← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 98

Sashe 97

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashin hankali sosai ya nuna karara a kan fuskar dukkansu, Mourad kam rungume Ammi ya yi tare da sakin kuka sosai!

"I knew all this would happen!"ya fad'a cikin kuka, sosai tausayin Mourad ya kama doctor bama shi kadai ba har da sauran mutanen wajen

Mikewa doctorn ya yi daga in da ya ke zaune ya zaga wajen Mourad dake kuka kaman ba Namiji ba, handki ya mik'a mai tare da patting bayan sa ya ce

"Ba kuka ya kama ta kayi ba doctor, ga wannan papers din kayi signing sai mu shiga da ita theater din a cire abinda ke cikin ta"

Karb'an papern ya yi cikin rawar hannu tare da signing, Iqbal kam mamaki ne ya cika sa ganin yanda Mourad ya ke kuka kaman ba namiji ba.

Ba b'ata lokaci doctors suka hau shiryawa za'a shiga theater, suna shiga sauran suka tsaya a wajen glass suna kallon su,

Cikin zafin ciwo ta ke rola kan ta daga wannan side din zuwa wannan side din caraf idanuwan ta ya sark'e a na Mourad da ya rufe bakin sa da hannu yana kuka

A hankali ta mika mai hannun ta alaman ya zo, wani irin farinciki ne ya ziyarci sa cikin sauri ya bar wajen tare nufan ta wajen kofan da zai sada shi cikin theater din

Wata nurse ce ta tare shi wai ba zai shiga, ai nan ya bad'e jajayen idanuwan sa da toka yace baisan zencen ba

"Ta ya za'a yi kice bazan shiga ba! Kinsan miye kike cewa kuwa! Wallahi sai na shiga" ya fad'a yana kokarin ture ta daga hanya, hayaniyan da Su Ammi suka ji yasa su tafiya wajen su da sauri, nan suka hau bata baki itakuma tayi kameme a hanya wai bazai shiga ba

Doctor ne ya fito daga d'akin theater din"ashe ga kan nan!  Wallahi matar ka tak'i bada had'in kai fa!  Ta ce sai ka shigo gashi time is going kuma in ta kai 1:00am a cikin wannan yanayin bazan iya cewa ga abinda zai faru ba"

Kallon agogo suka yi a lokaci daya suka ga 12:40am ne

"Toh ka shiga mana! "Suka fad'a cikin had'in baki,

"Shiga ka chanxa kayan ka kaima kasan yanda abin ya ke! "Doctor ya fad'a yana nuna mai d'akin chanxa kaya! ko b'ata lokaci bai yi ba sai gashi ya fito yana zuwa daidai inda nurse din ke tsaye ya bangaje ta wanda yasa takusa fad'uwa kasa...

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya hango ta, a hankali ta bud'e rinannun idanuwan ta ta d'aura a kan sa! Murmushin karfin hali ta sake mishi ta mika mai hannun ta ganin ya ja ya tsaya

Cikin rawar kafa ya karaso wajen ta tare da fad'awa a jikin ta yana sak'in kuka

"Happy birthday pumpkin! "Ta fad'a kaman ba'a cikin ciwo ta ke ba

A hankali ya ce"Happy birthday to you too and happy one year anniversary! "

"Pumpkin! na baka wahala ko?" Ta tambaye sa tana shafa kansa da ke kan kirjin ta, d'agowa ya yi tare da girgiza ma ta kai

"Abin da ka fad'a mun yamin ciwo sosai! Amma for making you suffer sorry I love you! " ta fad'a tana shafa fuskar sa

"Let start! " Doctor ya fad'a, rik'e hannun ta Mourad ya yi yana Kallon fuskar ta daya koma wani iri

Kaman zata yi kuka ta ce"Naso na haihu da kai na Pumpkin! Naso naji yanda mata keji yayin haihuwa ashe bazan iya haihuwa da kaina ba! "

"It's okay haka Allah ya kaddara! "Ya fad'a yana Kallon cikin idanuwan ta! "

"In na mutu ka yafe mu kaji? "

Hannu ya d'ora a lips din ta alaman ta yi shuru, murmushi ta sake tana cewa"kar ka Kara mun abinda ka yi kaji! "

Gyada kai ya sake yi, ganin ta fara fad'in shirme alaman alluran da aka ma ta yasoma aiki yasa shi fara tofa ma ta Addua kuma bai kalli inda ake aikin ba saboda bazai iya jura ba....

