← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 98

Sashe 23

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan yayi parking neh ya juyo ya kalleni abaya, murmushi yasake ganin yanda nayi nashe nashe akan seat sai kwasan bacci nakeyi.

Saukowa yayi ya bude baya, daukoni yayi a hannun shi kaman wata jaririya...

"Sannu da gida Umma"yafada lokacin daya harba daita azaune

Umma nah dake zaune tana jiran dawowar mu, tana ganin  ta tashi cikin hanzari ta taho wai zata karbe ni

Cikin sauri ya matsa yace"ki bari nakaita karmu wahalar dake"

Badan taso bah ta barshi ya kaita dakin da aka basu soboda har yanzu bata gama sakewa dashi bah, shimfida ta yayi akan gado tareda sumbatar goshin ta dakuma kuncin ta sannan ya fice.

Bayan shi Umma ta bi da kallo cos sosai take lura da yanayin dayake ciki gameda yar'ta.

Tashi na kenan na ga kaina akan gado banyi wani mamaki bah soboda nasan yay Mou dina neh yakawo dakin.

Sauka nayi daga kan gadon tareda yin mika wanda akayi in mutum yatashi daga bacci.

Hanyan bayan gida nayi fitsari nayi tareda dauro Alwala soboda ko kadan bana wasa da Sallah.

Fitowa nayi na tada sallah sannan na zauna inayin Addua , ban idar bah Umma nah tashigo cikin dakin

"Daman cewa nayi bari nah taso ki lokacin sallah har ya wuce"

Murmushi kawai na sakar mata ina dan lumshe Ido , shafa Adduan nayi tareda gaishe ta.

"Ina yay Mou dina yake??" Natambaye ta 

"Yana dakin shi inaga shi din ma bacci yakeyi"

Zaro Ido nayi nace" Allah yasa dai yayi sallah "

Tashi nayi na nade sallaya sannan nace"bari na taso shi"

Ban jira cewan Umma bah nayi waje, ina fita natina ashe bansan dakin shi bah.

Wani ma'aikaci nagani yazo wucewa, tsayawa yayi ganin kaman akwai abinda nake nema cikin turancin shi na turawa yace

"Do you need anything??" Kure shi da ido nayi cos ko kadan ban dago abinda yake fadi bah.

Kara maimaita abinda yake fadi yayi cikin kosawa nace" nifa dakin yay Mou dina nake nema inma zaka nuna min ka nuna min bawai ka tsaya kana lankwasa harshe bah"

"Pardon?" Zan sake yin magana naji muryan shi ta baya yana waya,

Cikin sauri na juya nayi wajen shi , bude hannun shi yayi na fada aciki tareda sa kaina akan kirjin shi.

Jin yana labarci yasa namiyar da ido na cikin nashi kaman mai jin abinda yake fadi.

"Ammi nah ga Zulynah din nan"

Da ido na mishi alaman waye neh , daga wayar yayi a kunnen shi kadan "yace uwata ceh"

Murmushi na neh ya fadada daidai lokacin da yasa wayan a handsfree.

Wata daddadiyar murya ceh tamin sallama, kara kallon fuskan yay Mou dina nayi kafin na bude bakina da kyar na amsa sallamar ta.

Ja na yayi zuwa wajen sofa din palourn,zama yayi ya daura ni asamar cinyarshi.

Cikin nutsuwa na gaisheta amsa min tayi daga dayan bangaren, muryan  Yay Mou dina naji yace" Ammi nah ya kikaji muryan Zulynah??"

"Kai masha Allah ka iya zabi wlhy muryar ta kaman ana busa sarewa har tafi naka dadi"

Dariya nasake jin abinda tace akan murya na bansan yaushe na Budi baki nace" nasan kawai kin fada neh amma acikin nan kowa yasan wanda muryan shi yafi dadi acikin ni da Yay Mou dina"

Wani irin dadi Ammi taji jin abinda nace

"Haba Zulyn Mourad karki fadi haka mana"

"Amma acikin ku biyu muryan ki yafi nashi"

"danAllah fah" tafada cikin Jin dadi, shagwabe fuska Yay Mou yayi irin baiji dadin nan bah 

Ko kallon dayake gefo min baisa nayi shiru bah saima gwalon danake mishi kuma idona daga kanshi bah saima gwalon danake mishi

"Wlhy"nafada tareda sakin murmushi ina shafa sajen shi zuwa gemun shi soboda bakaramin kyau suke min bah.

