← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 98

Sashe 37

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai wasu taurari tafara gani kafin taji ta bugi  jikin Wani abu jikake tarwatsewan abu taasssss karar fashewan gaban glass din mota

Wani irin ihu su Yusayrah suka kwala Dalilin ganin hatsarin da Zuly tayi, fitowanshi kenan yayi turus yana computing abinda yake gani da kwakwalwar shi domin komai  nashi tsayawa yayi cakk...

Wata kyakyawan matashiya wanda bazata wuce 23 bah tafito atsorace da ganin abinda ya faru in a blink of an eye, kukanta neh  yadawo dashi cikin sauri yakarasa wajen Zuly  dake yashe asaman mota , cakk yadauke ta daga saman mota  kaman baby yayi ta inda motoci suke wucewa

Cikin sa'a ya hadu da cab wanda yazo ajiye passenger ai duruwa yayi cikin cab din jikinshi na  Wani irin rawa, Yusayrah neh ta koma cikin gida tadauko motanta,  daidai wajen su Nihal ta tsaya tace musu su shigo dukda bata San takamamen asibitin dasuka nufa bah,

Shiga sukayi inda matashiyan tadinga kuka tsoron ta daya kar ace ta kashe yar mutane...

_Hospital_

KO sallaman mai cab baiyi bah yayi cikin asibiti da gudu, cikin sauri nurses suka tashi ganin an kawo emergency,  ganin yanayin condition dinta neh yasa sukace yaje ya police station, Suna cikin maganan neh su Yusayrah suka shigo arikice

Matan neh ari waya takira wata number tareda mikawa doctor,  bayani aka mawa doctor din tukunna suka shiga cikin  emergency daita...

Sun jima sosai kafin suka fito  daita zuwa resting room, kiransu doctor  yayi akan su biyoshi office  din shi...

"Sannu koh" doctor yafada

Gyada kai kawai sukayi Suna kallon shi

Ajiyar zuciya yasauke kafin ya miyarda hankalin  shi wajen Iqbal yace " zan iya Sanin dangantakan Ku?"

Ba tsoron Allah Iqbal yace " yar aikin mu ceh "

Sororo su Yusayrah sukayi Suna kallon shi da mamaki, kallonsu matan tayi tana kwankwanto akan abinda yafada Kuma sosai tayi sensing cewan karya yakeyi muryan Doctor sukaji yace

"Anyi nasarar daidaita numfashinta dakyar cos abinda muka lura dashi shine ita yarinyan bata son rayuwa cos she's not really responding to treatment and Kuma tana da hawan jini and zuciyarta yayi weak am afraid she developes a heart attack

"What???" Dukkansu suka furta atare

Gyada kai doctor yayi yace"am sorry to say but I think yarinyan bata jin dadin zama daku kokuma akwai abinda yake damunta irin sosai dinnan and zanyi advising naku akan Ku miyarda ita  inda kuka dauketa cos she's  dying from inside  and it's very dangerous soboda karancin shekarun ta"

Banda innalillahi babu abinda Iqbal yake fadi azuciyarshi, jikinshi yAyi Sanyi sosai cos yasan koda akwai  abinda yake damunta to shine he knows he has  tormented her a lot, lumshe ido  yayi yana kallon yanda idonta yakoma Kaman wata scary cat..

Matan data buge Zuly kuwa banda kuka babu abinda takeyi, she really pity the girl and azuciyarta  banda tsinewa su Yusayrah  babu abinda takeyi  cos gani take su suka korota daga cikin gidan har ta samu bugeta,  Amma Alhmdllh tinda yar mutane bata mutu a hannun ta bah,

Gyaran murya  tayi tace "can we see her?"

"Sure" bata jira cewansu bah tayi gaba abinta, tana fita ta kalli mijinta a reception, karasowa wajenta yayi yana bin jikinta da kallo yace" _my Lut_ inafatan bakiji ciwo bah?"