1:30am

Tsaf suka gama suka ciro yara hudu amma daya ba rai saboda ruwan da ya sha a cikin ta, gyara su aka yi sannan aka fitar da su inda sauran kuma suka hau dinke Zuly

Mourad ya gama tara zufa ko ta kan yaran bai bi ba idanuwan sa na cikin na Zuly wacce bata san inda kanta yake ba sanda suka gama kafin a ka sake ma ta wani allura daban sannan aka fita da ita daga theater room din....

10:00am...

Kowa ka gani ya yi jugum kasancewan yaran ma ba'a kawo musu ba saboda an je duba lafiyan su, wanda ya koma ne ma aka basu a cikin Kwali

Basu wani b'ata lokaci ba aka sallaci yaron tare da kai sa gidansa na gaskiya....

A hankali ta fara bud'e idanuwan ta ya mutsa fuska ta yi tare da sanya hannun ta akan cikin ta, murmushi ta sake tare da karasa bud'e idanuwan na ta

"Alhmdllh ta farka! Fakhih kira mana doctor! "Ammi ta fad'a cikin murna

"Narasa abin ciki na ko? "Ta tambaya cikin son danne kukan ta, girgiza kai suka hau yi, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanuwa tana mai jin farin ciki na ratsa ta

"Zan zauna baya na yana ciwo! "Ta fad'a wa su Umma dake tsaye a gefen ta!

"Kibari doctor ya zo kinji! "Qudsiyah ta fad'a tana shafa goshin ta da ga jik'e da zufa, gyada kai ta yi kafin ta ce

"Ina Pumpkin dina? "

"Gani nan!"ya fad'a cikin murna lokacin da ya shigo cikin ward din, murmushi ta sakar mai

A hankali kaman mai tsoron magana ta ce"Miye muka samu naga babu Wanda yake magana a kai! "

"One boy and two girls!"

Zaro idanuwa tayi cikin murna, zata yi magana kenan ta ga yanda yanayin fuskar su ya ke

"Kuna bani tsoro! Miye ya faru! "Ta tambaya gabanta na fad'uwa

Zama ya yi akan plastic chair din gefen ta sannan ya rik'e hannun ta, a hankali ya ce"actually yara hudu kika Haifa amma daya ya koma"

Runtsa idanuwan ta tayi tana jin ba dadi a ranta, cikin dauriya ta ce"Allah yasa mai ceto ne! "

"Ameen! "Suka amsa in chorus

A hankali ta ce"Ina sauran suke? "

"Suna zuwa! "Doctor da shigowar sa kenan ya fad'a, ai kuwa sai ga nurses uku sun shigo kowannen su rik'e da baby

Karban babies din suka yi kowa na fad'in tabarakallah Masha Allah saboda kyau musamman baby girls din wanda suka d'auko komai na Zuly kuma ana kyautata zaton hasken Mourad zasu d'auko shikuma baby boy din kaman sa Sak da Mourad amma bai d'auko hasken sa ba saboda wajen kunnen sa da suka hango(kun gane yawancin babies ana gane hasken su kokuma duhu su daga kunne ne!)

Ita Zuly kam ma ba ta bi kan matan ba tafi focusing a kan Na mijin saboda tashi daya ta ji son yaron fiye da dukkan su acikin zuciyar ko dai saboda shi namiji ne ban sani bah(hhh)

Shikuma Mourad akan wacce ta fi kama da Zuly ya ke, kowa ka gani murna yake, su Qudsiyah ana chan ana ta faman d'aukan selfie a Snapchat 👻 da yaran.....

