← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 98

Sashe 54

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai bamuson shashanci fada mana abinda yafaru" Malam yafada a kaushashe, hadiye wani yawu yayi cikin fargaba yahau sanar musu da abinda yafaru, wata jijitacciyar Mari Umma tadauke shi dashi tsabar bacin rai har kuka takeyi tana nuna shi da yatsa bakinta na son furta magana

"Abinda kayi kokadan bai dace bah amma itama baikamata ace tabar gida bah harda zancen zuwa kotu ai wannan baifi abinda za'a sasanta agida b.."

"Sasanta miye Malam? Yanzu abinda zaka fada kenan?upon duk abinda tamai arayuwa amma yasaka mata da wannan?ciki uku fah yazubarwa yarinya what if su kadai Allah zaibata? Agaskiya bazata koma mishi bah saukin ka daya Shine kawai yasakar mun yarinya ai ba shine autar maza bah,in bama kaddara bah ai Zuly ba sa'ar aurenka bace,kuma daman tin ba yau bah na lura baka kwatanta adalci atsakanin su Don haka kabani takaddar ta Kuma Wlhy kanemo min diyata in bahaka ba...." takatse Malam dafada cikin kuka Kuka Iqbal yasake fashewa dashi yana rokon Umma wai bazai sake bah, Malam neh yadafa kafadarshi yace....

*DanAllah wattpadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 80*

Al-Hussain Abu Sameer this page is yours....

Kuka Iqbal yasake fashewa dashi yana rokon Umma wai bazai sake bah, Malam neh yadafa kafadarshi yace" ka kwantar da hankalin ka zamuga abinda Allah zaiyi"

Kafin Malam yagama magana har anyi sallama abakin kofa, amsa sallaman sukayi Suna karewa mutumin dake sanye da coat, gaishe su yayi suka amsa sannan yakalli Iqbal yace" naje gida ance mun  tafiyanka  kenan Azare shiyasa nabiyo  bayanka"... ganin Iqbal din baiyi magana bane yasa shi zura hannunshi cikin jakan dake rataye  abayanshi  yaciro envelop yace

"Daga  kotu  aka aikoni" hannu narawa yakarbi envelope din

"Tana Ina?" Yafada  cikin goge zufan dasuka wanke mai fuska

"Waye kenan?"mutumin yafada yana zuge  jakanshi

"Wacce tabaka  wannan" tsayawa mutumin yayi ya kallo Iqbal for few seconds  kafin yace

"Ni  messengern  kotu neh don  haka bansan wacece  kake magana akanta bah" yanagama fadin hakan yamusu  sallama sannan yafice.

"Bude mugani" Malam yafada yana kallon Iqbal, budewa Iqbal yayi ranshi duk bah dadi ahankali yace

"Sammacin zuwa kotu neh jibi"

"Gaskiya bata kyauta bah ai da koh shawara ma saitayi damu"Malam yafada yana kallon Umma da har yanxu bata daina hawaye bah

"Shawara? Shawara fah kace! Shi lokacin dayake zubar mata da ciki ya nemi shawarar kowa neh? Shine kake cewa data nemi shawara? Ai  tamin daidai Allah yakaimu jibi" tana gama fadin hakan tayi shigewarta cikin daki abinta.

"Toh  Allah yakaimu jibin  tinda bamusan inda take bah" Malam yafada cikin kwantar da murya Hawayen fuskar shi yashare  yace" Amee"...

Babu  abinda kake ji a toilet din sai tarinta  Wanda kwana biyun nan satayishi, tissue tasa tagoge bakin ta wanda duk jini neh,  kallon fuskarta tayi acikin Mirrow  sannan tafashe da kuka, duk takode  tayi Wani irin fari  ga idanuwanta  duk Sun koma ciki harda rami wajen  idanuwanta yayi ga wani irin bakin da wajen yayi, Cikinta ta rike tana kallon kanta a mirror tace

" miyesa! Ka shigeni  lokacin da banshirya  bah  nasan Kaima zubar dakai za'a yi your father is a murderer! KO dai kawai nazubar dakai neh? No bazan iya Kisa  bah , kawai dai zan haife  ka muzauna mu ukunmu nida kai dakuma babynah , zamu tafi waje mai nisa inda babu mai takura mana ! Koh dear?"

