Sashe 62
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da muka fara ajiye Adda Maryama a sashe na sannan Gwaggo ta sanar da shi inda zai kai mu. Abin da ya daure min kai shine wani sashe muka shiga, wanda ko ranar da aka kawo ni na zazzaga ba'a kai ni ba. Shiru banyi magana ba duk kuwa da tarin dimbin tambayoyin da nake son yi mata.
Tunda muka fito daga cikin mota hadimai suka fara yi mana kirari tare da barka da zuwa har muka shige cikin sashen da gwaggo tasa driver ya yi peeking. Tun daga babban parlor zaka gane inda ka shigo saboda wani katafaran hoto dake sakale jikin bango yana kallon kofar shigowa. Gabana ya yi mukun bugawa lokacin da nai ido biyu da hoton, sai dai karfin da addu'ar baki na ta yi shine ya hanani shiga cikin wani yanayin na daban.
Babu kowa a cikin parlorn, Gwaggo ta nuna min kujera na zauna, tana shirin zuwa wani daki sai ga Abdullah ya fito yana faman hade rai, alamar wani abu ya hado shi da mahaifiyar tashi. Har zai wuce be gaida Gwaggo ba, sai kuma ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba ya shiga mika gaisuwa. Itama kin amsawa ta yi sai binshi shi da kallon sama zuwa kasa tana tabe baki tace.
“Ashe ka dawo?”
“Eh na dawo, ya gida?”
“Yana inda kasan shi. Kai yanzu Abdullah duk tsahon lokutan nan ina kake tafiya baka zuwa ko hutu? Ko ka manta har yanzu mahaifiyarka tana nan a raye? Baka koda sha'awar zuwa ka ganta sai lokacin da ka fa dama kamar haka ko?”
Ya yi shiru ba tare da yasan abinda zai iya furtawa ba. Kada kai kawai ta yi ba ta kuma cewa dashi komai ba ta shiga cikin dakin, ya yin da shi kuma ya turo baki ya fara tafiya ya ganni zaune ban masa magana ba shima kuma be yi min ba, sai dai ya tsaya cak yana bina da ido tamkar ya sanni. Na dago ido muka hada dana juna sai duk muka sauke a kusan tare, yana kama da Salman, sai dai Salman ya fishi cikar zati, sannan shi yana da matukar haske, amman daka gansu kasan cewar tsatso d'aya ne ya haife su.
“Uhmm....Ke kuma fa?”
Na samu kai na cikin izza ta yadda naki koda nuna cewa dani yake, sai da ya kuma yin magana sannan na kalleshi a yatsine.
“Kai ma waye?”
Ni ma na tambaye shi ta irin sigar da ya yi min tambayar, na kuma dauke kai na zuwa kallon gefe.
“Kut...! Kin san ko waye ni kuwa? Toh idan baki sanni ba baki san matsayi na ba ki tambayi ta fada zata gaya miki. Mtseww.”
Ya karasa yana jan tsaki duk da cewa na yi masa kwarji duba da ko ido baya son mu hada. Saboda kar ya yi tunanin wani abun hakan yasa na dan daga murya yadda zai jiyo ni sosai nace.
“Na ce maka ina son sanin ko kai waye ne? Bana bukata dan haka kar kai tsammanin zan tambayi Gwaggo.”
Abdullah ya juyo a fusace yaga alamar nima bani da mutunci yadda yake magana nake mayar masa a matsayinsa na yarima dan marigayi sarkin Basannabas kuma kani gurin sarki mai mulki a wannan lokacin. Sai da yazo dai dai inda nake sannan ya tsaya yana kuma kare min kallo, ganin ko motsawa banyi ba yasa shi dan matsawa baya kadan yana cewa.
“Da me kike takama ne?”
Kai tsaye nace dashi.
“Allah... Da shi nake takama a duk cikin lamari na.”
“Ba wannan nake nufi ba. Nayi zaton ko kina takama ne da mulki ko sarauta.”
“Kai a zaton ka sune kawai abin takama a cikin duniyar nan? Akwai yan kasuwar da sunfi masu mulki da sarauta komai na rayuwa. Akwai kuma masu takama da ilimi kaga kenan abubuwan tin kaho suna da yawa.”
“Ke d'in a wane rukuni kike? Ina son naji.”
“Kaje ka tambayi duk wanda kake so a cikin masarautar nan, zaka samu amsar ka yadda ya kamata. Sannan bana son wata tambayar, ina bukatar hutu yanzu.”
Kamar daurin baki ya kasa cewa dani komai haka ya juya ya fita yana huci kamar wani tafasasshen ruwan zafi. Ni kuma na saki murmushi cikin rai na ina jin babu wanda zan bari ya rai na min hankali a cikin kannansa, dan naga alamar suna da jiji da kai irin na yaran masu farcen susa.
Cikin daki kuwa da Gwaggo ta shiga, tarar da Gimbiya Sa'adatu tayi tana faman girgiza kai alamar wani abun Abdullah ya yi mata. Sai da Gwaggo tayi sallama kusan hudu sannan ne Ammie taji tayi saurin amsawa tana kallon bakin kofar.
“Kina na kin ci gaba da sanya matsalar yaran nan cikin ranki ko?”
“Ba haka bane Gwaggo, sannu da zuwa shigo ciki.”
“Na shigo ciki kuwa, saboda tare nake da yarinya a can parlorn.”
“Au to bari ni na taso muje can d'in, ko Maryama ce?”
“Ba ita bace ba ma. Bari ina so muyi magana dake kafin muje parlorn.”
