← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 98

Sashe 40

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saukowan su kenan daga room nasu sukaji kamshi ya bade musu gida, kallon Yusayrah yayi  ya dage mata gira daya alaman miye neh haka, girgiza mishi Kai kawai tayi.

Zaunar daita yayi akan kujera tareda daga mata yatsun shi biyu alaman 2mins kafin yabar wajen.

Sanye take cikin pink Ralph Lauren Silk Sleeveless Blouse da wani pencil long high waist skirt ga kamshin mai dadin dayake tashi daga jikinta.

Cakk yatsaya abakin kofan shiga kitchen yana ka're mata kallo daga sama har kasa, ahankali yafara takowa don karta Lura dashi

Kanshi ya sakalo ta wiyar ta yace"yau kece dakanki?"

Arazane tajuyo cos ya mugun tsorata ta ganin shine yasa ta buga kirjinshi cikin wasa tace"this not fair abokina"

Rungumeta yayi yana shakar kamshin dake fitowa daga jikinta  ta hanyar manna hancin shi da wuyar ta.

Murya chan kasa yace"miye sunan perfume dinki?"

Lumshe idanunta tayi cikin sigar Jan hankali tace"_DKNY Golden Delicious Million Dollar Fragrance Bottle_"

Cirota yayi daga jikinshi ba don yaso bah yace" babu littafi a hannunki aina kike karantowa?"

Cikin rashin fahimta tace"miye nake karantowa?"

"Dogon turancin dakikayi mana"

Dariya tayi tace"sunan turaren kenan fah"

Shima dariyan yayi tareda shafan gefen fuskarta

"Turaren ya maka dadi neh?" Ta tambaye shi ganin yana shirin juyawa

Gyada Kai kawai yayi yana cigaba da kallon figure 8 dinta,

"Tayani fitarwa"tafada tana mika mai tray din hannunta

Tabe baki yayi yace"ni sa'an ki neh"

"Lahh karka manta you're my friend"tafada tana turo baki, Jan bakinta yayi yana murmushi kafin ya karbe tray din hannunta tareda ficewa,

Yusayrah dake mamakin dadewar shi ta hango shi da tray a hannu,

Cikin mamaki tace"ya naganka da tray?"

Baikai ga magana bah sukaji murya Zuly tace"laifi neh don ya taya matarshi kuma kawar shi fitowa da abu?"

Shiru Yusayrah tayi tareda tabe baki amma azuciyarta tarin mamaki neh fal dakuma wani abun da batasan miye bah

Serving din kowa tayi kasancewan bawani abincin kirki bane cos sandwich neh dakuma tea din daya ji kayan kamshi da had'i 

Yau kam ya yaba abincin cos har santi yakeyi afili...

        ★★★★★★★

Zaune suke akan kujera daya kowa na danna wayan shi duk sunyi tsit, Zuly neh ta katse shurun da fadin

"Wai nikam waye kake ta kokarin Kira neh haka??"

Ajiyar zuciya yasauke tareda Jan guntun tsaki yace"wlhy someone special kuma numbern baya shiga"

"Someone special?"ta tambaya tareda warce wayan daga hannun shi

*Mi Miss*shine sunan daya bayyana afuskar wayan rike haba tayi tareda kanne mishi Ido daya tace" kar dai daita zakayi na uku?"

Dariya yasake alaman ta Sosa mai inda yake kyaikayi yace"Kai Friend kin chanka daidai"

Mika mishi wayan tayi cikin mutuwar jiki kafin tace" oya ka fada min numbern na Kira maka ita da layi nah"

"Ohhh thanks my friend"yafada cikin jindadi, kirawo numbern yayi ita kuma ta sambadawa anata wayan

Abin mamaki numbern ta na US neh she was so surprised ita fa tazata ya manta daita, tah tina har gayyatan shi budan Art gallery dinta na Dubai tayi amma baizo bah(in Baku manta bah lokacin suna cikin hall tadinga gwada numbern shi amma baya dagawa),

Jijigatan dayayi neh yasa ta dawowa daga duniyar tunanin data fada, kaman dagaske tayi dailing din numbern amma bai shiga bah

"Toh wayan Miss dinka baya shiga" tafada tana kunshe dariyanta ganin yanda yayi da fuskarshi kaman na karamin yaro

"This face fah"tafada tana jan karan hancinshi

"I miss her voice,her talk and even everything about her Allah yasa tana lafiya"yafada cikin sanyi murya

Itama tamiyar da fuskarta kalan tausayi as if batasan akan wa yake magana bah sannan tace"do you love her neh?"

