← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 98

Sashe 20

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Buge hannun shi tayi tana jifanshi da harara tace" dallah sakeni don naxo wajen masoyi na shine zaku na raina min hankali "

"Zulfa zo ki tafi gida" bafaden yafada cikin daure fuska shikuma baturen harya koma ciki domin sanar dasu abinda ke faruwa

"Kai ban barin nan wajen sai naga masoyi na" tafada da karfi duk da ahalin yanzu daurewa kawai takeyi

Janta yashiga yi ganin tana neman distracting dinsu...

Wani irin zafi neh yakai mishi farmaki wanda yasashi sakin ta batareda ya shirya bah

Wani irin tsinkewar gaba yaziyarce ta dalilin faduwar da take shirin yi soboda sakinta dayayi abazata.

Cikin wani irin super yakarasa gareta ganin tana shirin kaiwa kasa.

Runtsa idonta tayi gam soboda tagama sadaukarwa fadi zatayi amma abin mamaki saitaji wani magnet yayi hanging dinta.

Wani ajiyar zuciya yasauke ganinta safe ajikinshi, bafade kuwa gabadaya yagama jikewa da zufa soboda yasan Umma batada sauki ko kadan akan Zulfa, ba'a taba tama ya aka Kare ballantana an taba ta...

Tagama sadaukarwa zata fadi kawai saitaji tayi hanging.

Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata bah tace" lah nayi karfin su Aminta (Amitabh) bachan.

Wani murmushin neh yasubuce mai jin abinda tace bafade kuwa dariya nah Yakama shi dukda mugun tashin hankalin daya ziyarce shi bada jimawa bah.

Yunkuwara tayi domin daidaita tsayuwar ta amma takasa sosai abin yabata mamaki cos bakaramin riko yamata bah amma shashashan ko bude idonta batayi bah.

"Zulynah!!!" Yakira cikin sweet voice nashi.

Waro idonta tayi domin ganin wanda yakirata ai kuwa idonsu yasarke ana juna.

Sosai taji dadin ganinshi amma saita fuske tana neman raba jikinta danashi cos sosai take jin haushin shi.

Saketa yayi ahankali amma cikin rashin sa'a wa....

*Pls kuyi hakuri soboda matsalar dazaku na encountering daga gareni gabadaya waya nah neh yake bani ciwon head(har na gaji mah🤕)*

*Pls banason stickers dinnan cos storage din waya nah ya cika bana iya gani*

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 34*

Saketa yayi ahankali amma cikin rashin sa'a wata Jiri ta kwashe ta cikin zafin nama ya tareta ajikinshi.

"Zulynah miye ke damun ki"

"Ni dallah kasakeni, na mah yi fushi dakai karka sake min magana" tafada hade da ture shi ganin bai tattareda alaman yunwa

"Miye nayi Zulynah"yafada muryan shi na rawa ganin har hawaye yafara silalowa daga idonta

"Ai ka kyauta kacemin zakadawo muci abincin rana amma shine baka dawo ba koh, daman nasan ba so na kakeyi bah kawai dai kafada neh"

"Wayyo Allah kiyi hakuri Zulynah wlhy naso dawowa amma Allah bai nufa bah kuma wlhy inasonki sosai"

"Kaci abinci??" Ta tambaye shi tareda kafe shi da ido

Gyada kanshi yayi alaman erh, murmushin takaici tayi tace"har ka iya cin abinci??"

Kallon ta kawai yakeyi ga zuciyarshi na wani iri sakamakon hawayen da har yanzu basu daina zuba" kidaina zubarda hawayen ki am really sorry"

"Ka iya cin abinci shine kace karna ci najiraka?? Ba damuwa nagode"tafada tareda barin wajen tana tafiya tana hada hanya

Dasauri ya tareta  yace "kiyi hakuri Zulynah bansan zai bata miki rai bah"

Murmushi tayi tace" shi neh nace ba damuwa nagode"

Tafiya tadinga yi har ta shige side dinsu dasauri yakarasa binta tareda tsayawa abakin kofa

"Yar Umma yadai baki ganshi bane??"

