← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 98

Sashe 1

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

Page 1&2

*Jericho Oxford, USA. 6:00am*

Wani hadadden guri nagani wanda duk kasan wajen malale yakeda grass carpet,ga iska mai sanyi Sai kadawa yake,ga kyawawan flower awajen wanda ajere suke according to their colurs,acan wani gefe daban kuma swimming pool neh wanda bashida zurfi sosai kuma colourn sea blue.

Can na hango wani bature sanye da black suit and white shirt taciki yazo ya wice,inda yatafi nabi da ido,saina kalla yana mawa mutum magana amma dai banjin abinda suke fadi,juyawa naga yayi inda yafito.

30 minutes later

Gani nayi wata mata wanda nakeda yakinin cewan yar Nigeria ce tawuce,sadaf sadaf nabi bayanta

"Oh Allah yan'nan tindazu fah ake jiranki,amma Kika wani zauna kaman wata sarauniya,kindai San nafada miki banson walakanci,in hardai bazaki musu aikin da suka kawo bah kifada musu tinda bake kadai Kika iya abinda suke so bah,haba don kawai kunga Allah yamiki farinjini,nikam mah komawa zanyi bazan iya cigaba dazama da kebah" matan tafada wa budurwan da bazata wuce 17 yrs bah cikeda bacin rai.

"Wayyo Allah ummata kiyi hakuri karki tafi kibarni bazan sake walakanci bah wlhy"budurwan tafada cikin kuka cos babu abinda ta tsana arayuwarta kaman ganin bacin ran wannan matan.

"Ya isa basaikin mun kuka bah,muje kiyi wanka sannan kije ki sallame su"matan tafada cikin kwantarda murya, Sai yanxu nakare musu kallo, farace tas amma irin bafulatanan nan ce ita kuma bazata wuce 47yrs aduniya bah ga jikinta amurmure alamun hutu yazauna ajikinta,while ita yarinyar dirariya ce Wato full option(figure 8) cos komai nata yazauna dabbas acikin wata yar karamar half vest din jikinta Sai dan wando wanda yakusan kaiwa gwiwa amma a matse yake ,kuma yarinyar bah fara bace irin bakakennan wanda ake kiransu da Black beauty ga eyes nata manya kuma a lumshe suke bakin nan dan tsut dashi saika rantse big bom sweet bazai shiga bah (irin na fa'eeda nah kenan...lol) hancin nan kaman Biro tsantsan tsinin ta ga Suma kwance lufluf akan goshinta har irin sajennan yamata agefen fuska ga sumanta akwai tsayi cos har reto yakeyi a gadon bayan ta (irin na my Fa'iza and Hasynah...lol)ga lips din nan tsakiya neh pink wanda black line neh ya zagaye su (@hasynah). In takaice muku gaskiya yarinyar ta hadu fiyeda tinanin mai tinani cos babu abinda wasu fararen zasu nuna mata in banda haske. Wani hanya naga sun nufa daga baya,suna isa wajen kofan wajen yabudu dakanshi.....

*8:00am......*

Maganganun da nakeji kasakasa neh yasani karasawa wajen kofan inda nakeji din,tsayawa nayi ina karewa wajen kallo, hmm hadadden wajene wanda komai nawajen fari da golden neh ,ga dogon table dakuma kujerun dake zagaye dashi wanda irin nacikin conference room neh,kowani gaban gujera akwai tea cup dakuma sandwich wanda nake kyautata zagin breakfast neh,ga gurin babu bakin fata kodaya dukkansu baturai neh Sai wani mutum wanda yadauke min ido cos shine kawai yafita daban acikin su soboda bashida bambamci da balarabe tsantsan haduwarshi dakuma yanayinshin da baiyi dibi da wa'incan dinbah .

Wani bature naga yashigo sannan yayi clearing voice nashi kafin yace

"Excuse me here!!!"jikake tsit cos duk sunyi shiru sannan yacigaba da fadin

"Miss is on her way here"yana gama fadin hakan yajuya while wata mai irin shigarshi amma ita skirt neh ba wani bah tashigo da trolley,nan da nan tafara kwashe teacups da sandwich plates din gabansu wanda wasu ancinye wasu kuma rabi akaci ,tana dauka tana goge wajen cikeda nuna kwarewar ta a aikinta,tana gama wa ta bar wajen.

