← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 98

Sashe 72

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jeka zan neme ka" Gyada kai yayi tareda wucewa bangaren shi, tin daga bakin kofa yake jin sautin kukan matarshi, ajiyar zuciya yasauke sannan yashige da sallama abakinshi Mikewa tayi da sauri hade da rungumeshi wanda yasashi sakin ajiyar zuciya soboda abinda bata tabayi  bah kenan tinda ya aureta  muryanta yaji tana fadin

"Wayyo Abbu Umayyah Wlhy banson in rasa ka Wlhy mugun sonka!" Cirota yayi daga jikinshi yana share mata hawayen fuskarta tareda cewa

"oh Ummu Umayyah waye yacemiki zaki rasani?" Jan hanci tayi tace

"tace tana sonka kuma daga gani yarinyan bazatayi mutunci bah DanAllah karka aureta!" Jiyayi juya na shirin kaishi kasa cikin sauri ya zauna akan kujera yana miyarda da numfashin wahala, kallon mamaki take binshi dashi ganin yanda yakoma lokaci guda

"Abbu Umayyah lafiya kuwa?"ta tambaya zuciyarta na tsalle

Murmushin yake yakirkiro tareda girgiza mata kai irin bakomai dinnan... Mikewa yayi dakyar yana kallon agogon dake manne agaru yace

"lokacin sallah yayi saina dawo" Da ido tabishi tana jin wani irin Kishi na turnuketa, wani yawu mai daci ta hadiye tana rufe idanuwanta tareda karanto Addua....

             ★★★★★★★

Daure take da daurin towel akirji sai faman goge fuskarta take da cleanser saiga Maram tashigo da cup a hannunta dayan hannun Kuma waya neh gakuma Bluetooth akunnenta da alamu ma video call takeyi abinta Ajiye kopin tayi agaban Zuly tana fadin"wai gashi kisha!"

Kallon ta Zuly tayi daga sama har kasa ganin ta cire khimar din kanta yarage daga ita sai half vest wanda ya bayyana shafafiyar tumbinta ga gashin nan masha Allah har gadon baya gashi kuma gabakidaya tinda tasan Maram bata taba ganin kitso akanta bah da alaman haka take barinshi

"Wayyo Allah darling DanAllah kazo kadauke ni Wlhy bazan iya bacci nikadai bah"tafada cikin shagwaba Dan zaro idanuwa Zuly tayi tana cigaba da kallonta cikin mamaki, bata dai ji miye aka fada daga dayan bangaren bah taga Maram ta daka tsalle tana fadin

"You are so sweet darling shiyasa nake Kara sonka kullum!" Kiss ta manna wa wayan saikace ba dazu dazun nan ta rabu dashi bah!

Ganin zata fice neh yasa Zuly fadin "Nikam kuna waya da kawarki Mom kuwa naga banganta awajen biki bah! "

Karasa sanya khimar dinta tayi tareda rike hannun kofa tace "gaskiya rabona da nakirata tin 2 weeks ago Naga ma yanzu bawani son kawance mu takeyi bah shiyasa na kyaleta"

Girgiza kai Zuly tayi tace"ya za'ayi ki kyaleta bayan kinsan yanzu neh take bukatar Ku! Pls kitaimaka kidinga kiranta koda sau daya neh a sati"

Kallon wayan hannunta tayi tana yamutsa fuskar tareda bude kofa dakyau tace"InshaAllah"

Ganin yanda takeyi neh yasa Zuly cewa"Wai Ina zuwa daddaren nan neh haka?"

Kanne idonta daya tayi tace"wajen mijina zani soboda bazan iya bacci bah indai ba a kirjinshi bane"

Tab'e baki Zuly tayi tace"Allah ya kiyaye hanya"

"Ameen Kuma kimana Adduan Allah yasa yau kwallon yashiga raga" Zaro idanuwa tayi kafin tayi magana har Maram tafice abinta dasauri, girgiza ka tayi tana sakin dariya chan Kuma ta tsuke bakinta tana shafa cikinta soboda tunawa datayi da cewan itama fah abu yataba zama acikin cikin

"Allah yayi Ku ba rayayyu bane shiyasa"tafada tana share kwallan fuskarta, maganin dake gabanta tasha kafin ta dauki kopin tsumin dake gabanta shima ta shanye harda lasan labba soboda dadinshi...

             ★★★★★

●●●● Da taimakon Allah Mom tasamu ta isa gida, ko cikin gida bata karasa shiga bah tazube akasa summamiya, Mai bawa flower ruwa neh yayi maza yakira mutanen gida ba bata lokaci aka wuce daita asibiti....

