Sashe 95
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallama tayi da mahaifiyar tata, Ta kashe wayar tana sakin nannauyar ajiyar zucia. Ta ina zata fara ne? Sashen nasa zata koma? Ko kuwa zuwa zata dingayi kullum? To idan taga Khadija fa? Wallahi zamu kwashi yan dambe kuwa.... ‘Zuciar ta tabata kwarin gwiwa. Haka taita zance ita kadai tana bawa kanta amsa. Rabin zancen kuwa duk kwashewa dije albarka take.
*GIM. KHADIJAA*
.....Koda gari ya waye, Wanka na sake yi na shirya cikin wata atamfa dinkin bubu, Taje kai na nayi bayan na tsefe kalbar na d’aure da ribbon. Scented hair cream din *yerwaincense&more* na dakko na shafa a cikin gashi na, Ina tuno shi jia yadda yake fadan wai kamshi, Dadi, Laushi... Na daura d’ankwali na samfurin ture kaga tsiya..
Wadataccen babban mayafi na na yafa, Sashen Ammi na fara zuwa da hadimai na guda biyu, Acan na rashe munata hira. Sai bayan magriba na dawo sashe na. Tunawa nayi duk yau banji duriyar Salman ba,
Sake faffesa turaruka nayi na shiga sashen nasa. Yana dakin sa akan gado a kwance yana danna ipad dinsa. Yana hango ni ya mikomin hannu na riko nasa,
“Zawjatii.. Yanzu nake tunanin ki a rai na..”
“Ranka ya dade.. Kaci abinci ko kuwa a dafa wani.?”
“Ni na isa na tashi gimbiya shiga kitchen duk wannan kamshin da take zubawa?..”
Samun kai na nayi da murmushi kawai nace,
“Ka isa har kayi yawa yallabai.. Ko a hado coffee?”
Mikewa nai na isa wajen tea shelf dinsa, Na dau kofi kenan zan dauraye..
Da gudu ta shigo cikin dakin tamkar wata zakanya ranta a matukar tashe, Allah ya taimake ni na sauka daga kan gadon ina tsaye wajan coffee table Ina hada mishi. Kai na tayo gadan-gadan ta shako min wuya na, coffee d'in da na zuba ya baro min a kan kafa ta, shakar da tai min itace ta hanani yin ihu saboda azaba.
Salman dake kwance akan gado yana kare min kallo, shigowarta dakin yasa shi dan zama, ganin ta shako ni kuma yasa shi saurin sakkowa daga kan gadon ya nufo inda muke. Hannunsa yasa yana son ya kwace ni amman ya kasa saboda ba rikon wasa tayi min ba, gashi idanunta sun rufe so take kawai taga bayana.
“Shaheedah ba magana nake miki ba, ba zaki saketa ba.”
Wallahi taki saki na gashi ko kwakwaran numfashi bana iya yi, bacin rai yasa shi daga hannu ya wanke ta da marin da shi kansa besan ya yi mata Shiba. Toh ya yi Iya yinsa wajan ganin ta barni amman taki, shi yasa ya zuciya tare da daukar wannan danyan hukuncin da yana sauke hannu ta sakar min wuya na koma gefe ina kakarin amai idanuwa a waje saboda rudewa.
Shaheedah kuwa shiru tayi hannunta dafe a gurin, tama rasa daga Ina marin ya taho, kuma ta hana zuciyarta amincewa da yarda akan Salman ne ya yi mata shi. Kallansa tayi cikin tsantsar mamaki tana son taji yayi magana yace bashi bane amman taji shiru alama shi d'in ne yayi mata ba wani ba. Idanunta suka cicciko da kwalla ta dinga girgiza kai baki na rawa tace.
“Salman kai ne kasa hannu ka mare ni? Kai ne ka mare ni akan wannan munafukar yarinyar?”