Dora Zuly yayi akan cinyarshi tareda rungumeta yana sinsinar wuyarta cikin shauki kaman Miss dinshi neh yace"at first ba sonta nakeyi bah amma kuma daga baya nayi realising cewan ina mugun sonta"

"Ayyerh she most be very beautiful then"tafada cikin sonjin abinda zaice dukda tasan bai taba ganinta bah

Cikin shakakken muryan shi yace" I know she must be beautiful cos abubuwan nakeso are beautiful"

Giranta daya ta daga kafin tace"You know kuma?"

Dago fuskarshi yayi ya kalleta da jajayen idonshi cikin sanyin murya yace" erh mana cos bantaba ganin ta bah, lokacin daya kamata ace mun hadu I was admitted a asibiti so bamu hadu bah kuma bamu sake yin waya bah"

"Ayyerh sorry" tafada cikin jimami,sake miyarda hancinshi wuyanta yayi yace

"Naduba wannan perfume din ance ba'a cika kawowa bah cos yanada tsada"

"Bashida wani tsada fah" tafada hankali ta kwance

Kallon bakisan miye kike fada bah yamata kafin yace "kinsan nawa ake siyarwa neh?"

Dariyan karaina min hankali tayi tace" Favorite perfume dina neh fah koda yaushe dashi nake amfani so don't ask me nawa ake siyarwa"

"Uban waye neh yake yawan siya miki turaren $1 million dollars?" Yatambaye ta cikin rainin hankali

Turo baki tayi tace"kana nufin bazaka iya siyawa Miss dinka bah kenan?"

Dariya yayi yace"Zan iya mana"

"Toh ai nima Yay Mou neh yasiya min"

"Yauwa waye Mou dinnan neh wai?"

Lumshe idanunta tayi kafin tabude tace"Mourad asalin sunan shi... Daga nan tabashi labarin yanda suka hadu dashi kafin tayi shiru

Girgiza kanshi yayi kurun ya ajiyeta yace zaije hutawa...

             ★★★★★★

Acikin wata daya sosai Zuly take Jin dadi cos he's giving her what she never expected, he's treating her equally as his heartbeat kaman yanda yake kiranta,

She can say she's living a new life agidan Iqbal cos haka kawai zai kaita saloon dakanshi yakuma jira a mota har sai angama kuma suna spending time tare,

Gashi yanzu ta ajiye harkar zanen kudinta cos dakanta take directing dinsu wajen Iqbal din kuma ba karamin kudi yake samu bah.

Yanzu Yusayrah wani mugun kishin Zuly takeyi dukda tasan for sure har abada Iqbal bazai taba kinta bah saidai wani ikon Allah(nace zamu gani ai)...

```10:59pm...```

Zaune take akan kujera tana kallon TV dukda ba wani abu take tsinta acikin abinda akeyi bah soboda rashin lafiyan da friend dinta yakeyi tin kwana biyun dasuka wuce,

Mikewa tayi tafice zuwa dakin su Yusayrah soboda yar hayaniyan datake ji.

Sallama tayi suka Yusayrah ta amsa cikin sanyin murya, bata kula Yusayrahn bah tayi wajen gadon da Iqbal yake nukurkusawa , 

Zama tayi agefen gadon hawayen tausayin shi na diga da idanunta, hannunshi ta rike cikin nata gam har sanda yayi yar kara,

Juyowa yayi ya kalleta tareda sakar mata murmushin yake, ai kuwa ta fashe da kuka tareda fadin sai sunje asibiti,

Amsa daya yake bata shine zaiji sauki, kwantawa kawai tayi ajikinshi,

Yusayrah da zuciya ya ciyo ta tayi waje cikin fushi,

"It's late jeki kwanta"yafada dakyar, dallewa kan gadon tayi gabadaya tana makaleshi tace

"Anan Zan kwana"

Matsar daita yayi daga jikinshi tasake shige mishi, murya a shake yace"pls mana friend"

"Toh"tafurta a sanyyaye tareda ficewa, Yusayrah na ganin fitarta itama ta koma dakin...

