← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 98

Sashe 17

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba bata lokaci manya suka shiga maganan atakaice dai auren soyayya sukayi .

Bayan wata daya Rumaisa'u tasamu shigar ciki,sosai aka yi murna.

Lokacin data haihu akayi sa'a ta haife santalelen namiji kuma alokacin mah matar Malam itama takusa haihuwa.

Ranan suna yaro yaci suna IQBAl...

Sosai suke hidima daita dukda ita din ma Ramatu tana da nata shigar cikin amma ko kadan bai bata matsala bah.

Rana daya Allah yayi musu haihuwa inda dukkansu suka haifi mata.

Ana gobe suna Allah yayi wa yar Ramatu rasu wa sosai mutuwar ya jijiga su,duk wanda ya ganta saiya tausayamata(Allah sarki😭😭).

Ranar suna kuma aka rada wa baby ZULFA'U wanda daman shi Ramatu zata sawa yarta...

Zuwa dare kuma Salamatu tafara ciwon ciki abu kamar wasa jiki yaki saketa.

Ramatu kuwa nan da nan bata iya matsawa koda second daya bata barin ta.

Daff da asuba Salamatu ta bawa Ramatu kyautar ZULFA'U halak malak, tafada mata alakawarin auren dake tsakanin Iqbal dakuma Zulfa(Akwai matsala fah🙄)

Sannan takara neman yafiyarta kafin Allah ya amshi ranta Kuka sosai Ramatu tayi lokacin da Salamatu given up ghost😭😭😭(saidai muce Allah yajikan ki)...

Bayan shekara biyu...

Sosai Zulfa tayi wayo har an yayeta mah, son da Umma kemata kuwa ko wa yar cikin ta albarka.

Tafiya ce takama Abubakar da  Abdullahi mijin Rumaisa'u soboda neman su da akeyi agarin Abuja, kasancewan dukkansu sunyi karatu sosai.

Malam ma yaso zuwa amma soboda matsayin dayake dashi na sarkin Azare yasa bai samu zuwa bah...

Tareda iyalensa yatafi  soboda bayanda za'ayi  yabarsu,inda Abubakar yace shi sai an kwan biyu zai taho.

Bayan sati biyu Abubakar yabi bayansu Allah sarki Ashe ajalinshi neh ke kiranshi cos ko rabin hanya basuyi bah Allah yamai hatsarin mota...

Lokacin da labarin mutuwar ta riskesu sun shiga tashin hankali matuka inda Ramatu tadinga sumewa.

Sosai abin yabawa Malam mamaki ace ba mijin ta bane yarasu amma shine take haka nan kuwa yadaura ayan tambaya akan(🙃)...

