← Book details Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 114

Sashe 45

Kibiyar Ajali Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shaheeda dake zaune kasan carpet kanta yana kan cinyar Gimbiya Huwaila sai faman bubbuga bayan ta take yi alamar lallashi. Cikin kukan bakin ciki ta fara magana tana dafe kirji da alama zuciyar ta tana cikin hargitsi, tace.

“Bana tunanin Salman ne yace yana son auran nan, wallahi ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba nasan jan zuciyar shi akai ta hanyar yi masa asiri. Ban da haka ta ya za ai ace wanda ko daga ido ya kalli mutane ba ya iya ya bare har yaga wata banza wacce ba kowan kowa ba yace zai aura? Na rantse da Allah asiri suka yi mishi, kuma wallahi sai ta gwammace ba ta aurar min miji ba. Saboda ni kadai ce tashi babu wacce ta isa ta shigo min bukka dan shiga cikin sheka ta, wallahi sai nai mata abin da zai sanya ta gudu da kafafuwanta yar iska kawai.”

Magana take cike da tsantsar bakin ciki wanda idan zaka kashe ta ba zata iya maimaita abubuwan da ta ke furtawa ba, su kuma duk sun zuba mata ido ko wanne da irin abin da yake cikin zuciyar sa. Shaheeda da komai ya fi yi mata zafi saboda abubuwan da take gudun faruwarsu suna da yawa a game da sarki Salman da ita. Waya kuwa ta kira shi yafi sau ashirin amman ba ta shiga, shi tuni ya sauka a birnin Cyprus cike da tunanin abubuwan da ya baro a gida Nijeriya. Mikewa tayi tana sharar hawaye ta kalli su Gimbiya Jaleela wacce ke dafe da goshi tace musu.

“Dole zan yi tafiya zuwa gida dan sanar da lamarin nan a gurin iyaye na, duk da na kira wayoyin sa bana samu gobe zan shirya na tafi ku kuma kuci gaba da tsara komai kafin na dawo.”

“Baki da damuwa ai Shaheeda, kuma ko baki fada ba kinsan tabbas wannan fadan ba naki bane ke kadai har da mu. Kije lafiya ki dawo lafiya, zaki ci gaba da rayuwarki ke kadai a birnin zuciyar Salman.”

Jaleela tayi maganar cike da karfafawa Shaheeda gwiwa.

_____Su kuwa can bangaran suna ta shirya sashen amarya, basu gama ba gashi har dare ya yi dole sai dai abar wasu shirin zuwa wayewar gari sai a karasa. Sun kafa gadaje sun sanya kujeru da dining da sauran su, kitchen ne dama ya rage basu kammala ba, gashi ana ta kiran su akan su dawo za'a dauki amarya a kawo ta gidan ta. Haka suka tashi suka harhado komatsan su suka dawo cike da mamakin abin da ya sa aka hana su zuwa wani sashe dake gefe (mahaifiyar sarki Salman) dogarai dake bakin gate din su suka shaida musu cewa wai tace kar wanda ta shiga ba taji dadi ne.

Suna dawowa suka tarar na gama kimtswa da taimakon Aisha cikin janyo min ayoyin Allah tana fassarawa har sai da naje na yi wanka nasa kayan da suka fito min dashi sannan ta shafa min mai a kafafuwa saboda cewa na yi babu abin da zan kuma yi bayan sanya kayan. Zata shafa min a fuska wai nayi kwalliya ko hoda ce na sa amman na dage akan cewa ba zan yi ba sai dai idan an kai ni ya koro ni, amman ba zan wani yi masa kwalliya ba dan babu wannan tsarin a cikin zuciyata. Kawu daddy, kawu Kabiru da kawu Hashimu sune suka yi min nashiha, sannan suka saka ni yi musu alkawarin zama da miji na lafiya kamar yadda iyaye na suka yi gashi yau babu su ko daya a cikin su sai labari.

Daga nan kuwa suka riko ni ina ta kuka suka sanya a mota, Aisha ta samu ta shigo kusa dani da taimakon matar kawu Kabiru. Sai da aka cika motocin da aka tanada wajan kai ni, sannan aka dauki hanya cike da kide-kide da bushe-nushen abubuwan sarauta har muka je cikin masarautar Basannabas, wacce a baya ina burin naji ance za aje cikin ta naji ina ma dani za a shiga saboda murna, sabanin yanzu da babu masarautar da na tsana irin ta. Kirjina ya dinga bugawa tamkar zai zazzago ya fado, ga wani mugun bacin rai da nake ji a rai na ko addu'a na kasa yi bare naji sassauci, sai ma kara zafi da zuciya ta ke yi....

ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, AMANA CE A HANNUN DUK WANDA YA SIYA, NEMI NAMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFIN DOMIN MALLAKAR NAKI, KI GUJI KARANTA NA BATI.. DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU RUBUTAWAR..._

*24*

Sanda aka bude min mota wai na fito, sai naji wani dummm.... A cikin kunne na kamar an cire min duk wani sauti, sai magana kawai da nake ji kai tsaye daga bakunan mutane kamar suna dariya. Da kyar na sakko da kafafuwana ina rike da Aisha gam sai kace ance guduwa za ta yi ta barni. Kai tsaye sashe na aka nufa da ni kasan cewar su Ciroma sun ce ba sai an kai ni wajan kowa ba,Naji dadi kuwa dan ni dama ba so nake yi na ga ahalin shi ba nasan raina baci zai kara yi tunda ba kaunar su nake yi ba nima.

“Shiga da kafar ki ta dama Dije, kiyi addu'a ki shiga Allah yasa mutuwa ce zata raba ku keda mijin ki.”

Matar kawu Hashim ta fada tana daga gefe na wajen hagu, Aisha kuma tana bangaran dama na rike ta sosai. Bismillah kawai na yi a zuciya ta nasa kafata ta dama kawai na shiga, sauran suka biyo baya na suna guda kasa-kasa dan su kansu sun gane cewar akwai abin da yake faruwa a cikin masarautar. Babu abin da ya burgeni a cikin parlorn da muka shiga, sai ma wani irin wari da nake ji ya cika min hanci na. Nayi saurin janyo mayafi na tare da toshewa amman still kara karuwa warin yake, Na saci kallon mutane naga babu wadda ta rufe hancin ta sai ni, na fara tunanin su basu ji bane? Abu kamar zai bata maka ciki ko ma nace zai lalata kwakwalwa.

Suka dinga jana har cikin bedroom din wanda ya gaji da tsaruwa. Allah sarki kawu daddy, hakika ya yi min abin da ko a mafarki ban taba zaton zan same shi ba. Komai royal ya yi min wanda ko su Ya Shukrah iya abin da zai yi musu kenan. Aisha ta zaunar dani a gefen gado, Na zauna sai naji tamkar an cake ni da kusa saboda wani zafi da naji a hq dina kafin na yi wani yinkurin kawai naji wani abu yana fitowa daga gurin kamar an kunna famfo.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un.” Na furta da d'an karfi.

“Me ne ne Khadija?”

Na janyo ta ina dafe kai nace.

“Period ne ina jin ya dawo min, kuma fa ban dade da yin wankan tsarki ba.”

“Subhan’Allah, Amma ai ba abin damuwa bane tunda daman yana yin haka. Kedai kici gaba da kirga kwanakin.”

Sai raba idanu nake yi. Ta cikin laffayar jiki na nake hango komai. Kaya kala kala sai kawo su ake yi a baskets da gift boxes dana cikin paper bags. Wasu kayayyakin aka kawo cikin wasu irin basket da aka yi da kaloli masu kyau, kowanne kaya ne acikin sa fal. Baskets din zasu yi kala goma. A gaban Mami wasu mata suka ajiye, Tamkar ba zasu yi magana ba, da kyar wata daga cikin su tace,

“Ga kaya inji fulani.... Wato Gimbiya kuma Sarauniya sannan uwargidan Sarki Salman, Gimbiya Shaheedah diyar Sarki Ibrahim Hashimu da ke masarautar ‘Bullo.. Tace a shaida gaisuwar ta, Kafin taga amarya.”

Gaba na ya yanke ya fadi. Oh ni Dije! Wai kishiya ce da wannan aiki haka? Babu karamin kaya a cikin kayan da ta bayar a kawo. Turamen atamfa da shaddodi kuwa harda na iyaye duk an sako. Sai wulkita idanu nake.

Sannu ahankali kowannen su sai an bayyana mana na gurin Gimbiya wance ne. Da alamun na matan baban sa ne. Saboda yadda ko wacce take nuna bajinta, Tana bani waje na fiki komai. Kowa cikin shigar alfarma da dandatsa dandatsan kayayyaki, Wai ashe budar kai aka yi.

Matar kawu Kabiru ta rakani wani band’aki dake cikin sashe na tasa nayo wanka. Na fito tsab dani bayan na saka pad a jiki na. Cikin wasu hadaddun lace ta shirya ni. Aka doramin alkyabba wacce tafi wadda na cire da safe kyau da tsari, Waziri da kansa ya shigo da wasu mata yan mata su wajen biyar yace ga masu tayani hidima nan. Duk abunda nakeso na sanar musu. Akwai zagi kuma da duk aiken da zanyi fada shi zan tura. Sannan yace za a yi min rakiya sashen mutanan masarautar.

Sannu ahankali sauran yan uwa da suka rako ni suka sani agaba aka fara rarrakani gaishe da matan gidan. Banda sashen d’aya daga cikin matan marigayi sarki da aka ce mana bacci take yi. Amma sauran matan da bangama sanin su waye suba duk an kaini sashen su. Kowanne ya karb’e ni babu yabo babu fallasa..

“Ni wacece me babban dakin ne acikin su...?”

Hairah diyar Kawu kabeeru ta tambaya tana mai daukar hoto na awayarta.

“Kila acikin wa’ennan guda 3 take.” Cewar Ya Shukrah!
Chapter 45 · 0% Book details