← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 98

Sashe 53

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abangaren Zuly kuwa ranta fess harda runguman phone din cikin sauri taciro wayan daga kirjinta ta kira Iqbal as usual bai dauka bah shiyasa tarubuta mai message Kaman haka: Afuwan ! DanAllah zandanje gidansu Kuwahnah kayi hakuri ban nemi izini tintini bah amma in baka yarda bah kana iya fadamun kafin nawuce... ZULY.

Lutfiya takira, cikin farinciki tafada mata abinda yafaru itama tanuna farincikin ta tareda fada mata cewa basaitaje gidan Kuwah bah kawai takirata tafada mata awaya, ai kuwa tayi na'am da zancen , tana gama wayan takira Kuwah mah tafada mata duk haushi yagama cika wannan budurwan dake zauna sai tsaki take ja..

"Haryanzu bakiji alert bane?"tafada wa matan tana tattara abubuwansu

"Erh" tabata amsa caraf budurwan tace

"Wai nikam nawa dubu 5 da mutum bazai iya bayarwa bah? Kodayake ai bah shakka ko kwandala babu atare dake Kuma in har haka neh kiroke ni nabiya miki"

Kallonta Zuly tayi tana dage giranta daya tace" emmata akwai abinda natsare miki neh anan? Banfa sanki bah! Agidan kitso muka hadu Kuma anan zamu rabu! And in najiki dakyau cewa kikayi in rokeki koh bah haka bah? Ni nafi karfin na roki abu awajenki saidai inke kirokeni! Kuma inshaAllah saikin rokeni abu! Tsaya mah tukunna miye kikedashi?... tsaki taja tace... Natsani shishigi arayuwata kingane?"

Hannu tasa ajaka taciro bundle din 500, kadan tazara aciki sannan ta ajiyewa mai kitson sauran tace gashi, tazo daukan BabynZuly data jima da bacci message yashigo wayar matan tana dubawa taga alert, Dasauri ta mike hartana b'ata kunshin hannun budurwan tace

"Dubu dari biyar aka turo"

"Rabonki neh ahakan ma baiga kunshin bane da kudin yafi haka, nabarki lafiya"

Zuly tafada cikin murmushi tareda yin hanyan waje, muryan matan taji tace

"Toh ga wanda kika bani"

Girgiza kai Zuly tayi tace"haba ai Sun zamo naki"

"Nagode sosai Allah ya Kara bude yakuma biya muku bukatunku na Alhkeri" matan tafada

"Ameen" tafada tareda ficewa daga gidan ranta fess, ajiyar zuciya matan tasauke kafin tajuyo wajen budurwan data cika tayi fam tana tunanin wacce wannan wanda tafi ta dakuma wanda yabada kudin kunshin dabai gani bah , ajiyar zuciya tasauke tana Addua Allah yatunkudo mata irin wanda ya biyawa Zuly kudi....

Tana parking taga motan Awad a compound din gidan fitowa tayi daga cikin motan tazagaya tasab'a Babynta akafada sannan tadoshi cikin gida, ahankali tabude kofa tana mamakin hayaniyan datake jiyowa daga ciki , zatayi sallama kenan taji Iqbal nacewa

"Wai nikam Zulfa kanwar Uwarka neh dazaka tsaya kana fadamin maganan banza akanta, kai bari kaji Wlhy saidai in bata Kuma daukan Wani cikin bah amma mudin ciki yashigeta Wlhy babu ruwana zubarwa zanyi , nace maka ya'yana Sun ishe ni bana bukatar wasu daga kowacce mace, ni biyu Sun ishe ni , inkuma kaga dama kafadamata cewan Nike zubar mata da kowani cikinta I don't ca..." shiru yayi yana kallon Awad dake ta zufa yana kallon bakin kofan shigowa bakinshi sai motsi yake yi amma yakasa furta kowani magana, tsaki yaja shima yajuya yana fadin

"Munafiki miye kake kal. ."Makalewa maganan yayi sanadiyar hango Zuly dayayi tsaye abakin kofa.

