← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 114

Sashe 76

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khaleel ya goge hawayen daya zubo mai yana jijjiga kansa,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.... So ya yan majalisar ka? Ka gano masu maka zagwan kasan?”

“Ai ka bari kawai Khal... ni yanzu na san ina zagaye da makiya gaba d’aya sun yi min zobe. A fuska tamkar masoya amma a zucia ba haka bane..”

“Ya matar ka..”

“Matan ka zaka ce.. Suna lapia..”

“Ahh na manta fa.. kace min ka yi wani auren Gimbiya Khadijaa itace amarya ko? journalist ce ko?”

“Eh... Khadijaa ba..! My brave little lioness ba.”

Ajiyar zuciya Khaleel ya sauke yana mai sauke tagumin da yayi..

“Bana tunanin ku, Na kasance cikin wata iriyar rayuwa. Wani lokacin nakan ji tamkar na manta wane ni.. Meya kawo ni nan ma? Daga ina nake? Wallahi Yaya komai goge min yake wani lokacin. Toh sai kwanan nan nafara mafarkin gida sama sama haka, Da Ammi da kuma ku.. Harma naji inason komawa gida, Inason jin sautin muryoyin ku ko da awaya ne.. Sai kawai kuma ka kira ni. Alhamdulillah Insha Allah k’arshen wahalar rayuwar da aka jefamu ne yazo..”

“Ni ma hakan take awaje na Khal.. and sai Khadija ce ke gayamin halin da aka jefa Abdullah ma.. wasu basu da imani Khal.. shin me muka tsare musu Khaleel!?”

“Qiyayya ce kawai Yaya.. ba’a so aka haife mu ba kagane? So ya za’ai damu! Shi yasa ake tagayyara mana rayuwa yadda aka ga dama...”

“Toh ta Allah bata suba Insha Allah rayuwar mu zata gyaru kamar yadda take a baya. Kasan abdulqadeer ma an bashi sarauta.. Sun sani a gaba dole na bashi.. Yanzu ma sun nemi kudaden auren su munaya a guri na.!”

“So suke ka sauka fa ta dole Yaya.. Zuri’ar Masekiri kuma sani ne basu yi ba amma sarautar su tagama tabarbarewa tun shekaru aru aru baya..”

Ajiyar zuciya Salman ya sauke yana girgiza kansa,

“General Checkup nakeso kuyi min Khal.. Da full blood count dina.. So nake na gano wasu abubuwa a kai na. Wai shin da gaske ne bazan taba haihuwa ba? ko kuma rabo ne babu tsakani na da Shaheedah?"

“Shaheedan? What about her? Shin metayi haka?”

“Birmingham, Cyprus, India , Luxembourg, France, Da Mauritania. Kaga 6 countries ko? Duk Sai da tasa muka jajje Khal... aka ce wai ni... Ni Salman nine bana haihuwa.”

“Kai....! Kuma ka tsaya Yaya tun a lokacin ba kai komai akai ba?”

“Khal ina tattare da makiya, Na gayama sun zagaye ni, Banida tacewa, Dole na dau zancen tamkar gaskiya, Sanin kanka dana karyata Za’a illata ni tun kafin mu baro kasashen ma.”

“Subhan’Allah! Allah ya dubemu Yaya. Wannan zancen ya kamata a bayyana gaskiya kowa ya sani.”

“Abinda ya kawoni kenan Khal.. Saboda nayi General checkup din.. Ya kuma zamto kaima ka dawo wajen Ammi.. Ni kuma daganan zanci gaba da gudanar da rayuwa ta yadda ya dace har sai na kammala bincike na.”

“Allah ya temake mu Yaya.. Allah ya fisshemu kunya. Ka watsa ruwa ko? Sai mu koma asibitin, Ko kuma mu tafi can Busan ayo maka acan.”

Hakan kuwa akayi. Salman yayo wanka suka sake shiryawa suka nufi busan. Acan doctors suka fara yiwa SAS gwaje gwaje, Har Sai da aka dau tsawon kwanaki 3 ana yi tukun sannan result ya fito. Result yafito lapiar sa kalau babu abunda ke damun sa sai ulcer saboda abinci da bayaci. Amma yana haihuwa kalau yake, Bashi da wata cutar da zata hana shi haihuwa. Kukan farin ciki Salman yayi, Khaleel ya rungume shi.. Falaki yanata murmushi yana yiwa Allah godia shima.

Satin su Salman d’aya a Korea suka tattara suka dawo kasar Nigeria. Dama ca yai dasu Wambai ya tafi meeting da wani babban dan kasuwa akan project da zasu yi anan masarautar, Lokacin da suka isa airport din kano, wani murmushi yai irin na gefen bakin nan, Zuciar sa cike da abubuwan da zai aiwatar.. Ta ina zai fara? Akan suwa zai fara binciken sa. Khaleel bai samu damar biyosu ba sai bayan sati biyu, Sakamakon hanashi tafiya da board of directors sukayi.. Kan sai ya gama aiwatar da project din dake hannun sa. Ba kadan ba suke son sa, Saboda Khaleel mutumi ne shi faram faran kuma ya iya aikin sa, Ba wasa. Ko sanda yana gida Ammi da shi suka fi hira saboda baida girman kai da rashin magana irin na Salman da Abdullah...

*SAS*

Tun a airport aka bashi wani daki na musanman ya shiga ya sauya kaya izuwa na sarakuna. Driver ya ja shi suka koma masarauta. A bakin kofar yamma suka sauke falaki ya tafi gida wajen iyalin sa. Har kofar sashen sa akai parking ya sauka ya shige ciki sam baibi takan dogaran dake masa kirari ba.

