← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 114

Sashe 71

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kowa be shigo ba, oh su..matan baba sun zo duba ni dazu.”

“Mata? Wane irin mata kuma?!”

Yayi shiru tsawon lokaci sannan ya ce.

“Mama Huwaila.”

Na tabe baki a hankali naje na dakko turaran kamshi na jona burner na zuba, nan da nan kamshi ya gauraye dakin, na karasa kusa dashi tare da jan hannunsa na kai shi kan kujerar da yake hutawa ya zauna sannan na warware masa towel d'in na ajiye a gefensa.

“Kana jin warin har yanzu?” Ya daga min kai alamar eh.

“But kadan-kadan ne.” Ya fada yana satar kallo na.

“Okay karka damu zai dena gabaki d'aya insha Allahu. Bari na koma sister's dina ne suka zo.”

Kamar zai hana ni sai kuma ya jin gina bayan sa jikin kujerar tare da lumshe idanunsa be ce min uffan ba. Ni kuwa na juya na tafi dan kar su yi zaton wani abun bare suje su gayawa Mami cewar nai musu rashin mutunci. Koda na koma bangan su a parlorn ba, ina shirin tambaya na jiyo muryarsu a sama suna ta shewa, mamaki ya kamani. Sai na bisu har ina hardewa, na hange su a wani bedroom suka kalle ni cikin rashin damuwa Ya Hameedah tace.

“Zazzagawa muke muga yanayin gidan.”

“Ah lallai Dije duniya sabuwa irin wannan daula haka? Kinga bathroom d'in nan? Wallahi tuna min ya yi farkon zuwan ki gidan mu kika kasa shiga bathtub, amman yau gashi ke ce mai wannan dankareran jakuzzi d'in.”

Ya Shukrah ta fada cikin shakiyan ci, duk sai na kasa magana ganin yadda suke ta dariya harda kawayen su. Nai murmushi tare da karasawa na bude wata wardrobe na ciro wasu laces da material ina cewa.

“Kunga wasu kaya ina ta so randa zanje gida na tafi muku da shi sai gashi kunzo. Idan zaku tafi sai a sa a mota.”

Ganin irin dankara-dankaran laces d'in yasa suka kasa rejecting, hannu biyu-biyu suka karba, sai dai Ya Hameedah sai da tace.

“Wai yau Dije ce da yi mana kyautar bajin ta. Aure mai dadi mu ma dai Allah ya kai mu lokacin namu muji yadda ake ji.”

Duk suka yi dariya tare da tafawa, ni kam na kagu su tafi musamman da naga suma kawayen sun fara yi min abinda suka ga su Shukrah nai min. Allah ya taimake ni suka sakko tare da shirin tafiya, bayan ko wacce ta dauki abin da take so a gidan, ban yi magana ba ni dai buri na kawai su kara gaba, naji dadin ganinsu dan a kalla nasan mutane zasu san nima ina da dangi. Har wajan gate din sashe na nai musu rakiya suka tafi suna ta magana da ban san ko ta menene ba, kai tsaye na shiga toilet nai alwala.

*<<<<<>>>>>>>>*

Sallama dauke cikin siririyar murya ta na shiga bedroom d'in nasa, Salman tsaye wajan mirror ya gama shirinsa na fita fada zai gana da wasu ƴan majalisar jiha. Ban ko kalle shi ba na wuce zuwa inda ake ajiye masa tray din coffee ko tea ko dai wani abin da yake so.

Ya juyo yana kallo na wanda na gane hakan ne a jiki na, sai dai bai ce min komai ba nima kuma ban juya ba sai kokarin had'a masa coffee d'in da nake yi. Cikin rai na haushi ne cacim saboda rashin kulawarsa gare ni tana bata min rai duk da ba wai ina bukatar ta bane. Har na kammala hadawa na rufe ban juyo ba duk da cewar babu abin da nake yi a wajan, naji ya tako a hankali ya tsaya a baya na yana bin kai na da kallo.

Dan kwalin naji ya cire nai saurin mikewa tsaye babu shiri, ido waje kuna na kalle shi dan tsananin mamakin shi. Da kyar na daura d'an kwalin kasan cewar na lace ne kuma yana da nauyi, amman shine saboda ya lalata min ya kama ya cire min ba tare da sani na ba. Yadda yaga ina kallonsa ne ya tabbatar masa da cewa rai na ya baci, amman ko a jikinsa dan bai nuna ba a fuskarsa, cikin yatsina fuska nace.

“Ya haka? Kasan da yadda na daura shi?”

Bai ce komai ba sai kallo na da yake yi, cikin jin haushin dark shades d'in idanunsa masu kallon mutane ba tare da sun sani ba, nima nasa hannu na ciro shi ina tsuke baki.

“Ni ma na rama.”

Na fada cikin gaskiya ta. Maimakon ya kalle ni a'a sai kawai ya lumshe idon sa da haka ya miko hannusa tare da kamo kafaduna ya rike, ban yi aune ba kuwa naji ya sanya ni cikin faffadan kirjinsa, tare da dora habarsa a kai na. Ware ido nayi ina jiran jin abinda zai wakana, sai kuma naji tattausar muryarshi a cikin kunne na yana cewa.

“Baki iya gaisuwa ba?”

“Oh ai ban san da mutum a ciki ba, dan nayi sallama amman ba'a amsa min ba.”