Jikake kwas kwas kwas ma'ana karar takalmi nan kuwa kallo yakoma inda suke jin sautin amma banda wannan balaraben cos shine wanda ainihin yabawa kofan baya,eyes nashi ya lumshe lokacin da kamshin perfume dinta yamawa kofar hancinshi sallama,ahankali yake bude idonshi,fes kuwa ya budesu abanyanta don harta shigeshi,itakuwa sanye takeda wata doguwar riga mai budedden kasa peach color gashi tayi daurin turban akanta , ahankali take takawa harta karasa wajen zamanta

"Good morning Miss!!" Suka fada in chorus lokacin da ta zauna amma banda wannan balaraben,wani bature ne yafara magana cikin harshen turanci yake fadin

"Miss, my name Is Maxwell Ernest and am the MD of our company,munkawo miki wani aikin neh Kuma munsan ke kadai zaki mana yanda muke bukata" wani remote yadauka sannan ya danna nan take wani katon photo ya bayyana ,itadai babu abinda takeyi illa binshi dana shanun da takeyi,sannan ya cigaba da fadin

"This is the Mumbai Phoenix Mall,we want the exact drawing plan of this mall,here is a flash,in this flash there's the complete view of the Phoenix mall and kuma zaki iya zuwa can Mumbai din kigani cos it's said that experience is the best teacher,and your fee will be $2,000,000(which is equivalent to 720,000,688.00Naira in Nigeria money) ,I hope that's okay with you?and all you need is just to sign here to show your approval"yakoro mata bayani hade da tura mata wani file din hannunshi,kallon file din tayi kurun hade da kauda kanta gefe , while dukkansu suka zuba mata na mujiya ga wajen ya dauki shuru banda karar AC babu abinda akeji acikin conference room din,jitayi ajikinta ana kallonta cos tinda tashiga wannan gurin take jin feeling din, mayar da dubanta tayi ga wanda yakafeta da ido,caraf idanunsu ya sarke dana juna wanda ya haddasawa dukkansu shiga wani yanayi, shi yafara daukan idon shi daga gareta cos yasan ko shekaran zasuyi ahakan bazata daga idonta bah kuma bayason ta bata musu lokaci.

"I will go through it later"tafada dada daya kuma cikin sanyin murya

"It's okay Miss" wanda ya wakilcesu Wato Mr Maxwell yafada hade da mika mata hannu alaman handshake batareda ta musaba itama tabada nata hannun yayinda sauran ma suka bata suna fita da da daya, yanzu mah idon shi nakanta kuma baiyi Shirin tashi daga inda yake zaune bah, wani bature ne yashigo wanda nake da yakinin cewan Shima mai aiki neh cos kayansu daya da nadazu, file dinda suka bari yadauka sannan yafita dashi,cikeda nutsuwa tatashi zata fita , daidai ta isa wajenda yake zaune

"Zulynah!!!..." Yafada,cak ta tsaya cos sunan har tsakiyan kanta takeji aduk lokacin da ya kirata da wannan sunan ....

"Zulynah,fushi kikeyi dani koh?? Yatambaye ta cikin rawar murya(ikon Allah daman yana jin Hausa...) kaman wani mace, gakuma yanda yake furta maganan zaka San larabci yazauna daram a bakinshi.....

"Zulynah pls kimin magana ko zuciyata zata daina zafi dayake "yayi adding kaman zaiyi kuka

"Ya Mou..."tafada hade da fadawa jikinshi,tsam ya rungumeta harda kankameta tareda sauke ajiyar zuciya

"Bakai bane katafi ko sallama bamuyi bah"takara fada tana me barkewa da kuka

"Zulynah kiyi hakuri wlhy emergency aka kai NMC Speciality Hospital Al-Qusais shiyasa natafi , ki gafarce ni DanAllah bazan kara bah kuma kidaina kuka inba sokike nima nafara bah"yafada still Voice dinshi narawa ga hannunshi Sai yawo a bayanta yake,ga idanunshi mah sunyi ja alamun kuka yakeson yi,dasauri ta dago kanta cos tasan halinshi sarai

"Ya Mou...nadaina kuka karkayi kaima"tafada tareda karasa breaking hug din tayi while yagoge mata hawayenta ,itakuwa tabashi best of her smile wanda duk sanda tayishi narka mai zuciya yakeyi

"Inasonki sosai Zulynah"yafada cikin serious tune

"Nima inasonka ya Mou..."