Jin haka yasa Ammie komawa ta zauna, itama Gwaggo guri ta samu ta zauna tana sauke numfashi.
“Zahiri da badini kowa yasan kina cikin damuwa Sa'adatu, an shiga hakkin ki sosai. Amma ki kai ta hakuri, kuma yanzu ma shi zan ce ki ci gaba da yi saboda shine kawai zai fitar dake da taimakon Allah.”
Tayi murmushin karfin hali saboda ta nunawa Gwaggo cewa babu komai, sai dai ta makara dan tuni Gwaggo ta Fada tasan cewa duk abinda zai fito daga bakin ta dauriya ne kawai da iya yadda da kaddara a duk yadda tazo.
“Gwaggo ai babu wani abu, kamar yadda kika fada ne komai yana da ranar karshe. Fatana kawai shine Allah ya kara min karfin gwiwa, na ci gaba da yadda cewa komai daga gare sa yazo min. Na gode da kulawarka akan duk wani lamari na, Allah ya ji kan iyaye da kakannin mu.”
“Amin... Amin Sa'adatu, daman bakuwa ce kuma yar gida na kawo miki ita dan na hada ku kusan juna. Idan har ba haka na yi ba toh ban san lokacin da za'a nunawa kowanne a cikin ku matsayin juna ba. Amaryar Salman ce kawo miki ita dan tace ran da tazo ba'a kawo ta gurin ki ba har na sauke ta.”
Kirjin Ammi ya buga, a farkon auran da taji labari ta yi murna sosai. Amman ganin har tsahon wannan lokacin na yau bamu hadu ba yasa ta karaya tayi zaton ko nima haka nake kamar su Shaheedah masu jiji da kai.. Muryar Gwaggo ta Fada ce ta katse tunanin ta, inda take cewa.
“Baki da matsala da yarinyar nan yar mutunci ce, tana da nutsuwa da hankali dan gaskiya Salman ya yi dacen mata. Kuma insha Allahu alkairi ne a tsakanin su damu baki daya.”
Jin haka yasa Ammi yin murmushi saboda babu abinda take bukata a cikin rayuwarta irin taga wanda zai so su tsakani da Allah babu wani tuggu a ciki. Ta dinga kallon kofar shigowa dakin da alama ta kagu ta ganni, hakan da Gwaggo ta gani ne yasa tai dariya tare da cewa.
“Zaki iya zuwa parlorn ne?”
Cikin sauri Ammie ta ce.
“Eh zan iya.”
“Toh muje ku gaisa, daga nan dakin ta zan mai da ita.”
Jin ta ambaci daki yasa ta tunawa da tijarar da Abdullah yazo ya yi mata yanzu, na cewa wallahi sai an bashi sashen shi babu inda zai koma. Gashi wadda aka bawa gurin ta dawo bata san yadda zata yi masa bama yanzu, dan koda ta lallaba shi da cewar ya bari za tai magana kin yadda ya yi, har da cewa waye zai ji maganar ta a masarautar bayan duk sun rai na ta.
Da wannan tunanin ta mike da kyar ta gyara hijab din jikinta ta bi bayan Gwaggo ta Fada. Lokacin da suka fito bacci ya fara dauka ta a zaune, har sai da Gwaggo tai min magana sannan na farka cikin sauri ina murza ido. Na sakko kasa ganin sun fito da wata wacce nake da yakinin cewa mahaifiyar Salman ce, na kasa kallon ta sosai bare na gane da ita yake kamanni ko kuwa da mahaifinsu.
Har suka samu gurin zama ban dago ba, haka kawai naji nauyin dago kai na. Ina shirin gaida ita sai naji muryar Gwaggo tana cewa.
“Khadija ga mahaifiyar mijinki Salman ku gaisa.”
Kamar jira nake a bani dama, cikin ladabi da sunkuyar da kai na gaishe da ita, ta amsa cike da fara'a kamar daman ta sanni yadda naji tana ta murna. Daga nan kuma hira ta barke ni dai murmushi ne kawai nawa bana iya cewa komai saboda yadda suke min kwarjini duk kan su, har Adda Maryama ta shigo itama ta zauna aka dora da ita, Ammie tasa mai yi mata hidima ta kawo mana abubuwan motsa baki, duk muka ci a tare bisa umarni Gwaggo, kuma da alama Ammie taji dadi dan ta ware sai hira take cikin jin dadi wanda ta manta rabon da taji makamancinsa.
“Ga magani nan mun taho dasu, akwai wanda naki ne sai nasu Abdullah. Ku fara yin amfani dashi muga yadda zai kasance, insha Allahu komai zai tafi azo aga kamar ba a yi wata rayuwar ba makamanciyar wannan da ake ciki.”
Ammie ta karba tana godiya tare da sake jin kaunar Gwaggo ta Fada dan ita ce kawai mai jin ciwon duk abubuwan da ake yi mata a cikin masarautar Basannabas. Daga nan muka yi mata sallama su Gwaggo da Adda Maryama suka yi min rakiya zuwa sashe na bayan anyi yayyafin ruwan ganyen magarya a duk inda zan taka, baki na kuma cike da addu'o'i har muka shiga parlor na wanda tuni aka canza kujerun, na karamin parlorn aka dawo dasu babba, na babban kuma aka mai dasu karamin parlorn.
Zaman mu ba dadewa sai ga Jakadiya ta shigo cikin rawar jiki, ganin ta yasa Gwaggo ta Fada tsuke fuska dan tasan irin bakin munafuncin dake cikin Jakadiya, shi yasa ta tsane ta fiye da abin da baki zai furta.
“Ya akai Jakadiya?”