Sashe 27
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin wasa nayi maganar dan karma ya karasa nasan maganar ta rashin kunya ce, aikuwa naji kit ya katse babu shiru. Na kwanta kan gado ina ta dariya dan banyi wannan zaton ba na cewa zai ji tsora idan na yi haka koda ma ace da gaske Kawu Isma'eel din ne ya shigo. Ya Waleedah ce ta shigo dakin, nayi saurin mikewa zaune tare da hadiye dariyar da nake yi ina gyara zama na tace min.
“Lallai Dije, saboda kawai ance kiyi girki baki ga dama ba shine kika yi ta yadda kika ga dama ko? Suwaye kike nufin zasu ci wancan jagwalgwalon da kika yi? Toh kije Mami tace yanzu ki yiwa Daddy tuwon shinkafa da miyar zogale kafin ya dawo.”
Nayi saurin kallon agogo dake makale jikin bango naga karfe takwas da arba'in da hudu na dare, shine ake son nayi tuwo kuma wai na shinkafa saboda tsabar ana son a wulakantani. Toh wai dan Allah me nayi musu? Meye laifi na a cikin gidan nan? A gani na tunda kyautatawar da kawu yake yi min ne basu so me zai sa su hanashi ya dinga yi min tunda sun fini kusanci dashi? Sun takura min Allah Allah suke nayi abinda zasu yi min rashin mutunci kuma Allah yana kare ni sai dai su kirkiro wani abun su lika min. Sai kawai na gyada kai tare da sakkowa daga kan gadon nace mata.
“Toh Yaya bari nazo.”
“Ya fiye miki kam.”
Ta juya ta fita ni kuma na zauna a bakin gado zuciya ta tana zugi. Wai dama haka rashin iyaye yake? Kodai ni kadai ce bana dace da marika nagartattu? Tabbas duk lalacewar iyayen ka, duk talaucin ku, duk tsiyar ku gwara ace kana tare da su akan kana hannun wani da basu ba. Naja majina tare da tashi na saka wayata a charge sannan na fita zuwa kitchen dan dora tuwon kamar yadda aka umarce ni.
Ruwan tuwon na fara zubawa sannan naje na debo shinkafar na wanke na zuba sannan na nufi gurin hada abubuwan da zanyi miya. Banda Daddy ne zai ci wallahi sai na yi rashin mutunci naki tuke tuwon sosai, to dan dai kawai shine zan tsaya na yi har ya yi dadi. Ina jiyo muryoyin su daga kitchen, ba bu wanda ya leko ni yaga a wane hali nake ciki saboda ba damuwar su bane ba. Sai wajan tara da hamsin da uku 9:53pm na kammala naje na dora akan dining table a lokacin ne Mami tace min.
“Kin gama ne?”
“Eh Mami na gama.”
“Guda nawa ki ka yi?”
“Leda biyu ne Mami.”
“Biyu kuma! Me ya sa baki yi da yawa ba?”
Nayi shiru dan ba a ce na yi shi da yawa ba, kawu kawai aka ce na yiwa kuma na yi masa dan haka ba damuwa ta bace.
“Shikenan dakko min guda daya ki zubu min miya ki kawo min, idan yazo yaci dayan.”
Ban wani damu ba, nasan idan tace zata cinye ko su Ya Shukrah suka ce zasu ci ba iya hanawa zan yi ba. Ni fatana kawai Allah yasa kar su kuma sanya ni wani abun, ina son naje na huta nima kamar yadda suke yi a yanzu. Na juya naje na sako mata na kai mata sannan nima naje na dibi taliyar da nayi dazu na wuce daki saboda karma su ganni su dinga aike na ko saka ni aiyuka. A daki na naci na wanke hannu ko plate ɗin ban fito dashi ba saboda bana son ma su ganni wallahi dan babu alkairi tsakanin mu.
Washe gari tunda na idar da sallar asuba na shiga kitchen dan shirya breakfast bana son na makara a fara ganin gazawa ta. Ina tsaye ina kada kwai zan soya dan na kammala soya Irish sai ga Mami ta shigo tana yatsina fuska. Daga bakin kofa ta tsaya tana kare min kallo, na yi saurin durkusawa har kasa kamar yadda nake mata tub farkon zuwa na har yau kuma ban dena ba na gaishe da ita.
“Mami ina kwana?”
“Tashi tsaye ni ki dena gaishe ni a kasa, so kike mutane suce gallaza miki nake yi?”
Na mike naci gaba da aikin ba tare da na kuma gaishe da ita ba.
“Kunu zaki damawa Alhaji yace yau ba zai sha tea ba. Kin tambayi su Shukrah sun gaya miki abin da zasu ci ne matsayin breakfast?”
“A'a Mami, nasan suna cin Irish shine ya sanya ni yi. Sannan fa shayi can shima nayi, naga sunfi son shi.”
“Jiya ai sunce wainar fulawa zasu ci, dan haka kinga yanzu sai kiyi musu abinda suke so.”
“Mami dan Allah su taimaka min su ci wannan d'in, idan na dawo daga gurin aiki sai na yi musu. Wallahi Mami bana son yan gurin aikin mu suyi zaton ko bani da serious akan aikin.”
Mami ta saki baki tana kallo tare da fadin.
