Sashe 34
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin kalamanta yasa ransa fara tafarfasa saboda zafin su da yaji, bata da wani abu da take yawan yi masa gori irin rashin haihuwar sa. Amman saboda tsabar shakkarta da yake yi sai bai ce mata komai ba har ta kuma yin magana.
“Ni wallahi kasan ba da ban soyayyar da nake yi maka ba, da tuni nasa ka sauwake min naje nayi wani auran na haihuwa. Amman saboda na san babu matar da zata iya auran ka yasa nake daurewa ina lallashi zuciya ta akan ta hakura ta zauna tare da kai.”
Ta yi shiru na dan wani lokaci, shi kuma wata irin tsanarta ce take sake zama sabowa a zuciyar shi. Shi be ki ta ce ya sauwake mata ba indai har tana da bukatar yin haka, baya jin komai a game da ita sai zallar shakka da son bin duk wani abu da take so. Kansa a kasa dan ko da ta shigo be dago ya kalleta ba sai ji ya yi tace.
“Honey dago ka kalle ni.”
Ta na rufa baki kuwa ya daga yana kallanta, ta yatsina fuska tare da mika hannu ta zare bakin glasses d'in idan shi yadda zata ganshi sosai.
“Haba Honey, ba na hanaka kallo na da wannan glasses d'in naka ba? Na yi na yi da kai ma ka dena saka baki amman ka kasa bari, idan ka sashi kamar wani tsohon makaho wanda bashi da d'an jagora.”
Da yasan wannan maganar ce zata kawo ta da duk yadda zai yi sai ya hana su hadu, sai dai ance rashin sani yafi dare duhu. Kuma idan da sabo yaci ace ya saba da duk wasu abubuwa da ake yi masa a masarautar. Ita kuwa kallon shi kawai take yi tana jin wata zazzafar kaunar shi, hakan ne yasa bata son taji ana cewa ya kara aure shi yasa take kuma rike shi ta hanyar da zuciyarta ta aminta.
“Sannan kullum nice nake nema ka kai babu wani abu da yake damunka. Ina tunanin rashin haihuwar nan taka tana da nasaba da rashin sha'awa da baka da ita. Ko kai kayi zaton sarakuna basa mu'amala da matan su?”
Salman ya yi shiru dan shi sam ba wani farin ciki yake ji ba idan suna yi. Shi kawai yana yi ne ko Allah zai sanya ya samu rahama, ya kuma fita a hakkin ta na aure. Ganin ba zai yi magana ba yasan yata tashi tana murmushi ta wani jujjuya ya masa kugu ya kawar da kai, ba burgeshi take yi ba, hasalima ji yake tamkar ya fashe da kuka dan haushi da takaicin abin da take yi. Tana fita ya sauke ajiyar zuciya tare da rintsa ido kawai ya hangi Dije tana ta yi masa murmushi a wajan fuskar shi. Sai ya samu kansa da kin bude idon yana jin wani dadi a yadda yake ganin ta. Kiran sallar magariba shine ya tayar dashi daga gurin, ya shiga toilet ya daura alwala daga nan ya shirya ya fito zuwa masallaci dan kagabar da sallah.
°°°°°°°° °°°°°°°°° °°°°°°°°°°°
Tun da ta idar da sallah ta mayar da goshinta kasa bata sake dagowa ba, addu'a kawai take yi tana zubar da hawaye. Cikin kaskantar da kai take gayawa Allah muradanta duk kuwa da cewa tasan yasan tana cikin halin bukatar taimakonsa. Sannu a hankali ta dago fuskarta sharkaf da hawaye, tasa bayan hannunta tana sharewa. Gimbiya Sa'adatu kenan wato mahaifiyar sarki Salman, mace mai tsantsar hakuri da juriya tare da kawar da kai.
D'an ta ne, amman ba ta da wani iko akan shi, daga nesa kawai suke hango junan su amman basa haduwa face to face saboda an riga an janye mata shi daga gareta.
