← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 98

Sashe 31

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yanda take mikawa Mourad dinta abu a walakance yasa tace" ki ajiye papern in ya gama zai duba"

Murmushi yayi cos ya dago miyesa Zuly tace ta ajiye

"Zulynah ki Kira Paul yashirya zai kaini Abuja"

"Nima zanje Yay Mou" tafada cikin sauri

"A'a kam baza kibishi bah"Umma ta katse ta

Narai narai tayi da ido cikin son yin kuka tace"DanAllah Umma"

"Umma pls kibari ta bini bazamu kwana bah" Mourad ma yasa baki

Girgiza kai tayi tace" kunga jibi daurin aure kuma gabadaya taki yarda amata komai soboda rashin ji daga gareka kaga kuwa kwana biyun dasuka rage yakamata ace tayi kitso da lalle"

Hadiye wani abu mai kaman madaci Mourad yayi sannan yashafa sumar kanshi hade da mikewa yace" karki manta ki Kira Paul ni yanzu zan tafi"

Cikin rashin jin dadi ta girgiza kai ,inda an bi nata to basai anyi wani kitso da lalle bah cos bin Yay Mou dinta yafi mata komai...

Rike hannun shi tayi tace"Muje in rakaka mota" 

Matse soft palm dinta yayi acikin nashi sannan sukayi gaba ana mai adawo lafiya.

Kaman karsu rabu haka sukeji Zuly harda hawaye nan ma fah ba rabuwan gabadaya bane 

Cikin sanyin jiki ta tajuya domin komawa cikin gida idon ta ya sauka akan Iqbal dayake jifansu da mummunar kallo

Tsakin haushin tafiyan Mourad taja kafin ta murguda mai baki tace" husband to be in banji duka bah bansan kanayi bah"

Iqbal da tinda suka fito yake kallon ta har runguman dasukayi yana gani yace" shegiya mai bakin fuska mummuna yar iska"

"Makaryaci kawai" tafada tareda wucewa dagudu cos Yay Mou dinta yace yana da ciwo akira mutum babba da makaryaci

Kwafa yayi yace"zan kama ki neh ai mahaukaciya"...

"What Ammi!!!"yafada with so much anger bayan yashigo wanda yasa dukkansu tsorata

"Lafiya dai koh?" Ammi ta tambaya ahankali inda suka zuba mai Ido , Zuly kam mannewa tayi ajikin Ammi tana mamakin Sabin halayen Mourad dinta

"Ammi you can't imagine ace tsantsan rainin hankali wa Zulynah aka zuba wasu cheap cheap things"

Da gefen ido Umma da Zuly ke kallon Iqbal wanda yake jin takaicin abinda Mourad yace

"Kimma ga lefen da aka hada mata neh yah Salam wlhy ko amafarki ban taba mafarkin za'a hadawa Zulynah irin wa'inan cheap things din bah, anya wanda zai aureta yasan worth dinta kuwa??"

"Calm down Yay Mou" tafada cikin sanyin murya tareda tashi taje ta debo mishi ruwa a cup

Zama dashi tayi tazauna agefen shi tareda samai cup abakinshi sanda yasha rabi yacire abakinshi sannan yakai sauran bakin ta 

Ajiyar zuciya yasauke yace"thanks darling"

Lumshe idanunta kawai tayi tareda sake budewa kosu Iqbal sun lura akwai strong chemistry a tsakaninsu

"You've changed alot" tafada tareda mikewa ta miyar da cup din

"Not my fault"yafada hopelessly ganin danta yana shirin yin kuka agaban su Iqbal yasata fadin

"So yanxu kasa an chanza mata neh?"

Kallon shi yamiyar wajen Ammi yace"it's must ai ki Kira min Fakhiha nace mata tashiga Amazon ta hadamin kaya so ki tambaye ta Kota gama hadawa, sai turo"

"Inners dinta anan za'a siya kenan" Ammi ta tambaya ta lalubo wayar ta

"No nariga da na fada mata sizes dinta dakuma creams da perfs dinda take amfani dashi"

Jin yace sizes yasa Iqbal kallon Zuly da mamaki ai ma baikamata ace yaji mamakin su bah amma abin da tsayawa arai

"Yay Mou nayi loosing weight fah kalle ni" tafada tana jujuyawa takaici duk yagama cika Iqbal har baisan yaushe yafice daga cikin palourn bah 

Yusayrah ma kawarai tana mamakin su tace" bangane kasan sizes dinta  bah?"

