← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 98

Sashe 74

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mumyn Izma wa ceh ga Maman su Momina! A saudiya suke dazama soboda transfern da aka mawa mijinta zuwa wajen daga wajen aiki, sunada yara uku. Biyu maza dakuma mace Guda daya!....

            ★★★★★★

"Wai nikam bazaku bar tafiyan nan harsai ta gama warkewa bah!? "

Ammi ta tambayi su Mourad dasukayi da-daya akan kujera "Kaii Ammi Allah tawarke fah tinda kikaga an sallamemu daga asibiti"

Mourad yabata amsa cikin sanyin murya Dage kafadarta tayi tace"Tohh Allah yataimaka!! "

"Ameen Ammi! Inace baki manta gobe dasafe jirgin ku zai daga bah? "

"Taya za'ayi namanta!"tafada tana murmushi Shima murmushin yasake yana shafa sumar kanshi, chan kuma yakai dubanshi zuwaga Fakhih dake ta faman chatting sai murmushi yake jifan Maram dake zaune agabanshi dashi da alamun da ita yake chatting din!

Gyaran murya yayi tareda kallon Maram yace "Maram Ina fatan kun gama harhada kayayyakinku kinga saura mintuna talatin lokacin tafiyarmu yayi? "

Dan zaro idanuwa tayi tana kallon Fakhih daya zuba mata na mujiya kaman yasamu TV, Ganin yanda tayi neh yasashi sanin cewan bata gama bah!

"Toh atashi aje kar lokaci yagama kurewa" Mikewa tayi tafara tafiya kaman wacce kwai yafashe mata aciki,

"Soulmate jirani mana muje nataya ki"Fakhih shima yafada yana mikewa, ko kallon da Ammi dakuma Mourad ke jifanshi dashi bai kula bah yawuce abinshi

Dariya Fakhiha tafashe dashi ganin yanda Fakhih yake wani bouncing kaman wani babban mutum, suna hada idanuwa da Mourad tasake fashewa dawani dariyan tana jinjina wa yen uwanta soboda kowannesu da nasu salon soyayyan

"Gaskiya yakamata aje aduba ki soboda nasan tabbas ba kalau bah!"yafada tareda nufan kofan dake rufe Cikin zolaya Fakhiha tace

"Yaya wanka fah takeyi! " Harara ya gallara mata tareda shigewa abinshi ko arzikin knocking kofan baisamu bah.

Yana shiga yaga har lokacin batafito bah wanda yanzu two hours kenan da shigarta in bawai ya manta bah, sunanta yafara Kira yana dosan kofar bayan gidan, ji yayi gabanshi yafara dukan uku-uku dasauri yabude kofan

Turus yatsaya cikin mamaki ganinta acikin jacuzzi tub idanuwanta arufe da alamun bacci neh ma yadauketa ga wireless headphone akanta tana jin waka

Karasawa yayi wajenta tareda zama akan steps din shiga cikin jacuzzi din yana kare mata kallo, sake mikewa yayi ya cire jallabiyan jikinshi yarage daga shi sai boxer, six packs din shin nan MashaAllah gakuma Z tattoo din kirjinshi yadada yin baki kaman yashafa mai abu

Komawa wajenta yayi yadan dagota daka kwancen datake ya matso daita jikinshi sosai har gadon bayanta mai jikan kumfa nataba kirjinshi

Runtse idanuwanshi yayi dalilin jin jikakiyar fatar jikinta a nashi, bude idanun yayi dakyar tareda daukan Soso, wanketa yayi tass ahakan yanayi yana tabe-tabe kuma still bata farka bah amma tanadan jujuya wa

Danna wajen zubda ruwan yayi yasake tarar wani sabo yadauraye mata jikinta dashi kafin daga karshe yacire headphone din daga kunnenta yasa anashi kunnen donjin miye takeji.

Murmushi yasake yana kallon fuskarta kafin ya ajiye agefe sannan yahau dauraye mata jikinta, yana gamawa yasab'ata akafada yayi cikin daki daita Akan gado ya ajiyeta tashinta yasoma yi bayan ya lulubemata jiki da towel, saita yi kaman zata farka saitakuma komawa bacci ,mamaki neh yakamashi ganin irin baccin datakeyi haka kaman wacce tasha kwaya Kyaleta yayi tareda komawa wajen dressing mirror dauko man shafawanta! karaf idanuwanshi yasauka akan kwalban ruwan allura dakuma allura agefenshi, dakatawa yayi tareda daukan kwalban yana kallo cikin mamaki da firgici

"_Erthropoietin (EPO)_ " Yafurta asarari cikin kidima, kallonshi yamiyar ga Zuly dake ta sharar baccinta, ajiye kwalban yayi tareda komawa wajenta dasauri yana mai kiran sunanta a hargitse har hawaye sun wanke mai fuska, sanin bazata amsa bane yasashi mikewa tareda shigewa cikin toilet da gudu, Rigar daya dauko ma abaibai yasashi, jikinshi nawani irin rawa yadauki kwalban dakuma Syringe yafice a sittin..

