← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 98

Sashe 21

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yauwa" tafada tareda karasa wajen zamanta.

Koro mata bayani yayi inda itama mamaki yacika ta sosai cos ta sha ganin Zulfa na Zane amma ita duk a shirme take daukan su.

"Ya kike ganin za'ayi??"

Saisaita kanta tayi gudun karta kunyata shi a idon jama'a  tace "duk yanda kake ganin shine daidai"

Wani boyayyen ajiyar zuciya yasauke jin bata nuna kaman tafishi iko akan Zulfa bah.

Gyada kanshi yayi yace"toh madalla, kaman yanda na fada muku zan yi tunani akai toh aka din neh don haka gobe ku dawo.

Fita sukayi dukkansu inda Umma ta tashi,zata fara tafiya kenan taji ya riko hannunta ta baya.

"Am so sorry I never meant any single word I said to you last night"(dayake Umma tanajin turanci amma basai sosai sosai bah)

"Ai ka riga kagama yanke hukunci na yarda ni waiting ceh amma that's in Zulfa bata gaba na but mudin da rai koda ban ajiye na kaina bah babu wanda ya isa ya Kira ni da juya!!!"

Tafada tareda kwatar hannunta tabar wajen, tsaki yaja tareda komawa ya zauna awajen zaman shi yana ayyana abubuwa da dama acikin ranshi...

Komawa cikin gidan tayi tasamu Zulfa kwance akan kujera cos daman jiya baccin da rabi da rabi tayi soboda yunwan data kwana dashi.

Ahankali takarasa kusa daita ta gyara mata kwanciyan ta tanajin wani sabon sonta azuciyarta.

Cream din ciwon da akaji mata ta dauko, bude rigarta tayi tana kallon yanda hakwaran Hibba yadan yi zurfi asaman nonon ta.

Tsaki taja tace "Mayya kawai" cos sosai take jin ba dadi azuciyarta, ahankali ta shafa mata cream din awajen gudun karta tayar da ita.

Tagama shafa mata kenan Mourad yayi sallama, amsawa tayi tana gyara mata rigarta.

"Sannu Umma"

"Yauwa, saidai fah bangama Sanin kai waye bah"

Shafa kanshi yayi yace" Suna na Mourad, ina zaune neh cikin Jericho Oxford a US amma fah aiki nakeyi awajen.

"Toh amma bakayi kama da bature bah"

Murmushi yayi yace" erh mama na yar Nigeria ceh babana kuma Balarabe neh.

"Aww Madalla ai nasha mamaki danaji kana hausa"

Murmushi kawai yasake yi yace"Umma zaki yarda Zulfa tabini muje US"

Zaro Ido tayi tace" ni Ramatu waye ubana da zan bar maka Zulfa katafi daita, taya za'ayi na yarda katafi min da raina gashi bawai nasan ka bah haka kawai nadauki rayuwata guda na damka maka"

" Ki fahimceni Umma a makaranta zansa ta bawani abu zan mata bah"

"Ai bance zaka mata wani abu bah amma maganan gaskiya ka kwanta min amma bazan iya damka maka y'a guda dayan da Allah ya mallaka min bah"

Cikin rashin jin dadi yace "toh Umma ba damuwa, bari natafi tunda tana bacci"

"Yauwa"adawo lafiya

Komawa yayi wajen makwanci su cikeda damuwa aranshi wayar shi dayayi kara ne yasashi dawowa daga duniyar daya dan shiga.

Daukan wayan yayi tareda yin sallama cikin muryan damuwa

"Ya kukayi da Ummanta??" Ammi ta tambaye shi

Cikin rawar murya yace"Taki yarda Ammi"

"Miye kace mata??"

Nan yakwashe yanda sukayi da Umma yafada wa Ammi

"Why not kace zaku tafi tare daita??"

"Kina ganin zata yarda??"

"Do one thing for me ka kaiwa Ummanta wayan I will talk to her"

Cikin farinciki yace toh, cikin sauri yafita yayi wajen cikin fada straight part din Umma yayi.

Jin sallaman shi yasata fitowa daga cikin daki har lokacin Zulfa bata tashi bah.