Hawayen da take kokarin rikewa neh ya gangaro mata sharewa tayi takwanta akan kujera tace" naganshi"

"Toh Madalla barina kawo miki abincin toh"

"Bazan ci bah"

"Taya za'ayi kice bazaki ci bah bayan rabon ki da abinci tin jiya da safe"

Zama Umma tayi agefenta tace"miye faru"

"Umma nah ashe shikam ma mantawa dani yayi yaci abincin shi bayan yace min karna ci nawa zai dawo muci tare" tafada cikin kuka

"Kiyi mishi uzuri mana"

"Toh Umma kawo min abincin toh"

Sosai jikin shi yayi sanyi yaji bai kyauta bah kwata kwata shifa ma a wasa yafada mata amma ta dauka dagaske soboda bai dauka zata dauki abin serious bah.

Sallama yayi inda Umma ta amsa lokacin tana kokarin shiga cikin kitchen din part din ta.

Gaishe ta yayi ta amsa a dakile cos itama bataji dadin abinda yayi bah.

Hadiye masifarta tayi tace"ka kyauta shine kasa min y'a tajiraka bayan kasan bazaka dawo bah gashi yarinya har tafara ramewa"

"Amin afuwa wlhy gabadaya ba acikin gari na wuni bah naso shigowa amma dare yayi sosai shiyasa ban shigo bah amma Wlhy tana raina"

Haka kawai ta samu kanta da yarda da abinda yafada tace"aww hakane?? Toh kadawo lfy??"

"Lafiya, danAllah kitayani bata hakuri"

Tin kafin Umma tayi magana tace" ai nace babu komai koh??" 

"Erh kinfadi hakan"

"Kawai dai banji dadi bane shiyasa"tafada cikin nuna rashin jin dadi shigewa Umma tayi yayi saurin matsowa wajenta tareda rike hannunta

"Sorry once again" yafada tareda pecking din kumatun ta

"Ai dai kasan banjin turanci koh??" Tafada cikin shagwaba

"Toh kiyi hakuri"

Murmushi tayi tace"amma zaka koya min turanci koh??"

"Sosai mah har yawo zaki kaini kafin nabar garin nan"

"Zaka bar garin nan fa kace??"

"Erh mana aiki na yana jira na achan da nah zauna"

"Yanzu zaka tafi ka barni nadaina ganin ka kenan??"

"Toh da bazai koma inda yafito bane?? Umma ta yakatse su

Abinci ta ajiye agaban su cikin tray, bude cooler din tayi wani kamshin dadi ya kaiwa hancin su farmaki.

Wani sabon yunwa taji yakamata ba bata lokaci tadauki plates biyu tareda saka cokali daddaya.

Zuba daidai wanda tasan zata iya ci tayi acikin plate, zata zuba mai ya rike hannunta tareda girgiza mata kai yace.

"Basai kin deba min bah muci tare" cikeda rashin damuwa tamiyar da spoon nashi cikin plate dinta tareda Zuba juice acikin cups biyu.

Duk abinda sukeyi Umma na kallonsu girgiza kai tayi tareda basu waje domin su sake dakyau.

Cin abinci sukeyi babu wanda yace uffan acikin su harsuka karar basu sani bah.

Mourad ji yayi kaman baitaba cin abincin da yakai wannan dadi bah tinda yake arayuwar shi.

Juice din ta dauka tasha juice tana ajiye wa ya dauki nata yaushe"zan iya sha"

Da murmushi takalle  shi tace" duk abinda yake nawa daga yau kaima sun zamo naka"

Cikin Jin dadi yace"dagaske??"

"Erh" daidai saitin da janbakin ta ya taba ya kafa bakin shi idonsu a sarke acikin kowannen su.

"Nagode koma miye na mallaka kema naki neh" murmushi kawai tayi har suka gama cin abinci.

Wayan shi dake kara ya dauko ganin sunan dake yawo a screen din yasashi fadin

"Ya Subhanallah"cos gabadaya ya gama mantawa da yabar wasu suna jiranshi.

Hankalin ta tamiyar gareshi  tana jiran yayi magana.

Daukan wayan yayi yace" I will be there in the next 5mins"

"Miye faru??" 

"Ashe na tsayar da wasu, barina je nasame su" yafada tareda mikewa

"Nima zan bika" batareda second thought yace muje.

Umma ta kwala wa Kira tace saisun dawo.