Tafada tana  shafa cikinta "Komai zai kare daga gobe, zai sakeni  nima nahuta wa rayuwa nah" hawayen fuskarta tashare sannan tawanke  fuskarta kafin tafito.

Kasa tasauka  inda tasamu Babynta nawasa  gakuma Chirstine na tayata hada puzzle,  karasawa wajen su tayi sannan tanemi  waje tazauna cikin rashin kwarin  jiki,

"Kina  bukatar Wani abu neh?" Christine ta tambaya cikin ladabi Girgixa kai kawai tayi tana lumshe idanuwanta,  da kallon tausayi chirstine ke binta tana tausayawa halin da uwar gidan take ciki, itafa Wlhy bazata iya wannan wahalar bah ace duk dukiyarta Wani banza na  wahalar daita taab....

_WASHE GARI....._

Sanye take cikin lemon green din dogon riga  mai dogon matsesen hannu, kanta yane  da gyallen kayan , side bag nata narataye a kafadarta bayanta kuwa Christine neh dauke da Babynta , mota suka shiga inda tawuce dasu park, saukesu tayi tashafi  kan  Babynta tace"my baby oya go to play zan  dawo nadauke  ku anjima kinji?"

"Ohk  Zulynah karki dade adawo lafiya"tafada tana pecking din Zuly akumatu, murmushi Zuly tayi tana jin son Babyn har cikin bargonta.

Sauka sukayi daga cikin motan, sanda taga shigewar su sannan ta tada  nata motan sai kotu.

Tana  sauka daga cikin motan en jarida  sukafara rufeta da tambayoyi

"*miye yayi zafi haka da bazaku solving matsalarku  agida bah har saikun  zo  kotu? Malama  ko zamu iyajin abinda yasa kikace sai mijinki yasakeki?*"

Sune ire-iren tambayoyin da suke mata Amma ko dago kai batayi bah balle ta dubesu har ta shige  cikin court din.

Mikewa Lutfiyah dake zaune kusa da mijinta tayi cikeda mamaki tace"wancan bah Zuly bace?"

Shima t.v yasake kallo yace "itadince inaga"

Zaro ido Lutfiya tayi cikin  kidima tace" nashiga uku  rabasu  fah  za'ayi, DanAllah kazo muje ko ta chanza ra'ayinta"

"Ohk  dauko key" yafada yana mikewa, dagudu tashige cikin dakin, kallon mamaki yake binta dashi yace

"wannan fah"

"Erh ai ba kullum ake fita da mota bah muje kawai da machine"tafada tana Jan hannun shi tayi suka fice inda shi kuma yadinga girgiza kai....

Tana  shiga cikin court tahango Ummanta zaune, karasawa waje  Umman tayi suka rungume juna tareda fashewa da kuka, "Yi  shiru Allah zai saka miki kinji"

Umma tafada cikin rarrashi, cikin sheshekar kuka tace "Umma nah  Wani cikin neh dani fah Ina fatan ban dauki wrong decision bah"

Shafa kanta Umma tayi tace" Insha Allah, kidaina  kuka kinji" Gyada kai tayi Kaman wata karamar yarinya sannan tazauna agefen Umma  tana sauke ajiyar zuciya,  tintini data shigo yakafeta da kodeddun idanuwan shi sai hawaye yake sharewa jefi-jefi ga duk en gidansu zaune Sun jiran shigowar Alkali.

"Zuly!!" Lutfiya  takirata lokacin da taisa  wajen su, Wani irin  banzan  kallo Zuly ta jefa mata kafin tajuyar  da kanta cos sosai take jin haushin Lutfiya na b'oye mata ainihin abinda ke zubar mata da ciki, sororo Lutfiya tayi tana kallon Zuly da mamaki, gaishe da Umma tayi cikin girmamawa itakuma ta amsa cikin sakin fuska, zama tayi agefen Umma tace

"Kodai  Aljannunta neh suke kusa" Kura  mata idanuwa Umma tayi tana kallon Lutfiyah datayi magana kasa daurewa tayi tace.

"Bangane aljanunta  bah?" Wani yawu Lutfiyah ta hadiye tana zaro idanuwa tace

"Mijinta yace tana da Aljanu wai su suke zubar mata da ciki shine nake tambaya  ko Sune suka motsa dalilin ganin irin kallon datake jifana dashi"

Ai Umma batasan sanda hawaye suka silalo mata bah kafin takaigayin magana har Alkali da tawagarsa Sun iso  bah bata lokaci aka fara gudanar  da shari'a bayan mai buga guduma  yabuga guduman shi mutanen wajen sukayi tsit.