Tsaye yake ko gurin Dijen ya kasa zuwa ya lallashe ta saboda shi kansa yasha mamakin yadda ya Iya daga hannu ya mari mace, macen ma kuma matarsa ta aure ba wata ba. Sai dai yadda yaji tana aibata Dijen shine ya sa shi kallonta a yatsine yace.
“Ke ta yiwa munafinci bani ba Shaheedah. Amman ke ni kike munafinta nasan duk wani makirci naki wallahi. Kinsan Allah? Kallonki kawai nake yi akwai lokacin da zan baje ki a fai-fai ta yadda zaki san waye munafiki a cikin ku, amman yanzu baki san komai game da kalmar munafunci ba.”
Cikin bacin rai da zafin kalamansa duk kuwa da cewa ta firgita jin yace yasan duk wani abu da take yi masa. Amman da yake ita d'in makira ce kuma tasan yadda zata kawar da maganarsa sai tace.
“Ka mare ni saboda kayi sabon aure ko Salman? Akan wannan bagidajiyar kake neman ka wulakanta ni bayan na rufa maka asiri ina tare da kai ban taba jin cewar zan barka ba saboda baka haihuwa. Shikenan wallahi kayi da yar halak Salman, zaka san kuma ka mare ni wallahi.”
Daga haka ta fice fuuuuu kamar wata iska, shi kuma yaje ya rufe kofar ya dawo gurin da nake durkushe Ina kukan takaici da bakin ciki. Kafata ya kamo yana duddubawa saboda yaga yadda nake ta faman rike ta saboda zugin da take min.
“Sorry my love, bari na dakko kankara na saka miki a gurin.”
Bance masa komai ba dan har lokacin ban gama dawowa daidai ba, ya dauke ni ya dora akan gado sannan yaje ya dakko kankara a cikin fridge yasa a karamin towel yana gasa min gurin.
“Kiyi hakuri dan Allah, ni ban ma san abinda ya shigo da ita cikin dakin nan ba.”
Muryata na rawa nace.
“Ga abinda ya kawo ta nan kana gani, zuwa kawai tai fa dan ta kashe ni tunda sunyi Iya yinsu sunga ban mutu ba. Wallahi lamarin masarautar nan tsoro yake bani, na rasa me nayi musu suke neman kassarani.”
"Kiyi hakuri, nasan koma menene ni na janyo miki tunda ni na auro ki na kawo ki cikin masarautar, dadin dadawa ma kema ba so kike yi ba. Amman kiyi hakuri, insha Allahu komai zai zama tarihi. Gobe ki shirya muje gidan kawu daddy ya bamu address d'in gidan uncle na Lagos mu kai masa ziyara.”
Ina haka wani farin ciki ya mamaye ni na manta da halin da nake ciki. Wai zanje na gano su Mami wayyo ni Dije dadi kashe ni. Salman ya tsaya yana kallo na ganin yadda na kasa boye farin ciki na, a ranshi kuwa tausayinta ne sosai. ashe ya dade yana cutar ta be sani ba, yasan tunda ya aure ta bata sake zuwa gida ba sai yanzu da yake yi mata wannan albishir din.
Ya janyo hannuwa na yana son sanya idanunsa cikin nawa amman naki biri, ya tausasa murya bayan ya sumbaci hannu na yace min.
“Nasan kinyi kewar su ko?”
Na daga kai banyi magana ba.
“Toh kiyi hakuri insha Allahu haka ba zata kuma faruwa ba. Yanzu zanje na sanya Falaki ya shirya mana komai a sirrince, kema idan kinje gida bance ki gayawa kowa cewar tare zamu yi tafiyar ba saboda tsaro.”
“Toh takawa babu wanda zan sanarwa.”
“Wai ke meye wani takawa?”
“Sunanka ne ranka ya dade.”
“Haba dear takawa sai kace wani tsoho. Toh ko zamanin su Ammi wallahi nawan take cewa maimartaba bare kuma ni duka duka da shekara nawa kika girmeni.”
