← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 114

Sashe 2

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dan guzumar uban ki mezan miki? Kafaffiyar yarinya bakida aiki sai fada a gari, kin gunduri kowa. Zaki cigaba da wanke wanken ko sai na lallasa ki.?”

Idanuwa na suka kawo ruwa, Cikina sai neman agaji yake. Na dinga rarraba ido cike da tashin hankali, yunwa nake ji sosai tamkar naci kasa haka nake ji, saboda jiya ma haka na kwana ban samu abin da zan kai ciki na ba. Wajan bishiyar darbejiyar dake tsakiyar gidan mu na nufa tare da sanya hannaye na na rungume ina sakin wani marayan kuka. Da haka mahaifi na ya shigo daga zaure shi yana gyara hular kanshi wacce ko lankwasuwa ba tayi tsabar rashin gyara da ba'a mata. Kafadar sa ta dama saqale take da fatanya da alama daga gona yake. Shi dinma sai jera hamma yake. A hankali ya shigo bakin sa dauke da sallama. A jeme yake tafiya saboda wahala sautin jan kafarsa ce tasa na juya na dube shi ina mai shanye hawayen daya tahomin,

“Baffa! Sannu da zuwa.”

“Sannun ki d’iyar albarka.”

Dake haka yake kira na kasancewa ta yar fari. Karasawa nai kusa dashi na karbi fatanyar na ajiye ina jera masa sannu. Kallo d’aya yai min ya zura hannu a hujajjen aljihun sa. Murtala/Nera ashirin ya d’akko da alamun ita kadai ce dama aciki. A kudindine tasha facin salatif,

“Ungo diyar albarka. Jeki sayo ko awara ce a bakin yar kasuwa kici kinji.?”

“Baf...”

Ban karasa ba sakamakon iskar danaji tashige da gefen kunne na, Ashe Gajiyalle ce ta cika tayi fam zata fashe,

“Guzumar uba! Bashari nagaji da wariyar launin fatar da kakeyi a gidan nan, Kullum dan munafurci da bakar mugunta, Ba zaka bada ishasshen kudi ayi cefanen abinci ba sai dai kaba shedaniyar yarinyar nan tasai kayan kwadayi, Idan anyi magana ka fara sakin karairakin ka na yau da gobe. Gotai gotai dakai kana tafiya a jeme, Wai ungo diyar albarka. Toh wa aka samu bata hanyar halas ba?..”

Ta karasa fada tana gwada yadda Baffan mu ke tafiya. Baffan mu yai murmushi kawai yana mai saqale hular kansa akan gajeriyar katangar gidan mu data rabamu da gidan su Mari mai kitso. Tab’e baki nayi na fara kokarin wucewa don siyo abin da zan sanya aciki na kenan Gajiyalle ta danko wuya na,

“Ai babu inda zaki shafaffiya da mai, Har sai kin kammala wanke wanken can da kika bari.”

“Kyaleta taje zan karasa yi.”

Cewar Baffan mu, Ya fada yana mai nunamin hanya dana tafi. Arcewa nai a guje ban tsaya ko ina ba sai yar kasuwa wajen masu saida kayan dadi. Rasa abunda zan siya nayi na nera ashirin. Cikin haka sai ga Nafisan kansila tana tafe tana afawa bakinta awara. Gabanta na sha na Kece da dariya ina buga zani,

“Dan-dan-dan wa na kama?”

Nafisa tayi rau-rau da idanu, Tana bin ko’ina da kallo ko zata samu mai tare mata. Na sake shekewa da dariya ina bubbuga k’afa ta,

“Yanzun sai na caskala ki, Na casa ki. Nayi futu-futu dake kamar yadda ake casa maiwa. Dan bakin munafurci na sayi fadan kice ba zaki biya ba. Tabdijan.”

Na karasa fada ina mai nannade hannun doguwar rigar atamfa ta datai du’ku-duku saboda rashin tsafta. Nafisa ta rarumo hannu na cike da tsoro, Ta samin cakulet a hannun tana murmushi,

“Ungo chakulat kisha, Zan kuma sai maki kankarar madara mai sanyi ta murtala (Nera ashirin).”

___

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

*MISS XOXO*👩🏽‍🦯
*KIBIYAR AJALI.....!!!!*
_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_
🏹👑👩‍❤️‍👨💝

*MALLAKAR:- NANA HAFSAT*🧕🏼
*(MISS XOXO)*

*©️®️ZAFAFA 5 2021*
(PAID NOVELS)

*BABI NA 2*

Na karbe da sauri tare da gyara tsayuwa saboda naji banza ta fadi, dan dama Nafisa ba wani cikakken wayo ne da ita ba. Turo kallabi na nayi gaban goshi tare da kama kugu ina girgiza jiki nace mata.

“Idan karya kike min wallahi duk randa na ganki sai na fasa miki hanci, kinsan ni fa bana san alkawarin yan nefa.”

Cikin raunin murya Nafisa ta kwaso rantsuwa ta dire min tare da kallon cikin ido na tana cewa zata bani da gaske, sannan ne na matsa mata ta wuce nima na tafi ina dukan cinya tare da cewa.

“Hahahaha hooo ni Dije..., Dijan gala ta mai gari bazan auri talaka ba... Kodan bakin cikin Gajiyalle matar uba.”

