Sashe 20
Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abincin dana sayo na janyo, Na raba shi kashi biyu, Na shiga bashi a hankali dakyar yaci rabin sa, Ni kuma na cinye sauran. Na wanke tulin kwanukan da na gani awajen, Kafin na ha’da wuta na dora ruwan wanka na. Baffan mu na shiga nunnunawa kyaututtukan yai murna kwarai tare da kwarara min addu’a. Ruwa na na zafi na shiga band’aki na yo wanka. Ina futowa mu kai kicib’is da Mudi na koma ciki da sauri, Domin kwanan nan haka yake yi. Sai yaita kallo na yana lashe lebe hade da kashe min idanu. Ya zama direban hayis, Ya siyarda tumakin Gajiyalle da sauran jarin ta ya sai mota yana lodi gari gari, Ga shaye shaye da yake yi du ya bata maza yaran karkarar mu da yi.
Sai danaga ya fuce sannan na shige daki da sauri na canzo kaya na, Bana sallah. Hakan yasanya na canza auduga na zura hijabi na d’auki kayan koyan d’inki na mufi gidan Bara’atu me koyamin dinki. Baffa na yana ta baccin sa. A hanya muka had’u da Balki da gayyar yara rab’e rabe wasu na bin wasu har su bakwai. Ta manyanta sosai tamkar ba Balki ba.
“Balki..”
Na fada cike da mamakin ganin ta.
“Dijengala!! Rai kanga rai? Yauhe rabon da na saki a ido na?.”
“Ai kuwa dai an jima, Ina wuni Balki, Yaran ki ne wannan?”
“Eh nawaje na ne, Biyu sun rasu ma..”
“TubarkAllah. Allah ya raya su. Balkin Haladu, Ina Haladu?(mijin ta)”
“Uhm dan bankadaddiya, Mayaudari. Ke fa kihiyoyi na biyu. Namiji ba tabbas ingaya miki an sa ranar sa da y’ar gidan babire farkon watan gobe. Mu hud’u kenan. Ke shika biyu yamin saura d’aya auren mu ya datse.”
Na rike baki ina mamaki,
“Subahanallahi! Allah ya tsare, Yasa ku zauna lapia.”
“Amin dai. Walle ki tsaya ki cigaba da karatun ki. Yanzu ba hi nan ba tamkar na haife ki. Aure ba dadi kud’in cefa nema nera talatin.”
Sirrin gidan ta data fara fad’amin yasa na dan gyara tsayuwa ta ina kallom agogon hannu na,
“Allah sarki! Bara na wuce Balki sai gani na biyu.”
Na zaro ragowar hamsin din jakata na mikawa yaran, Kafin su karb’a ta wafce tana cusawa a kanta,
“Mungode Dije. He anjima.”
“Mu jima dakyau.”
Gaba nayi abuna na wuce gidan Bara’atu, Hankali kwance ta cigaba da koyamin d’inki, Sosai nake ganewa. Sai bayan magriba na koma gida.. Haka rayuwa ta cigaba da garawa yau da dad’i gobe babu...
..
______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.
______________________
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
*S & K*
*MX*
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI TA NAMBOBIN DAKE KASAN SHAFIN NAN.*
*11*
*Ranar* wata sanyayyar asabar da damina, Muka tashi da babban tashin hankali a karkarar mu ta Durbun. Bayan na temawa jinjiri mun gogewa Baffan mu jiki, Na bashi magani yasha, Sai na lallaba na tafi gidan Bara’atu koyo dinki. Gab da la’asar naji gaba d’aya banajin da’din jiki na. Daman haka na Kwana jiya ban rintsa ba Ina tunani, Haka kawai na shiga zaryar hawaye daren jiya. Shin meyake damuna? Bansani ba.
Mik’ewa nai kawai Bara’atu ta tsaya tana kallo na, Harhada kayan dinkin na shigayi ina cusawa a leda,
“Dije! Meye haka?”
“Gida zani Bara’atu. Raina sam babu dadi wallahi.”
“Subhan’Allah! Kiyita addu’a kinji!? Amma ki dakata ki kammala dinke kafadar mana?”
“Aa Bara’atu. Sauri nake yi wallahi. Bazan samu nutsuwa na Idan ban koma ba. Nagode sai kinji ni.”
Bantaba sanin wannan itace kalmar karshe da zata kara had’ani da Bara’atu ba akan dinki. Banta’ba sanin wannan ce rana ta karshe da zan sake zuwa gidan Bara’atu ba. Sallama na mata na fuce, gaba na sai tsananta bugu yake. Tamkar zai fadi kasa, Haka na kara sa gida gaba d’aya jiki na ya kara sanyi. Bantaba sanin wannan ce bakar rana da rayuwata zata kara shiga ha’ulai ba. Bantaba sanin yau ne zan shiga stage na biyu a fagen sabuwar rayuwata ba.
Baffan mu na tsakar gida a yashe, Fuskar sa tamkar yana murmushi. Na karasa kusa dashi na zauna a gefen sa,
“Baffa na... Na dawo.”
A duk lokacin da na dawo hakan nake yi, Dake bashi da nauyin bacci, Dana fad’i haka zai farka yace min Sannu da dawowa yar Baffan ta. Na sake matsawa kusa dashi na kamo hannun sa na dama, Tamkar na dau kara sam babu nauyi kuma ya saki.
