← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 114

Sashe 104

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tsaye tana kallon bango da alamun wani tunanin take, Can taja tsaki, Ba jimawa suka gama waya da hajian su, Ta Kara bata haku’ri da sake dorata akan yadda zata b’ullowa lamarin, Ajiyar zuciya ta sauke tanata mita kamar zararriya, Harda hawaye, Tana mai jujjuya kanta gwanin ban tausayi,

“Wayyo Allah na, Salman kaci amanata, Ta tabbata kai da yarinyar nan kunyi auratayya. Shikenan ni shaheedah dole na sauya taku. Wayyo Allah na. Mena rage maka da har zaka karo aure? Kodan ba ganina Kayi kace kana so na ba Eh? Kodan auren had’i ne? Salman why? Why? Why?”

Tashiga ball da flower vase din da aka Kawata su a parlorn, Cikin haka jakadiya Abu tashiga kanta a kasa,

“Ranki ya dade gani.”

“Jakadiya kin munafurce ni, Shin nawa aka biya ki akan uban kudaden dana baki da har kika dena kawomun zancen mai martaba Eh? Shigar sa futar sa komai nasa da duk abunda ya aikata nace ko a rubuce ne ki gwajajjala ki kawomun. Ba magana nake miki ba?”

“Tuba nake ranki shi dade. Babu wanda nake kawowa rahotan sashen mai martaba sai ke, Amma Idan k’arya nake a abunda zan fada kisa sarkin yan lufdi ya zanemun duwaiwai. Mai martaba da kansa ba ai keba ya jaddadamun karna kara shiga sashen sa, Iyakata harkar fada da yiwa al’ummah iso bayan haka yace komai ya sahalemun na de nayi na daga ayyukan dana keyi a baya.”

“Ya isa, Salman dinne zai ce ki dena zuwa sashen sa? Salman din ne zaice ya cire ki a al’amuran sashen sa bayaga ison fada kawai? Toh waya dora akai? Idan kikai mun Karya to tabbas zansa amiki jina jina tare da zaman gidan yari na lokaci mai tsawo.”

“Allah yaja da ran gimbiya, Abunda labbana suka furta gaba d’aya babu karya jikin sa. Falaki da Alhassan babban bafade, Su mai martaba ya dora akan komai nasa da yankin kofar kudu baki d’aya..”

Hannu kawai shaheeda tai mata alama data tashi taje, Jakadiya na fita shaheedah ta rafka tagumi tana jijjiga kai,

“Lallai Salman... Cin amanar har ya kai haka? Wacce irin soyayya kuke haka da har cire jakadun ka daga bakin aiki.?”

Kwalawa hadimarta kira tayi tazo jikin ta na rawa, Ta shiga umartar ta kan leken asirin da zatai mata akan shige da ficen Salman,

“Sadiya sunan ki ko?”

“Eh ranki ya dade.”

“Yauwa ki kula sosai da duk abubuwan dana gaya miki, Karki batamin aiki kin daiji labarin abunda nayiwa Batula data batamun aiki ko?”

“Eh ranki ya dade, Insha Allahu zaki same ni me cikar aminci da gaskiya.”

“To tashi kije.”

Fita tai, Ita kuma shaheedah ta shige cikin dakin ta tana kokarin sake kiran ta hajiarta a waya.

*F A D A *

GABA d’aya an hallara anata fadanci, Wani zancen Salman ya tanka wani yai shiru, A haka har aka kammala. Manyan yan majalisa suka zauna. Don sake zantawa da sarki zama na biyu.

“Sarki na sauraron ku. Ayi a gaggauce saboda yaje ya huta.”

Chiroma ya matsa gaba yana rissinawa,

“Allah yakara maka Lapia jibi ne daurin auren nan dakace ka amince.”

Nan Kowanne ya dauka wambai nayi, Galadima na karasawa. Salman dai duk yana sauraron su har suka kammala. Yai gyaran murya yana cewa,

“Toh dik naji batun ku.. Kuma... Na amince da fari sanda kukai min zancen ban tubure ba nace na yadda a auramun su, To bayan munyi haka, Sai naji sha’awarar karanta rayuwar sarakuna na baya na yankin basannabas, Na karu kuma na ilmantu sosai. Waziri ka karanta ko?”

Waziri ya kad’a kai cikin tabbartawa, kamar gaske. SAS ya cigaba da cewa,

“Na kwadaitu sosai da yanayin tsarin mulkin su, Musanman tsatson Masekiri Tajiri, Suna mulki ne bisa tsari da bin doka, Kuma dokar ta hau kan kowa komai girman rawanin mutum , Kai Allah ya jikan magabatan mu...”

“Aamin. “

Suka amsa baki d’aya, Kowannen su ya gaza fahimtar inda zancen SAS ya dosa. Murmushi yayi kafin ya cigaba da cewa,

“Batin na karo aure babu.. Bank’i ba nan gaba Idan ni na canza ra’ayi, Wanda gaba d’aya yanzu dai ni Salman ‘Da ga Aliyu jikan Salmanu babban Da ga Ibrahim... “

Bai karasa ba galadima ya mike har yana tuge rawanin sa,

“Akan wane dalili? kai ka isa ka ki amsar abinda muka yanke...?”

“Na isa Baba.. Duk wani hukunci da za’a yanke inde akwai cutarwa aciki magabata sun rawaita cewa Kayi fatali dashi.”

“Bangane ba ranka ya dade... Shin wanene zai cuce ka mai martaba? Waya isa balle har ya isar?”

Cewar waziri yana kallon su galadima ta wutsiyar idanu. SAS ya daga kai yana dan sake daga muryar sa sama,

“Inaga ba kuma lura da yanda aka sauya tsarin kayan cikin fada ba...”