Yana shiga ya kishingid’e a doguwar kujera yana tuna khaleel kanin sa da suka sha zumunci. wani b’angare na zuciar sa kuma na jin dadin sakamakon da ya nuna lapiar sa lau..

Sanar masa akai zuwan waziri ya bada iso, Waziri ya shigo yana harhada hanya cikin girmamawa,

“Sannu da dawowa uban kowa, Takawar ka lapia Sarki Salman jikan salmanu, Sawun giwa badda na rakumi shugaban mu, Hadarin sama sai sauraro sarkin mu, Kai ka dai ka iya Kai zaka cigaba da yi baban kowa, Sun buga sun barka ya zasuyi da kai? Dole su goce.. Barka da dawowa sarkin mu.. Yan majalisa da sauran yan zaman fada na murnar dawowar ka...”

Murmushi Salman yai ya mike ya zauna daga kishingid’en da yake..

“Na amsa waziri... Ina kuma godia.”

“An baro su lapia...?”

“Lapia qalau.. Ai ansamu nasara sunce nan kusa zasu fara qaddamar da gine ginen cikin masarautar nan.”

“Toh Masha Allahu! Tafiya tayi kyau. Babu wani kedararren acikin yan majalisa daya kira ka ko? Sanar mun yanzu ba sai anjima ba na aiwatar da hukunci..”

“Noo babu wanda ya kira.. Ai ka tsayamun waziri.. Godia nake.”

Hira suka taba sama sama, Waziri ya masa sallama ya tafi.. Ahankali Salman ya mike ya kashe hasken wajen gaba d’aya, Dakin sirrin sa ya shiga ahankali. Zama yai akan kujera, gurin tsab tamkar ma yadda ya tafi ya barshi, baya tunanin khadija ta shigo tai mai aikin da ya sanya ta. Yana kallon waziri ta cikin computer, murmushi yai lokacin da ya hango sashen da waziri ya nufa.

Ajiyar zuciya ya sauke. Ya shiga jujjuya kansa ajikin kujera. Ya jima a haka kafin ya mike ya fita ya koma dakin sa. Wanka yayo yayi sallah, Kallo d’aya yaiwa abincin da aka jere masa akan dinning table ya dauke kansa. Kaya marasa nauyi yasa ya dora alkyabba akai.

Amintattun dogaran sa guda biyu yasa agaba suka shiga zazzagaya masarautar. A kofar sashen gimbiya shaheeda suka tsaya ya shiga ciki kansa tsaye. Yana shiga hadimanta suka bashi waje. Kansa tsaye ya nufi dakin ta. Ya turnuke da hayaki sai tari take yi.

Juyowar da zatai kawai tagan shi a kanta, Da sauri ta mike idanunta sunyi jawur saboda azabar tururun hayakin dake tashi...

“Sas..Salman.. Y..Yaushe ka dawo?Tuttu..turara maganin sauro nake yi.”

Jijjiga kansa yai alamun ya yarda, Ya rufe idanun sa ahankali ya bude akanta, Hannunta ya jawo suka fito. Daga ita sai daurin zani. Jikin ta sai kakkarwa yake ta dauka ya gane abunda take zai mata hukunci ne. Dakin kusa da wancen ya shigar da ita. Ya sakata a tsakiyar kofa yana toshe hancin sa da handkerchief..

“Maganin sauro.. wani iri kike turarawa haka...?”

“Bb... Wani ne hadimata ta aikomin .. s.. Saboda sauron da ake kwana biyu.”

“Okay.. Kidena wahalar min da kan ki.. Duk ga masu aiki nan ki dinga sasu kinji?..”

Yana magana ya goge mata gumin dake goshin ta, Dadi taji ya lullube ta, Dama turaren mallaka ne hajian su ta aiko mata.. Da alama aikin sa kamar yankan wuka yake. Domin gashi tun ba’aje ko’ina ba hankalin Salman ya fara karkata izuwa gareta..

“Kinji ko... My Queen..?”

“Naji my king..”

“Okay jeki wanka ki zubamin abinci.... Idan na koma danaci sai bacci ko..?”

Dadi ya sake kama shaheeda tayi murmushi tana jijjiga kai.. Da sauri ta shige ban’daki tayo wanka. Ba abinci. Sai Indomie tasa aka dafa jikin ta na rawa tasa aka juye masa a warmer. Har bakin sashen sa ta rakashi, Yana shiga gida ya kira dogarin sa ya bashi yace yace ya cinye. Yoghurt ya dauka me sanyi yasha yana lumshe idanun sa.... Bincike ne da yawa agaban sa da zai yi, yaso suyi tare da Khadija amman a tunanin sa ba zata bashi goyan baya ba saboda tana ganin ba son gaskiya yake mata ba. Kuma Kowanne sai yayi taka tsantsan akan gudanar da binciken kamar yadda ya boye yar camerarsa me recording komai a dakin shaheedah.. Dai dai lokacin daya jinginata a kofa.. Da kofar shiga sashen duk ya saka...

“Yaa Allah... Ka bani sa’a a wannan bincike da zan fara aiwatarwa.. Allah ka bamu nasara.. Allah ka dora mu akan makiyan mu..”

Haka Salman yaita maimatawa yana mai daga hannayen sa sama alamar roko izuwa ga mai sama.. Domin shi din mubuwayi ne gagara misali....

Asubah ta gari... Sarki Salman Aliyu Salman (SAS)

..
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

PG: 16
BOOK 2.

BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻

*SAS*
Chapter 76 · 0% Book details