← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 98

Sashe 33

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yay Mou neh yace min konayi aure agida daya zamu zauna dashi"

Wani irin kallon kinma haukace Kuwah kebinta dashi  kafin tace" wai ke wata irinyan mahaukaciya ce? Ina kika taba ganin anyi haka?"

Turo baki tayi tace"toh aini ma haka yacemin"

Tsaki Kuwah taja zatayi magana kenan Mourad yashigoda sallama, tashi tayi zata tarbeshi Kaman yanda tasaba yayi saurin dakatar daita da hannu

Gaishe shi Kuwah tayi kafin tafice domin basu waje cos ta fahimci da akwai magana abakinshi...

"Baki daina kukan bane Zulynah?" Yatambaye ta lokacin daya aza murmushinyake asamar fuskarshi

Marairaice fuska tayi tareda kamo hannun shi duka biyu tace "pls katafi dani duk inda zaka"

Share hawayen daya zubo mata yayi yace" ba amfanin hakan"

"Why??"

"Soboda akwai auren Wani akanki"yafada cikin sanyin murya

"Muje toh mu rokeshi yasakeni"

Girgiza kanshi yayi yace"bakisan babu kyau mata ta tambaye mijinta saki bah?"

Kuka tasaka mishi tana mai kwanta mai ajiki,ahankali yacireta kafin yasa hannu a aljihu yafito da wasu envelopes  guda  3

"Wannan duk lokacin da kike cikin bakin ciki kidauka ki karanta"yafada yana mika mata red envelope

"Wa'inan biyun Kuma a kowani birthday dinki zaki dauki daya ki karanta" yafada yana bata sauran biyun

Kallonshi takeyi tace"why are you giving me this?"

"Just, I will miss you"

Zatayi magana kenan yakatse ta da fadin" oya get ready you know long drive zamuyi zuwa Abuja baza mutafi a jirgi bah"

"Yes kace zamuyi having nice tym"

"Erh"yafada yana lumshe ido ganin yanda takeyi...

Shiryawa tayi cikin simple wedding dress amma batayi kwalliya bah cos cewa tayi babu  amfanin yinshi,haka suka barta badan sun so bah

Wajen Malam akayi daita inda yana Mata fada sosai da nashihohi dayawa akan zaman aure,jikinta yayi Sanyi kalau amma ko kuka batayi bah soboda Mou dinta yace tamai alkawarin bazata sake zubarda hawayen ta bah, idonta tarr akan Malam as usual amma expensive gyalen dake yane akanta ya hana aganta...

"Afitoda Amarya" wasu goggonita suka fada

Kuwah ce tafito da ita daga cikin Fada hannun ta sakale da nata, banda tsaki babu abinda takeja

Wajen motan da wasu goggoninta suke ta nufi daita

Tsayawa tayi tace"Ke miye haka?"

"Na miye fah?"

"Naga kin Wani Jani zuwa wannan kurbebiyan motan neh"tafada tana nuna wata Lexus din gabansu

Zaro ido Kuwah tayi  dajin abinda Zuly tace zatayi magana sukaji muryan Mourad ta baya yace " zo mutafi"

Juyawa tayi tana sakin murmushi datin dazu takiyi ido daya ta kanne mai ganin ya kureta da ido, shafa lausasiyar sumar kanshi yayi ya mikar da hannu shi tareda dan rusunawa yace"please"

"Sure"tafada cikin murmushi tareda zare hannun daga na Kuwah sannan tayi gaba

Sororo Kuwah tayi tareda bin bayanta,dakanshi ya bude mata bayan mota tashiga

"One minute pls" yafada wa Zuly bai jira jin miye zata fada bah yakai gaba abinshi.

Jiyayi yayi karo da mutum daidai kofan shiga fada, mikar da ita yayi yace" baki kallon gabanki neh?"

Dagowa tayi daga karkade zaninta idonta ya kyallo abinda tazo nema, ajiyar zuciya tasauke, ganin batayi magana bane yasashi zai ratsa gefenta ya wuce cos he don't want to keep his Zuly waiting

"Kayi hakuri DanAllah "tafada cikin sanyin murya mai ratsa zuciya

Cakk yatsaya yana tariyo inda yasan wannan muryan, juyowa yayi cikin tsananin fushi cos ko amafarki neh bazai taba mantawa da Mayyan data yi sanadiyar tabon jikin Zulynshi bah

"In banyi hakuri bafa? "Yafada cikin daga murya

Sunkuyar dakanta tayi gabanta na Wani irin bugawa na tsoro,tsaki yaja tareda cikawa rigarshi iska, kumatunta taba soboda tuna marinshi dayayi sanadiyar ciruwan hakorin ta guda daya, ahankali taja yan matan kafafunta tayi waje.