"Umma wai Ammi nah zata miki magana"

Kujera Umma ta nuna mai ganin yana kokarin Zama akasa cos shikam yamanta da akwai kujeru acikin palourn.

Kiran wayan Ammi yayi ko ringing biyu baiyi bah ta dauka

"Ammi nah barina bata"

"OK" tafada while yabawa Umman waya

Sallama Umma tayi Ammi ta amsa gaisawa sukayi cikin mutunci sannan Ammi ta fada mata abinda takeso daita.

"Toh a gaskiya naji dadin wannan batu amma kinsan bani kadai nake da iko akanta bah duk abinda Babanta yafada toh shi za'ayi amma yanzu awaje na bah matsala"

Wani sabon dadi Mourad yakeji yakosa Zulynshi ta tashi yafada mata wannan albishirin cos yasan itama zatayi farinciki da hakan.

Sallama sukayi inda ta mika mishi wayan karba yayi yakara a kunne cikin farinciki daya kasa boyuwa yace

"Shukran ya Ammi jzkllah fil jannah" 

Murmushi tayi tace"Ameen ya Mourad, yanzu hankalin ka ya kwanta kenan??"

"Erh mana Ammi bakiji wani dadin da nakeji bane, Ammi I love her"

Cikin sauri Umma ke kallon shi ganin ko kunyan ta baiji bah shikam ma ko sanin tana kallon shi batayi bah sai zuba yake mawa uwar shi.

Sunfi minti 30 suna magana da Ammin shi kafin sukayi sallama alokacin Kam Umma har tayi cikin daki cos sosai yake bata kunya yanda yake wani shagwabe wa Ammin shi.

"Yay Mou dina yaushe kashigo?" Ta tambaye shi lokacin da ta farka

Da murmushi akan fuskarshi yakeyi yace" tinda dazu nashigo"

Murmushi tayi tace"yaushe zamuje yawo din?"

"Ai inaga sai kin gaji dazuwa yawo mah"

"Ana gajiya da zuwa yawo neh??"

"Erh mana"

"Toh ni bazan taba gajiya dazuwa yawo bah"

"Haka dai kikace" yafada yana shafa kanta

"Yauwa in tambaye ki mana??"

Gyada mishi kai tayi batareda tayi magana

"In nace kibini mutafi tare kuma babanki ya amince mutafi zaki yarda ??"

tace" zanso inbika amma bazai yiyu bah"

Kwalalo Ido yayi yace"miyesa toh bayan ya yarda??"

Umma dake jinsu acikin gida tasake murmushi jin abinda tace" ni bazan bika....

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

Wannan page din naka neh kayi yanda kakeso dashi *AL HUSSAIN ABU SAMEER* Nagode sosai Allah yasaka da alkheri. Allah yabar zumunci...

*Page 36*

Umma dake jinsu acikin gida tasake murmushi jin abinda tace" ni bazan bika nabar Umma nah bah"

Ajiyar zuciya yasauke jin abinda tafada kuma yaji dadin hakan da tayi

"Ai da Umma zamu tafi"

Cikin zumudi tace" dagaske kake yi??"

"Ai bazan miki wasa da irin wannan abin bah"

"Wayyo dadi kenan bazamu rabu bah kullum Muna tare " tafada cikin murna

Murmushi yayi yace"erh Muna tare"

"Ina zuwa" ta tashi tareda nufar cikin daki

"Umma ki fara hada mana kayanmu mun kusan barin gari"

Kallon ta Umma ta tsaya yi tace " ai naga babanki bai yarda bah tukunna"

"Sai ki dinga kiranshi da baba na" tafada tana murguda baki

Wani dum Umma taji acikin ranta tace"ai baban ki neh"

Girgiza kanta tayi tace" ai dolanci na bai kai haka bah,bayan ko yaushe a class sunan babana daban dana su Marwa"

Ajiyar zuciya tasauke tace"koma dai Yaya neh sai ya yarda tukunna"