_Tirkash🙆🙆 kardai watan cin Ubanshi neh Yakama..._

*DanAllah wattpadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 79*

*Meem@rtjj Novel Group, MATAR SO COMMENTS ROOM,SADNAF NOVEL FANS,RABO AJALI FANS📚📚,QADDARANMU CE TAZO A HAKA Fans grp, 🔵🔴AL-HEENE🔵🔴 [email protected] ,Zeeta Hausa Novels, Gorgeous Writers Fans, TASKAR MARUBUTA...📚,'YAN CINKI FAN'S 2, UMMU SUHAIL FANS, WATA UWA, SANAZ NOVELLA, ME MAGANI FANS, Ammin Manal Hausa Novel📚.... kuyi hakuri fah bansamu kiran sunayen Ku bah Wlhy yawa gareku. .. much love wannan page din nakune💋💋*

Jitayi kaman ba aduniya take bah, ahankali tasoma takowa tana layi duk akwai babynta a kafadarta,gabadaya jikinta sai rawa yakeyi kaman mazari, Awad naganin kaman zata gefar da babynZuly yayi maza yakarbeta.

Gaban Iqbal ta tsaya tana kallon kwayar idanuwanshi, idanunta duk sunyi jahzir, cikin rawar murya ta nunashi da yatsa tace "kaine daman kake zukemin ciki? Why? Ashe kai bazallan mugu bane you're also a monster, a beast, a murderer

Daskarewa yayi awajen cikin firgici yana karanto duk Adduar datazo bakinshi, abinda ma yasa yake daga muryar shi yazata bayanzu zata dawo bah tinda tayi messaging dinshi gashi daman Yusayrah ta tafi wuni gidansu.

"Wayyo Allah nah! , miye na maka arayuwa dayasa nayi deserving haka daga gareka? Nazata yau ranar Farinciki na neh ashe kuwa yau neh worst moment din rayuwata, wai nikam ya'akayi kazamo dakiki Mara tunani neh? Ka kashe rayuka 6 acikin shekaru 3 kcal! Yeah rayuka 6 tinda kowani cikina en biyu neh ! You killed our children, kamiyardani abar tausayi batareda Kasan cewan Kaine abun tausayin bah! Yeah kai abun tausayine and when i mean tausayin i mean asalin abun tausayin, nazata tsanarka nakeji acikin zuciyata ashe haushin Kane kawai soboda wannan feeling din da nake ji shine tsana cos I feel like strangling you to death" tafada hawaye na gangarowa dacikin idanuwanta, juyawa tayi wajen Awad dake rike da Babynta, mika mai hannu tayi shi kuma yamika mata baby, batareda tayi magana bah takarbe ta tanufi hanyar waje

"Karki yarda ki fita daga gidan nan " yafada cikin borin kunya Kojuyowa batayi bah tace

"Wlhy hakkin ya'ya nah bazasu taba barinka bah, karka sa aranka zandawo gidan nan , nabaka kwana biyu koka furta min kalman sakina ayanxu kokuma ka rubuta min cikin lallami kokuma na maka ka akotu! Kuma I don't care ko nawa zaiyi costing dina."

Ragwaf yazube asaman kujera zufa duk yagama wanke mai jiki, hannu yasa arufe fuskarshi cikeda damuwa, Awad naganin haka yayi hanyan waje abinshi , zai bude kofa kenan yaji muryan Iqbal nacewa" yanzu Kaima barina zakayi?"

"Uhmmm what do you expect? Karka damu matar so dinka takusa dawowa saitazo ta rarrasheka."yana gama magana yafice abinshi yana Kuma godewa Allah da ba'a bakinshi Zuly taji maganan bah...

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

_DUBAI_

Zaune take a parlourn gidansu tana shan fruit dukta rame ta yankwane Kaman ba Qudsiyah bah, Kaman daga sama taji sallaman Mourad acikin dodon kunnenta, dago kai tayi ta kalleshi , ai wani irin zaro idanuwa tayi cikin rashin yarda da abinda take gani, mikewa tayi dasauri tace"kardai gizon daka Saba yi mun neh.?"

Murmushi yasakar mata tareda riko hannun ta yace"ba gizmo bane Qudsiyah"

"What! !" Tafada dakarfi

"Ke karki tara mun jama'an gidan nan mana" yafada cikin sanyin murya tareda zaunar daita yace

"Uwar kwadayi kawai" Kallonshi takeyi Kaman Wani sabon hallita, hawaye neh suka gangaro mata , hannu yasa ya dauke mata su yace

"yanxu maimakon kibani KO irin ruwan nan ko irin abincin gidan sarautan kun nan saiki sani agaba kina zubomin ruwan hawaye"

Dariya tasake hade da mikewa tace"Kadawo asalinka Sweet, bari nasa a hada maka dining"

Jawota yayi ya zaunar daita yace"Kubar kayanku watarana zanci Amma ba yau bah" Murmushi tayi tace

"ohk" Gyara murya yayi yace

"Nazo neh muyi settling tsakaninmu" Murmushi tayi hawaye na saukowa daga cikin idanuwanta tace

"Are you sure you're the one saying this? Gyada mata kai yayi yana rike hannayenta acikin nashi, rolling din idanuwa tayi tace

"I will think about it" Zaro ido yayi cikin mamakin jin abinda tace shifa yazata yana fadin hakan zata fara tsalle tana murna amma wai zatayi tunani akai.