"Excuse me Miss you have a phone call"wata ma'aikaciya ta katse su,karbar wayan tayi,tana ganin mai Kiran ta bari ya katse sannan takara Kira tashi tayi daga cinyarshi hade da Jan hannunshi zuwa kan daya daga cikin hadadiyar sofas din dake edge din conference room din

"Manya Manya maganin Kanana Kanana"shine abinda wata tafada daga dayan bangaren

"Matar Aminin Saurayina "itama tafada,wani irin dum yaji azuciyar shi dukda ba'a ranar tafara fadan wannan mumunar Kalmar bah inji shi da fada,ahankali yakare hannunshi daga cikin nata hade da resting bayanshi ajikin sofa , lumshe sexy eyes nashi yayi yayinda zuciyar shi Sai dukan tara tara yakeyi

"Manya Manya, Albishirinki" aka fada daga dayan side din

"Goro"

"Naci wake fah" tafada cikin murna

"KUWAH... dagaske kikeyi??"

"Wlhy ZULYN MOU.. ,am so happy"ta bata amsa

"KUWAHnah am also happy for you, kicewa abokin Saurayina nima ina yatashi murna kuma Allah yasaukeki lafiya"

"Ameen Zuly, ya Mou dinki??"

"Yah Mou dina yana lafiya"sanda tayi magana tatina ashe suna tare,without waste of time tace

"Gashi ma kifada" Gaisawa sukayi yamata Allah ya sauke ta lafiya cos wayar a handsfree yake...

★★★★★

*ROOM 5 SHERATON HOTEL, WUSE ABUJA NIGERIA...*

*1:30PM*

Ashh...washh... Uhmm..... Shine sounds din dake tashi acikin wannan room din,batareda bata lokaci bah na kutsa cikin dakin don dauko rahoto,abinda natarar ne yasani yin turus tareda jinjina wa ajikin kofa cos wani nagani yake cin wata in a naughty way tsantsan mugun ta harda buga mata bumbum.....

*3:30PM*

Sararawa juna sukayi badan sun gaji bah kuma Sai alokacin nakare musu kallo, farine kuma babu laifi kyakyawane daga ganin bakinshi zaka gane yana zuke zuke soboda bakin da yayi... Itama macen fara ce tas yar duma duma amma ba cancan bah,kananan ido ne daita kuma tanada dan tuddun labba,babu laifi itama kyakyawa ce cos it's said that everybody is beautiful in their own way.

"YUSAYRAH, bazaki kwana min bah??"yatambaye ta

"Oh DAKHIL kadaisan yau mijina zai dawo soboda haka bazan samu daman kwana bah" tabashi amsa daidai lokacin da take sanya kayanta

"Nikike fadawa mijinki zai dawo!?" Yatambaye ta cikeda bacin rai...

"Wayyo masoyina kayi hakuri bahaka bane wlhy kawai dai banson ya zargi wani abu daga gareni shiyasa kuma fah yace in yadawo zai bani kudin da katambaye ni domin business dinda kafadamin zakayi" tafada cikeda kwantar da murya cos tasan halinshi sarai..

"Ohk, ya babies dina??"

"Ohh nasan yanxu sun dawo daga school bari nayi sauri natafi"tafada daidai tagama sa dankunne

"Yanxu Sai yaushe Zan sake ganin ki??"

"Karka damu Zan kiraka a waya"

" Yauwa masoyiya kuma karki manta da kudin"

"Taya za'ayi namanta da kudin masoyina kaima kasan bazan taba mantawa bah,yana dawowa zance yabani check din 2.5m saina karbo kudin nakawo maka" tafada tana murmushin jin dadi sanadiyar ganin murmushin shi

"Shiyasa nake sonki wlhy"

"Nima inasonka " tafada hade da pecking dinshi sannan tafita dasauri daga room din,waige waige take cikin style har tasamu tafita daga cikin hotel din,parking loot tawuce sannan ta dauki car dinta kafin tayi gaba...

*Freetown St. 23, WUSE II Abuja Nigeria.*

"Oyoyo mumy!!!" Shine abinda wasu yaran da basu 4yrs ke fadi
Chapter 1 · 0% Book details