Nayi dariya kamar ina kusa da wani sai dai babu kowa hasalima kowa harkar gabansa yake yi ba ruwan wani da kowa. Gaskiya chakulat akwai dadi, tunda nasa ta a baki na naji ina neman rasa harshe na, duk a zato na ma harshe na ya tsinko daga cikin baki na saboda zaki, tabbas ina son dadi gashi Allah be yo ni a gidan da ake cin mai d'an maiko-maiko ba.

Kai tsaye wajan mai siyar da kan kifi naje na siyo na naira biyar, na tsaya a gurin na dangwali yaji na cinye. Daga nan naje na siyi yajin masau shima na naira biyar ya rage sauran goma, na hango rumfar mai gasa zabi, wayyo Allah garin daɗi yana nesa, miyau na ya tsinke sai kawai na girgiza kai tare da tsayawa gurin mai rogo na siyo na goma. Gefe guda na samu na zauna na cinye tas sannan na samu randar da ake zuba ruwa, duk mai bukatar amfani da ruwa indai bashi da kudin siyan wanda ake kulawa a farar leda to wannan ruwan shi zaka sha, almajirai, yan garuwa, masu walda da dai sauransu duk da shi suke amfani, haka nima naje na dauki abin diba nasha, aikuwa na saki wata katuwar gyatsa kamar naci duniya da abinda ke cikin ta.

Kwanaki biyu da yin alkawarin mu nida Nafisa naji shiru bata kawo min ba, bayan na gama share tsakar gidan mu da Gajiyalle ta sanya ni nayi, na dauko mayafi na naci d'amara kamar yadda na saba yi. Da gudu na fita dan karma ta kuma sa ni wani abun daman ga wanke-wanke nan ba'a yi ba kuma idan har ta ganni sai ta ce ni zanyi, dan haka kai tsaye gidan su Nafisa naje, tana zaune a tsakar gida ita da kawayenta suna wasa, gani na da tayi yasa ta saurin mikewa ta shiga dakin Umman su. Ko tsoro banji ba haka na tsaya ina faman girgiza kugu alamun akwai tsantsar rigima a tare da ni, can sai gata ta fito rike da kankarar madara tana zuwa ta miko min jikinta yana rawa tace dani.

“Dan Allah Dije kiyi hakuri, tun jiya na siyo zan kawo miki gida aka hanani fita. Gashi nan Umma ce tasa miki a cikin kankarar zobo shi yasa ma bata narke ba har yanzu.”

Nan da nan na saki jiki tare da karɓa ina yake baki, har cikin rai na naji dadi dan tun kwakin da Gajiyalle ta damka min a hannu ban sake saka komai a cikin baki na ba. Na zauna wajan su muka ci gaba da wasa, amman fa nice na zama shugaba a cikin su, domin sai naga dama ma zan bari a taba kayan wasan kuma babu mai ce min dan me? Tun daga lokacin kuma muka zama kawaye sosai da Nafisa, kullum ina gidan su muna wasa har ranar da Baban su ya siyo musu talabijin ina gidan akai ta murna kansila ya siyo talabijin da janarato.

***A duk lokacin da naji mahaifina yana sauraron radio ko kuma idan muka je gidan su Nafisa wato ƴar kansilan mu muna kallo a talabijin, na kan yi mafarki da kuma hasashen nima ina ciki ana damawa dani. Babban abin da yake daure min kai shine ta ina mutanan radio suke shiga suyi magana har a jisu radau kamar yadda muke ji? Abin sake daurewar kan kuma shine, wadanda nake gani a talabijin, kuma kullum cikin shiga ta alfarma, na kan ce ko a ina suke samun kaya tsala-tsala haka? dan naga basa maimaita su idan suka sanya.

Kasan cewar baki na baya iya yin shiru akan duk abin da nake son sani, Hakan yasa na ke yawan tambayar Bello yayan Nafisa cewar.

“Wai dan Allah Bello ya za'a yi nima idan na girma zan iya irin wannan aiki?”

Sai ya galla min harara irin ta wulakancin nan yace min.

“Ke dalla gafara yiwa mutane shiru, uban waye ya gaya miki jahili ko jahila suna iya yin aikin jarida? Tafi ki bawa mutane guri keda ko fensir baki iya rikewa ba bare shiga aji d’aukar darasi.”

Ya kamata inji haushi idan ya furta min haka, amman ina wata irin k'ek'eshasshiyar zuciya Allah ya bani da ba komai ke bata min rai ba, musamman irin wannan da nice na tambaya. Sai na yatsina fuska na taɓe baki ina jujjuya idanuwa, a rai na na kan ji tabbas zan iya aikin jarida koda kuwa zan riƙewa ma'aikatan abin da suke magana dashi. Idan na koma gida na kan tambayi Baba na.

“Shin Baffa ya zanyi na zama ƴar jarida?”

Ya kalle ni yana dariya irin tasu ta masu hangen nesa, ya gyara zama yace dani.

“Ummi na zaki iya amman sai kin yi ilimi na zamani da na addini.” Lokacin ina cikin duhun kai, sai na ce dashi.

“Toh Baffa a ina suke ilimin zamanin dana addinin yanzu naje na debo san rai na?”

Baffa ya yi dariya cike da ganin wauta irin tawa.

“Ummi na kenan, su ai ba shukawa ake yi ba, kuma ba a kasuwa ake sai dawa ba bare kije ki siyo. Karatu ne na boko dana islamiya, su zaki yi sai ki zama ƴar jarida ko likita ko lauya da sauran su.”

Ina jin haka a lokacin nace da Baffa.
Chapter 2 · 0% Book details