← Book details Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 98

Sashe 26

Zulfa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima katse ta yayi da fadin"Bangane bah?? Taya za'ayi kice batasan abinda take fada bah bayan tace ta yarda, wannan ma maganan banza neh nidai nagama magana nan da next month zan masu aure" 

Yana gama fadin hakan yafice daga palourn umma kam daskarewa tayi a wajen cos tasan shikenan aikin gama ya gama...

Rawa tahau yi agaban mirror har towel dinta ya tsince bata bari bah kuma bata dauki towel din bah daga ita sai pant and bra

"I will soon be Mrs Iqbal Alhmdllh"tafada cikin farincikin Jin wannan lamarin 

Wajen wardrobe dinta ta nufa ta dauko wani Lace Trim Silk long Dress dinta 

Wani irin juyi tayi saigata agaban dressing mirror,ajiye kayan tayi ta bude wani expensive _Orlane,creme royale_ ta shafa shi a fuskanta kafin tabi jikin ta da wani cream daban kafin ta shafa powder a face dinta tareda lip gloss

Fuskanta kwance da murmushi ta hau sa kayanta, Princetown Velvet Slipper tadauko tasanya shi

Dankwali tadaura akanta cos bata manta gargadin da Yay mou dinta ya mata bah dukda kuwa baya nan...

Iya damuwa Umma ta shige shi itakam ma bawanda takejin tausayin shi sama da Mourad  cos ita tasan zafin so 

"Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi" tafada asarari shigowan Iqbal neh ya katse ta inda yace mata zai juya in ana sauran kwana 3 za'a daura aure zai dawo

Ba yabo ba fallasa tace "Allah yakaimu"

Ameen yafada yana mai jin wani tsoro tsoro aranshi cos baisan ya zasu kare da Heartbeat dinshi bah...

```Freetown St. 23, WUSE II Abuja Nigeria```

Fitowarta kenan daga kitchen taji tsayuwar motarshi kaman kullum yau ma tsaki taja tareda hayewa sama da sauri

Powder tashafa a fuskarta da Jan baki , abakin kofa sukayi gware sanda shima ya kutso kai cikin dakin

"Ouch Heartbeat zafi" yafada yana mulmula goshin shi, ya mutsa fuska tayi tace "ni yakamata nace da zafi"

Tafada tareda rabewa gefen shi zata wuce cos ya bata haushi , janyota yayi baya tareda rungumeta yace" don't you miss me?"

"I do mana" tafada atakaice

Cikin sanyin murya yace"Am sorry"

Tabe baki tayi tace" kadawo Lafiya"

Murmushi yayi yace"Alhmdllh, miye aka ajiye min neh?"

Jan hannunshi tayi cikin dakin tace"bari na hada maka ruwan wanka cos nasan ka gaji"

Dan murmushi yakara Jin ba amsan abinda ya tambaye ta ta bayar bah,

Shafa keyar shi yayi daidai lokacin da take cire mai takalmi yana Jin wani sabuwar kaunar ta na kara huda kahon zuciyar shi.

Towel ta Mika mishi daidai tagama cire mai kaya ya rage daga shi sai boxer , tura shi toilet tayi tareda nufar wardrobe ta cire mai kayan da zaisa kafin tafice zuwa kitchen...

```Washe gari...```

Cikin sauri tagama shiryawa cos tagama abinda yakawota Christine neh ta tayata daukin purse dinta sukayi wajen da jet yake jiran isowar ta

Cikin farinciki ta shige cikin jet din harda dagawa Christine hannu...

Suna isa cikin Bauchi suka kama hanyan Azare tana Allah Allah su isa cos yau kam ma dakyar taga safiya tayi

Taso tafadawa Yay mou amma sanin bata tabbatar bah yasa tayi shiru gudun karta bashi wrong information...

Suna isa tayi cikin fada dagudu har zata shiga bangaren su sai kawai ta wuce bangaren Malam kasancewan tasan ba yanxu yake fita cikin fada bah

Da sallama ta shiga inda yake zaune akan kilisarshi yana shan miye oho

Gaishe shi tayi ya amsa cikin sakin fuska yace"an dawo kenan?"

