← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 98

Sashe 63

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai nikam miye ke damunki neh? Kowa fah anan yasan Zuly tafiki da komai, gashi Kuma Mourad nasonta kaman ranshi tinda ke dakanki kikace soboda ita Zuciyarshi take seizing gashi Kuma yace in bata ce ta amince ya aureki bah bazai aureki bah so what are you waiting for? Wlhy bakiga tazama bah ki je gidanta tinda kin sani inyaso murakaki ki bata hakuri ta yarda ya aureki"

Maram tafada tana hararan Mom sai Allah Allah takeyi Mom ta yarda ita kuwa taje ta nuna wa Fakhih asalin Soyayya soboda tasan yana son Mom Kuma inhar Mom bata auri Mourad bah toh waje Fakhih zata koma!

Rausayar dakanta tayi tace "toh"

Tsabar farinciki har Maram batasan lokacin ta sa tafi bah har suka tsaya Suna binta da kallon mamaki, far da idanuwa tayi tace

" miye muke jira? Muje yanzu soboda da zafi-zafi ake dukan karfe"

Mikewa sukayi gabadayansu suka shige motan Mom sanna taja su...

'''AZARE'''

Kwance yake akan bargo a cikin parlourn Umma duk ya dishe ya jangwame Kaman ba shi bah soboda inba farin sani kamawa Iqbal bah bazaka taba cewan shi bane, idanuwan shi a lumshe yake Amma ba bacci yakeyi bah, zunzurutun yayi nisa acikin tunani har baisan ana mishi magana.

"Ya Iqbal!!!"Shine abinda take fada bayan ta ajiye basket din abinci agefenshi, ganin bai amsa bane yasata tsugunawa kusa dashi har kafarta na taba jikinshi, hawayen daya zubo mata tashare tana jin tausayinshi na ratsa ta gawani kibiyar Soyayyan shi dayake kaiwa zuciyarta suka, Ganinta shafa gefen fuskar shi baiyi motsi bane yasata kai bakinta daidai saitin nashi, runtse idanuwanta tayi tareda manna labbanta asaman nashi, ahakan ma ko gizau baiyi bah, sake kai bakinta tayi sannan ta tsotsi bakinshi na yen seconni 5 sannan ta daga bakinta wanda yayi daidai da bude idanuwan shi dayayi, Cikin sauri tazo mikewa amma cikin rashin sa'a hijabinta ya nannade kafanta wanda yasata zube mishi ajiki Zaro idanuwa tayi tana kokarin tashi cikin tsananin kunya don azatonta bacci yakeyi amma kuma yarike kugunta gam yana mai sakin mata murmushi tareda lumshe idanuwan shi yace

"Zuly miyesa kike guduna?"

*DanAllah wattpadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team Zuly
#team Mom

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 89*

Runtse idanuwanta tayi tana kawar dakanta gefe guda sai so take ta mike amma yaki barinta,

Gyara muryan da akayi neh yafargar dasu cikin sauri yasaketa itakuma tafice da gudu batareda ta kalli inda akayi gyaran muryan bah.

Tashi yayi yazauna yana bin bayanta da kallo kafin ya miyarda hankalinshi inda akayi gyaran murya

Murza idanuwanshi yayi yasake kallo kofan shigowa sannan ya miyarda hankalinshi wajen wacce tayi gyaran murya

Cikin sanyin jiki ta karaso wajen dayake tareda Zama agefenshi tana jawo basket dinda Hibba tazo dashi,

Shidai kawai kallonta yakeyi kaman TV chan yasauke ajiyar zuciya yace

"Zuly kwana biyu miyesa kike Guduna gashi kuma kaman baki da lafiya soboda ramar dakika yi"

Murmushin yake tasakar mishi kafinta dage girarta daya tace"kana sonta koh?"

Tsaki yaja yana cewa"matsalata dake kenan wlhy ina tambayanki abu daban kina fada min abu daban"

Abinci ta debo cikin chokali tana nufan bakinshi dashi tace"in zaka warware gwara ka warware soboda wannan tunane-tunanen bazai fisheka bah"

Kallonta kawai yakeyi yana karantan yanayinta, daga yanda take magana ma zakasan dauriya kawai takeyi,

Wayarta neh yayi kara cikin sauri takai dubanta wajen tana Adduan Allah yasa yay Mou dinta,

Tsaki taja cikin jin haushi ganin bashi din bane sannan tadauka ta kara akunnenta.

"Ina wuni"taji anfada daga dayan bangaren

Jinjina bayanta tayi ajikin kujera sannan ta amsa sallaman

"Sunana Momina!"