'''RANAR DAURIN AURE'''

"Ankusa daurawa fah ki tashi kije kiyi wanka kafin lokaci yayi!"Kuwah tafada wa Zuly dake kwance akan gado, bude idanuwanta tayi dakyar tana yamutsa fuska Kaman zatayi kuka Chan Kuma tafashe da kuka tana juyi akan gado hannuwanta akan marar ta,

Hawa kan gadon Kuwah tayi tana fadin"wai miye haka neh tin jiya daddare kike ta kukan banza !kawai dai kallon ki nakeyi"

"Oh kardai har yanzu baki tashi bah kodai ciwon cikin neh baisakeki bah"Fakhiha data shigo da abinci a plate tafada

"Wayyo Allah mutuwa zanyi!"tafada cikin murya mai ban tausayi still hannunta na kan mararta

"Innalillahi wai dama abin yakai haka neh?"Kuwah tafada cikin tashin hankali ganin yanda Zuly takoma lokaci guda Saukowa tayi daga kan gadon tana fadin

"ai bamuga tazama bah"

"Ina zamuje toh?"Fakhiha ta tambayeta tana ajiye abincin hannunta akan dining din cikin dakin

Ina zuwa kawai tace tareda ficewa inda Fakhiha takarasa wajen Zuly tana fadin

"Gaskiya sister inlaw wannan ciwon cikin baiyi bah haka kawai zai Kama mana ke ana saura minti talatin daurin aure!"

Itakam Zuly Ina tasan tanayi banda kukan da take ta sharba, Kuwah ce tadawo da Kopi ahannunta tareda nufan Zuly dashi, saiga su Ammi da Umma ma sun iso cikin, tashin hankali Umma ke fadin

"Ya akayi kuka bari yayi worst haka?"

"Mun zata zai tafi neh lokacin da muka bata Lipton da lemon tsami!"Kuwah tafada tareda dagota tana kokarin kafa mata kopin abaki

"Kibarta na kira doctor tinda daman kun bata baiyi aiki bah"Ammi tafada Kaman zatayi kuka

Wayan Zuly dake kan dressing mirror neh yafara Kara , dauka Fakhiha tayi tana fadin

"Yaya neh fah! "

"Karki cemai batada lafiya soboda kar hankalinshi yatashi kawai kice tashiga wanka neh!"Umma tafada ahankali

Dan matsawa daga wajen Zuly Fakhiha tayi soboda kukan da takeyi kaman ance mutuwa zatayi wayan neh yakatse ko secon 2 ba'a Kara bah yakuma daukan Kara, ahankali tayi receiving tareda karawa akunne

"Zulynah na iso fah, ya za'ayi naganki kafin daurin auren soboda tin jiya zuciyata takasa nutsuwa"

"Yaya!" Dum yaji gabanshi yafadi

"Ina mai wayan?" Gyaran murya tayi Kaman babu komai tace

"Ango mai wayan tashiga wanka neh shiyasa nadauka" Ajiyar zuciya yasauke yana fadin

"Amma inace tana lafiya koh?"

"Lafiyan ta lau mana" Dan Jim yayi yace

"Ya nake jin kaman sheshekar kuka?

"Aww.... hmm.. tv muke kallo yaya"

"Allah am starting to have strange feelings" yafada cikin sanyin murya

"Chill bro! bari naje kar Ammi tayi ta jira"bata jira cewarshi bah ta katse wayan tana kallon su Ammi dake kallon Zuly kaman Sun samu Tv.

"Wayyo marana zai fashe! wayyo fitsari nakeji"Zuly tafada cikin kuka sosai, rigaye rigayen kamata sukafara yi, Ammi da Umma neh suka kaita toilet din tareda fitowa suna jiranta tagama su miyar daita kan gado

Doctor ceh tashigo tana gaishe su daya bayan daya tareda neman ganin Mara lafiyan sai A sannan ma suka ga Kaman ta dade

Knocking Umma tayi tana fadin"kin gama neh?"

Shiru dukkansu sukayi suna kallon fuskar juna, murda handle din tayi tareda lekawa

"Innalillahi wa inna illahir rajiun"Umma tafada da karfi

*DanAllah wattadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team Zuly
#team Mom

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 100*
Cikin keftawar ido dukkansu suka isa wajen da Umma tayi freezing , kutsawa sukayi wajen Zuly dake kwance akasa tana fitar da numfashi dakyar, buge Umma da akayi neh yadawo daita tunanin ta wani irin kuka tafashe dashi ganin yanda aka kinkimo zuly kaman kayan wanki.