Yana rufe baki Kowanne ya shiga duddubawa, Sosai gashinan an caccanza yanayin zaman wasu abubuwan, Duk kuwa da dai kayan ciki ne dai, Salman ya cigaba da,

“Shekaran jia ne nasa dogarai su canza yanayin tsarin saboda karbar bakuncin matemakin shugaban kasa, Badan ya fa’di zuwan nasa a kurarren lokaci bama da sabbi za’a zuba komai. Toh Allah cikin ikon sa, Dogarai na caccanza tsarin ciki ne sai sukayi gamo da wani bakin tsibbu.”

“Ba’kin tsibbu ranka ya dade?”

“Kwarai waziri.. Gaba d’aya duk kusurwoyin ma’ajiyar abu an dasa tsibbu a kasanta, Wani abun tsoratarwar ma shine har kasan kujerar da nake zama sai da aka hak’o wata kwalba mai dauke da layoyi wadda gaba d’aya nasa an bincikamun duk dan a cire ni ne daga karagar mulki, A cutar dani a kuma lahantamun rayuwa... Waziri dakai ka’dai na yadda shin a ganin ka zan yadda da zancen su wambai na cuci kai na na ki kuma koyi da yadda sarakunan magabata su ka zartar da tsarin mulkin su?”

Jikin waziri sai ya nemi fara rawa yai azama ya dawo gaban SAS yana rissina masa,

“Allah yaja zamanin ka.. Ban fahimce ka ba, Ace ina cikin masarautar nan aka aikata wannan danyen aikin? Toh Allah ya Kara maka Lapia shin anga sunayen wanda suka binne tsibbun?”

SAS ya girgiza kai yana murmushi,

“Waziri.. Kwantar da hankalin ka, Lapia lou nake, Kuma na tabbata babu sunan ka acikin wanda suka yi, Koma dai suwa nene yan majalisar sarki ne. Bazan kira suna ba, Ko suwaye sunsan kansu, A takaice dai nasa an kona duk abubuwan da aka tono... Saboda haka maganar karo aure bazan yi ba gaskia.”

Wambai ya sake mikewa yana kumfar baki,

“Toh kai kanada yakinin an binna ne don a cuce ka? Kuma ni banyadda ba gaskia wannan zance ne irin naka don ka kawo yadda Za’a fasa auren ka. Ko kuwa?”

Su Galadima suka fara tofa albarkacin bakin su, Waziri yai musu alama da suyi shiru.

“Ranka ya dade ka gafarce ni, Gaba da baya kanada makiya a masarautar nan, Baka gani wasu ne daban suka so suga bayan ka..?”

“Waziri!”

“Allah ya ja zamanin adalin sarkin mu.. Tuba nake.”

“Bakai lefi ba Waziri... Da kai d’aya tak na yadda kaf masarautar nan. Kuma nasan ba zaka hada kai da wasu ba don acuce ni, Saboda haka ka kara sanarwa su wambai nace bazan karo aure ba, Wannan magana an fasata, Domin Za’a iya auramun wa’enda za’a hada baki dasu, zasu shigo su kashe ni, Allah basshi nan gaba idan nayi ra’ayi don karan kai na na karo auren.”

Gyaran muryar da yai ne, Dogaran sa suka yayyabe shi ya mike ya fice hankalin sa kwance yabar su waziri suna tattaunawa akan zancen, Kowanne tamkar zai amayo wuta dan bakin ciki.

“Sannu ahankali kunata batamun shiri, Agaskiya nayi dana sanin hade kai na da ku..”

Cewar Waziri cikin tsantsar bakin ciki, Su wambai suka shiga bashi hak’uri, Waziri ya tuge rawani ya shiga fiffita dashi yana sharce gumi duk kuwa da na’urar dake sanyaya fadar.

“Ranka ya dade.. Ni Ina ganin hargagiya ce kawai don kada a aura masa su... “

Waziri ya watsawa wambai dayai maganar harara yana sake sharce gumin fuskar sa,

“Kai dai wani lokacin idan kayi magana sai na rasa tayaya kake bari tafito saboda rashin amfanin ta. Hargagiya? Bakasan ire iren abubuwan nan zasu zama yadena yadda dani ba? Idan ba yarda a tsakanin mu kuma kuma taku batayi kyau ba kuwa.”

“Tuba nake ranka ya dade... Ni sai nake gani kamar yaron nan tunanin sa ya fara dawowa, Du bada yadda yake magana cikin izza.” Cewar chiroma.

“Anya kuwa? Banaji gaskia, Domin da hankalin sa ya dawo dole zai waiwayi mahaifiyar sa..... Yan uwan sa, Dama karbar ragamar mulki gaba d’aya batare da bata lokaci ba. Gigin auren sa da yarinyar canne yake dibar sa.”

Waziri ya bashi amsa cikin tabbatarwa, Duk suka aminta da zancen sa, Kowanne ya shiga tofa albarkacin bakin sa.

“Yallabai ya za’ai kenan yanzu? Ina mafita?”

Wambai ya dukar da kai kasa yana tambayar Waziri cikin girmamawa.

“Maganar ‘karin auren sa a soketa gaba d’aya kawai, Kowa yaje yai tunanin wani abun da zamu yi amfani dashi wajen yakarsa har ya hakura ya sauka ko mu hada kai da sauran yan majalisa a sauke shi..”

Da haka duk suka tsaida magana d’aya, Maganr karin auren SAS an fasa, Sai sun bullo masa ta wani wajen da bai Zata ba.

Duk abunnan da suke SAS na saurarar su yana kuma ganin su ta na’urar computer. Murmushi yai irin na gefen bakin nan kafin ya sake danna madannin nan dake adana masa dukkanin bidiyon sirrin sa.....

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
Chapter 104 · 0% Book details