"Momina!"ta maimaita aranta cikin son tino inda ta tab'a jin sunan, jitayi tace

"DanAllah Anty Zuly kiyi hakuri ki barni na auri Mourad!"

Runtse idanuwanta tayi dakarfi tana kuma cizon labbanta

"DanAllah kiyi hakurin abubuwan danake miki rashin sani neh yajawo hakan"tasake fada cikin sanyin murya

Murmushin takaici Zuly tasake tace"yau kin rokeni abu emmata! Naji dadin hakan sosai"

Mom data gama kulewa tace"kin yarda ya aureni?"

"Erh"tafada cikin rawar murya hawaye na gangaro mata

Mom bata sake magana bah ta katse wayan cikin farinciki.

"Miyeke faruwa neh?"Iqbal ya tambayeta cikin damuwa

Kuka tafashe dashi tace"narasa shi akaro na biyu!"

Zai sake magana kenan yaga har ta mike tareda shigewa daki dagudu

"Narasa shi akaro na biyu!... Waye tarasa?"yatambaye kanshi

"Yah Salam! Mourad neh!"yafada lokacin daya tina ta tab'a rasa shi

"Allah sarki ashe shiyasa take ta ramewa"yafada cikin tausayinta kaman shidin ba arame yake bah, lumshe idanuwanshi yayi yana sake lulawa cikin duniyar tunanin shi...

'''ABUJA,NIGERIA'''

"Ammi nah mutuwa zanyi wlhy!"yafada cikin azaban rad'adin ciwo

Rikeshi Ammi tayi tana jin tausayin dan nata, tari yayi saiga jini nan kuwa computern gefenshi yasoma kara yana fitowa da wutan danja (jah)

Rudewa mutanen wajen sukayi gabadaya suna ririkeshi shikuwa sai fadi yake"wlhy inna rasata mutuwa zanyi! Kitaimake ni Ammi kibarmu! Nayi hakuri akaron farko amma yanzu ban tunanin zan sake wani hakurin, mutuwa zanyi yanzu kam wlhy nagaji sosai kibarni nasamu Farincikina danAllah am nothing without her,without her am a living de..."

Bai karasa fada bah sakamakon Alluran da aka danna mishi

Kowa awajen kuka yakeyi sosai, tari Fakhih yafara shima wanda ya miyarda hankalinsu kanshi,

Kawar da kanshi yayi soboda bayason su san halin dayake ciki amma kuma Qudsiyah tariga da tagani

Cikin muryan tashin hankali tace"nashiga uku bro jini fah nake gani yana fitowa daga bakin ka!"

Zaro idanuwa akayi inda Ammi tamike tareda jawoshi tana cire hannunshi daga bakinshi,

"Allahumma Ajirni Fi musibatin..."shine abinda Ammi ke maimaitawa sabin hawaye nazubo mata

"Miyeke damunka?"tafada kaman mai tsoron magana

Hawayen da suka zubo mishi yashare tareda girgiza kanshi yana kokarin kwace jikinshi daga hannunta,

Tana sakinshi yafita daga dakin gabadaya ko kallon gabanshi bayayi, jiyayi ya buge mutum amma ko sannu bai iya fada bah soboda daman bawai yana gani dakyau bane...

"Hey dear!"yaji anfada daga bayanshi lokacin daya zauna a haraban asibitin

Juyawa yayi kadan yakalleta sannan ya kawar da kai

Zama tayi agefenshi tace"ina laifin wanda yace yana sonka?"

Sake kallonta yayi yaga tama fi Mom kyau nesa ba kusa bah,girgiza kai yayi yace

"Banason takuri"

Idanuwanta suka ciko da kwalla cikin sanyin murya tace"in soyayyan bazai yiyu bah why not mu kulla abota?"

Runtse idanuwanshi yayi soboda sosai maganganun ta yashige shi barin ma yanda ta miyarda muryanta kalan tausayi

"Kije kawai"yafada cikin rashin damuwa,batareda tasake magana ba tawuce abinta tana mai jin haushin kanta....

'''DUBAI,UAE'''

Ganin yanda jikin Mourad ya tsananta neh yasa Ammi yanke shawarar miyarda shi Dubai, ba bata lokaci dukkansu harda Uwar iyayi wato Mom...