“Baffa na.. Baffa ga Ummin ka fa! “
Nan ma shiru ba amsa. Gaba na ya tsananta bugu, idanuwana suka kawo ruwa.
“Nashiga uku! Baffa na. Gaji! Gajiyalle.. Ga Baffa baya motsi fa.”
Haka naita fada ina kai kawo a farfajiyar gidan mu. Gajiyalle ta fito daga d’aki tana hamma hade da daga hannuwa tayi mika,
“Ya akai? Kincikawa mutane kunnuwa da kururuwa, Meya faru.?”
Cikin hawaye shab’e sha’be na tsugunna ina rike kai na,
“Gaji! Baffa baya motsi. Ki tayani mu dauke shi mu kaishi asibiti.”
“Asibiti? Can birni!? Baki da hankali.”
Tsayawa tai akan baffan mu tana sakatar hanci,
“Bashari! Bashari! Kai bashari! Meye haka ne.?? “
Kafa tasa ta shure shi, Ya rigingina bako motsi. Banbi takanta ba na fuce ko dankwali babu, Na hango dandazon masu bin mai gari da shi kansa mai gari jamilun da alamun daga zagayen gonaki suke,
“Mai gari! Dan Allah kuzo kuga baffan mu baya motsi.”
“Assha gamu nan.”
Komawa nai ciki da sauri na zura hijabi gaba a baya. Gaba d’aya bana cikin hayyaci na, Su mai gari suka shigo, dube duben su sukai. kafin su mike kowanne jikin sa a sanyaye. (Allah ya jikan iyayen mu da rahama.)
“Ai Bashari dan aljanna ne da yardar Allah. Kiyi hak’uri Dije, Duk kan mai rai mamaci ne, Yau ga wanin ka, Gobe gare ka. Idan lokaci yayi dole a tafi. Kai Rabilu ku kama shi ku sashi a dakin can ko, Domin a kintsa shi. Ungo Musa zoka yanko likafani, Kace Malam na Masallaci suzo za’ sallaci Malam Bashari rai yayi halin sa, Ku auno tsawonsa ku taho da makara.”
Kan baffan mu nayi, Matan da suka shigo suka rirrike ni, Na kwace na rungume shi ina kuka,
“Wayyo Allah na Baffa na. Dan Allah kakka tafi. Babba ka tsaya, Wayyo Allah na baffa. Shikenan gaba da Baya bani da iyaye. Umma ta tarasu, Gashi Baffa sai ka tafi ka bar Dijen ka? Wayyo Allah nashiga uku na lalace. Wayyo mutuwa mai yankan k’auna”
Wannan sune ka’dai kalaman da zan iya tunawa na fade su. Daganan ban sake sanin inda kai na yake ba. Na yanke jiki na fadi. Ban farfad’o ba sai bayan an kai ni asibiti a birni. Kwanaki uku mu kai acan nida tsahare yar ladingo sannan muka dawo gida. Ranar sadakan ukun Baffa na. Addua kadai nake iyayi sai kuka, abinci kuwa sai yan uwa na matsamin nake tsaku na, Duk wani buri na wa na duniya na yanke shi. Jira kawai nake nima tazo ta dauke ni. Astagfirullah Yaa Allah amma nikam nasan shikenan rayuwa ta yanzu zata kara shiga cikin jarabawa.
Haka akaita zaman makoki har na tsawon kwana ki bakwai. Gajiyalle tace wa mai gari tanada magana,
“Azo ai rabiyar gado. Amma fa wani hanzari ba gudu ba, Mai rasuwar nan kafin rasuwar sa yace ya barwa Mudi gidan nan wai yayi aure ya zauna.”
A razane na juya ina kallon ta, Yaushe sukai haka?! Allah ya saka masa. Yan zaman makoki kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa. Mai gari yai gyaran murya,
“Toh salamatu. Hakan yayi. Amma ina rubutaccen kyautar da yayi.?”
“Yo wane rubutu? Malam ya iya rubutu ne! Kai ma mai gari da tsohon kinibibin ka ta yaya Bashari zai iya rubutu?”
Mai gari yai murmushin takaici yana gyara rawanin sa,
“Toh ina shedu? Agaban wa da wa akai kyautar?”
Gajiyalle ta sosa kai tana zare idanu,
“Daga ni sai shi akai haka, Zan yi k’arya ne?”
“Assha! Yaushe zan karya ta ki a matsayin matarsa.? Kawai dai irin wannan babbar kyauta haka yakamata ace akwai ta a rubuce ko anyi ta gaban shedu.”
“Toh dai na baka ta rabaka da kayan ka. Wannan gida dai na Mudi ne.”
“Gaskia bai badu ba, Domin ko gaban alkali zaki abinda zai sanar dake kenan. Saboda haka kiyi hak’uri kawai, Domin Mudi ma Ai ba ‘dan cikin sa bane Salamatu. Ya zaai ga diyar cikin sa duk duniya ita kadai ce jal. Ace ya tsallaketa ya baiwa agola kyautar gidan sa sukutum? Wannan magana bata kamawa bace kiyi hak’uri. Gado dai yau zuwa gobe Za’a raba shi. Ke ki nada tumunin takabar sa ita kuma diyar sa tana gadon sa. Za’a raba ko dan saboda a sauke masa nauyin dake Kan sa.”