← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 98

Sashe 25

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shine sunan dayake rubuce agaban katon hadadden gurin cin abincin da mukaje...

Zama mukayi yakira steward tareda yin mana ordering din cannoli (tube din biscuit mai ricotta dakuma pistachio cream wanda yake hade da chocolate chips😋😋) sai hot coffee kasancewan ana sanyi...

Ci yakeyi yana kallo na yanda nake cin cannoli din harda santi ina dan sude hannu na kasancewan pistachio cream din yana bata min hannu

"Yayi dadi neh??"na tsinkayo muryan shi

Dagowa nayi na kalle shi sannan nace" sosai ma kuwa"

Giran shi daya ya dage min yace "Dagaske"

"Erh mana"

"Amma miyesa kika ce na gida babu dadi bayan duk mutum daya neh yayi??"

Cikeda mamaki nace"mutum daya kuma??"

"Erh mana wato mai inn dinnan shime mai dafa min abinci agida"

Kallon shi nayi da kyau nace"maganar gaskiya abincin yayi dadi amma Sam ni banji dadin shi bane soboda batare mukaci bah"

"Wonderful darling ai ni bansan haka bane"

Turo baki nayi nace "amma fah karka fada wa Umma nah"

Rike haban shi yayi tareda daga min gira daya yace"Kin miyarda ni parrot neh hala?"

"Farrot??" Nafada tareda lulawa duniyar tunani

Dariya ya fashe dashi yace "dullard kawai Aku nake nufi"

"Aww shine Farrot??"

"Ba Farrot bah parrot"

Dage kafadata nayi nace"ko ma miye"

"Karki damu daga jibi zaki fara zuwa makaranta"

Murmushi nayi nace"ai nadau kafada a wasa neh dazun"

"A'a ai bazan miki wasa da irin haka bah"

"Kardai shiyasa ka dade??" 

Gyada min kanshi yayi tareda marairace fuska 

Cikin sanyin murya nace"sowie ai basan hakan bane"

Wani shegen murmushi yasake yace" sorry zakice"

"Amma ai nayi kokari koh??😔

Shafa fuska ta yayi yace"Sosai mah kuwa"

Sai asannan nasake fuska tareda cigaba da cin Cannoli dina, steward yakira yabashi credit card dinshi  tareda yi mai magana wanda bansan miye yace bah

Baifi 5 minutes bah yadawo rike da paper bag mai tambarin INN dinsu.

Mika mishi paper bag din dakuma credit card tareda wani paper(receipt)

Tashi yayi yace"Mutafi"

Zaro Ido nayi ganin ban koshi ba kuma akwai saura acikin cute disposable tray din wanda ko daya baya kama da disposable one(wanda ake jefarwa bayan angama amfani dashi)

"Yay Mou dina ban fa gama bah😬"

"Erh muje"

Zaro Ido nayi nace"kuma ban koshi bah☹️"

"Zulynah dare yayi sosai karfe 11 fah nasan Umma tana jiran mu"

Badan raina yaso bah natashi tareda bin bayan shi, ina tafiya ina waiwayan table din mu wanda aka fara tattara abubuwan kai

Ban hankara bah naji hawaye sun dan zubo min cikin sauri nagoge dan karya gani yazata kodan abinci nake kuka(niko nace da dan miye kike kuka😇)

Bude min mota yayi na shiga sannan ya bude baya ya ajiye paper bag din tareda rufewa ya shigo motan sannan yaja mu muka tafi...

Ganin nayi shiru ina kallon waje ta glass yasashi riko hannuna tareda murzawa acikin palm dinshi(tafin hannun shi)

Jin dumi na ratsa ni yasani juyowa gareshi nace"kayi asaran kudin ka dazu"

"Bangane bah??"

"Erh mana bagashi bamu gama cin abincin bah kace mutafi nasan iyanxu Kam harsun gama sudewa😣" nafada tareda kawar da kaina gefe gudun karya ga hawayen da suka sake gangaro wa

"Kwadayayu kawai...

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 12:02] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 43*

```Wannan page din naku neh masoyan Zulfa Allah yakara dankon soyyaya```

Shiga cikin jet din tayi inda yafire da ita zuwa birnin tarraya wato Abuja🛫🛫...