```2 hours later...```

Bumm bumm bumm... Shi kakeji dakarfi, Zuly datake kan sallaya ta tashi afirgice tana zazzare ido tareda nufan kofan palourn ta da ake bugawa,

Budewa tayi taga Yusayrah a birkice, jitayi gabanta yayi mugun bugawa,

Cikin rawar murya Yusayrah tace" baya numfashi, yadaina numfashi kizo kiganshi"

Hankada Yusayrah tayi jikinta na bari tayi hanyan dakinsu, turuss taja ta tsaya daga bakin kofa tana kallon yanda Iqbal yakoma,

Da wani Irin gudu gudu takarasa wajenshi jikinta na wani Irin rawa

Dora kanshi tayi akan cinyar ta tana sakin kuka mai karfi ganin ko numfashi babu atare dashi...

_wayyo Iqbal..._

#team ZulynMourad 
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

 [19/09, 11:42] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO 

A Sweet and pitious Romantic love story 

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*wannan page dinki neh JAMILA SHU'AIBU (MUSLIMAAT) Nagode kwarai dagaske Allah yasaka da Gidan Aljanna*

*Page 62* 

"Abokina" tafada tana kwantar da kanta a kirjinshi cikin sauri ta tashi tareda rike pulse dinshi , jitayi ya harba cikin farinciki tace

"Kizo yana numfashi" itama jikinta na rawa takarasa wajensu, dakyar suka samu suka saukar dashi daga kan stairs din,

Ganin yanda jikin Yusayrah ke rawa gakuma yanayin rudewa atare daita yasa ta shiga driver's side itakuma Yusayrah tazauna dashi abaya

Bazata iya fadin Irin speed din data tsula wa motan bah, polisawan dasuke gadin anguwansu suka Mara musu bah soboda gudu gakuma rashin tsayawan da Zuly batayi bah.

Kafin sugama fitowa dashi daga cikin motan har polisawan sun iso

"Lfy kuwa"wani daga cikinsu yafada, ko iskan data kwaso su basu shaka bah Zuly tayi cikin hospital din dagudu tana kwalawa nurses kira,

Dagudu suka fito da gado Zuly nabinsu abaya itama...

Acikin Yusayrah da Zuly bazaka iya fadin wanda yafi wani rudewa bah,

A dare daya kachal duk sun yamutse sun kode tsabar kuka, Umma kawai Zuly ta iya kira da wayar wata tafada mata,

Da sassafe kuwa saiga yen gidansu Iqbal sunzo, bakaramin kuka suka sha bah ganin yanda yakoma so lifeless,

Da rana su Malam da Umma suka  iso, dagudu na rungumi Umma nah tareda sakar mata da kuka mai tsayawa arai cos har lokacin bai farka bah.

Zaune suke da umma awani kebanttacen wajen a asibitin, sai lallashin ta Umma ke yi akan taci abinci

"Haba yar Umma ki taimaka min kici wani abu mana ko sokike sai kin kwanta ciwo neh?"

"Umma nah Friend dina har yanzu bai farka bah am afraid nayi loosing dinshi kaman yanda nayi loosing din Yay Mou dina"

"Ba kuka yakamata kimishi bah Addua yakamata kiyi shima Mourad din am very sure bah loosing dinshi kikayi bah"umma tafada cikin rarrashi 

Kwantawa tayi ajikin Umma tana sakin ajiyar zuciya, muryan Umma taji tace

"Garin yaya Iqbal yasake ki?"

Arazane ta dago cos this the least thing she wanna hear a yanzu , hadiye wani yawu tace"umma nah mubar maganan pls"

"Ya za'ayi kice ta bar maganan¿" 

Atsorace suka juya inda sukaji muryan yafito, ai batasan lokacin da tamike bah 

Zazzare idanuwa suka yau ganin Malam neh, muryan shi  tasake yace" baki jina neh"

"Daman ranan da aka kaini neh yasake ni amma fah yadawo dani"tafada cikin rawar murya

Banda innalillahi babu abinda Malam yake fada ga idonshi yayi mugun ja" garin yaya yasake ki?"
Chapter 40 · 0% Book details