"Bana son gulma in ba'a kasa dake ba karki na shiga kinji Elephant kawai"

Sosai Elephant dinda suke kiranta ke kona mata rai 

"Kar mutum yasake Kira na da Elephant"tafada cikin daga murya

"If not?" Yafada cikin rainin hankali

"Mourad matar aurece fah" Umma takatse shi

"Ai tayi kama da su" yafada tareda ficewa daga palourn cos in yajima yana iya kai mata hannu kuma gaskiya dukan mata bah halin shi bane in fact yadauki masu dukan mata amatsayin mahaukata

Toh in banda hauka miye zai sa namiji dukan mace ai Mata uwayen sune mata suna da wani kima na daban , mata abin tausayawa neh, mata abin tarairaya neh, mata sunfi komai tsada , kuma ko wace mace tauraruwa ceh

Shifa da namiji ya duki mace gwanda ya kama garu da fada kokuma yaje inda akwai maza yaje Yakama su da fada

Amma ace wani jaki, doki yadauki guduman hannun shi yadaki abinda yafi kauna aduniya sosai abin yake damunshi idan yatina hakan 

In banda Allah yaso shi bah da a US suke wlhy babu abinda zai hana shi dau karar shi...

```Ranar daurin aure...```

Sosai take jin babu dadi acikin ranta wanda tarasa dalilin hakan gabadaya sai taji batama son ayi auren soboda maganganun da Kuwahysa tamata

Jitake kaman tagudu wa auren suje suyi rayuwar su da Mourad dinta cos sai Yanzu take jin wani kaunar...

_hmmm to ga wata sabuwa Zuly takamo wata tasha fah, yakuke ganin zamuyi fans?_

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

_wannan page din naki neh Ummu Minnataur-rahman Allah yabar kauna_

*Page 51*

Jitake kaman tagudu wa auren suje suyi rayuwar su da Mourad dinta cos sai Yanzu take jin wani kaunar Zama dashi barinma inta tuna moments dinsu

"Miye kike tunani kawata??"Kuwah tafada tareda Zama agefen ta

"Kuwahnah banason auren Yanzu in fact wani irin kunci nakejin kaina inna tina yau neh aurenah" tafada cikin hawaye

Murmushi Kuwah tayi tace"ko zan iya sanin miyesa"

"Kuwah zanyi missing mutum mafi soyuwa araina banason barinshi Yanzu kuma wani irin abu nakeji gameda shi wanda ko Iqbal banjin irin shi akan shi"

Cikin farinciki Kuwah tace"kenan kina kaunar Yay Mou dinki"

Zaro ido tayi tace"yes yes I think ina kaunar shi and zan aure shi"

"Iqbal din kuma fah??"Ammi ta tambaya daga baya

Juyawa sukayi wajenta Zuly tace" zan iya hakura da Iqbal amma bazan iya hakura da Yay Mou dina bah"

Wani irin farinciki Ammi tashiga  cikin sanyin murya tace"yau neh daurin auren fah am scared we're late"

"I don't think so bari naje nayi wanka and get dress up sainaje wajen Malam na mai bayani"tafada tareda mikewa cikin sauri, Umma ma kaman an tsunduma ta a aljanna haka take ji

Amma dukkansu babu wanda ya tuna cewan lokaci baya jiran kowa cos har bata lokaci sosai sukayi suna shirya ta harda su kwalliya wanda kuma hakan yadauke su kusan 2hours amma tsantsan zumudi da farincikin dasuke ciki babu wanda ya lura...

Tafe yake amma kana ganinshi kasan baya cikin hanyacin shi infact baya kallon komai akan hanya din,

Few minutes back yashiga the most shocking time of his life, lokacin daya ji Liman yace _*AN DAURA AUREN IQBAL ABDULLAHI DAKUMA ZULFA ABUBAKAR UMAR*_