Mikewa sukayi dasauri jin yanda aka bude kofa, hannu Fakhiha tasa tarufe baki ganin yanda yayanta ya jike da hawaye

Fakhih da basu jima da zama bah yace" miye fa... " Shiru yayi ganin yanda yafice kaman walkiya

"kabishi!" Ammi tafada tareda nufan dakin da yafito cikin sauri, sauran matan ma sukabi bayan Ammi cikin sanyin jiki gabansu nadukan tara-tara...

Yana fita daga cikin gidan ya warci key a hannun driver!

Yana bude motan Fakhih ma ya bude dayan barin yazauna "Miye faru neh wai yaya"

Fakhih yatambaya cikin sanyin murya, ko iskan da ya kwaso shi Mourad bai shaka bah yacigaba da tuki abinshi har lokacin kuma bai daina hawaye bah, shiru kawai Fakhih yayi tareda zubawa sarautar Allah namujiya...

Kuka Mourad yafashe dashi lokacin dayagama jin bayanan da likita yayi dukda daman yasan maganin miye amma bai gasgata bah soboda yana tunanin hasasshen shi ba gaskiya bane, shima Fakhih jikinshi yaji yayi sanyi, hannu yasa yana buga bayan Mourad alaman rarrashi

Shiru yayi tareda mikewa yana share hawayen fuskarshi da hannunshi sannan yadauki maganin daya taho dashi yafice abinshi batareda yamawa kowa magana bah

Fakhih neh ma yamawa likitan godiya tareda marawa Mourad baya dasauri, driver sit yashiga yazauna shikuma Mourad yakoma gefenshi still yana Kuka...

Kanshi yakwantar akan cinyar Ammi sannan yafara rairo sabon Kuka wanda ya jefa zuciyarsu cikin zulumi, yana ganin Umma tashigo ya rarrafa zuwa gabanta yana mika mata kwalban daya damke a hannunshi cikin muryar Kuka sosai yace....

*DanAllah wattadians ina bukatan Followers dakuma votes🙏*

#team Zuly
#team Mom

*Vote,comment&share*

*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 103*

"Ke kadai zakimin cikakkiyar bayani akan wannan"

Wani irin yawu mai daci ta hadiye cikin fargaban yanda zai karbi zancen

"Kifadamin mana! It's about really rayuwar zulynah DanAllah karki boyemin komai"yafada cikin sanyin murya yana kuma share hawayen fuskarshi

Atakaice tace"da koda daya take rayuwa!" Cikin firgici suke kallonta gaban dukkansu na dukan goma-goma, cikin rawar murya yake fadin

"lafiyanta lau kafin mu rabu how comes? "

"Erh bawai ciwo tayi bah! Asalima wa iqbal tabayar"Umma tafada ahankali

Dum yaji gabanshi yafadi, gigirza Kanshi yafarayi cikin rashin yarda da abinda Umma tace

Gyada musu kai Umma tayi alaman haka abinda yake, runtse idanuwa yayi tareda fashewa da kukan dayafi nada har shesheka yakeyi...

Dishi dishi tafara gani kasancewan bawai maganin yasaketa bane,  tin tanajin kukanshi kasa-kasa hartafara jinshi cikin tsakiyar kanta, tarr taware idanuwanta akan POP din dakin

Mamaki neh yakamata ganinta akan gado bayan tasan wanka tashigayi a toilet, sautin kukanshi dayakaru neh ya hankarar da ita juyar da kanta tayi idanuwanta yasauka akan Mourad dake ta rusa Kuka kaman ammai rasuwa

Mikewa zaune tayi tana binsu da kallo daya bayan daya cikin son gano waye yarage acikinsu da baya wajan,  gani tayi babu wanda ya ragu acikinsu

Cikin muryar wacce ta tashi daga bacci tace"Yay Mou dina!! "

Tsayawa yayi da kukanshi tareda dagowa yana kallonta kaman wanda yaga sabuwar hallita, sauran ma suka kalleta! 

