman bashi da tabbas tunda be sa an bincika ba tun dai dazu da aka tabbatar masa kowace tana bangaran ta.
“Allah ya baka lafiya Salmanu, Allah ya yi maka maganin duk wani mai son ganin bayan ka a boye ko a fili.”
Daga haka ta zauna a gefen shi tana ta yi masa addu'a tana tofa masa, amman mai makon sauki sai ya zamana tamkar tofin kara masa wani wutar yake yi, gwaggo ta gane hakan ne ganin idan ta karanta ayatul kursiyu ta tofa masa sai ya kara gigicewa yana dukan su wambai.
“Ko zan samu alfarmar ganin matansa?”
“Gwaggo yanzu?”
Cewar Waziri cikin sanyin jiki, da alama baya son su zo su ganshi a haka, mata ne zasu iya gigicewa.
“Eh kafin na koma can gida na ina son ganin su. Ba matansa bane ba? Suna da hakki su ji halin da mijin su yake ciki.”
Su waziri suka yi shiru basu saka an je kiran su ba, kuma basu cewa gwaggo komai ba, sai da kanta ta fito zata sa a kira mata Jakadiya. Sai gata ta taho cikin sauri daga gurin su Gimbiya Jaleela take, dama tunda taga zuwan gwaggo ta Fada tayi saurin zuwa ta sanar da su, shine suka turo ta dan taji abin da ya kawo ta koda kuwa ba komai ba. Ko amsa gaisuwar ta ba tayi ba, tace taje sashen uwar gida da amarya ta kirawo su tana son ganin su.