← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 114

Sashe 15

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kai! Malama ai bazan iya sata a zuciya ta ba, kinga girman makarantar kuwa?”

Ta girgiza kai,

“Ni ba haka nake nufi ba, ina nufin kiji kina son zuwa koyan karatu a cikin ranki. Haba Khadija ya za'a yi kina girma amman baki dena wasu abubuwan na shirme ba? Yanzu ina zaki je?”

“Oho, ni daga wajan kallon wasan kauraye nake.”

Ta girgiza kai tare da gyara jakarta a kafadarta. Kallo na tayi sosai sannan tace.

“Muje ki nuna min gidan ku”

Babu musu na amsa mata muka tafi muna hirar mu har muka hadu da malam Auwal zai tafi gidan liman, yana kallan mu amman yaki kula mu itama malama Mardiyya bata yi masa magana ba har muka wuce. Da sallama a baki na muka shiga ciki, Gajiyalle tana tankaden garin dawa da zata yi tuwo. Taki amsa min tayi tunanin ni kadai ce, sai da taji muryar malama Mardiyya cikin sallamarta da dole ne duk wanda yake cikin gidan ya jiyo.

“Sannuki da zuwa bakuwa, shigo mana.”

Gajiyalle ta fada tana janyo tabarmar dake bayan ta, naje na karba ina ta faman rawar kafa saboda malama tazo gidan mu. Malama Mardiyya ta zauna tana bin gidan mu da kallo ta ko ina, muryar Gaji ta katse mata tunanin ta inda tace mata.

“Ina wuni?”

“Lafiya lau, ya gidan?”

“Ƙalau muke, sai dai ban wanyeki ba.”

Gajiyalle tayi maganar tana ajiye rariyar da take tankade da ita sai kallon malama take yi kamar wacce aka kafewa idanuwa a kanta.

“Allah sarki daman ba zaki sanni ba gaskiya. Ni malama ce a wannan makarantar da aka bude. Kwana biyu naga Dije bata zuwa, shine na hadu da ita a hanya nace dan Allah ta kawo ni gidan su.”

Tunda Gajiyalle taji tace malamar mu ce shikenan ta sauya fuska tayi kicin-kicin da fuska da alama bata so hakan ba. Malama Mardiyya ta ce na zauna na samu guri a bayan ta na zauna dan ban san me zata fada mata ba, kar naje Gajiyallen ta kawo min naushi.

“Maman Khadija dan Allah me yasa baki tursasata akan zuwa makaranta? Gashi duk tayi wani yarbatsai kamar wata marar mafadi. Dube ta ɗan Allah kamar ba mace ba sai tsami take, ilimi fa yana da dadi Maman Dije, dan Allah kiyi kokari ki canza ta. Ni ban zo dan na gyara miki wani abun ba, amman dan Allah kisa ido akan ta koda wajan kula da ibada ne, ace kamar Dije amman bata san meye sallah ba bare tayi? Muna so muga an samu manya a cikin kauyan nan, amman burin mu ba zai cika ba sai da taimakon ku iyaye, musamman ku mata.”

Gajiyalle tasa kafarta ta buga a kasa tare da kankance idanuwa tana mai nuna malama Mardiyya da yatsa tare da cewa.

“Ke! Dakata min da wannan surutun naki haba, cacacaca kamar wata mai rubabban baki. Yo haka ne mana kinzo sai barin zance kike kamar wadda aka budewa makogwaro. A hayye na naye yau na ga ikon Allah, kizo har gida na kice zaki tsara min yacce zan dinga yin rayuwa ta? To ko hi mai gidan be isa ba ballantana wata ke fankan fayau. Dije kuma ai gaki gata nan sai ki maida ita yadda kike so kinji uwata? Ki tashi ki bar min gida kafin na dakko tabarya na ragargaji kanki walle.”

Da sauri naga malama ta tashi tana rataya jaka, ta kuma kallon Gajiyalle cike da takaici sannan ta wuce ta bar gidan. Nima juyawa nayi da nufin na bi bayan malama naji ta riko min riga ba zato kawai ta wanke min fuska da mari tana kuma dukana.

“Shegiyar yarinya kawai, bari na kashe ki na huta da janyo min magana da kike yawan yi. Saboda rahin mutunci irin naki sai kije ki dinga taho min da mutane, wato zuwa kike kina min hirri a waje ko? To walle talle ko babanki bai isa ya dinga yi min surutu a gari ba.”

Ta dinga duka na malama Mardiyya na ji amman ta kasa dawowa saboda kar taje bayan ta tafi ta barni cikin wata fitinar tunda ba tare zamu zauna da ita ba. Ranar nasha wahala a gurin ta, nayi wankin kayanta da wanke-wanke da shara ta hanani fita ko ina sai da aka yi magariba sannan na gudu da ta shiga bandaki.

Washe gari tun da sassafe na tafi gidan Sahura nayi layin karbar sadakar koko da liman yasa a dinga bayarwa. Na karba nasha daga can kuma na yi wucewa ta makaranta duk da cewa babu kowa haka na samu guri na kwanta har wani baccin ya yi gaba da ni ban sani ba. Hananiyar mutane ita ce ta sani farkawa naga har an fara taruwa, na tashi ina ta faman zaro ido karaf miƙa hada idanuwa da malam Auwal yana rike da bulala ya ce min.

“Nan ina ne?”

“Aji.”

“Shi ne kika zo kina ta yiwa mutane munshari kamar kina kan gado?” Na yatsina fuska ban kula shi ba.