°°°°°°° °°°°°°°° °°°°°°°
Kishingid’e gimbiya shaheeda take a doguwar kujera dake tafkeken parlorn ta na alfarma. Wanda komai na cikin parlorn kirar samfarin kayan sarauta ne wanda turawa kewa laqabi da ‘Royal design’. Kai hatta salular da ke saqale ajikin da bango itama ta Royal ce.
Bayinta biyu ne a zaune kowanne yana mata tausa a kafa d’aya d’aya. Sai lumshe idanu take ahankali tana mai cigaba da taunar tufar dake hannunta, Wanda take gutsira ahankali cikin k’asaita.
Wayar tace dake kusa da ita tayi haske alamar saqo ya shigo, Sai data mula tasha iska tukun sannan ta daga wayar ta duba. Ta jima kafin ta daga musu hannu alamar su dakata, Sannan ta mike ta gyara zaman wani hadadden mayafin jikin ta mai beza. Bayin guda biyu suka bi bayanta kowacce kanta a kasa.
Sashen su ta nufa, Dake dare ne, Tarwar masarautar take da hasken lantar ki. Tsuntsaye nata kuka. Shiga tayi cikin wani babban parlor. Duk sun hallara aciki, Kowacce tana hakimce a kujera tana jin kanta. Kallo d’aya zakai musu kasan manyan mata ne masu aji, Wanda ke watayawa a duniyar masu kudi.
Gaishe su tayi. Ta samu waje ta hakimce itama. Bayin dake wajen duk suka basu wuri. Babbar matar ta tsakiya dake hakimce ta mike kafafun ta akan center table itace tafara magana,
“Shin ya sanar muku da halin da ake ciki kuwa....?”
“Hmm! Ki bari kawai.. Mun fara sanya fa. Yacemin kwana biyu ya kasa gane kansa.”
Cewar Haj Huwaila ta bawa Haj Jaleelah amsa tana tana jijjiga kafafu.
“Shin Gimbiya Shaheeda kin fara ganin alamun canji kuwa?”
Haj Najwa ta tambayi Gimbiya Shaheeda dake kallon su baki d’aya. Gimbiya Shaheeda taja majina tana jujjuya zobunan daham din hannun ta.
“Toh.. Gashi nan dai.... Ba wani matsala gaskia. Yanzu ma wanka nakeso nayi ayimin iso wajen sa.”
“Karki sakaci da maganin nan Gimbiya. Wallahi Malam ya rantse da abinda zai kashe shi wannan maganin babu na biyun sa..”
Haj Jaleela tace da Gimbiya Shaheeda data mike lokaci guda tana Yatsina fuska,
“Duk yadda ake ciki...”
Sallama ta musu ta dauki hanyar sashen ta. Kallo d’aya tayi wa sashen mai babban daki tayi gaba tana sake daure fuskar ta.
Su kuwa ko bayan fitar ta sa zancen ta suka yi a gaba. Sunata shewa suna tafawa. Tamkar ba kishiyoyi ba ada. Aminan juna ne na qut da qut.
Gimbiya Jaleela ce ta gyara zama tana faman jujjuya ido tace.
“Ni wallahi so nake a fara bawa mata sarauta a kasar nan. Ina ji a jiki na zan iya duk wani abu da ake yi a cikin sarauta. Kuma nayi mafarki nan gaba kadan mata zasu dawo sune suke jan ragamar mulkin masarautar Basannabas.”
Ta gama maganar tana dora kafa daya kan daya tare da juyawa ta kalli sauran one by one. Cike da tsantsar dariya irin ta rainin hankalin nan Gimbiya Najwa ta mike tsaye tare da yin taku daya biyu zuwa uku ta tsaya a tsakiyar su tana gyara kafadun rigar jikinta tace.
