← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 98

Sashe 24

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kwadayayu kawai" nafada tareda Jan tsaki 

"Wai nikam don kin tashi baki gama ci bane kokuma soboda asaran kudin da kikace nayi kike duk wannan surutun"yatambaye ni cikin son danne dariyar shi

"Ehtoh duk wanda ka zaba" nafada tareda bude kofa cos har mun iso

Ajiyar zuciya Umma dake jiran dawowan mu tasauke 

"Haba ya zaku dade awaje har haka" tafada tana tashi tsaye

Turo bakina nayi nace "ahakan ma fah Umma ko gama cin abincin bamuyi muka taho gashi abincin bakaramin dadi gareshi bah😋" nafada tareda lashe lips dina

Dariya Yay Mou yafashe dashi harda rike ciki tareda zama akan sofa cos yasan yana iya faduwa kasa in baiyi wasa bah

Kallon shi muka tsaya yi sororo ga wani uban kyau daya kara,

Tsagaita dariyar shi yayi yace " Umma itafa barin abincin neh damuwan ta"

"Wani irin abinci neh hakan?" Umma ta tambaya tana kallon direction dina

Zaro Ido nayi ina kallon Yay Mou cos gabadaya ban tambayi sunan abinda naci nidai abinda nasani shine abinci yayi dadi

Hannu nasa akai alaman inason tino abinda yafada wa steward

Da dan karfi nace" cannoni an copee"

Wani dariya yasake yana jinjina kaifin kwakwalwar ta katse shi nayi da cewan" ban fada daidai bane Yay Mou dina??"

"Wlhy kinyi kokari amma Cannoli and coffee ake cewa"

Tabe baki nayi nace" ko ma dai miye"

Murmushi yasakar min sannan ya juya wajen Umma nah yace"Yauwa Umma nazaba muku gida uku gobe sai muje ku zabi wanda ya muku aciki sai mu biyasu kudi kafin wani yayi requesting"

Fuskan tausayi Umma tayi tace"Allah sarki kace yau kasha wahala" 

Murmushi yayi yace"ai ba wani wahala Umma ai duk yiwa Kaine"

"Toh Allah yakaimu gobe"

Yace"Ameen"

Mika min paper bag din hannun shi yayi yace"Gashi bari nashiga bacci gobe Inada zuwa hospital da wuri"

Karba nayi nace"miye aciki amma??" 

Taba min kumatu yayi yace"In kin duba zaki gani"

"Toh Yay Mou dina Allah yakaimu gobe kuma in zaka wuce ka tashia ni kaji??"

Pecking din goshi na yayi yace"Toh shikenan InshaAllah zan tashia ki"

Waving dinshi nayi nace"Saida safe"

Batareda yasake magana ba ya shige daki

Jana Umma tayi cikin daki itama , abakin gado na zauna tareda tankwashe kafafuna sannan na hau fitowa da abin cikin paper bag din

Kyakyawan nadi suka mai acikin foil paper dukda basan abinda yake ciki bah amma tsantsan kwadayi irin nawa har lashe baki nakeyi ina hadiyan yawu

Abinda ido na yaci karo dashi yasa nayi karamar kara wanda yaja hankalin Umma nah data fito daga bayan gida

Cikin sauri tayo waje na cos azatonta wani abu neh yasame ni

Cikin murna nace"Umma nah ga canno... Cannoli din da mukaci fah"

Yar karamar tsaki taja tace" har kin tsorata ni"

Fitowa dashi nayi ina dan lasan yatsa turo baki nayi nace" kiyi hakuri toh"

Gyada kai kawai tayi sannan ta zauna agefe na,tura mata nayi nace"Umma nah kici Kiji"

Daukan guda daya tayi ta gutsiri kadan aciki sosai itama yamata dadi

"Kinji dadi koh"nafada cikin santi raina yayi fari tass sai murmushi nakeyi tareda yima Yay Mou dina Allah yasaka mishi da gidan Aljanna...

Washe gari kaman yanda yamin alakawari haka yazo yacika ya tashiani ,

Atare mukayi breakfast cikin farinciki na kuma godemai akan cannoli din jiya

Azuciyarta sai Allah Allah nakeyi yadawo musake komawa muci( 😂😂).