```Agoyi Ironsi Street, Maitama Abuja Nigeria```

Afilin katuwar gidanta Wanda yake mallakinta jet din yasauka

Su Christine neh tsaye acikin filin ta bangare daya suna jiran isowan su...

Saukowa tayi daga cikin jet din, cikin takunta na kasaita take takowa wajen su inda suma wajen nata suka dosa

Gaisheta sukayi cikin girmamawa  ta amsa sannan suka sata a tsakiya sufa wajen da suka parka mata

Bude mata baya Christine tayi ta shiga ita kuma ta zauna agaba mata yayi gaba dasu 

Cikin 5mins suka isa ta gaban wani rantsetsen gida Wanda kana gani zaka zata wasu manyan mutane neh masu shi

Shiga cikin gidan sukayi  cikin turancin ta na Americans tace"kifada musu inason na huta sai zuwa 5 zanyi attending dinsu"

Amsawa tayi da toh tareda wucewa side din da bakin su suke...

```Azare, Bauchi```

"Umma ina yarki take" yatambaya daidai ya zauna akan expensive new sofan cikin palourn umma

Cikin Dan mamaki tace"Lafiya dai koh??"

"Erh Malam neh ke Neman mu"

Dan Jim umma tayi cos gabadaya ta manta bata fada wa Malam batun tafiyan Zuly bah

Ganin tayi shiru yasa shi fadin Harda ke ma cos so yake yakoma a ranan

Cewa tayi"je ka inazuwa"

Toh yafada tareda ficewa zuwa private palourn dake cikin fada

Da sallama tashigo cikin palourn sannan ta neme guri tazauna batareda ta lura da yanda Malam ke binta da Ido bah

"Ina yarki?" Malam yatambaya

Ahankali tace" bata nan"

"Da izinin waye tafita?"

"Da izini na" ta bashi amsa atakaice

Runtse idonshi yayi yana Jin bacin rai cikin sauri ya mike tsaye daga kan kujeran yana karata Addua acikin ranshi cos baison bacin rai yasa shi aikata abinda rayukan su zasu baci

Ganin bacin ran yaragu yasa shi Zama akan sofan shi tareda kallon umma da kanta ke sunkuye 

Gyaran murya yayi suka miyar da hankalinsu kanshi cikin muryan data jikin da mulki yace

"Iqbal tin da dadewa mun yanke hukunci akanka da kuma kanwarka wato Zulfa ina fatan zaku karbi hukunci da hannu biyu"

Kafeshi Malam yayi da ido yana karantar yanayin da yake ciki

Gabadaya wani irin mahaukaci bugu kirjinshi yakeyi inda umma alokacin zufa yagama wanketa

Cikin danne duk abinda yakeji ya kwakulo wani murmushin yake yace"inshAllah zamu zamo masu karban kowani hukuncin dakuka yanke ma...

Katse umma tayi da fadin" in kai ka yarda kana tunanin Zulyn mourad zata yarda??"

Cikin mamaki Malam yace"Zulyn mourad kuma??"

Kawar da kanta tayi tareda yamutsa fuska, sororo Iqbal yake kallon umma ga wani bacin ran daya soma fizgarshi sanadiyar sunan da Jin abinda tace

Haka kawai yaji bayason yaji tana kiran Zulfa da wannan sunan muryan Malam yaji yace" babu ruwana da in tayarda ko bata yarda bah hukunci dai munriga mun yanke shi I don't care"

Cikin ladabi yace " Allah gafarta Malam ko zamu iya Jin hukuncin da aka yanke akan mu?"

Cikin Jin dadi Malam yace"Allah yamaka Albarka Iqbal, daman ba komai bane face alkawarin aure da yake tsakanin ka da Zulfa"

Arazane ya dago kanshi Wanda wasu zazzafan zufa neh ke keto mishi

Cikin dauriya umma tace" tinda nasan basu son junansu miye zaisa a barsu kawai gashi kuma yanada matanshi?"

"Babu batun a barsu kuma aishi mijin mata 4 neh"

Wani irin kuka neh ya kufce wa umma, cikin mamaki suke kallonta sai Iqbal yaji dama shine yasa mu daman kuka cos zuciyan shi ba karamin nauyi yake mishi bah.

Jikin Malam neh yayi sanyi ganin yanda masoyiyar shi ke kuka, durkusawa umma tayi agaban shi tace"danAllah mijina kayi hakuri ka janye wannan maganan na tabbata wannan abinda kafada da kasan yanda rayukan mutane zasu shiga kunci da baka fade ta bah pls"

Wani dariya Malam yayi sai yaji gabadaya baya ma son yayi auren su dauwama a hakan ta dinga kiran shi da mijinta

Dagota yayi ya zaunar daita agefen shi yace" ba damuwa zan janye maganan nan"

Ajiyar zuciya umma da Iqbal suka sauke alokaci guda tareda yin hamdala acikin zuciyan su

Cikin farinciki umma tace"Nagode sosai mijina Allah ya barmu tare"

Murmushi yayi yace "Ameen amma akan sharadi daya tak"

Dasauri suke kafeshi da ido bugun zuciyan su na karuwa

Cikin serious tune Malam yace" na yarda zan janye wannan maganan amma sai dai Id...

