← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 98

Sashe 39

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cire veil din tayi cikin cracking Voice tace" bari nadauko abin gogewa acikin gida"

Wani irin kallon kinma isa yamata cikin daga murya yace "Malam Saleh akawo mana ruwa"

Ganin tana Shirin barin wajen yasashi dada fixgota yace"ubanwa yabaki izinin tafiya?"

Share hawayenta tayi wasu na zubowa tace"ce maka nayi zan dauko abinda zan goge"

Nuna hannun ta yayi yace"wanna tsumman fah?"

Runtsa idanunta  tayi domin kalman tsumma bakaramin bakanta ranta yayi bah cije  lip dinta tayi cikin dacin rai tace "ba tsumma bane cos abinda xa'a iya siya a million ya wuce akirashi da tsumma"

Buge bakinta yayi yace "Wlhy Nikuma nace dashi zaki goge in ba haka bah abakin igiyan aurenki daya"

Cakk ta kukanta yadauke gabanta na faduwa tana mai mamakin halinshi ace mutum kalman saki bai mawa bakinshi Wuyan furtawa, cikin dakiya tace"toh sai miye? Nace sai miye yau kafara neh uhmm?

Rike cikin ta tayi dalilin murdawan dayayi "arrrghh" tafada cikin ciwo tareda zubewa akan guiwar ta Amma Iqbal  ko tsayawa dubata baiyi bah  yayi gaba abinshi,

Baba maigadi da tunda taji Iqbal yace abakin igiyan aurenta guda daya yatsaya cakk cikin mamaki,  ahankali  ya karaso wajenta, cikin  tausasawa yakirata, dagowa tayi ta kalleshi da idanuwanta dasuka rine,

"Kiyi hakuri ki goge dashi"yafada in a pleading tune, girgiza kai tayi tace

"Bazan iya bah Baba"

"Soboda miye?"

"Baba wannan ba tsumma bace,  wannan gyalen yana da matukar muhimmanci agareni"

"Kina nufin kinfison igiyan aurenki daya ya mutu soboda gyalen dazaki iya siyan dubban su? Shin kinsan adadin matan dasuke neman mijin aure idonsu arufe, wanda  ace basuki ace koda kuturu, makaho kokuma kurma suka samu bah, ke fah Allah yabaki miji  nagani nafada Amma kike amfani da daman ki.

Shin kinsan miye Zawarci dakike Shirin shiga sawun su?hmmm na  tabbata bakisani bah ji kawai kikeyi Amma bari nafada miki abu kadan danasani akan Zawarci: Shi dai zawarci a fahimta ta kaman neman aure ne amma a nan ga mace da ta taba aure Kuma  Illar shi shine zaurawa da yawa ana complain kan cewa basu da hakuri wajen wajen jure zaman rashin aure wanda hakan kesa ta bada kanta ga namiji a sauwake ko kuma gaggawan son yin aure kuma tabbas zaurawa na fiskantar kalubale cos most maza na ganin su kamar yanzu darajarta ya ragu kind of cheaper dan idan tana budurwa...

"Narokeki da ki bar komai ahannu Allah kikuma dagewa da Addua" yafada mikewa daga tsugunnen dayake, Jan majina tayi cikin kuka cos maganar shi ya ratsa ta cikin dashahiyar murya tace

"Nagode sosai Allah ya biya ka da gidan Aljanna" Murmushi kurum yayi yana Ameen acikin zuciyar

"Ga ruwa" yafada yana matsar da ruwan tajikin mota, gyada kai tayi tamike daga zaunen datake da kyar soboda rikewa da cikinta yayi

Tana goge wa da Favourite veil dinta tana kuka babu abinda take tunawa sai randa tafara period: zaune take akan cinyarshi ta kwanta ajikin shi tana faman kuka soboda Ciwon cikin daya addabeta, shikuwa yawani rude yana mata sannu yake mata cikin muryan tausasawa cos baiki ace yadauke Ciwon daga jikinta ya miyar jikinshi

Dagowa tayi daga jikinshi ta kalleshi da jajayen idanunta tace"Yay Mou dina  Wani abu nakeji  ajikina"

"Kaman miye?" Yatambaye ta sounding so carefree Kaman baisan jikinshi yadade da baci da jinin period dinta bah

Mikewa tayi cikin zare ido ta taba behind tace "Kaman nayi fitsari"

Dariyan da baishirya yinshi bane ya kufce mishi ganin yanda takeyi Kaman wacce taci kudin aika, turo bakinta tayi cikin shagwaba tace" Miye neh kake Wani da..."