Na zaro ido tare da kama habata Ina cewa.
“Na fika ko ka fini? Ai ka ninka ni.”
“Zo mu gani idan baki fini ba.”
Yayi maganar yana kokarin leka min kirji nayi saurin dafe gaban rigar Ina hararasa, daman ta haka ake gane mutum ya girmi wani banda dai yaso ya raina min hankali. Ya dinga dariya kasa kasa yana sake janyo ni jikinsa, kansa a gefen wuya na ya sargafo shi yace.
“Ya kike ji?”
“Na me?”
Wuyana ya shafa alamar da nan yake, nace.
“Na dena jin zafin sai dai har yanzu gurin baya min dadin.”
Shafar gurin ya dinga yi a hankali ni kuma ina lumshe ido saboda yadda nake jin dadi, ya tashi daga baya na ya dawo gabana tare da kura min ido. Mamaki ne ya cika ni hakan yasa ni saurin yin magana ina murmushi kasakasa.
“Ya haka ne?”
“Tsoro nake ji Kar sai na kaiki gida ki cewa kawu daddy ba zaki dawo ba, ko ki gaya masa irin kalubalen da kike fuskanta a cikin masarautar nan.”
Na zabga masa harara Ina cewa.
“An gaya maka ni din yarinya ce.” Murmushi ya yi yana kallona.
“Oops na manta ashe fa an zama manyan mata.”
Yunkurawa nayi zan tashi ya yi saurin mai da ni yana dariya ni kuma nayi kicin-kicin da fuska ya rungume ni yana cewa.
“Sorry har yanzu ke yar babba babba ce kuma yar karama karama tunda sau biyu ne a...”
“Ni ka bar ni na tafi tun kafin waccen matar ta debo min mutanan masarautar nan bana san kananun zance dan zan Iya yi mata dukan tsiya wallahi.”
“Allah my love? Kai zan so naga yadda kike fada wallahi.”
Kamar yana kallo na haka na sakar masa harara kasan cewar ta baya ya janyo ne ya makale ni. Da kyar na samu Salman ya rabu dani na koma sashe na shi kuma ya nufi dakin sirrin sa dan yin bincike. Ina komawa na janyo yar karamar jaka na fara zuba kaya a ciki tare da addu'ar Allah yasa gobe tayi saurin yi dan naje naga su kawu dady.
*GIM. SHAHEEDAH*
Tana baro sashen Salman nata ta nufa Allah ya taimaka bata nuna wani abun ba a hanya da zai janyo mata idanun Mutane, tana shiga ta fara wurgi da kayan dake kan center table, ta ruga dakinta da gudu kamar wacce zaki mayunwaci da ya hango nama ya biyo ta. Kamar mahaukaciya haka ta kuma yin fatali da kayan dake jere kan mirro d'in ta, Sai a lokacin ta saki wani gigitaccen kuka wanda yasa jijiyoyin goshinta suka mimmike.
Kuka take yi sosai ta yake alyabbar jikinta da dankwalin kanta tare da fadawa kan gado tana birgima kamar wata yarinya. Juyi kawai take tana kuka tare da shure-shure da kafafuwa, bakin ta yana rawa take cewa.
“Ni Salman? Ni zaka wulakanta ko? Wayyo Allah Salman karka min haka, karka ce zaka wulakanta ni akan wata ya mace cikin duniyar nan.”
Ta zabura da sauri kamar an tsunkule ta taje ta dauki wayarta, a kunne ta kara bayan ta yi danne-danne a ciki. Bata dena kukan ba har aka daga, babu ko sallama haka ta fara magana a haukace.
“Na shiga uku hajjaju yau Salman ya mare ni, Mari na ya yi akan waccen annamimiyar yarinyar.”
“Kambalasti.... Kina nufin kice wannan maganin da su Falmata suka ce kinyi ya fara aiki a kan su, yanzu kina so kice min karya ne duk a banza?”