```Dafatan munyi sallah Lafiya?Allah ya maimaita mana Ameen```

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 12:02] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 44*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 44*

Cikin serious tune Malam yace" na yarda zan janye wannan maganan amma sai dai Idan Zulfa tace bataso amma mudin tanaso to lah shakka zan daura musu aure nan da wata 1"

Wani siririn murmushi neh ya kufce wa umma cikin sauri ta lalubo wuyarta domin kiran Zuly...

Fitowarta kenan daga cikin toilet taji ringing din wayarta dasauri ta karasa wajen bedside drawer tareda gyara zaman karamin towel din jikin ta,ganin ummanta neh ke Kira yasa ta bari yakatse tareda danna mata Kira 

"Umma nah harkin fara missing dina neh" tafada cikin shagwaba

Kurawa wayan ido yayi yana konkonto ko ita dince tayi magana cos wayan a handsfree yake

Umma zatayi magana Malam yariga ta yace" Zulfan Ummanta"

Tabe baki tayi tace"ranka shi Dade ina wuni"

"Lafiya lau yar ummanta"

Kallon wayan tayi sannan tace"ina fatan komi Lafiya koh?"

Da dan mamaki Malam da Iqbal suke bin wayan da kallo cos maganan tayishi neh kaman da masu aikinta take

Basarwa Malam yayi yace"daman wani magana ne mukayi da ummanki tace bata yarda bah shine nace in har kema baki yarda bah ta zan janye maganan"

Wani irin rass taji kirjinta ya bada a hankali tace "taya za'ayi umma nah bata yarda da abu bah ni in yarda?"

Umma ce tace"karki damu yar umma it's about your life kifadi duk abinda ke ranki"

Cikin sanyi murya tace"Ohk miye abin toh?"

"Yauwa yar Albarka daman bakomai bane face hada ki aure da yayanki"

"Wani yaya na din" tafada yayin da zuciyar ta ta shiga dukan tara tara

Kaman mai tsoron yin magana yace"Iqbal"

Afigice tace"what!!"cos maganan yazomata abazata

Dan murmushi umma tayi cos tasan hakan zata faru , dukda Iqbal bayason auren amma bazaiso  tace bazata aure shi bah.

Muryan ta suka tsinkayo tace"Allah yasa shine mafi alkhairi agaremu"

Wani irin ajiyar zuciya Iqbal yasauke Jin abinda tafada haka ma Malam

Cikin tashin hankali umma tace" ke kinsan abinda kike fada kuwa?"

"Erh Umma nah nasani kuma na yarda" tana gama fadin haka ta katse Kira

"Hello ! Hello!! Hello!!!" Shine abinda Umma ke maimaita wa akidime

Malam neh yace"toh Alhmdllh kai Iqbal kaje ka shirya nan da wata daya zan daura muku aur...

Katse shi Umma tayi da fadin" pls karmuyi haka daku na tabbata batasan abinda tafada bane inta da.."
Chapter 25 · 0% Book details