"Yau Kuma Wani akeja wa aji"yafada yana tab'e baki Gyada tayi tace

"Ai hakan yakamata ana muku"

"Toh kardai aja ajin har ya tsinke soboda kinga Sabin jini masu neman irin na yawa neh dasu"yafada yana dage giranshi daya

"Ai duk yarinyan da tace kai takeso tana tareda babban matsala" shine abinda tafada aranta cos tabbas tasan bayin kanshi bane zuwa wajentan dayayi.

Kallo shi tayi dakyau tace" kun waya neh daita?"

Shafa sumar kanshi yayi yace"Tarame sosai Kaman mai yin ciwo Kuma natambayeta abinda yake damunta she said babu komai I think Zulynah yanzu hankali ya isheta cos she talked maturely and in dah neh ko tunani bazata yi bah zata fadamin but yau tanuna min tagirma"

Runtse idanuwanta tayi sannan tabudesu fess akanshi ai daman tasan ruwa baya tsami banza, ajiyar zuciya tasauke tace" Kasan yanzu da dah ba daya bane"

"Hakane barina koma gida zuwa gobe zandawo naji ko kingama jan ajin" yafada yana mikewa cikin sanyin jiki itama tamike tareda taka mishi....

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

_ABUJA ,NIGERIA_ _BAYAN

SATI DAYA....._

"DanAllah sister kifada min inda take Wlhy bana iya bacci" Iqbal yafada wa Lutfiyah cikin rawar murya

"Ai Kasan bazan maka karya bah nima tin last week data kirani wayanta baikuma tafiya bah" Lutfiyah tafada cikin tausayawa soboda gaskiya yadamu dayawa cos kullum cikin zariya yakeyi agidanta, Gani tayi yana sharar kwalla kafin yamike yamata sai anjima, kallonshi takeyi tana mamakin abinda yafaru har Zuly tafita daga gida har tsawon sati gashi harda baby ahannunta

"Allah sarki Zuly ko Ina kike haka?, Allah ya bayyana mana ku lafiya yakuma tsare ku"tafada Kaman zatayi kuka...

"Wai nikam Maisona akan wannan yarinyar kabi kadamu har haka? Yarinyar da lokacin da baka da lafiya yawon bude ido tawuce abinta shine kawani zo kahana mu sukuni agida." Yusayrah tafada cikin yatsine

"Heartbeat bazaki gane bane, kawai dai kitayani da Addua Allah yasa naganta" yafada cikin sanyin murya Tab'e baki tayi tace

"kodai kafara sonta neh?" Juyowa yayi wajenta dasauri harda rike mata hannu yace" Inaga itama nafara sonta, yanzu dai Azare zan wuce nadubota Allah yasa tana chan"

Duk ruwa da jini dake yawo ajikin Yusayrah yatsaya cak bata ankara bah taji zubowan hawaye daga idanuwanta kafin takaiga yin magana har Iqbal yafice, zaman dirshan tayi akasa tafara rusa kuka Kaman wanda akamawa mutuwa......

_AZARE, BAUCHI NIGERIA_

"Lafiya daiko naganka Kaman mai ciwo? Ina fatan ya'ta na lafiya?"

Arazane yadago yakalli Umma dake zubo mishi tambayoyi cikin rawar murya yace "DanAllah kina nufin Zuly batazo nan bah?"

Mikewa Umma tayi cikin tashin hankali tace"bangane bah, rabon Zuly da nan shine lokacin daka kawota kuma tin wancan satin nake kiran wayanta baya shiga"

Wani irin mugun Sara yaji akanshi before you know it kawai naga Iqbal ya zube kasa asume , bakaramin rudani Umma tashiga bah cikin hanzari ta nufi cikin fada...

"Kuce mata tadawo Wlhy bazan sake bah wannan ma sharrin shedan neh"yafada yana kuka Kaman karamin yaro
Chapter 53 · 0% Book details