Today is the baddest day he could never imagine , he feel so lonely a yau he badly needs a shoulder to cry on,

He can't imagine cewan shine yabada auren abu mafi soyuwa aranshi, he can't tell how zuciyar shi yake kuna kawai dai daurewa yakeyi

He can't believe cewan auren ma yabayar dashi neh ga wanda baisan darajar ta bah wlhy dayasan Iqbal neh da bai bada aurenta bah dasai saidai duk abinda zai faru ya faru...

Sanye take cikin wata shegiyar expensive doguwar flowing gown peach color kanta yane  da wani cute small gyale ,

Agogon chopard secret wanda duk jikinshi diamond neh daure a tsintsiyar hannuta , tayi wani irin dan iskan kyau soboda makeup din fuskar ta

Wajen Malam takeson zuwa amma kuma sai taji in bata leka waje bah bazata iya shiga bah

Cakk ta tsaya tana mamakin abinda idon ta ya gane mata she's thinking maybe mafarki take amma kuma zuciyar ta tabata cewan this is the reality

Bata taba ganin Yay Mou cikin manyan kaya bah amma yau soboda alkawarin su yasa 

Yayi wani shegen kyau sanye yake cikin wata tsadadiyar shadda wanda aka mishi dan iskan dinki cos sosai aka bata kayan kaman bada kudi aka siya bah gashi da daukan ido cos karan kanshi kayan har wani kamshi na daban yake(😥 harna tina wani kaya, in na tina cewan akwai kudin neh sai in dauke abin daga raina)

Tsadadden hulan Damanga neh akanshi , sajen fuskarshi bakaramin sake kawata mai fuska yayi bah_Hublot million$ black caviar bang_neh daure a hannu shi kafanshi kuwa sanye cikin wani _Tom Ford_ takalmi sai yafito kaman shine ango cos ta tabbata ko Iqbal bazai kaishi haduwa bah...

Wata irin wawiyar runguma takai mishi wanda ya yadan razana shi

Harzai rungumeta shima sai yatina Yanzu da dah ba daya bane zare ta yayi daga jikinshi yana kallon fuskar ta yanda yayi mugun kyau

Wani kululun bakin ciki neh yataso mai ganin annurin farinciki kwance akan fuskanta

"Yay Mou dina baka taba kyau irin na yau bah you look extra ordinary handsome and breathtaking" tafada tana kokarin Kara kwanciya ajikin shi 

Fizgota taji anyi da mugun karfi , juyawa tayi taga Iqbal tsaye yana huci kaman wani zaki tabe baki tayi tace

"Wlhy Iqbal Yay Mou dina yafika kyau sosai kuma yafi kama da ango"

Zaiyi magana kenan Mourad yariga shi wajen kama hannun shi hade da hadawa dana Zuly yace" ga amanarta nan na baka DanAllah karka zalunceta cos Zulynah sorry i mean Zuly sai ahankali"

Kallon Mourad Zuly keyi kaman wata sokuwa kafin tayi magana har Mourad yafara tafiya

Fizge hannun ta tayi daga cikin na Iqbal tayi wajen Mourad da gudu hade da rike hannun shi tana fadin"badai barina zakayi anan bah"

Zare hannun shi yayi yana kirkiro murmushi yace" toh yah kikeson na miki Zulyn Iqbal"

"What!!" Tafada afirgice

"Erh mana you are now the Mrs Iqbal you can't wait to be, you're finally his"

"Kana nufin an daura auren??" Ta tambaya da daddaya kaman mai tsoron magana zufa na karyo mata

Hadiye wani abu yayi cikin son danne kukanshi ya gyada kai

Zaro Ido tayi tana girgiza kai kaman wanda take shirin cire kanta daga jikinta

"Miyesa kabari aka daura?"afirgice mutanen wajen ke kallon ta cos da karfi tayi maganan 
Chapter 31 · 0% Book details