"Twin sis wlhy inason Mina amma gabadaya yarinyar bata sona wai Yaya takeso"Fakhih yafadawa Fakhiha dake zaune a gabanshi

"Wani yayan?" Ta tambaya kaman batasan akan waye ake magana bah

"Yayan mu mana!"yafada cikin takaici

"Kardai soboda hakan ciwonshi yatashi?"ta tambaya

"Erh mana ai bakaramin kofsa mana Ammi tayi bah"yafada cikin sanyin murya

"Hmmmm... Amma Mina nan tanashan OMO neh koh?"

Hararanta yayi sannan yace"ki kiyayi harshen ki"

"amma kace akwai wata kawar Mina dake sonka why not kabata dama?"tafada cikin rashin damuwa amma a zuciyarta fal damuwa ceh aciki, she can't believe ace Fakhih wata ta budi baki tace ta tsana!her brother fah! Ji tayi gabadaya bata ma son ko sunan Mom akira agefenta kuma tayi alkawarin sai Fakhih ya auri kawar Mom..

Kura mata idanuwa yayi yana kallon yanda tayi magana kaman bata damu bah chan yace" toh yanzu yaza'ayi nasameta?"

Murmushi tayi soboda daman tasan dakyar ya yasar da magananta,

Ajiyar zuciya tasauke tace"kokai fah! Ai duk wanda yanuna baya yinka kaima saika share batunshi tinda ba'a dole... Yanzu maganan number kabarmun zan nemo maka"

"Thanks sis"yafada yana sakar mata murmushi...

"Ammi taya za'ayi ki hada Momina da Yaya bayan kisan Yaya nada wanda yakeso haka ma Fakhih shima yana son Momina!"

"What"Ammi tafada tana kallon Fakhiha

"Erh mana Ammi! DanAllah kiyi hakuri Fakhih ya auri Mom inhar zata yarda inkuma bata yarda bah shikenan sai a kyaleta tayi tafiyarta daman yarinyar bawai inayinta bane"tafada cikin kwantar da murya

"Wlhy bansan Yana sonta bah! Amma yanzu dakika fada mun zan mawa yayana bayani"tafada tana share hawayen fuskarta tunowa datayi Mourad na kwance rai a hannun Allah

Murmushi Fakhiha tayi tace barina je nasanar da Zulyn Mourad

Itama murmushi tasake tana kallon Mourad dake blushing akan gado

Riko hannunta yayi yana sakin murmushin karfin hali soboda sosai yake jin jiki amma yanzu dajin wannan maganansu Ammi yana jin kashi hamsin na zafin Ciwon dayake ciki yana tafiya

"Nagode Ammi nah!"yafada cikin farinciki

"Kayi haku.." kafin ta karasa yasa yatsan shi abakinta yana girgiza mata kai...

Su Mom an samu duniya sai shagali akeyi, koda yaushe cikin zuwa yawon shakatawa takeyi, hotuna kuwa kaman hauka haka tadinga daukawa ana daurawa a IG dakuma statues,

Itakam ma batasan wainan da ake toyawa bah, gefe daya kuma Fakhih neh dakuma Mysha suna shan soyayyansu dukda bawai sun gama sakewa bane da juna...

'''AZARE, BAUCHI NIGERIA'''

"Yaya!!"tafada tana fitowa hannunta daukeda farar takarda

Juyawa yayi ya kalleta yana fadin" haba kanwata irin wannan kiran kaman wacce taga aliens"

Turo baki tayi tace "shikenan bazan kira sunanka bah?"

"Ohk sorry dear"tafada yana kaman kunne

"Ga wannan!"tafada tana Mika mai takardan hannunta

"Nikam kwana biyu miye sirrin neh naga sai wani kyau kike karawa gashi kullum cikin murmushi kaman wacce aka mawa albishiri da gidan Aljanna"yafada cikin kulawa

Sunkuyar da kanta tayi tace" Ammi takira ni kuma ta yarda Yay Mou dina zai aureni...

Hawayen dasuka dan zubo mata ta share tace... Ina cikin farinciki sosai Yaya zan aure shi kaman yanda nake buri"

Baisan sanda hawaye suka gangaro mai bai, har yau bai daina nadaman abubuwan daya mata bah watarana har kunyanta yakeji inyaga yanda take tarairaya shi dukda itadin ma ba isheshiyar lafiya gareta bah

Jan hancinta tayi tace"Yay Mou dina yana sona sosai, you won't believe tin lokacin da Ammi tace natafi yake kwance agadon asibiti kuma haryanzu ba'a sallameshi bah! Gaskiya inaga ban mishi adalci bah soboda nasan son yake min ya ninka wanda nake mishi sau hamsin soboda he live only for me and he can die for me and i love him to the edge of infinity"
Chapter 63 · 0% Book details