"Toh Zulyn Mourad nagode"

"Kai Ammi miye abin godiya kuma anan"nafada ina zumbura bah

Murmushi kawai tayi tace" ya naga yayi shiru ko yabar wajen neh??"

Dariya nayi still ido na akanshi nace"Lah Ammi inaga kaman ruwa neh ya cinye shi azaune"

Itama darawa tayi tace"toh Zulyn Mourad sai anjima koh?"

"Toh Ammi sai anjima" ina gama magana ya katse kiran, hannu na na tusa cikin gashin kanshi ina mai Susa lumshe idonshi naga yayi gashi still baiyi magana 

Bude idonshi yayi sannan ya daga ni daga kan cinyarshi

Cikin mamaki nake binshi da ido ganin lokaci daya ya sauya min,

"Miye faru yay Mou dina??"

Bude bakin shi yayi yana cizan labban shi da kyar yace"...

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 40*

Bude bakin shi yayi yana cizan labban shi da kyar yace"kai na neh yafara ciwo"

"Yah Salam"nafurta cikin kwalalo ido

Miyarda shi nayi yazauna nakara komawa saman cinyarshi shidai da ido yake bina gani yayi na kama kanshi

Addua nayi ta tofa mai kaman yanda Umma nah kemin nan da nan yafara zufa...

Da murmushi asamar fuskarshi yace"thank you my doctor" 

Murmushi na miyar mai tareda mikewa daga samar cinyarshi  wanda kuma yayi daidai da fitowar Umma daga daki

"Kuna nan ashe??" Ta tambaye mu

"Erh Umma gashi kuma wai kanshi yana ciwo" nafada cikin rashin jin dadi

"Wai haka??"

"Ai naji sauki yanzu cos harta kama min" yafada yana kallon saiti na tareda sakar min murmushi

Zaro Ido Umma tayi tace" ta kama maka fah kace?? Ai bata iya bah" zumburo baki nayi ganin Umma tana underestimating din

Kama min kumatu yayi yace"Lah Umma dagaske ta kama min kuma naji sauki sosai"

Tabe baki Umma tayi tace"toh Allah ya sauwaka"

"Ameen muka amsa in chorus"

Sanar damu akayi angama shirya dining table ba bata lokaci muka dunguma zuwa dining room din...

```washe gari...```

```8:30am```

Shi yafara tashinmu mukayi sallah, wanka nayi inda na tarar har ya kawo min kayan da muka siya jiya a boutique...

Daya daga cikin kayan nasa inda ba karamin kyau yamin bah, wajen mirror na nufa sannan nadauki powder na shafa har zan dam bara jam baki sai na tina da turawan dana gani jiya ba haka sukayi bah

Lipstick kawai nadan shafa dan daidai saikuma naga ashe mah yafi mun kyau fiyeda jambaki.

Fitowa nayi daga dakin cos alokacin Umma nah bata ciki

Samun turawan nan nayi suna shirya dining table dauke,juyawa nayi na kalle ta wajen da Yay Mou dina yafito jiya

Ahankali nake takawa zuwa wajen ban kaiga zuwa bah Umma nah takira ni 

Wajen ta nakoma ina turo baki nace" ina kwana Umma nah"

"Lfy, ina kuma zakiyi acan??"

Dan murmushi nayi nace" zanje in taso Yay Mou dina neh naga bai fito bah"

"Ai Mourad yafita bayan anyi sallahn asuba"

Zaro Ido nayi nace"tin asuba🤔?? Toh ina yaje haka da harma bai zai cemin zai fita bah??"