Girgiza kai tayi tareda Jan hannun shi zuwa dakin da aka kwantar da Zuly, kuka neh ya kufce mata ganin yanda aka nada wa Zuly rawani da bandage hancinta manne da abin oxygen( am sorry namanta sunan abin😁) , rike mijinta tayi tace" kaga yanda na  miyarda yar mutane koh"

Girgiza mata kai yayi yace"Don't  cry my Lut everything  will be ok"

Sakin shi tayi tareda karasawa wajen gadon tana karewa mata kallo, the girl looks so innocent, rike fuskanta tayi tayi  bending daidai wajen kunne ta tayi mata Addua tareda mikewa...

Da sallama suka shigo cikin dakin duk jikinsu asanyaye wajen gadon suka karaso Suna binta da ido cikin tausayinta ganin yanda lokaci daya kamanin ta suka sauya  cos Sun tabbata baza'a rasa scars ba afuskarta ga lips nata yayi Wani irin Jah...

"Kuyi hakuri  akan abinda yafaru I swear to Allah she bumped on me" Matan tafada wa Iqbal cikin sanyin murya

Girgiza kai Iqbal yayi yace" karki damu haka Allah ya kaddara"

Gyada kai tayi tace" zan tafi but insha Allah zanzo gobe Allah ya kiyaye na  gaba"

"AMEEN" suka furta Kusan atare , musabaha Iqbal da mijin matan sukayi sannan suka fice...

'''3 DAYS LATER...'''

Acikin kwana ukun nan da Zuly  tayi akwance batareda ta farka bah amma an cire mata bandage din fuskar ta sosai suka shiga damuwa musamman Iqbal da wannan matan da kullum saitazo Kuma tinda safe idan tazo takankai dare bata tafi bah ga hidimomin datakeyi...

Yanxu mah zaune suke acikin ward din duk sunyi zuru zuru, hardan  rama Iqbal yayi Kuma har lokacin bai fada wa mutanen gida bah wasu Kuwah kawai yafada wa,

Matan neh ta lura da motsin ta cikin sauri ta tashi takarasa wajenta tana observing dinta

"Ta farka" tafada tana mai gyara drip din hannun Zuly  ganin bakinta na  motsi neh yasa ta cire mata oxygen din, daidai wajen bakinta ta kai kunnenta inda taji tana fadin

"Wlhy bazan yarda bah sai nafada wa Malam abinda kake min"

"Ku kira doctor mana" matan tafada daidai ta Mike, dasauri Iqbal yafita, da ido tabishi tana mamakin ace akan yar aiki yayi wannan raman

"Something is fishy" tafada Chan Kasan makoshinta tana kallon Yusayrah  da gefen ido,miyarda dubanta tayi wajen Zuly taga har yanzu magana takeyi girgiza kanta tayi tace

"Miye sunan ta?"

"Zulfa" tafada daidai shigowan su Doctor

Ahankali takirata Amma ko amsawa batayi balle ta bude ido, doctorn neh ya mawa Zuly allura cos inta cigaba da magana haka toh akwai matsala...

Kuwah neh tashigo da basket ahannun ta da sallama alokacin kuma Iqbal yafita amsawa sukayi atare inda ta gaishe su tareda yin wajen Zuly ,

"Ta tashi amma bata bude ido bah dukda kiran sunanta da akeyi" matan tafada cikin sanyin murya cos she getting fed up, matsa mata kadan Matan tayi Kuwah tace

"Zulyn Mourad" ai sai tar Zuly ta bude idonta, sosai matan tasha mamaki yanda akayi ta bude ido daga kiranta sau daya takk, murmushi Kuwah tayi tareda rike hannun ta

Lumshe ido tasakeyi hawaye na  gangarowa daga idonta, tayata sukayi tamike zaune duk jikinta ciwo,

"Zan Shiga toilet" tafada bayan ta share hawayen ta, kamata Kuwah tayi takaita toilet, fitsari kawai tayi da alwala tafito inda bakaramin zafi taji bah soboda Ciwon fuskarta, a zaune mah tayi sallahn cos sosai takejin  gajiya from no where...