Maganar ta makale mata neh daidai lokacin da idonta yasauka akan gutun wandon shi dakuma fararen cinyoyin shi mai cike da bakaken gashi wanda ya baci da jini dayawa Kaman an yanka kaza,  zaro ido tayi cikin tsananin firgita tana taba Kafan nashi da akwai jini da hannu daya , Sam bata lura da jini dayake hannun ta dalilin shafo behind dinta  datayi ta dora hannun afuskar shi cikin tsananin kidima tace

"Miye ke damunka Yay Mou  dina?  Yaushe kaji ciwo? Miye ya jimaka ciwo?baka jin zafi n..."yatsan shi yadora akan lips dinta yace

"Shiiish, calm down Zulynah"

Girgixa kai tafara tace" taya zakace min inyi  calm down  bayan you're not ok?, tashi muje hospital cos bazan iya treating dinka haka bah"

Dariya yayi ganin yanda ta Wani damu kanta akan abinda batasan daga jikinta yafito bah, cikin rashin jin kyamarta yashafo behind dinta sannan cikin Zolaya yace" Zulynah tadawo yanmata"

Kallon rashin fahimta  tamai dafari kafin daga baya ta zaro idonta waje tace"My menstruation  right"

Gyada mata kai yayi yana jinjina kaifin kwawalwarta cos ya tabbata dawatace dayanxu ta Birkice awajen ganin abinda take mai neh yasashi dowawa daga duniyar tunanin dayashiga.

Itakuwa ganin yanda ta bata mishi jiki da fuska neh yasata warware veil din kanta tana goge mishi jiki wanda alokacin wasu gurare har Sun bushe babu abinda take sai fadin"Am so sorry na  bata maka jiki kayi hakuri"

"It's nothing Zulynah go inside" yafada yana mikewa shima yayi dayan room din....

Share hawayen fuskar ta tayi ta dago daidai tagama goge inda ya baci sannan tayi cikin gida, dakyar tasamu ta hau saman stairs din cikin dukawa cos bata iya mikewa dakyau.

Duk abinda takeyi yana kallonta sosai yaji tausayinta Amma fah shi Sam kazanta neh bayaso fitowa daga daya labulen dayake yayi hanyan waje Don zuwa ganin ko ta goge da kyau...

Zaune take aka gado idonta a lumshe tana dafa daidai mararta da Wani abu acikin socks gefenta Kuma goran ruwa neh dakuma Wani expensive cup , da sallama yashigo cikin daki inda ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta

Amsa sallaman tayi Kaman mai Ciwon baki sannan ta kawar da kanta daga gareshi still bata daina abinda takeyi bah, takowa yafara yi yana sakin murmushi ganin yanda ta Wani ci bom Kaman wata boss.

Daga kafarta yayi ya zauna awajen sannan ya miyarda kafanta kan cinyarshi yana shafawa ahankali , dage kafanta yayi yasake kamowa ya cigaba da abinda yake mata

Kuka tafashe dashi cikin konan rai , tsayawa yayi yana kallon yanda take rufe fuska da pillown data dauka agefenta, sanda tayi mai isarta tukunna tayi shiru jin Kaman yafita domin ya dade da ajiye mata kafanta

Dagowan dazatayi idanunta ya sarke cikin nashi daya zuba mata sai kallonta yakeyi daga zaune dayake

"Kicigaba mana kukanki dadi yakemin" yafada yana Dade matsawa da cute stool dayake zaune daf daita, turo baki tayi tana kawar da fuskanta cikin jin haushin shi, da ace Yay Mou neh yanzu da har saita gaji dajin maganar da baya mai wuyar furtawa wato sannu Zulynah kokuma am sorry, maganar shi taji yace

"Bai kamata ace muna haka tsakani na dake bah amma kuma duk yanda na kauce saikin nemi hanyan dazaki bata min"yafada yana juyowa dakanta, sake kawar dakanta tayi yace" oya kidaina jin haushin let's settle our differences let's bygones be bygones

Turo bakinta tayi hawaye na saukowa daga idonta tadauke su "are we good?"