"Erh yanxu dawowa ta ko wajen Umma nah ban shiga bah"

Kallonta yayi daga sama zuwa kasa yau dai ba wani matsala cos tana sanyi cikin exclusive blue _The Fling High-Waist Jeans dakuma wani pink Saint Laurent Logo T-Shirt gashin ta cikin blue cute hula_

"Naji kace zaka hadani aure da Iqbal" tafada idonta kur cikin nashi

Kawar da kanshi yayi yana jinjina rashin kunyarta azuciyar shi afili yace

"Ko bakiso neh"

Zaro Ido tayi tace"wane ni ince banso, nidai Allah yasa Alkhairi neh"

"Ameen"yafada yana mamakin ta

"Yaushe neh auren  inason in fadawa mutane na cos su samu daman shiryawa"

Dan murmushi yayi yace"iwar haka next month kin zamo amarya"

"Masha Allah Nagode Allah yakara girma"tana gama fadin haka ta fice da gudu cikin Farinciki

Girgiza kanshi yayi yana jinjina haukar ta...

Umma dake zuba turaren wuta acikin burner ta dago tana kallon  Zuly data shigo da sallama

Amsawa tayi tareda kura mata ido ai bata gama nazarinta bah Zuly tafada mata ajikin tana dariya

"Miye faru??"

"Am so happy Umma nah"tafada 

"Soboda?"

"Za'a min aure da Iqbal next month"tafada bako kunya

Zama umma tayi tace cikin sanyin" Mourad fah??

Murmushin fuskanta neh ya fadada tahau lalubo wayarta acikin purse tace" nasan zaifi kowa farinciki let me tell him the good news"

Kafin umma tayi magana har ya dauka cikin muryan nuna jin dadi tace" Yay mou dina Albishirin ka"

Mourad da kanshi ke kan cinyar Ammi yatashi dakyar cos tin jiya yake jin zuciyan shi nazafi irin sosai dinnan Wanda yarasa miyesa 

Dan murmushi yayi jin muryan Zulynshi wasai yace" miyesa mun Zulynah farinciki yau neh??"

"Yana ji muryan ka haka" tafada cikin nuna damuwa cos haka kawai jikin ta yabata akwai abinda ke damunshi

"Tunanin ki mana"yafada yana sakin dariya 

Itama dariya tayi tace"ai nan da next month dolenka kazo Azare

Zaro Ido yayi kaman yana gabanta yace"haba Zulynah"

"Erh mana"

"Toh Allah yakaimu amma fah sai in banda aiki alokacin"

"Ai ko kana da aiki dole su hakura"

Dariya yasake yi yace"you're not serious"

"OK toh yanxu kana nufin maybe kazo aure na??" Tafada cikin turo baki

"Haba Zulynah taya za'ayi ace bazanzo ranar auren mu bah"

Da dan karfi tace"Yay mou dina aurena....

```Nace anzo wajen fah hmmm```

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
[21/08, 12:02] +234 806 421 6666: *ZULFA*

@MHIZZPHYDO

A Sweet and pitious Romantic love story

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*Page 45*

Da dan karfi tace"Yay mou dina aurena next month nida Iqbal"

Wani irin dum yaji cikin dakewa yace"ke banson shirme fah"

Dariya tayi tace"I know abinda zaka fada kenan Yay mou dina amma wlhy wlhy wlhy rantsuwan Muslim kenan next month iwar haka nazamo amarya agida Iqbal"

Wani irin jiri neh ya shiga dibanshi dukda azaune yake jiyake kaman zai fadi sake wayar yayi akasa tareda rike saitin zuciyar shi

Ammi ganin halin da yake ciki yasa ta shiga tashin hankali"miye faru ta tambaye shi

"Ammi nah kirike ni zan fadi" shine abinda yake maimaita wa yana lalubo ta kaman wani makaho cos gabadaya jinshi da ganin shi daukewa sukayi diff

Rike shi tayi tareda daukar wayar inda taji muryan Zuly nafadin" Yay mou am so happy amma fah nasan kafini farinciki dajin wannan maganan wlhy I can't wait to be Mrs Iqbal..."

Jin abinda take fadi yasa tadago abinda yasamu danta cikin sauri ta katse wayan tareda kashewa gabadaya jikin ta na wani irin rawa sannan tamiyarda da dubanta zuwa gurin mourad

Zaro Ido tayi ganin yanda idon shi yakafe cikin tashin hankali tahau girgiza shi tana kiran sunan shi,

Jin kaman ana kuka a palour yasa Fakhih nufar wajen don ganin abinda yake faruwa ai wani super yayi ya karasa inda Ammi ke jijiga Mourad

Kira ya hau kwalawa masu aikin gidan suma da sauri suka iso ba bata lokaci suka cicibe shi zuwa mota

Ammi kam daga ita sai dankwali ta bisu dagudu, abaya tazauna tadaura kanshi akan kafarta tana kuka sosai...

Jin ankashe wayan yasata kallon fuskar wayan sake dailing tayi taji akashe

"Miye yace" Umma ta tambaye ta

Cikin sanyin murya tace"bansan miye same shi bah naji ya katse wayan tareda kashewa gashi kuma bai gama jin abinda nakeson fada mai bah"

Wani irin tsoro neh ya shige Umma tace "sake kiranshi muji"

Haka tadinga gwadawa amma still kiran wayan Ammi tayi inda yadinga ringing amma ba'a daga bah sosai taji hankalin ta yatashi

Ahankali tace"Allah yasa dai suna lafiya"

"Ameen" Umma ta amsa mata...