Ya sake sanya bakinsa cikin kunne na ta yadda na dinga jiyo numfashinsa wanda ke sa tsigar jikina tashi. Nai saurin kawar da kai na, ai kuwa muka hada fuska dashi a lokacin ne kuma ya bude idonsa muka hadu da na juna kowannen mu da abin da yake sakawa a cikin ransa. Bashi da niyar yin magana hakan ya bani kwarin guiwar fincike jikina zan matsa Salman ya yi saurin janyo ni, naki waigawa saboda abin nan nashi ya ishe ni, sai dai yai ta yin shiru kamar wani kurma, yana ji kana magana amman yaki kulawa. Rai na a bace na fara magana dan ni dai gaskiya ba zan ci gaba da jure wannan wulakancin nasa ba.

“Wai kai dan Allah a haka kake yin mulkin naka cikin shiru da rashin yin magana? Ta ya kake sauraran talakawan dake karkashinka bare har ka tallafa musu a inda suka kawo kukan su? Wannan shirun naka yana yin yawa gaskiya, gashi nan har ta kawo baka kula mahaifiyar ka. Ammi tana t.....”

Ammi da na furta shine ya sanya shi saurin fisgoni ba tare da na karasa maganar tawa ba. Ya yi min wani irin kallo wanda na kasa gane ko na menene. Shin na tsana ne ko gargadi ko kuma mamaki? Ban sani ba ni dai, zafin rike min gashi da ya yi yasa ni cewa.

“Ni ka sakar min kai na, dan sauran kiris ka dena gani na a cikin sashen nan naka, bana son yin taraiya da wanda yasan mahaifiyarsa na da rai amman be damu da rayuwarta ba, bai san ina take ba bare yasan ya ta kwana ta tashi tsahon lokaci kuma a gida d'aya. Shi yasa lokaci nake jira wanda zaka sallama min naje nai rayuwata yacce naga dama, ba da kai ba da ban san dali.....”

Ban karasa ba naji muryarsa cikin tsawa tare da sake matse min gashin yana kuma dago fuskata.

“Ya isa! Ya isa haka please.”

“Toh naji sakar min kai na nima.”

“Ki min shiru na ce.”

“Ashh... Wayyo Allah kai na zai cire min gashi.”

“kin rai na ni ne?”

Ina faman matse ido saboda zafin rikon da ya yi min nace.

“Ban gane ba.”

“Kince kin dena zuwa nan ko?”

“Eh na fada fa, amman cewa nai idan baka gyara mu'amalarka da Ammie ba.”

Ya yi saurin sakar min gashi tare da dafe kanshi ya sunkuya zuwa kasa yana furta

“Kai na... Kai na zai...zai ci.....”

Hankali na yai mugun tashi ganin yadda lokaci guda ya birki ce min, ban san sanda na durkusa a wajan shi ba ina bashi hakuri a gigice dan nasan koma menene ni ce sanadi, na fahimci indai zan ambaci sunan Ammie toh dole yana shiga cikin wani yanayi da shi kansa be san yana shigarsa ba. Kofar da naji an kwankwasa ne ya kuma tayar min da hankali, kafin nai wani motsi an bude an shigo ciki.

Jakadiya ce kanta a kasa kamar tsohuwar munafuka, nai saurin kallon ta ido waje. Ganin yadda take kallon Salman yasa ni nace.

“Daman kina da damar shigowa nan Jakadiya?”

Cikin sauri tace.

“A'a wallahi ranki ya dade, ina parlor ina jiran na yiwa Gimbiya Jaleela iso ne sai naji kamar kin kira ni.”

“OH kinsan ina ciki kenan?”

“Wallahi tallahi ban sani ba ranki ya dade, dogari ne ya sanar dani.”

“Okay please bashi da lafiya ba zai iya ganin kowa ba a halin yanzu.”

“An gama ranki ya dade Allah ya ja kwananki.”

Ta fada tana mai bita da baya da baya cike da son ganin gulma. A rai na nace zan yi maganin ki babbar kawai.

*SAS*

Tsaye yake a jikin window din dakin sa, Sanye cikin bathrobe, Da alama wankan bacci yayo. Agogon dake saqale a jikin wallpaper ya kalla, Sha biyu saura kwata, Yanzu ne lokacin da Khadijaa ke fitowa daga wanka itama, Dama sashen sa yana kallon nata. Kuma curtains din dakin da take kwana a saman irin shara-shara dinnan ne, Yana hango ta idan tana shiryawa. Kansa ya dafe da hannu d’aya. Saboda tsananin yadda yake sara masa, Gashi bayaso ko da second d’aya ya kauracewa kallon ta. Tun sanda tazo yana tare da shaheeda dinnan bata sake komawa ba.

“Gani kike ko bana sonki ko?......Lokaci zai bayyana komai.”

A hankali ya fada yana mai zama akan kujerar dake kallon setin windon ta. Cikin haka kuwa sai ga Khadija tafito, Itama da rigar wanka, Ta wanke yalwataccen dogon gashinta baki sidik, A hankali ta shjga saka comb tana taje shi, Salman ya jinginar da kansa a jikin kujera yana lumshe idanu.. Lokaci kawai yake jira ya bayyana mata zuciar sa.

Tashi yai da sauri yana zura kansa ta window tamkar zai fada ganin tana kokarin sab’ule hannun ta d’aya na rigar wankan jikin ta. Abun karo ganin abu ya sanya a idanun sa yana kara zooming dinta. Tamkar ta gane ana kallon ta. Ta maida hannun rigar ta mike tsaye ta fice..
Chapter 71 · 0% Book details