"Please pumpkin ka bari nayi naming din baby boy dinnan kai kuma kayi naming din baby girls din! "Ta fad'a in a pleading tune!

"Anything for you mine! "....

Ranar Suna...

Sosai kowa ya sha mamakin sunan da aka sawa yaran harda su masu saka sunan

"MOURAD! ZULFA!! dakuma SABREEN(takwarar Ammi!), wow wannan sunan ya yi fa, amma Miye sa sweet bazai mun takwara ba? "Qudsiyah ta fad'a cikin kishi," to ba'a sa din ba!"

"Allah ban tab'a had'uwa da masoya irin wannan ba, wallahi sun burgeni! "Hibba ta fad'a tana Kallon Yusayrah da ke sa souvenirs a cikin jakan da aka yi pressing din sunan babies din

"Baki ga komai ba! Ai ina gaya miki in kika kalli gadon bayan Zuly ta wajen waist dinta sunan Mourad zaki ga anyi tattoo da shi! "

Dariya suka sa gabadayansu sannan suka cigaba da aikin da suke yi. Hidima suna aka yi sosai kaman ba gobe kuma sun samu mutane da dama wanda suka hallarci taron....

"Wai nikam sister laifi na mawa Momina  ne Naga ko barka bata mun ba balle ta Zo suna?”

"Aww ai bata da lafiya ne shiyasa ba ta Zo ba!”Lutfiya ta fad'a a hankali

"Miye ke damun ta ?"ta tambaya cikin damuwa

"Hmmm ai dady ne ya bud'a ma ta wuta akan saita fito da miji shiyasa fa!”

"Shi ustaz din fa?"

"Har yanzu babu labari saboda har yanzu matarsa!”

"Ya za'ayi naga matan nasa!”Zuly ta tambaya cikin takaici

"Zan sa Raeez ya taho dashi dakuma matarsa"Qudsiyah ta fad'a lokacin da ta shigo da kofin kunnun kanwa

"Bravo Sis! Wallahi ke ta dabance!"

Dariya kawai suka yi gabadayan su sannan suka cigaba da hirar su har sanda Mourad ya shigo kafin suka fice....

Sosai Zuly ta buga kan Matar Ustaz da nasihohi wanda yasa jikin ta yin sanyi

Har gidan su Momina suka Je amma banda Zuly saboda Mourad ya ce babu inda zata je

Suna ganin yanda mom ta dawo jikin kowannen su ya yi sanyi

Da murmushin karfin Hali ta tarbe su inda mazan suka fita tare da barin su biyu

Straight wajen baban Momina suka je suka mai gaisuwa sannan suka tambaya yaushe iyayensa zasu zo....

Kan kace Miye har an sa rana, farin ciki a wajen Momina kam ba'a magana, tashi daya ta warke ta murmure kaman ba ita ba....

Anyi auren Mom da Usataz da kuma Raees da Qudsiyah, ko wani bangare farin ciki ake, anyi taro sosai inda Zuly ce kirjin biki donma Mourad yana kawo cikas

Bayan an kai amare da washe gari suka koma Dubai abinsu, Zuly harda kuka Wai bazata koma ba, Dakyar dai suka lallashe ta suka tafi

_DUBAI_

"Mine baki fad'a mun batun cikin da suka zube ba! "Mourad da ke rik'e da Zulynsa saboda yanzu sunan Zuly ya tashi daga Zuly ya koma Mine itakuma tana Kiran namijin da Mou dina

Ajiye Mou tayi a kan gadon sa bayan ta gama bashi nono sannan ta karb'i Zulyn Mourad a hannun Mourad Domin  shayar da ita

A hankali ta ce"some words should better be left unsaid!"
Chapter 97 · 0% Book details