```Freetown St. 23, WUSE II Abuja Nigeria```

"What!!!" Tafada da karfi

"Pls Heartbeat listen to me Wlhy nima bason auren nan nake bah ita tace ta yarda da auren kuma Malam yace angama magana next month zai daura mana aure"yafada cikin muryan tausayi

Wata zufa data karyo mata tagoge da bayan hannunta , jin ruwa ruwa afuskarta yasata kai hannunta wajen

Shafowa tayi taga hawaye neh, runtse idonta tayi tareda dafe kanta dake shirin tsagewa gida biyu

Zuciyar ta har wani tsale yakeyi bude idon tayi tana mamakin kanta ita da tasan ba sonshi takeyi bah miye zaisa tashiga wannan yanayin?? Ta tambaye kanta acikin zuciyar ta

Dafa kafadarta dayayi neh yasata dawowa daga duniyar tunanin data shiga ajiyar zuciya tasauke tace"kana sonta koh??"

"Wlhy Heartbeat bantaba jin tsanar wata hallita sama da ita bah arayuwata"(kuji abinda yake fada fah)"

Wani irin dadi taji azuciyarta toh daman miye zaisa taji haushin auren dazai kara?itadai tasan duk bakauyiyan data shigo mata gida tashiga uku, duk illiterate dinda tashigo gidan ta saita gwammaci mutuwar ta tunda da bakin shi yace baya son ta

Wani hawayen tasake shareware tace"Maisona karka yaudareni fah"

Murmushin jindadi yayi yace"inshAllah Heartbeat Allah yabarmu tare"

"Ameen"

"Iya jeki shirya muje shopping sabon mall din da kika fada min jiya"

Cikin farinciki ta tashi tace "ohk, amma kafin nan inason na neme alfarma awajenka"

"Miye??"

"Inason nine zan hada mata lefe"

"Ohk awani country zakije??"

"Country kuma ai anan Abuja ma zan hada basai naje wata uwa duniya bah"

Gyada kanshi yayi yace "kaman nawa zaku bukata?"

"I think 10 million will be okay kaga harda funitures zan siya cos nasan da wuya amata mai kyau"

Sosai taji dadin abinda tace yace "ba damuwa zan baki and kema kinada tukuicin 5million"

Washe baki tayi cikin farinciki zata ci riba  tace"thank you so much Maisona"

Bayanta yabi kallo zuciyar shi wasai cos yazata bazata sauko dawuri bah...

```3 weeks later...```

Kwance take akan kujera rungume da wayarta tayi fayau daita dukda wani fresh din gyaran data kara sosai ta rame cos sai anyi dagaske kafin take cin abinci

Umma ce tashigo da plate a hannu , ahankali ta zauna agefen Zuly tareda dan matsar daita 

"Yar Umma tashi kici abinci "

Girgiza kai tayi dakyar tace" Umma nakoshi "

"Ya zakice min kinkoshi  bayan tinda safe baki ci abinci bah"
Chapter 26 · 0% Book details