Cikin sauri Fakhih yafita daga dakin soboda har lokacin towel neh ajikinta kuma babu wanda ya lura da hakan sai yanzu! 

Sauran ma ficewa sukayi cikin sanyin jiki inda aka barta da Mourad dake zaune kaman wani soko!

Hannu ta mika mai alaman yataho gareta ganin yanda ya kafeta da idanuwa har lokacin kuma bai daina hawaye bah!

Da rarrafe yakarasa wajenta, yana isa jikin gadon yamike yazauna tareda kifa Kanshi akan cinyarta yacewa"why! Why!!!"

Shafa kanshi tayi cikin son yadaina kukanda yakeyi gashi gabadaya tunaninta ya cunkushe! 

Babu abinda take son sani yanzu inba dalilin kukan dayakeyi bah!

"Plsss... "tafada ahankali kaman mai jin bacci idanuwanta nakuma lumshuwa alamun fah haryanzu tana jin baccin

Tashi yayi daga kan cinyarta tareda damka mata kwalban ahannunta yana kallon kwayar idanuwanta daitama shi take kallo, Idanuwanta tasaukar ta kalli abinda ya damka mata, kallonshi tasake yi sannan tasaki murmushi tareda share mai hawayenshi tana fadin

"Akan wannan Kuka?I gave him willingly kuma ai taimakon rai nayi so kadaina bata hawayenka and kuma yadade gashi bana ciwo tinda inashan medications dina akan lokaci!"

Da dunbin mamaki yake kallonta soboda gabadaya tunaninshi yafi bashi cewan tursasa ta yayi kafin tabashi!

Ashe abin bahaka bane ita tabashi da kanta! Fuskarshi takama tana kallon kwayar idanuwanshi tace"abinda nayi ya dace kuwa? "

Kawar dakanshi yayi tareda girgiza Kanshi alaman bai dace bah, sake juyowa da fuskarshi tayi tareda turo bakinta tace"miyesa bai dace bah bayan kasan abu mai kyau neh taimakon wanda yake butakan taimako indai kanada halin yin hakan! So why kake cewan bai dace bah? "

"You should have buy it tinda ana siyarwa"yafada cikin sanyin murya

Dan zaro idanuwa tayi tace"karka manta fah shi miji na neh! Taya za'ayi ace inada abinda ake bukata kuma naki bayarwa kuma yana matsayin mijina! "

Mikewa yafara kokarin yi soboda bayason kishi ya rufe mai ido har yayi abinda ba daidai bah don inhar tacigaba da furta kalman Miji baisan abinda zai biyo baya bah

Gam tarike hannunshi tana mai kallon mamaki "Sake ni kishirya lokaci natafiya"yafada atakaice, sakin hannunshi tayi cikin sanyin jiki tareda sauka daga kan gadon shikuma yayi ficewarshi batareda ya sake waiwayan ta bah!....

Lumshe idanuwanta tayi cikin rashin jin dadi ganin yanda Mourad yake wani sha mata kamshi kaman baisanta bah, bude idanuwanta tayi tareda lekawa bayan sit tana kallon Mourad daya wani sa headphone akunne jefi-jefi kuma yakan saki tsaki.

Hawayen dasuka ciko mata tashare tareda komawa ta zauna dakyau sannan tadauki magazine tafara bi dukda bawai fahimtar abubuwan datake kallo takeyi bah

Maram data gama kumburewa kaman dough din dayaji yeast ceh ta taba Zuly cikin jin haushi

Sauke magazine din tayi ta miyar da hankalinta wajenta "Wai nikam dakuka samu matsala da naki mijin  miyesa naji bashi hakuri tinda wuri ba! "Maram tafada kaman zatayi Kuka, da mamaki take kallon Maram, chan tace

"shine yace miki mun samu matsala? "

"Toh baga alamu sun nuna bah! Gashi kin ja ya rabani zama da mijina! "takarasa cikin rawar murya

"Toh kiyi hakuri"Zuly tafada cikin sanyin murya

Atakaice tace"Wa shi zaki bada hakuri bawani bah! "

Gyada kai kawai Zuly tayi tana searching laifin da tamawa Mourad din kaman yanda Maram tafada Sake juyawa tayi taga yamike, cikin sauri ta cire seatbelt tareda mikewa tabi bayanshi..

"This way Ma'am"wata hostess tafada tana nuna mata wani hanya dabam ko kulata batayi bah tashige inda taga ansa _gents_ Wanda tasan nan neh Mourad yashiga
Chapter 74 · 0% Book details