← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 98

Sashe 92

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe idanuwa ya yi yana shafa bayanta, a hankali ya d'auke chak tare da ficewa da ita daga kitchen din, straight cikin d'aki ya nufa da ita

Yana ajiye ta a kan gado gaban ta ya fad'i, haurawa kan ta ya yi, cikin rawar murya  ta ce

"Bari na wanke baki na! " girgiza kai ya yi tare da sa hannu a bakin sa alaman ta yi shiru, button din rigar ta ya hau tsincewa cikin sauri ta rik'e hannun sa

"Please bakina yana warin miyan kuka! "

"Ai ba ke kadai ki ka cin abinci mai miyan kuka ba! "Ya fad'a tare d'aura bakin sa a nata....

Yanda ya bar ta haka ya dawo ya sameta kuma har lokacin ba ta daina kukan da take yi ba, cikin rashin jin dadi ya karasa in da ta ke

Tana jin an hau saman gadon ta had'iye kukan ta tana share hawayen fuskar ta kaman ba kuka ta keyi bah

"Mine! "

Mik'ewa tayi da sauri tare da wucewa toilet saboda bata son ya fahimci kuka ta keyi, shafa gashin kan sa ya yi tare da runtsa idanuwan sa saboda shi gabadaya ya kasa fahimtan ta

Tana fitowa ta zauna a bakin gado a lokacin har ya sa kaya

"Mine miye ke damun ki ne? "Ya tambaya cikin sanyin murya, girgiza kai ta yi tana sa kayan ta

Wajen ta ya dawo tare da rik'e hannun ta yana mai kallon jajayen idanuwan ta, a hankali ya ce"Baki son ina tab'a ki ko? Baki son muna samun intimacy ko? "

Murmushin yak'e ta yi tana shafa fuskar sa cikin tsananin son sa, girgiza kai kawai ta yi tana cewa"ni kawai ina son mu koma gidan ne na gaji! "

"It's ok bari na yi magana a nema mana ticket! Wait ma wani gida daya zamu koma? "Ya tambaya a zuciyar sa kuma Addua ya ke Allah yasa ba na 9ja zata ce ba

"Gidan Ammi! "Ta fad'a a takaice,wani irin dadi yaji ya ziyarci zuciyar sa cikin sauri ya mike yana fad'in

"Bari na fara parking din kayayyakin mu!"

Murmushi kawai ta yi tare da kwanciya tana bin sa da ido kafin ka ce kit har bacci ya yi a won gaba da ita....

Farkawar ta da wuya ta kalle ta ajikin sa ma'ana har flight din su ya tashi, d'ago fuskar ta yi ta kalle sa,

"Sannu da tashi! "Ya fad'a yana ajiye magazine din hannun sa, murmushi ta yi tare da turo baki tana cewa

"Shine baka tashia ni bah? "

"Afuwan!  Bana son katse miki bacci ne shiyasa amma am sorry! "

A hankali cikin romantic voice ta ce"I love you more than words can explain! "

"Same here mine! "Ya fad'a yana kissing forehead din ta....

Sanda suka isa Dubai tukunna Mourad ya kira Fakhih ya zo ya d'auke su a airport

Maimakon ya ga Fakhih kawai ai nan ya ga zugan su Qudsiyah, Fakhiha, Momina dakuma shi kan sa Fakhih sun shigo cikin airport din, kowa ka gani bakin sa a washe kaman an musu albishiri da Aljanna

Girgiza kan sa ya yi yana shafa fuskar Zuly da ke kan cinyar sa"sun zo fah"

Mikewa ta yi a gajiye tana ya mutsa fuskar ta "sorry koh! Kin kusa hutawa! "

Gyada kai kawai ta yi, hannu ya d'aga saboda ya lura a cikin dukkansu babu wanda ya gan su

"Gasun chan! "Qudsiyah ta fad'a cikin murna lokacin da ta hango su, ai nan suka runtuma wajen su cikin murna

Ai ba su hankara ba kawai suka ga Qudsiyah da Fakhiha na kokarin rungume Zuly

"Zaku fad'ar da ita ne? "Mourad ya fad'a cikin tashin hankali, tsayawa suka yi suna kallon juna chan kawai suka fashe da dariya

"Wayyo Sweet daga hugging sai kace zamu fad'ar da ita? "Qudsiyah ta fad'a tana hararan sa

"Ai sai kuyi hugging din ta daya bayan daya ko ba haka ba? "Ya fad'a yana kallon Fakhih da ke ta zabga murmushi

Shafa gashin kansa ya yi yace"ai kuwa kar su mana asara ba! "

Jawo Zuly da ke kallon su cikin sha'awa ta yi tare da rungume ta tana cewa "To sai anyi hugging din"

Dariya dukkansu su ka saka kafin aka hau gaishe-gaishe kafin suka wuce mota

"Kai yaya wallahi kai good striker ne! "Fakhih ya fad'a cikin zolaya

Sune kai Zuly ta yi saboda kunyan da ta ji ya rufe ta, a haka a haka suka dinga hira har suka karasa gidan Ammi...

Gatan da Zuly ta gani no be small saboda ko ta wani bangare kulawa ta ke samu, Ammi kuma bata gajiya da had'a mata kayan kwalama kuma da kanta ta keyi

Ko spoon ba ta d'auka a gidan daga kwanciya sai sallah sai fita yawo gashi kuma Mourad ya koma wajen aiki,

Taso a barta ta je gida amma Ammi ta ce a'a kuma ba yanda ta iya haka ta hakura balle ma ba wani abu ta rasa ba, musamman Ammi ta sa aka had'o ma ta abubuwa daga 9ja saboda kwad'ayin Zuly...

3months later...