"Take me away from here Kuwahnah" tafada tana sa kanta asaman cinyan Kuwah Dan tsaki Kuwah taja tace

"Matsala ta dake kenan kullum adinga maimaita miki magana daya" tafada Kaman bada mara lafiya take magana bah

"Kibita ahankali mana" matan tafada

"Haba  ace yarinyan nan tasan banjin turanci amma tadinga min"

"Toh yi hakuri Kisan  bata jin dadi Kuma cemiki tayi ki tafi daita daga nan"

"Aiho sai yanxu naji zance"

Shigowan Iqbal neh yakatse su, kallon shi Zuly tayi tace"kabani wayana"

Karasowa yayi wajenta cikin sanyin murya yace" we can settle this?

"Wlhy nikam sai kaban phone dina" tafada cikin son yin kuka cikin sauri yaciro wayan daga aljihun shi yamika mata,

Kallon wayan matan tayi tunani take kila she's daydreaming, mintsin kanta tayi taga it's the reality, irin wannan neh wayan Yar aiki while masu gidan Suna rike da wayan da baikai ko rabin rabin na yar aikinsu bah,

"Am calling Malam right away" tafada babu alaman wasa a fuskar ta,

"Am really sorry zuly" yafada sounding guilty

Dakatawa tayi tana kallon shi, kankance idonta tayi tace"repeat abinda kace"

Cije lip dinshi yayi yace" I said am really sorry"

Yar murmushi tayi cos tinda take dashi bai taba mata magana sounding so polite lyk today before, sake tamke fuska tayi tafara danna wayanta tace" yau zamuyi ending din komai"

Kallonta sukeyi gaban Iqbal na Wani irin bugu ai bai gama tsinkewa bah sai sanda yaji tace.....

_toh team Mourad sai afara Addua😁😁_

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*
*ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 59*

Kallonta sukeyi gaban Iqbal na  Wani irin bugu ai bai gama tsinkewa bah sai sanda yaji tace" Umma nah Ina Malam"

Daga chan bangaren Umma tace" haba yar Umma ko Sallama babu"

Turo baki tayi hawaye na taruwa a idonta cikin rawan murya tayi sallama nan da nan hankalin Umman ta yatashi dasauri tace" yar Umma miye ke damunki?"

Kuka tafashe dashi tace" nidai ki kaiwa Malam wayan I need to speak with him"

"Toh daina kuka zan kaimishi yanxu"

Jan hanci tayi tana hauna wa Iqbal harara tace" nagode kiyi sauri"

Rike hannun ta Iqbal yayi ta fixge cikin sanyin murya yace"pls kiyi hakuri mana , we can settle this without involving anyone"

"Yeah Zuly we can settle it" harara ta jefa wa Yusayrah datayi magana kafin tace

"Babu Wani zancen sasantawa"

"Excuse me but I think ki bari Ku fahimce juna dukda bansan laifin suka miki bah" matan tayi interrupting

Kallon fuskan matan sukayi Zuly tace"who are you"

Gyaran murya matan tayi tace" sorry banyi introducing kai na bah sunana Lutfiyah, nayi karatuna a baze university inda na karanta medicine amma kuma bana aiki babana shine commissioner of police and unfortunately na fito daga gida ranar sai tsautsayi yasa na buge ki am so sorry"takarashe maganan ta cikin nuna rashin jin dadi

Gyada kai tayi zatayi magana kenan wayanta yadauki Kara , gabansu neh ya yanke ya fadi, sanda wayan ya katse kafin tasake danna kiran while dukkansu Suna mata kallo Dan Allah kiyi hakuri

"Malam baya nan fah sunje Wani daurin aure" Umma tafada daga dayan bangaren

Ajiyar zuciya Zuly tasauke hawaye nasake zubowa daga idonta ahankali tace" shikenan kawai kibarshi"

"Toh ni kifada min abinda yake faruwa koh yasake sakin ki neh?"

"A'a Umma nah Ammi takiraki kuwa? Daman inason naje na dubo Yay Mou neh shine nakeson neman izini daga wajen Malam?"

Ajiyar zuciya suka sauke alokaci daya ganin yanda ta shararo karya,

"No nasan yana lafiya Kuma zaizo ki kwantar da hankalin ki kinji yar Umma?

Gyada kai kawai tayi kafin tace "toh Umma nah Kuma kitayani da Addua Kema "
Chapter 37 · 0% Book details