“Kwarai kuwa Hajjaju, ina jin kuma ni aka bawa damar karasa yin wannan daddadan mafarkin naki da kika fara. Domin kuwa ni na hango kai na akan wannan kujerar ta sarauniyar Basannabas. Kuma a cikin d'in bin halacci na har na baki mukamin Baba na, wato waziriya ta. Ke kuma..”
Ta Nuna Gimbiya Huwaila wato yar ciroma tare da cewa.
“Ke kuma na yi miki mukamin Baban Hajjaju Najwa, wato Galadima. Na san dai wan.....”
Bata karasa ba Gimbiya Najwa tayi saurin da katar da ita ta hanyar cewa.
“Ya isa dan Allah, wannan ai shirme ne. Idan zaku dawo cikin serious d'in ku toh ku dawo, amman ta ya zaku zauna kuna ta yi mana wasu zantuka na shirme. Yanzu mu maida hankali wajan ganin yarinyar nan ta yi aikin da muka bata, Salman d'an girman kai ne, ko uban shi be yi wannan jiji da kan ba wallahi.”
“Haka ne kam, dan naga kwanan nan itama ya fara yi mata gardama, juya dashi amman sai shigen fadin rai.”
Duk suka yi dariya tare da yin tafi da hannayensu. Gimbiya Huwaila ta ce.
“Sa'adatu ce ma ni take bani mamaki, matar nan Sam taki yadda da cewa yaran nan baya son ganin ta, amman kullum cikin wahalar da kanta take wajan koke koke da wasu addu'o'in ta na shirme. Ai gara ka yiwa kanka maganin matsalar ka, amman kace zaka jira ai sai ka dade, koma ka mutu baka cimma burin ka ba.”
“Ai Baba (Madaki) yace abu d'aya ne yasa shi barin matar nan. Shine baya daukar ta a matsayin mutun mai rai, amman da tuni yasa anyi shekara lahira.”
“Gaba d'aya manta ta nake a cikin tsarin rayuwa ta.”
Jaleela ta fada cikin yatsina fuska. Haka suka zauna suna ta shirya makircin su kamar yadda suka saba. Ita kuwa Sa'adatu tana sashen ta tana kukan zuci da na idaniya. Kuncin da take shiga wani lokacin har mutuwa take roko tazo ta dauketa saboda wahalar da ranta yake yi. Amman tasa a ranta komai daga Allah yake zuwa, yasan kuma lokacin da zai warware mata wannan masifar da take ciki.
Tsab ya yi shirin bacci, yaje ya kwanta akan gado sai gata itama ta shigo cikin shigar kayan bacci masu santsi gasu shara-shara. Gadon itama ta hau tare da rungume shi ya kawar da kai, tunda tasa hannunta ta shafi kirjinsa shikenan ya nemi nutsuwa ya rasa. Kansa ya yi girma yaji kamar an dora masa duniya da abinda ke cikin ta. Wani barin na zuciyar shi kuma yana kusanto masa ita akan ya yi mu'amala da shi.
Kafin kace menene ya firgice sun zama abu d'aya, koda suka dawo cikin hayyacin su wani gigitaccen bacci ne ya dauke shi. Ta tsaya tana kare masa kallo mai cike da fassarori kala-kala. Kanta ta dora saman kirjinsa take itama bacci ya dauke ta a jikinsa.
Garin ya yi shar gwanin dadi, sarki Salman ya fito akan farin doki da aka kawata shi da ado mai daukar hankali. A hankali yake tafiya har ya isa wajan wani ruwa inda wata tsohowar mata tana durkushe sai kuka take yi. Ya tsaya tare da sakkowa yaje kusa da ita cikin sassanyar murya yake mata magana.
“Baiwar Allah lafiya? Me yasa ki kuka a cikin mulki na?”
Ba tare da ta wai go ba ta gyara yagaggen mayafin da ke jikin ta tana share hawaye tace.
“Yara na duk sun guje ni, ba su san gani na bare ganin fuskata.”
“Suna raye kuma?”
Tace,