Zaune ta ke a bakin dressing mirror na d'akin Ammi saboda yanzu a nan ta ke, ko kadan bata bada chance din da Mourad zai ce ta zo su kwana ba sarai ya gane cikin ta ba mai sa jaraba bane kuma ya lura Ammi na d'aure mata gindi saboda da zaran dare ya yi sosai bata Barin sa ya fita da Zuly amma yakan faki idon Ammi in bata nan ya je ya la-latsa  ta... 

Cikin ta take shafawa a hankali tana jin farin ciki na ratsa ta har magana ta na yi ita kadan ta, yanzu cikin ta watan sa hudu kenan ciff, har ta fara sak'an su huluna masu kyau da showel kuma komai uku-uku ta keyi, 

kullum sai su Fakhiha sun tsokane ta saboda yanda ta ke nuna son cikin har rasa wanda ya fison cikin a cikin familyn a keyi saboda kowani bangare shiri suke sosai, kuma suma komai uku-uku su ke yi saboda yanda suka ga Zuly ta daga cewan su uku ne a cikin jikin ta, 

Wani sa'in ma kuka ta ke musu Idan suka ce bai kai haka ba shiyasa kawai suka barshi a yanda ta fad'a din, abu kad'an babies dinmu abin dariyan ma har sunaye sun rad'a wa yaran da ko motsin su ba'a fara ji ba!

Ammi ce ta shigo da cup din kunnu a hannun ta saboda shi Zuly ta ce zata sha, Tsayawa ta yi a bakin kofa tana cewa

"Ohh Allah ZulynMourad kar dai ko shafa mai baki yi ba kuma sarai kinsan mura ki keyi kalan anjima ki kasa bacci ko!?"

"Ammi na, magana fa na ke musu! " ta fad'a tana turo baki, karasowa Ammi ta yi ta ajiye kunnun a kan dinning wanda yake cike da kayan kwad'ayi

Wajen wardrobe ta nufa tare da d'aukan ma ta kaya har da rigan sanyi tana fad'in"to maganan ya isa haka shafa mai kizo ki sa kaya!.. Ganin da tayi ta turo baki yasa Ammi karasowa wajen ta tana bud'e lotion had'e cewa... Ko dai na shafa miki da kaina ne? "

"Zan shafa! "Ta fad'a cikin shagwaba

Shafa kan ta Ammi ta yi cikin tsananin son ta ta ce"Yauwa good girl! "

Ba b'ata lokaci ta shafa mai din tare da sanya kayan da Ammi ta chiro ma ta, tafara cin abinci kenan Qudsiyah da Fakhiha suka shigo

"Sannu fah maman uku! "Suka fad'a cikin had'in baki,gira daya ta d'aga musu saboda kofin da ke bakin ta, sanda ta cire tare da had'iye kunnun da kyar ta ce

"Mun fushi ku koma!"

"Haba dai! Kuyi hakuri mana Allah kin gannin nan na yi bala'in gajiya saboda yau mun shiga theater ni da sweet a haka ma gudowa na yi saboda na samu na muku sai da safe! "

Qudsiyah ta fad'a tana zama a kan kujeran dake facing na Zuly, kallon Fakhiha da tayi kalan tausayi Zuly ta yi ta ce"ke fa? "

Ita ma zama ta yi ta ce"kin ga am sorry kawai! "

Zata yi magana kenan ta ga Qudsiya na tura kosan ta a baki, zaro idanuwa ta yi ta ce"what? Na ga kawowa ya kama ta ace kin yi amma ya na ga kina tayamu ci "

"Am sorry mu ci tare Allah yunwa na ke ji sosai! "

Caraf Fakhiha ta ce"Toh shine ba zaki je kitchen ki d'eba ba? "

"Ke dallah! "Ta fad'a tare da hararan ta, kurb'an kunnun Zuly Fakhiha ta yi da sauri ganin bata kallon ta

"Nikam na shige su miye ne ku ke mun haka? "

"Abincin ki akwai shiga rai ne gabadaya sai na ji da nima ina da cikin"Fakhiha ta fad'a tana turo baki

Ya mutsa fuskar Qudsiyah ta yi ta ce"Nikuma wallahi na kosa kunmun aure na koma 9ja! "

Dariya Zuly tayi ta ce"Allah yasa kina koma gida a ce an sa ranan ku ke kuma Allah yasa yau ki samu! "

Ba kunya suka ce Ameen,rufe bak'in su da wuya Ammi ta shigo cikin d'akin

"Yaushe kuka zo? "

"Yanzu Ammi! "Su ka fad'a tare da gaisar da ita, sun jima sosai kafin suka wuce in da Qudsiyah zata koma asibiti ita kuma Fakhiha ta wuce gida

Zata haura ta koma d'akin su taji kafafun ta sun rik'e, yar kara ta kwala tare da zama a wajen stairs tana miyar da numfashi kaman wacce ta yi gudu

Ganin har kusan minti talatin Zuly bata dawo ba yasa Ammi bin sawun ta, ciki sauri ta karasa ganin ta a zaune akan tiles

Mikar da ita  Ammi tayi sannan cikin kulawa ta ce "Lafiyan ki kuwa? "

"Ciki na ne yake murd'awa! "Ta fad'a tana damke hannun Ammi saboda  yanda ciwon ya sake ciyo ta

A hankali Ammi ta shige da ita cikin d'aki, da kyar ta samu ta yi sallar isha! Tana idar wa kuma ta birgine a wajen,

Ammi ce ta kawo ma ta kopi mai cike da ruwan zamzam wanda ta topa mata Addua a ciki, tana sha kuwa taji ciwon ya lafa nan zufa ya rufe ta kafin ka ce me har idanuwan ta sun shige ciki,
Chapter 92 · 0% Book details