Hannunta acikin nashi suka jera suna tafiya gwanin ban sha'awa, koina suka wuce sai an nuna su cos they look so perfect.

Shiga sukayi cikin gurin inda baturai sunkai 10 awajen.

Cikin turanci wani bature yace " it's like we are missing something in this drawing"

Kallon hoton takeyi tace" Yay Mou dina wannan hoton baiyi bah"

Kallon ta yakeyi da mamaki cos sai architects neh kawai zasu iya concluding cewan baiyi bah gashi ba turanci takeji bah da yace don taji anfada neh.

Karasawa tayi wajen board din tayi ta dauki duster ta hau gogewa.

Zaro Ido sukayi ganin tana goge wahalan da sukeyi.

"Bari na zana muku wanda yake kaina" tafada cikin murmushi

Tambayan shi sukayi abinda tace shikuma ya fassara musu , har zai hanata wani bature wanda alamu suka nuna shine oga yace  yabarta(kun dai san turawa basu underestimating din mutum).

Zanawa tafara cikeda kwarewa kaman wanda tasaba yi daman, baki da hanci suka sake suna kallonta.

Juyowa tayi tace" ya kuka gani"

Tafi aka fara acikin wajen inda cikin ransu cike yake fal da mamakinta, ware mata hannu yayi alaman tazo gareshi.

Cikin sauri ta karasa ya Rungumeta tsam tareda daga ta sama yashiga juyi daita.

Itakuwa dariya duk ya cikata wai akan dan wannan abin suke ta murna.

Ajiye ta yayi baturan suka fara takowa wajen ta kowa na  Mika mata hannu suyi handshake.

Wani irin dadi taji kawai ta washe hakwara tareda Mika musu hannunta itama.

"Yay Mou dina duk wannan murnan na miye haka?"

"Kinsan nawa neh kudin da aka sa a abinda kikayi kuwa?"

"Dan wannan abin??" Ta tambaya da mamaki

Zaro Ido yayi wani farinciki na shigar shi soboda tunanin dasuka shiga kaikawo acikin kwakwalwar shi.

"Muje" yafada tareda yin gaba da ita

"Ina zamuje??"

"Wajen babanki!!"

"Babana kuma?"da mamaki

Tsayawa yayi yace"erh mana babanki sarkin garin nan"

Fizge hannunta tayi tace...

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 35*

Fizge hannunta tayi tace "ni kadaina kiranshi da babana "

"Why?"

"Barina koma gida"

Ganin bata gane abinda yace bane yace"Nace miyesa??"

"Ohhh toh ai ba baba na bane"

"Miye sa kika ce hakan??"

"Toh ai kowa yaji sunana zaisan bashi ya haifeni bah"

Numfasawa yayi cikin basarda shirmen ta yace "toh muje wajen shi"

"A'a kaje in kadawo ina wajen Umma nah"bata jira cewan shi bah ta ruga aguje abinta...

Da kallo ya bita  sannan ya girgiza kanshi tareda bin bayan wa'inan baturen zuwa cikin fada...

```cikin fada```

"Kuna nufin kuce Zulfa ce tayi wannan zanen??" Maimartaba  yatambaye su cikin turanci ga mamaki kwance asamar fuskanshi

"Erh" 

"Daman in bazaka damu bah inason natafi daita USA zan nema mata makarantan Architects soboda gaskiya bai kamata ace wannan basirar tata yatafi abanza bah" Mourad yafada cikeda neman alfarma

Numfasawa Mai martaba Malam yayi yace" kabari zanyi tunani akai"

Toh yafada yana adduan samun nasara azuciyarshi sannan suka mishi bayanin kudin da daman aka sa akan zanen.

Mamaki sosai Mai martaba Malam yayi ganin dan wannan zanen da aka samishi makudan kudi.

Aika yayi akira mishi Umma zuwa fada ba bata lokaci akaje aka kirata.

Sanda ta bata lokacin ta wajen daukan wanka sannan tafito cikin tafiyan kasaitan ta.

Da sallama tashiga cikin fadan inda idonta yasauka akan masoyin yar'ta.

Murmushi tasakar mai inda Mai martaba Malam yayi mamakin hakan.

"Sannu da fitowa Umma"
Chapter 20 · 0% Book details