“Inyeeee, lallai seriously?. Wallahi Dije kinga gurin bacci na. Wato kinfa bawa yan wajan aikin ku muhimmanci akan mu ko?”
“A a wallahi Mami ba haka nake nufi ba kiyi hakuri.”
“No no noooo Dije ai kin isa karki wani damu. Idan kin kammala dama kunun ki kawo min.”
“Toh Mami, amman dan Allah ki....”
Tayi banza dani ta wuce tamkar ba da ita nake ba. Haka ina ji ina gani na kammala soya kwan daga nan na dora ruwa na dama kunun naje na kai mata dakin ta na kuma komawa kitchen na fara hada kullin wainar.
Saboda tsabar rainin hankali sai gasu sun fito lokacin na fara suya, na gaida Ya Shukrah da ta shigo kitchen d'in tana faman gyara earpiece d'in kunna ta. Bata kula ni ba sai kofi da ta dauka taje ta tsiyayi ruwan tea tazo ta dauki wainar fulawa guda daya tare da janyo yaji ta fara ci. Sai da ta cinye wacce ta dakko sannan ta kalle a yatsine kamar ta ga Jummai mai aike a gabanta, ta ce dani.
“Kwai nawa ki ka saka a kwabin?”
“Guda biyu ne.”
“Toh ba bu kwan a gidan ne ki ka saka iya biyu kawai?”
“Akwai Ya Shukrah, amman gani nayi wainar da zan yi ba wata mai yawa bace shi yasa ban sa da yawa ba. Kuma a haka tafi dadi akan ace an kara.! kwai da yawa.”
“Kinga malama, su wa ki ke yiwa? Mu ko ke?”
Haushi ya kamani, toh ko su kadai zan yiwa ai tunda dai zan yi d'in dole nima naci koda kuwa guda d'aya ce. Amman dan kar ta je ta gayawa Mami tazo ta kuma sanya ni wani aikin yasa ni cewa.
“Ta ku ce Ya Shukrah.”
“Toh sai ki kara mana kwan.”
“Toh shikenan bari na kara muku.”
Tana tsaya sai da na kara guda biyar kuma duka duka kulin fulawar gwangwani d'aya ne, sai ya yi kauri tamkar ba fulawa ba. Juyawa tayi ta bar kitchen din dama jira take taga ko nayi abin da tace. Na ja tsaki a can kasan magogwaro na naci gaba da su ta, itama Ya Hameedah tazo ta diba ta koma parlorn suna ci. Ko sha'awa bata bani ba haka na shirya na yi tafiya ta gurin aiki. Bayan na shiga na yi program din da zan yi sai kawai fito muka hadu da Mas'oud muka ci gaba da hirar mu ta masoya.
••••. ••• •••
Haka naci gaba da rayuwa ta a gidan kawu na mai so na, shi kadai ne yake min abu a matsayin uwa da kuma uba da zance na rasa a rayuwa ta. Bayan wasu yan kwanaki naje gurin aiki ina shirin shiga studio na hango M.D da wasu ma'aikatan gidan a tsaye suna magana, sai na juya na karasa inda suke na gaishe su cike da wasa da dariya, har na tashi zan tafi sai mai kula da sashen siyasa na gidan radion ya dakatar dani tare da cewa.
“Malam Khadija ko ke zamu wakilta ne?”
Nace,
“Yallabai ina za a wakilta ni?”
“Wajan taron nan da za a yi ranar Asabar. Kawai ke zamu turo tunda dai kina da himma sai kije ki dakko mana rahoton yadda abubuwa suke gudana a wajan.”
Murna ta kamani dan ni akan aiki na bana jin wani fargaba ko tashin hankali. Dan haka da murna ta na karbi ta yin da suka yi min tare da yin godiya na tashi na karasa dan yin aiki na. Bayan na gama na fito naje wajan Mas'oud na sanar dashi, yana ta tsokana ta wai kar naje naga abubuwa da yawa na rasa wane rahoto zan dakko saboda rudewa. Nayi dariya cike da shaukin soyayyarsa, dan har ga Allah a koda wane lokaci Allah kara sanya min soyayyar shi yake yi.
Yau kam aikin sa har dare hakan yasa ba zai samu damar zuwa kai ni gida ba, sai na yiwa driver waya yazo ya dauke ni na koma gida. Mami na zaune a wajan hutawa naje na sanar da ita cewa gobe idan Allah ya kai mu zanje na wakilci gidan radion mu kasan cewa ni aikin radio nake yi, ita kuma Hameedah nurse ce a asibiti. Shukrah kuma business take yi, Kawu ya bude mata botic a can kan titi tana siyar da kaya kala-kala na gida dana waje masu kyau kuma. Kai kawai ta daga ba ta ce min komai ba babu addu'a bare fatan alkairi, duk ta bi ta kwarzabi kanta damuwa ta yi mata yawa saboda kawai ina cin irin arzikin da yaranta suke ci a wajan mijin ta. Na tashi na shige cikin daki na baki na sai addu'a yake na kar Allah yasa su saka ni aikin da zai hanani shirya abubuwan da zan gudanar a wajan taron. Cikin ikon sa kuwa babu wacce da neme ni saboda sunyi baki ya'yan yan uwan Mamin sun zo suna daki sai hira suke yi.
*WASHE GARI...*