"Wajen aiki ya tafi" tafada tareda jan hannu na zuwa dining room din

Sosai naji bah dadi da fitan shi, Umma nah da kanta ta zuba min abinci 

Kallon plate din nayi ina tunanin ko zan iya ci tinda daman da Yay Mou dina nakeci

Duk dadin danaji abincin yayi jiya sai naga nayau ko dadi baiyi bah

Spoons biyu nayi naji na koshi, tura plate din da nayi neh ya miyarda hankalin Umma nah gareni

Tin kafin tayi magana nace" na koshi neh"

"Bangane kin koshi bah?"

Kwabe fuska nayi nace"Umma nah wlhy abincin babu dadi shiyasa"

"Toh in dafo miki wani abun daban??"ta tambaye ni cikeda kulawa

Da murmushi asamar fuskar na nace"A'a Umma nah ki barshi kawai, bari na zaga gidan nagani"

"Toh banda tsokana da barna"

Dariya nayi nace"kai Umma nah ai bana jin turancin da zanyi tsokana dashi amma in Yay Mou dina yadawo zan mai magana yasani a makarantan koyan turanci"

"Ahtoh kin kyauta wlhy"tafada daidai tagama cin abincin

Tare muka tashi inda ita ta zauna a palour nikuma na fita...

```8:00pm```

Zaune nake a palour bayan na idar da Sallah banda kallon kofa babu abinda nakeyi 

Bini bini saina saki tsaki cos sosai idanu na suke son ganin shi ga wani yunwan dayake chasa ni

Karan motan dana ji neh yasani ajiyar zuciyan da har Umma nah sanda taji shi

Girgiza kai kawai tayi lokacin dataga nayi hanyar waje

Turus naja natsaya abakin kofa bayan na fita, murmushi naga asamar fuskarshi lokacin da yayi harba dani

Ware min hannun shi yayi still yana murmushi ganin masu aikin gidan sai kallon mu sukeyi yasa nayi harraman zuwa gareshi soboda daman bana niyan yi mishi oyoyo soboda rai na yabaci sosai amma bazan so in yarfa shi agaban masu aikin shi bah

Ina zuwa wajen shi na fada ajikin shi atare muka sauke ajiyar zuciya, kankameshi nayi sannan nafara kukan shagwaba

Dagoni yayi daga jikinshi yana taba wuya na yace"Yah Salam!! Zulynah waye taba min ke??"

Turo bakin na nayi nace" ba.. bakai bane"

Zaro Ido yayi yace" ni kuma??"

Gyada kaina nayi tareda yin hanyan cikin gidan, hannu na yaja sannan ya matso dani jikinshi yace" am so sorry Zulynah ki fada min laifin danayi"

Hannuna na fauce na daura su akan karamin kugu na nace" daman aikin ku daga sassafe har dare kuke kaiwa neh??"

Girgiza kai yayi zaiyi magana na katse shi nace" Toh miye ka tsayi yi har dare bayan kasan ka ajiye mutane agida??"

Kallonta yakeyi daga sama har kasa cos sai yanzu ya lura da dressing dinta shafa silk gashin  kanshi yayi yace" kinyi kyau Zulynah"

Gaba tayi tace"Inka shirya amsa min tambayan dana maka saika neme ni"

Girgiza kanshi yayi tareda sakin murmushi yana mai bin bayanta

Suna shiga na nemi sitting agefen Umma na dora kafa daya akan dayan murmushi kurun yasakayi cos sosai yanda nakeyi yake kara dakon sona acikin zuciyar shi

"Sannu da gida Umma"

"Sannu da dawowa yah aiki"

"Alhmdllh Umma"

Zaro Ido nayi soboda tunowa da nayi ban mai sannu da dawowa wa bah nace"Lah sannu da dawowa yay Mou dina" 

Murmushi yasake Jin abinda nafada yace" sai yanzu kika ganni Zulynah"

Kawar da kaina nayi daga gareshi nace" kai ana tambayan ka wani abu daban kana bada amsa wani abun daban"

"Am sorry my dear"

"Kaima kasan bana jin irin wa'inan yaren"

"Karki damu zuwa ji...

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 42*
Chapter 23 · 0% Book details