Yau Kam baidade bah yadawo, wanka yayi mukaci lunch sannan muka fice zuwa ganin gidajen dayace yazaba mana

Shike jan motan nikuma ina gefen shi Umma nah kuma abaya kaman big Boss😉

Duk gidajen daya zaba babu na bari cos sosai suka hadu kuma story building neh( gidan sama)

Wanda yake dan kusa da gidanshi nazaba cos ko kadan banson muyi nisa da juna kuma da an bita nawa nikam banki ace muna kwana agida daya bah☹️

Atake awajen yasiya mana gidan sama yamawa Umma bayani akan da kudin zanen da nayi a Azare neh yasiya

Interiors din gidan bakaramin kyau sukayi bah inda anan neh kuma tunani yakamani ganin duk wannan uban gidan mu biyu neh kawai zamu zauna

Babban abin tashin hankali kuma shine nida Umma nah neh kadai zamu nayin wahalan gyara wa🙆

Komawa gida mukayi inda na matsa mai sai mun fita, 

Gargadi Umma tamana akan kar mu dade, boutique naga ya nufa damu ashe takalman zuwa school mukaje siya

Kusan kafa bakwai yasiya inda nadinga kwararo mai ruwa godiya dakuma Addua

Shidai kawai da murmushi yake bina,komawa mukayi cikin mota inda adaidai lokacin neh wayar shi tadau kara

Connecting wayan yayi da Bluetooth din motan nan wata siririyar murya tamana sallama

Murmushi kan fuskarshi neh ta fadada inda suka dinga hira da wance takira da larabci

Chan yakoma magana da hausa yace nayi magana kanwar shi ceh

Gaishe da junanmu mukayi cikin fara'a soboda daman nikam banda wuyan sabo...

Wani INN daban dana jiya yakaimu sannan yayi mana ordering din wani abin daban 

Jin ba cannoli bane yasa ni interrupting da hannu na cewa steward din yatsaya sannan najuya wajen Yay Mou nace ni cannoli nake so

Dariya kawai yayi yakara mawa steward din magana...

Dawowa yayi da trolley sannan ya ijiye mana agaban mu, nikam takan Cannoli dina nayi, wraps biyu baci na dauki na Yay Mou dina naci wato _Lebanese mezze_

Sosai shima yamin dadi sai asannan nagane ashe bah Cannoli kadai keda dadi bah...

Washe gari nafara zuwa school inda nayi kawa mai suna Philadelphia Nanthel (rival dina kenan I miss her) 

Ita ke taimaka min da abubuwa acikin school din cos ita tafara koya min turanci

Wata uku kacal nayi da Philadelphia inda alokacin neh nayi candy cos ashe ajin karshe aka sani na kum iya turanci sosai 

Umma nah tasha mamakin yanda akayi nayi na biyu a aji tinda daman tasan ba ilimi gareni bah abinda bata sani bah shine ada wasa neh fal araina amma a yanzu ina next level neh...

Sosai Yay Mou yataka rawar gani acikin rayuwata kuma ina mugun Sonshi don bana shakkan fadan haka agaban koma waye neh...

Wannan kenan...

Bude mata kofa da akayi neh yadawo daita duniyar tunanin data fada

Wani murmushi tasake tareda rike saitin zuciyar ta tace" ina son ka sosai Yay Mou"

Saukowa tayi ahankali inda wajen banda iska babu abin yake kadawa sakamakon private jet dinta dake wajen...

Shiga cikin jet din tayi inda ya.....

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 41*

"Karki damu zuwa jibi zaki fara makaranta"

Cikin sauri nakoma ta inda yake zaune nace" dagaske kakeyi??"

Batareda ya amsa min bah ya mike tsaye yajuya gurun Umma nah yace" bari nashiga na watsa ruwa"

"Toh afito lafiya"

Tsayawa nayi sororo ganin bai amsa min tambaya ta bah, baikaiga shigewa bah cikeda rashin kunyan dana kware ayinshi nace" Yay Mou hala icce neh ke maka magana anan??"