Ba bata lokaci aka fara gudanar da sharian inda aka nemi Zuly dakuma Iqbal da su shiga cikin witness box, shiga kowannen su yayi saiyanzu mah talura dashi "miye sameshi? !" Shine abinda tafada azuciyarta ganin yanda Iqbal yarame Kaman mai kanjamau , tabe baki tayi tareda hararan shi kafin takau da idanuwanta daga gareshi.

Muryan Lawyern govnati taji yace" Malama Zulfa ko zamu iya Sanin miyesa kikace sai an araba aurenku? "

Hadiye wani yawu tayi hawaye na ciko mata, kallon Umma tayi Umman ta gyada mata kai sannan tayi gyaran Murya tace

"Zubarmin da ciki yakeyi!"

"Shikenan abunda yake miki?" Gyada kai kawai tayi cos gabadaya jitayi bazata iya magana bah gashi kuwa kowa ita yake kallo harwani rawan disco kafarta keyi, juyawa wajen Alkali dake rubuce-rubuce Lawyarn yayi sannan cikin turanci yace" ya Mai girma mai shari'a Inaga wannan baikai hujjan da za'a raba auren bah.."

"Objection my lord" Wani bature yafada da alaman shike kare Zuly

"Objection sustained!" Takawa yayi gaban Iqbal yace

"kozaka iya fada mana miyesa kake zubar mata da ciki? " Share hawayen shi yayi cikin rawar murya yace

"Aikin shaidan neh ,DanAllah karku rabani da mata ta Wlhy inasonta" Arikice Zuly ke kallonshi tana girgiza mishi kai alaman karya mata hakan, juyawa Lawyern yayi wajen Alkali yace

"Ya Mai girma mai Shari'a DanAllah inason adubi case dinnan da idon basira Mar azo ayanke hukuncin da baiyi bah"

Yana gama fadin hakan ya zauna, sanda Alkali yagama rubuce-rubucenshi kafin yadago yakalli Iqbal dake kuka Kaman ranshi zai fita gakuma Zuly sai auna mai harara takeyi, gyaran murya Alkalin yayi yace

"Agaskiyan magana baka yi abinda yadace bah cos gabadaya zubda ciki ma a adinnin musulunci ma babu kyau koda kuwa bah Dan Sunna bah balle wannan Dan Sunna neh don haka sai an cika taara, gareki mai kawo Kara... yafada yana kallon Zuly... ayanayin kima na lura Kaman bason auren kike bah dukda dai abinda yamiki bai dace bah.

"Hukunci na shine: Nabawa wa'inan ma'auratan watannin 4 da suje su gyara tsakanin su in har lokacin yacika ba'a samu sauyi bah to saiku dawo"yana gama fadin hakan yamike!!!

_Tirkash!!! Miye zanji haka🙆🙆 gaskiya Alkalin nan baiyi bah. Sorry naso nakawo muku karshen zaman su yau amma Allah baiyi bah! Kumun afuwa zan warware komai a sannu_

*DanAllah wattpadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 81*

Jikake Tim Zuly tazube asume akasa dagudu sukayi wajenta kasancewan Iqbal yafisu kusa daita yasa yarigasu isa wajenta, ba bata lokaci ya cicibeta sai waje...

Babu abinda kakeji acikin ward din banda kukan Zuly, Umma sai rokonta takeyi amma kaman Zugata takeyi.

"Umma nah danAllah kicemai yasake ni wlhy nagaji" tafada cikin muryar kuka

Girgiza mata kai Umma tayi tace" kibari kawai tinda Alkali yariga da ya yanke hukunci, ai nan da watanni hudu kaman yau neh kinji?"

Jan hancinta tayi tareda gyada kai tana runtse idanuwanta cikeda tausayin kanta...

Da Sallama Lutfiya tashigo cikin dakin, ciki-ciki Zuly ta amsa sannan tajuya mata baya, ahankali ta taka taje inda take tace

"Zuly!!!"amma ko gizau Zuly batayi bah

"Please zan iya bayani" Lutfiya tasake fada , mikewa Zuly tayi daga kan gado sannan tayi taku kusan biyar cikin kausasiyar murya tace
Chapter 54 · 0% Book details