Sanda tayi wata biyu kafin ta dawo daidai dukda tasan abinda takeyi bashi da kyau amma babu yanda ta iya nan kuwa soyayyar datake mawa Zulfa ya nadu.

```10 yrs later```

Abubuwa da dama sunfaru a shekarun da suka wuce, haryanxu Umma bata sake yin wani cikin bah amma bata wani damu bah.

Sosai take son Zulfa inkaga Zulfa baxaka taba cewan ba ita tahaife ta bah.

Zulfa black beauty ce (we all know that black is beauty) kyakyawa ce sosai,tana son wasa shiyasa ma ko a skull in batayi na karshen aji bah Toh zatayi nabiyu da karshe amma ko akwallar riganta.

Tana da kawa daya tak mai suna Kuwahysa itama din halin su daya amma saidai Kuwah tafi Zuly zafin rai.

Zuly batada kunya kokadan(nace tasha a nono) gata shagwababiya duk abinda takeso tana samu.

Sau da dama Iqbal yakan zo Azare amma abin mamaki ko sunan Zulfa baison ji in yazo cos shi gabadaya bayason bakar mace(Zulyn fah ba wata baka bace).

Duk sanda Zuly taji zai zo har wani farinciki take jinta aciki dukda cewarta karamar yarinya...

Lokacin da Iqbal yazo da Yusayrah amatsayin wanda zai aura sosai Zuly tanuna rashin Jin dadinta cos gabadaya saitaji Yusayrah din bata mata bah...

Wasa sukeyi inda take yin Zane acikin kasa kuma haka kawai takejin wani iri acikin zuciyarta wanda bazatace ga takamemen abinda ke damun ta bah

Wasu arnayen motoci neh suka shararo cikin garinsu...

Zaune yake abayan mota manyan idanunshi arufe ga giran nan cikeda gashi eye lashes dinshi mah abin kallo...

Jefi jefi yake sakin wasu murmushi wanda suka bayyanar da boyayyen sirrin kyaun fuskarshi cos tinda yaji sunan wannan garin ya tsince kanshi cikin farinciki mara misaltuwa.

Motocin da suka gani neh hadasu rugawa kofar fada aguje ita da sauran yaran cos sunsan duk bakin da suka shigo cikin garin da mota Toh lah shakka wajen Malam sukaxo.

Parkawa sukayi sannan wani bature yazo ya bude mishi mota.

Kafar daman shi dayake cikin Christian Louboutin shoe ne yafara musu sallama.

Sosai takalmin yadauki hankalin ta shiyasa ma batasan lokacin daya karasa fitowa bah shikuwa sanda yayi 5mins jinjine da mota gakuma hannu shi dayasa ya rike saitin zuciyarshi...

Zaro Ido tayi ganin balarabe agaban su azuciyarta tana fadin(dama akwai wanda suka fi Iqbal kyau neh)...

Shikuwa tinda aka bude mishi kofa yahango ta .Wani mashi neh ya kaiwa kahon zuciyarshi wani mugun soka shiyasa ma bai fito dawuri bah...

Gabanta yanufa straight tareda tsugunawa inda duk mutanen wajen sukayi tsit suna binshi dana mujiya...

Hannun shi yasa yarufe mata bakin da lokacin harya fara tsiyayan yawu.

Ganin shi agaban ta bakaramin mamaki yabata bah,har zata fara mai rashin kunya wanda yayi daidai da dauko handki dinshi dayayi...

Idanunwansu na haduwa tanemi duk rashin kunyan ta tarasa soboda mugun kwarjinin daya mata.

Shikam wani irin shock yadinga,cikin sauri ya janye kwayar idonshi daga cikin nata sannan yasaki wani murmushin daya fito daga kasan zuciyarshi.

Handki din hannu shi yasa yagoge mata inda yawu yabata sannan ya miyarda handki din aljihun shi.

Hura mata idon dayayi neh yasata sunkuyar da kanta tareda sakin murmushi.

"Kamin kyau dan gaye, Hibba  kizo kice mai yamin kyau da turanci kuma ni inasonshi" tafada da karfi cos  hibban nata bayan ta neh kuma duk azatonta baya Jin hausa.

Wani murmushi neh yasake subuce mai Jin abinda tace amma abinda Hibba tace neh yasa murmushin shi bace wa

"Ke wace irin jaka ce wai??daman taya za'ayi ki san miye zaki fada bayan kwakwalwar kifi ce gareki ko kuma ance miki wannan sa'an ki neh,toh in fada miki ko mafarki kikeyi gwanda ki farfado soboda wannan balaraben yamiki nisa" shine abinda Hibba tace

"Daga kawai tace kizo kimai turanci shine zakici mata fuska??" Kuwah tafada cikin bacin rai.

Kallon shi yamarga Zulyn datace"danAllah ba dan halina bah kitayani fada mai karya tafi"

Ganin yanda Hibba keyi neh yasashi yin magana daman kuma baiyi niya bah amma kuma ahalin yanzu kafarshi tagama yin tsami.

"Nima inasonki" sukaji daddadar muryan shi da fada,ai daskarewa suka yi suna kallonshi da mamaki...

Wata murmushi Zuly tasake Jin abinda yace

Mikewa yayi hankali sannan yace"miye sunan ki??"