Yatamabyeta girgiza kai tayi cikin shagwaba tace " are you sorry?" Kai ya gyada mata tasake cewa "then say sorry"

Kallonta yakeyi kafin yasaki Murmushi yace"sorry"

Murmushi tasake mai tamika mai hannu alaman suyi handshake tace" let be friends daga yau babu zagi babu duka babu hantara"

Dage giranshi daya yayi tareda mika mata hannunshi shima yana sakin murmushi,rungumeshi tayi hartana neman fadowa daga kan gado amma gap din dake tsakanin su da baya da Wani tazara sosai yayi preventing dinta, as usual yau ma shock yakeji Kaman wanda aka Jona da transformer, Ajiyar zuciya yasauke shima yarungumeta sun jima ahakan kafin taraba jikinta tana sakin Murmushinta mai kyau tace"daga yau we will be good friends"

"Natambayeki mana?"yafada yana komawa kan gadonta, gyada kai kawai tayi yace"what is friend or who are friends?"

Dariyan karaina min hankali tayi cikin kwarariyan turancinta tace" A person other than a family member, spouse or lover whose company one enjoys and towards whom one feels affection .A boyfriend or girlfriend or An associate  who provides assistance and lastly A person with whom one is vaguely or indirectly acquainted

Kallon dan karamin bakinta kawai yanda take furta kowani kalma cikin basu hakkunnansu,

"Wow friend dina ashe kwakwalwarta na ja"yafada cikin sigar zolaya, dukan kirjinshi tayi cikin wasa da shagwaba tace "banson zolaya fah"

"Wai aina kika koyi turanci haka Kaman wata wanda taje turai?

Dariya tayi tace " sirri neh"

"Amma Kisan ba haka rules din friends yace bah" yafada yana forming face Kaman ya ji haushi, kumatun shi taja Kaman Wani danta tace"sake face din mana abokina"

Juyar dakanshi yayi Alamun dagaske yakeyi, su Zuly uwayen son jiki har da dalle jikinshi tana juyowa dakanshi tace"sorry mana abokina I promise zan fada maka amma I will make it a surprise"

Murmushi yasake yana mamakin yanda akayi takeda mugun son jiki haka cos har wani kankameshi takeyi tana kwantar da kanta kan kirjin shi

"Abokina?"takirashi cikin muryan bacci

"Uhmm" yabata amsa

"Put me to sleep" tafada mai, ahankali yadaga ta yajiyeta akan gadon hade da rufa mata blanket cos shima ya kagu yatafi soboda yanayin data fara jefa shi Kuma gashi a timetable dinsu yau bah ranan making love bane yafara tafiya kenan yaji an riko hannun shi,

Juyawa yayi ya kalleta ta sakar mai murmushi tace"abokina what about good nyt kiss?"

Dukawa yayi daidai kanta yana kallon cute wet kissable lips dinta har zai kai bakinshi kan nata yatina ranan dayagan su ajikin mota Mourad na cin mutunci bakinta, runtsa idanunshi yayi Wani bacin rai na kowawa zuciyar shi ziyara ,

Ganin ya nufota ne yasata lumshe idanunta tana jiran kiss, Jin shuru yayi yawa neh yasata bude idanunta, wani tsoro neh yaziyarce ta lokaci guda, gawani faduwan da gabanta yasoma cikin tashi hankali taso tashi dalilin ganin yanda idanunshi sukayi jawur dasu Kaman wanda aka mawa wani laifi mai girman gaske

Ji kawai tayi ya.....

_longest page ever😰_

#team ZulynMourad
#team ZulynIqbal☑️

*Vote,comment&share*
*ZULFA*

@MHIZZPHYDO 

A Sweet and pitious Romantic love story 

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 61* 

Ji kawai yayi pecking din goshinta tareda ficewa dasauri, murmushi tasake kafin tayi Adduan bacci...

```WASHE GARI...```
Chapter 39 · 0% Book details