Batareda tayi magana tafice zuwa palour inda Mourad yake jiran ta...

```washe gari```

" Haba mai martaba taya za'ayi kace Umma ceh zata bita??"Hindatu uwar gidan Malam tafada cikin Jin haushi

"Daman waye zai bita??" Ya tambaye ta cikin isa

"Naga akwai Marwa miye zai hana su tafi tare kuma kaga duk sa'oin juna neh sai su cigaba da karatun su

"Wannan wani irin magana kike fadi neh hakan?? Taya za'ayi atura kana nan yara su kadai uwa duniya...

Caraf Zuwaira Amaryan Malam tace" gani sai na bisu na kula dasu"

Girgiza kanshi yayi cikin takaici yace"kun dai san mahaifiyar yarinyan nan bazata yarda bah"

" Malam ko ka manta ba ita ta haifeta bane Kam??" Ta tambayan daidai isowar Umma da Zulfa wajen

"Gaskiya Kam Malam ai muma muna da iko akan yarinyan kawai dai munyi shiru neh,in tana son tayi iko akan y'a ta haifo nata itama" Zuwaira tafada

Wani irin nauyi Umma taji akirjin ta  kaman an daura mata katuwar dutse akai.

"Erh bazallan ita keda iko akan Zulfa bah"Malam yafada

Zuciya neh taciyo Umma tace" sai miye in bani nah haife Zulfa bah? Nace sai miye??"

Afirgice Zulfa ke kallon fuskar Umman ta tareda girgiza hannunta

"Basai kunmin gori bah yau na yarda bani na haife ta bah amma kusani ko iyayenta bazasu kaini sonta bah, ina ce don karna bita kuka tada magana?? Toh bazan bita bah saiku zuba ruwa akasa kusha"

Kallon Zulfa Umma tayi hawaye na zubowa daga idonta tace" bazan iya cigaba da boye miki bah Zulfa bani ceh na haife ki bah ni kanwar mamanki ceh"

Wani kuka Zulfa tafashe dashi tace" ni ke kadai nasani kece Umma nah kuma ke kadai nakeso.

"No Zulfa sun riga sun fada abinda ban kaunar ji so kisani ni bah mamanki bace"tana gama fadin hakan ta fice cikin sauri.

Sosai jikin su yayi sanyi ganin yanda Umma tafita tana kuka mai tsuma rai.

Itama Zulfa dagudu tabi bayan Umman ta, daki tasamu Umma sai kwasar kayanta takeyi tana sa wa a akwati.

Itama Zulfa jawo akwatin ta tayi tana zuba kayanta aciki.

Hada Ido sukayi da Zulfa cikin sauri Umma ta rungumeta cikin kuka tace" inasonki sosai Zulfa ina mugun sonki amma yazama dole mu nisanci juna,bazan iya cigaba da Zama a inda za'a dinga min gori bah"

"Zan biki Umma"

"Taya za'ayi kibar gidan ubanki? Nan neh tushen ki"tafada tareda sakin ta ta zuge zip din akwatin ta...

Cikin sauri take share hawayen idonta sakamakon ganin...

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 37*

Cikin sauri take share hawayen idonta sakamakon ganin Mourad datayi abakin kofa kasancewan Zulfa ta bar kofa a wangale.

Cikin sanyi jiki yafara takowa cikin palourn, jin Umma tayi shiru yasa Zulfa waigowa ai tana ganin shi ta rugo da gudu ta rungumeshi tareda sakin kuka mai tsuma zuciya.

Wani irin zafi yaji zuciyarshi nayi sakamakon kukanta dayake ji.

Cuddle dinta yayi da kyau ajikinshi yana mai jin wani yanayi mai wuyar fassara atare dashi.

"It's okay dear" yafada yana tapping bayanta.

Wucewa Umma ta zo daidai su Zuly ta rike hannunta tareda sakin Mourad.

Tsungunawa tayi tace"Umma nah karki barni danAllah, ki share duk abinda suka fada ki zubda su a kwandon shara"

"Yay Mou dina katayani rokonta danAllah"tafada tana juyawa wajen shi

Ba bata lokaci shima ya tsuguna akan gwiwar shi dukda baisan miye ke faruwa bah

Kafin yayi magana saigasu Malam da matanshi, yanayin da suka samesu neh yasa hankalin Malam tashi cikin sauri yakarasa wajenta yace

"Haba Ramatu wannan abin baikai ace zaki bar gida bah"
Chapter 21 · 0% Book details