*"ZULFA!!!"*tafada cikin hanzari cos taga alamun tafiya yake shirin yi.

Juyowa yayi still murmushi asamar afuskarshi sannan yace"daga yau kintashi daga *ZULFA* kin koma *ZULYN MOUR..*"

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 30*

Juyowa yayi still murmushi asamar afuskarshi sannan yace"daga yau kintashi daga *ZULFA* kin koma *ZULYN MOURAD*" yana gama fadin hakan yayi gaba wanda baiso hakan ta faru bah cos bai gaji da ganinta bah amma ya yaiya??.

Babu abin da take maimaitawa azuciyarta sai Zulyn Mourad wata irin murmushi take sake tana maijin ta acikin wani yanayi na daban dukda karancin shekarun ta.

Gwalo tayi mawa Hibba sannan tace"ya kika gani ??kinki yin magana da turanci ashe dai shi din ma yanajin hausa" nan kuwa kowa yafara mawa Hibba dariya

"Wata dai taji kunya ahir dinki, oh daman wace kunya ce dake?? Amma gaskiya kin bada mata dayawa"Hibba tafada cikin bacin rai

Gwalo tasake mata sannan tace "wannan kuma ba damuwan ki bane tinda kinga shidin ma yace yana Sona"
Ai nan yara suka sake sa dariya sosai Hibba taji haushi ai basu hankara bah sukaga Hibba ta cakumo wuyar riganta.

Kyakyawan riko tayi wa Zulfa inda yara sai janye ta suke ai basu hankara bah sukaji Karar parkewan abu ashe Hibba ce ta parkawa Zulfa riga.

Nan kuwa kirjinta ya bayyana  Hibba batayi wata wata bah ta gantsara mata cizo asamar nono dayake yafara fitowa...

Wata Karar tafasa wanda ya haddasawa Mourad dake gaban mai martaba sarkin Azare wata faduwar gaba cikin sauri ya dafe saitin zuciyarshi.

"Lafiya dai koh" Malam ya tambaya

"Ina zuwa" yafada tareda ficewa...

Hango taron yara yayi ana rabon fada cikin sasarfa yakarasa wajen.

Daidai lokacin da Umma tafito daga cikin fada da hijabi a baibai.

Abinda yagani neh yasa ranshi mumunar baci ai baisan lokacin daya finciko Hibba bah.

Wata zazzafan mari ya kife ta dashi wanda yayi daidai da isowar Umma wajen.

Cikin sauri tadago Zulfa dake tsugune tana kuka.

Tana ganin Umma ta rungumeta tsam tareda sakin wata irin kara sanadiyar kirjin ta daya gogu ajikin Umma.

Arikice ya juyo wajenta daniyar yakamota amma ganin Umma yasashi dakatawa.

Idanunshi sunyi jawur ga jijiyoyin kanshi duk sun fito.

Ganin jini ajikin khimar din Umma yasashi sake birkicewa,ai wani hauri yakuma kaimata.

Marin dayakuma kaimata neh yasata fashewa da kuka ga bakinta daya fara jini dalilin fitan da hakorin ta ...

Lullube Zulfa akayi sannan aka wuce daita cikin fada...

Wata zazzafan zazzabi neh yarufe ta,cikin nutsuwa Umma ta goge mata saman nonon ta dayake fitar da jini...

Komawa yayi cikin fada din hoping zai ganta amma wayam baigan inda suka shige bah sosai yaji ba dadi haka yakoma wajen maigari suka cigaba da tataunawa akan abinda yazo soboda shi .

Ganin da maigari yayi kaman hankalin Mourad bai wajen yasashi sallamansu  akan suje su huta zuwa gobe zasu cigaba...

Fita yayi waje nan ya hango Kuwah ba bata lokaci takira ta"please ina neh gidan su Zulyn Mourad??"

Sunan tadinga jujuyawa acikin kwanyan ta sai alokacin tatina yace daga yau sunan kawar ta ya tashi daga Zulfa yakoma Zulyn Mourad.

Murmushi tasake sannan tace"daman wajenta zanje "

"Yauwa kaini na gaishe ta"yafada cikin hanzari

Jerawa sukayi sannan suka fara tafiya batareda kowannen su yasake magana bah.

Sosai takejin dadi azuciyarta wai gata ga balarabe suna tafiya.

Tsayar dashi tayi sannan tamawa Umma magana akan tana tareda wani.

Gyarawa Zulfa kwanciya akayi sannan tace ashigo dashi.

Da sallama abakin shi tashigo Umma ta amsa ta mamakin aina suka samo balarabe.

Gaisheta yayi cikin harshen hausa nan Umma tasake jikinta ta amsa mai cos haka kawai taji ya kwanta mata.

"Bari naje gidansu wanda takeson Kashe min y'a" tafada tareda ficewa daga dakin.

Cikin sauri ya matsa kusa da ita tareda dafa ta.

Ahankali take bude idonta dasuka rine  tasauke su akanshi

"Zulynah san...

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 11:59] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 31*

"Zulynah sannu koh"yafada cikin kulawa

Dukda tana Jin zafi amma haka tasakar mai da murmushin daya kusan shidar dashi.
Chapter 17 · 0% Book details