Fitowa yayi rikeda leather a hannunshi  sai Ammi agefen shi dakuma Umma da alaman tafiya Ammi zatayi,Wani mota daban,sallama sukayi da Ammi Kaman karsu  rabu cos dan zaman sun nan harsun saba...

Bai dade da zama abayan motan bah sukaji an kwankwasa glass din mota , winning down Zuly tayi taga Kuwah atsaye

"Banson rashin mutunci fah"tafada cos tin dazu take tsaye tana jiran abude mata mota

Kallon sama da kasa tamata tace"rashin mutuncin miye fah "

"Bude min nashiga"

Yar dariya Zuly tayi tace" 3 is a crowd ki je ki shiga Wani motan ba wannan bah"

"Me banson shirme fah"

"Kawar mu kiyi hakuri kibi Wani mota" Mourad yafada

Tabe baki Kuwah tayi tana mamakin su batareda tayi magana bah tayi gaba abinta, fitowan Iqbal yayi daidai da Tafiyan su Zuly , da ido yabi G.wagon dinsu , ganin Kuwah tsaye yasashi karasawa wajenta

"Lafiya dai koh?"

Kuwah data gama cika tayi dam taja tsaki tace"Ina fah lafiya wancan shirmemiyan matar ka ta tafi ta barni"

"Ina taje"

"Ina kuwa zata jeh? "

Xaiyi magana kenan Awad mijin Kuwah yafito

"Mijina mutafi kaji"tafada daidai karasowan shi

"Kai Amaryan fah?"yatambaya da mamaki

Yar tsaki taja tace"Amaryan da suke hanyan Abuja?"

Ganin Suna mata kallon rashin fahimta yasa tace" Mourad yatafi kaita, Kuma danazo shiga cewa tayi siri is a rowd "

Dariya Awad ya maze jin turancin matan shi ,murmushi yasakar mata kafin ya taba Iqbal daya shiga duniyar tunani yace" mukam muntafi abinmu tinda wacce mukazo kaiwa ta tafi"

Tsaki Iqbal yaja cike da rashin jin dadin abinda su Zuly sukayi,kwafa yayi tareda bawa Awad hannu...

"C'Mon Zuly eat something "yafada yana ajiye meatball dake cikin take away akan cinyarta

Kawar da kanta tayi tace"Nina koshi"

"Umma fah cemin tayi tin safe bakici abinci bah Kuma yanzu kice min baki jin yunwa"

"Feed me toh" tafada tana bude mai bakinta tareda cire gyalen kanta

Ciyar daita yahau itama tabashi  cos tasan shima baici abinci bah...

A katon parking space din farfajiyar gidan Iqbal aka yi parking alokacin har wasu yen uwa Sun isa ana ganin gida da Kuma jeren da aka mawa Zuly,  babu abinda sukeyi inbanda santi, kasancewan part daya mai dakuna 3 kitchen daya da palour daya dayake upstairs din cikin-cikin gidan aka ware mata sai ya kasance part din Zuly dana Yusayrah na facing na juna.

Masallaci straight Mourad ya wuce yin sallahr magrib kasancewan sunyi dare, dawowan shi yayi daidai da isowan Iqbal da Yusayrah,

Ai nan Iqbal ya murza toka a idon shi yace Mourad bazai shigan mishi gida bah babu yanda Mourad baiyi dashi akan Sallama zasuyi bah Amma yaki cikeda damuwa mai tarin yawa Mourad ya shige motan daya kawo su wanda alokacin  an fito dashi daga farfajiyan gidan

Wasu zafaffan hawaye neh suka zubo mai daidai lokacin da motan yatashi, motan na shigewa yafashe da kuka, juyowa driver yayi yana bashi baki ganin Mourad bazaiyi shiru bane yasa ya Kyaleshi,

Sosai yake kukan bakin ciki, kukan dayake fitowa daga Kasan zuciyar shi, kukan dayasan ba rage mai komai bah yakeyi, rike kirjin shi yayi da hannu daya yana jin zafin da bai taba jin irin shi bah.