Mtsww ya ja tsaki ya bar gurin ya zauna akan kujerar malamai yana ta bude littattafai har aka gama zuwa. Ya dakko rigester yana kiran sunaye, yana zuwa kan sunana ya dinga tsaki saboda ganin fashin da nake yi a ciki yafi na kowa yawa, kamar ba zai kira ni ba sai kuma ya ci gaba da kiran ragowar mazan.

“Maude Nalami...?” Ya amsa.
_“Present Sir..”_

“Yahaya Liti...?” Shima ya amsa.
_“Present Sir..”_

“Khadija Baffa...?” Ina sosa cikin kunne na ina amsawa.

_“Na'am..! Gani..!! Nazo..!!! Sa farazen...!!!!”_

Malam Auwal ya sanya kasan biron hannunsa cikin baki yana taunawa da hakori saboda takaicin da na bashi. Ya hura iska daga bakinsa yana sake matse ido kamar wani mai jin ciwon kai, ya dago yana kallo na cike da tsantsar tsana wacce na rasa dalilin da yasa yake min ita.

“Baki da kunya Khadija, amman zan gyara miki zama a cikin ajin nan wa wuya kawai.”

Yaci gaba da kiran sunaye jefi-jefi yana jan tsaki, ni dai tunda ya kira suna na ban sake kula shi ba, ana haka sai ga shi malama Mardiyya ta aiko cewar naje office na same ta, na tashi na fita tun kafin ma ya bani izinin tafiya. Ina zuwa ta taso tace muje ni dai ban tambaye ta ko ina zamu ba dan duk inda zata kai ni bin ta zanyi shi yasa ma ban tambaya d'in ba. Kai tsaye muka tafi gidan mai gari, bayan sun gaisa da matan sa dama mai gari ya riga ya sanar da su zuwan ta tayi mishi bayani tun jiya cewar zata zo da ni.

Mayafi ta gyara sannan ta dakko wani zani a cikin wata bakar leda ta miko min wai na cire kayan jikina na daura shi, nayi kamar yadda tace daga nan tace muje bandaki. Na shiga ita kuma ta dibo ruwa cikin bokiti ta kai bandakin, ta kuma dibar wani ta kai sannan ta dakko soso da sabulu ta shigo tace na cire zanin nawa na cire. Allah sarki malama Mardiyya mace mai mutunci mai kyauta da yin alkairi fisabilillahi. Sai da tayi min sabi uku harda goge faso duk da cewa bai fita ba amman an rage ba laifi.

Na daura zanin muka fito wata iska naji tana shiga cikin jikina mai matukar dadi da ratsa zuciya, na dinga jina tamkar a cikin furanni masu launi nake. Ta shafa min mai sannan ta ciro uniform da sabon pant na saka ta kuma shafa min huda da kwalli, tun a gidan su Baraka wato amaryar mai gari suke ta yi min tsiya, ni kuma ina ta dashe baki saboda farin cikin yadda nake jin na sauya gabaki d'aya.

“Ko kefa Khadija, kinga yadda kika yi kyau kuwa? Dan ma dai ba ayi kitso ba, amman soon shima zan yi aiki a wannan gashin naki.”

Malama Mardiyya tayi maganar tana nuna min wasu kaya a ledar da ta zo da ita, tace min idan an tashi daga makaranta nazo wajan Baraka na karba, riga da skirt ne na atamfa, sai dai daga gani ansa saboda ba sabo bane amman masu kyau ne tunda da kyansu har yanzu. Ta kama hannu na muka fito, mutane tun a hanya suke kallo na suna yi min tsiya, a haka muka karasa makaranta ta kai ni har cikin ajin mu, a lokacin daman period ta kusa fita mu shiga ta malam Auwal. Yan ajin mu baki bude suka kalle ni suna mamakin gani na a haka, sai kowa ya fara matsa min kusa dashi wai nazo na zauna ni kuma sai yatsina fuska nake yi, dan ji nake nafi kowa kyau a duniyar nan.

“Dije!”

“Na'am malam Habu.”

“Kinga yadda kikai kyau kuwa? Masha Allah, kai Allah ya sakawa malama Mardiyya da alkairi tayi kokari.”

Ina hura hanci na tafi karshen ajin na zauna sai faman bude ido nake yi. Malam Habu yana hada littattafansa yana cewa.

“Dama zaki ci gaba da tsafta da kinfi haka mutunci Dije.”

Ban kula shi ba ji dai dan magana ma a wannan lokacin wahala take yi min.

Malam Auwal ya shigo daman shine last period, ya dinga bin yan ajin da alama da alamar akwai abin da yake nema, na dora kai na akan benci dan bana son ma yaga fuskata bare yace nayi kyau bana son yabon shi.

“Ina Uwande da Dijeh?”

Ya tambaya yana kallon yan ajin.

“Ga Dije nan, Uwande kuma tun dazu ta tambayi malam Habu zata fitsari har yanzu bata dawo ba.”

“Guduwa tayi yau ma kenan?” Ya tambaya.

“Eh malam tallen wake da hinkafa ta tafi.”

“Okay! Ina Dijen ita kuma?”

“Malam gata nan ta boye?” Suka hada baki wajan bashi amsa.

“Ke Khadija! Ke! Ba magana nake miki ba ne?”

Kamar irin a film d'in nan idan za'a nuna star, haka na dago a hankali cike da yanga har na tashi gabaki d'aya. Da ya kalle ni sai da ya murza idanuwa alamar ko yana ganin gizo, saboda dazu ya san na fita kamar yadda ya sanni, amman yanzu ya dawo ya ganni fes kamar ba Dije Oganniya ba. Bakinsa a hangame yana shafa d'an siririn gemunsa ya lashi lebansa tare da cewa.

“Zo nan.”

Nayi tamkar banji ba sai da ya sake cewa.
Chapter 15 · 0% Book details