Tsayawa yayi cakk kaman zaiyi magana amma sai kawai ya cigaba da tafiyarshi yana mai mamakin yanda tayi mishi magana yanxu cos shi Sam baisan hallayarta bah...

Zan sake magana kenan Umma tamin alaman nayi shiru, badan naso bah nayi kum da baki na amma sosai rai na ya baci...

Wanka yakeyi amma gabaki daya hankalin shi akaina yake,babu abinda yafi tabashi sai yanda na mishi magana da bah dan son dayake min bah da yau saiya nuna min matsayina...

Umma nah kawai ya hango azaune cos nikam tsantsan bacin rai bansan yaushe na shige daki yin bacci bah dukda uwar yunwan danake ji...

Bayan ya zauna yace"Ina take Umma??"

"Inaga bacci tashiga yi"Umma ta bashi amsa

"Taci abinci kuwa??"

"Bata wani ci bah wai tace abincin bai mata bah"

"Dadi take nufi ko miye??"

"Erh wai bai mata dadi bah"

Zaro Ido yayi yace"unbelievable!!!"

"Miye faru?" Umma ta tambaye shi

"Umma wlhy mamaki naji ,takuwa san waye mai yin girkin gidan nan kuwa??"

Ido Umma ta zuba mai tana jiran miye zai ce,jin baiyi magana yasa Umma tace"waye mai girkin gidan nan??"

Sanda ya shafa kanshi tukunna yace" bakowa bane face _Mario Batali_wanda ya kasance mutum na biyu acikin mutane goman dasuka yi fice a girke girke acikin fadin American nan(wato second top chef in America)"

Rike haba Umma tayi da jin abinda yafada, itama tasan Zulfa tafada neh kawai amma hakikanin gaskiya abincin bakaramin dadi yayi bah...

"Bari na tasota karta kwana da yunwa yau ma" bai jira cewarta bah yayi dakin su...

Akan gado yasameni wanda nayi nashe nashe ina kwasan baccin wahala.

Sif ya nufa yadauka min doguwar rigar Chiffon Floral Dress da gyale cos harna cire kaya nadaura towel dukda uban sanyin da ake agari amma kasancewan akwai room heater acikin dakin shiyasa ban wani ji sanyi bah...

Dawowa yayi yazauna agefen gadon ahankali yajawo ni jikinshi tareda saka min kayan daya dauko min yana gama samin ya zare towel din sannan ya hau tashina...

Juya mishi baya nayi cos nariga nagane shine soboda perfume dinshi dana shaka

Cikin sanyin murya yace"Zulynah"

Turo baki nayi nace" kadaina kiran suna na tinda daman banda amfani awajen ka"

"Miyesa kike magana haka neh Zulynah??"

"Ai dole katambaya tinda har nine zan tambaye ka abu kaki bani amsa"

"Am sorry amma kin bata min rai neh shiyasa nayi shiru"

Cikin sauri najuyo jin abinda yafada kallon shi nayi da kyau nace" na bata maka rai fah kace??"

"Erh mana" yafada in serious tune 

"Miye nayi toh??" Ta tambaye shi

Tashi yayi tareda Mika min hannu yace"You somehow lack manners" 

Hannu na nima na mika mai kafin na girgiza kai nace" nifa nace maka bana jin abinda kake fada da turanci"

Samin dankwali yayi yace"Toh saiki ajiye acikin kwakwalwar ki duk randa kika fara jin turanci zaki san ma'anar abinda nace" 

Tabe baki nayi nace"toh, amma ina zamuje naga kasamin kaya??"

Atakaice yace"Restaurant"

"Ina neh kuma hakan??"natambaye shi

"Wajen cin abinci neh"

Tabe baki nayi nace"abincin da duk babu dadi nidai babu inda zanje"

Rike hannu na yayi gam yace"mu jeh dai cos yunwa nakeji sosai tin safe ban karya"

Zaro Ido nayi cikeda tausayin shi nace"ayyerh sannu yay Mou dina"

Gyada kai kawai yayi muka fito palour,kallon Umma nah yayi yace"Umma bari muje mu dawo"

"Toh adawo lafiya"

Waving dinta nayi nace"Saimun dawo Umma nah" ...

_MARIO BATALI INN _
Chapter 24 · 0% Book details