"Mun iso" driver yafada daidai ya bude wa Mourad kofa, ahankali ya dago rinannun idon shi  wanda sukayi jawur Kaman gaushin wuta, hancin nan yayi Wani irin Jah sobida kukan dayasha

Fitowa da kafar shi yayi dakyar cos jiyayi kafar ya mai nauyi sosai, dafa motan yayi yafito amma abin mamaki jiyayi baya iya daga kafafun shi, Wani irin zafin daya fi nada neh ya ziyarci zuciyar shi

Jikake timm yafadi kasa sumamme while jini nafitowa daga...

_Ina mai baku hakuri Team Mourad, haka labarin ya kunsa Amma ku saurareni inshaAllah zakuyi farinciki nan gaba_

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*
*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 54*

Jikake timm yafadi kasa sumamme while jini nafitowa daga bakinshi dakuma hancin shi , agigice driver yayi cikin gidan Don kiran Ammi...

Tin da ta idar da sallahn magrib take jiranshi amma haryanxu shiru before tayi tunanin saiya yi sallahn Isha zai shigo shiyasa tazauna jiranshi.

Tashi tayi daga kan sallayanta sannan tacire khimar dinta, ahankali take saukowa daga kan matakalan been,Hango su Yusayrah tayi akan dining sunacin abinci batareda tayi magana ba tayi hanyan fita daga palourn jitayi ance

"Ina zakije?"juyowa tayi taga Iqbal neh yayi magana ga fuskan nan a murtuke cikin sanyin muryan da bai San tana dashi bah tace

"Tin dazu yaje yin sallah Amma har yanxu shiru gashi 9 yayi nasan Ammi najiran shi and am very sure baisan ko ina anan bah Kuma tin dazu gabana yake faduwa lyk Wani abu Mara kyau yasameshi and am very scared shiyasa zanje duboshi a waje"

Tsaki yaja cikin bacin rai yace" in wani abu mara kyau yasameshi  who's at loss?"

Gabadaya ji tayi bata son hayaniya dashi duk da abinda yafada bah karamin bata Mata rai yayi bah cos Allah yagani bazata breaking promise dinda tamawa yay Mou dinta bah inda yace koya jata da fada kokuma zagi karta rama,  bata so making  promise din bah amma soboda matsayin dayake dashi azuciyarta yasa ta yarda, ahankali tace

"In Wani abu yasameshi mutane dayawa zasu shiga damuwa ciki kuwa har dani and bazan yafewa Kaina bah"

Runtse idon shi yayi sannan ya bude yace" go back right now"

Ji tayi ranta yafara baci batareda tayi magana bah tafice abinta zuwa compound din gidan , inda sukayi parking tagani wayam babu mota babu alaman shi , wajen maigadi tanufa tace " danAllah ina motan da aka kawo amarya acikinta?"

Gyara zama yayi akan Wani wooden chair dinshi yace" inaga mai motan neh yabatawa oga rai shine yace yafitan mai agida"

Runtsa idonta tayi gam tareda dafe kirjinta tana jin Wani bacin rai mai tsanani na shigarta

"Lafiya dai koh yarinya?"yatambaye ta kasancewa magidanci neh maigadin Kuma yasan yar shi nafari bazata wuci sa'an Zulyn bah

Bude jajayen idonta tayi tace"nagode"

Gyada kai maigadin yayi yana nazarin yarinya cos daga ganin kwayar idonta  yasan tashiga damuwa dakuma bacin rai , tajuya zata tafi kenan yace" minti daya mana yarinya"

Cak ta tsaya  tana jiran jin miye zaice ganin bazata juyo bane yasa yace " komi yayi zafi maganin shi Allah, ki yawaita maimaita sunan Allah azuciyarki karki zo kiyi abin  danasani"

Batareda tayi magana bah tayi cikin gida tana mai kiran sunan Allah azuciyarta Kaman yanda maigadin ya shawarce ta, atsaye tasamu Iqbal sai faman huci yakeyi tsantsan bacin rai.

Yana ganin ta yasake daura fuska batareda ta kalleshi bah tayi hanyar matakala domin komawa part dinta,
Chapter 33 · 0% Book details