Akan gado suka ajiyeta inda doctor tafara bata taimakon gaggawa kafin tace a dauko mota soboda sai anyi mata test tukunna...

'''AZARE,  BAUCHI NIGERIA..... '''

Zaune suke acikin masallaci dukkansu inda koina jama'a neh ga larabawa Kaman odernsu akaje aka yo daga garinsu  kowannensu cikin shigar alfarma kamshi kalakala sai tashi yakeyi , Achan gaba na hango Mourad da Fakhih  suma cikin nasu shigan sai Wani walwal sukeyi Suna daukan ido barinma Ango Mourad wanda bakinshi yakasa rufuwa sai murmushi yake dokawa kaman ammai Abishiri da gidan Aljanna

Dayan gefen Kuma Iqbal neh shima cikin nashi shigan, ba laifi fuskarshi asake yake dukda zuciyar shi yana chunkushe, sai so yake su hada Ido da Mourad Amma hakan baiyi bah soboda haryanxu Mourad najin haushin shi dukda sun gaisa sama-sama dazu.

Ko mintuna 10 kyawawa ba'a Kara bah Liman yace "Ayau neh aka daura auren Mourad dakuma Zulfa akan sadaki dubu 50! Fathia...

Ai nan Mourad yafara washe baki cikin murna! Mutanen gefenshi sai mika mai hannu sukayi suna main Allah Yasanya Alhkeri.

Liman neh yasake gyaran murya sannan yasanar dasu wani daurin auren ganin wasu sufara niyan barin cikin Masallacin

"Akwai wani daurin auren ma! " Nutsuwa akayi inda kowa yazubawa Liman na mujiya....

        ★★★★★★★★

'''BAUCHI, NIGERIA'''

Zaune Umma da Ammi suke akan kujera agaban likita duk sunsha kuka sun koshi idanuwansu yayi jazir kaman an zuba musu barkono aciki Gyaran murya doctorn tayi tace"ku kwantar da hankalinku bawani abu mai tsanani bane yake damunta kawai dai raki neh dakuma rashin sabo da shan abubuwan data dinga sha"

Ajiyar zuciya suka sauke atare suna godewa Allah azuciyarsu, likitan ce takara cewa"danAllah adinga kula da abubuwan da takesha soboda yanayin condition dinta"

"InshaAllah zamu kiyaye "suka afada cikin sanyin murya dukda bawai Ammi ta fahimci likitan bane .

Mikewa sukayi suka koma dakin da aka kwantar da Zuly...

Karar wayar Zuly neh ya dawo da dukkansu hudun daga duniyar tunanin dasuka Lula daman su Ammi  da Umma sun Riga sun koma gida soboda baki...

Kallon juna suka hauyi dalilin ganin cewan Mourad neh ke Kira.

Shahada sukayi Fakhiha tayi picking "You are now officially Mrs Mourad!"

Mourad yafada daga dayan bangaren cikin farinciki "Ba ita bace Yaya "

Fakhiha tafada ahankali "Oh sis wai miyesa kike daukan call din bayan bakece  Mai wayan bah?"

Yafada cikin takaici "Yaya tinda taga lokacin daurin auren yayi clicking ta kulle kanta acikin daki tana kuka"

tafada cikin Zaro idanuwa Kaman tana gabanshi "Yah Salam! Pls ki lallabamin ita ta karbi phone din mana"

yar tsaki taja tace"Allah ba budewa zatayi bah soboda ba yanda ba'ayi daita akan tabude bah!"

Cikin Sanyin murya yace"Ohk shikenan yanzu zamu taho make sure tayi shiru kafin mu iso!"

"Toh Yayana Ango Allah yadawo daku lafiya"tafada kaman babu abinda yake faruwa

Murmushi yayi yace"Ameen Sisto"

Ajiyar zuciya tasauke sanda wayar ya yanke, kallon Zuly dake kwance tana baccin wahala tayi!  Jefi-jefi take yamutsa fuskar tana rike marar ta alaman haryanxu tana jin ciwon,

Matsawa gefenta tayi tareda rike hannunta tana tofa mata Adduan samun sauki chan kuma takalli su Kuwah dasukayi jugum suna tinani tace

"Yakamata ace ku koma gida tinda Zulyn Mourad tasamu sauki saura kawai ta bude ido neh"
Chapter 72 · 0% Book details